NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:31 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAMANIN RAHIM IYYAKA NA, ABBUDU WA IYYAKA NASTA, IN, , , , ,

Muna fita har lokacin a tsaye waje muka samu su Amma mama hadiya hjy maryam da sauran yaran gidan kowa na mamakin ganin mu.
Amma har yanzu kina gun bara na gaida mamu nazo mu gaisa maimakon in nufi part din mamu kai tsaye na hjy maryam dake tsaya muka nufa.
Ganin haka tabar gurin itama ta nufo mu part din nata muka gaisa har lokacin wani irin kallo na mamakine karara a indon ta ban tsaya ba don irin kallon kurullan da take min din a lokacin.
Haka na fito dauke da Sultana murja da Fauziya a ko wani gefena muna tafe muna hira murja tana fadin A ruwa ga baki daya kin sauya kamar ba kece ba kin koma kamar balarabiya dake kunyi masifan kyau daga ku har yayan ku.
Wallahi kamar ba kece kika haifi yaran nan ba naku don kamar har yanzu kike budurwa kike.
Murmushi kawai nake mata muka shiga wurin Mamu mun sameta zaune a falo tana ba dan karamin yaron data haifa a bayana abinci.
Da sarsarfa na isa gurin ta na rungume ta a cikin murnan ganin juna tace kada ki karya mu da wanan nauyin naki haka ?
Na daga ina dariya kafin in zauna kasa wurin kafanta ina fadin mun same ku lafiya mamu na dubu yaron da aka haifa a bayana nace mamu wanan yaron naki duk mun fishi kyau dakin nan.
Ta dan kalleni tana fadin gashi ko gwaggona ko yaushe cewa take yana kama da mijin ki sosai duk shi ya biyo.
Dariya na kwashe dashi ina kokarin aje Sultana data makale min a jiki ina fadin haba mamu wanan ina yakai yaya umar kyau ?
Sultana taki zama Fauziya ta dauketa da karfi tana fadin bari a goyata ko zatayi barci anty.
Yau sai gamu ga mutanen turai har da tsaraban bakin fuska da karuwa aka samu bamu sani ba haka ?
Jin muryan mai magana yasa muka juya muna murmushi hjy maryam ce da imani ya cika ta kara biyoni part din mamu.
Ta shigo har cikin falon mamu ta zauna saman kujera muka kara gaisawa tana fadin gaba daya Fatima ta sauya kamar ba ita ba.
Murmushi mamu tayi mata kawai sai murja ke fadin abinda nake fada mata ke nan nima ai ba zakace ita ta haifi yaran nan ba kamar budurwa har yanzu.
Tace ai abu yayi kyau ai haka ake son aure ka auri namijin da zaka karu yan uwanka su karu shine dadin auren wayayyen namiji.
Shiru mukayi ba wanda ya tanka mata tana ta zuba can ta mike tana fadin bari na leka Umar da inga sauran yaran.
Ta mike ta fita tana bacewa murja tace munafuka gulma ya cita ta rasa yadda zatayi har da shigowa ta zauna.
Na kalli murja ina fadin har yanzu halin nata yana nan ne tace may zata fasa saidai Allah ya gyara tunda sun sawa ransu mugun abu kullun.
Yanzu ji abinda take fadi fa watau kin samu wuri yan uwanki zasuci arzikin da kike ci kema ke nan.
Mamu dai bata tanka muna ba sai cewa tayi a nan ke nan zaku wuni yau nace banyi tsamanin hakaba don yanzun ya gama fadin akai yaran gida sun ki sake jikin su.
Zasu sake ai yanzu basu saba damu bane basu sanmu ba shiyasa basu yarda ita wanan gata sun shige sunyi shiru da uwarta ciki kila tayi barcine ta samu baya.
Su mazajen nawa suna gun uwargidan su ta rikesu ke nan mama ai ta bar maki don cewa tayi kece kakarsu a kawosu wurin ki da zamu fito.
Sai mamu tayi murmushi tana fadin hjy ke nan har yanzu dai abin na nan kiyi kokari ki shaye duk wani abinda zata fada akan ku don darajan mijiki a wurin ki ita din uwace kuma a wurin ki.
Yara kuma ko taki ko taso jini ya riga da ya gauraye da ruwa tun farko sun makara.
Mamu kawu fa yana shagone tunda muka shigo naga part din shi a rufe na tambaye ta tace bai dade da fita ba kuka shigo kila baisan da zuwan ku bane ya fita.
Kin shiga wurin gwaggo ta tambayeni da cewa Amma nace yanzu dai zamu shiga daga gun su hjy muke.
Na mike kenan da zuman zuwa gurin Amma sai gashi yayi sallama ya shigo part din na mamu ta amsa mai a cikin mutunci.
Sai daya kai zaune suka fara gaisawa dashi tana mashi yaya hanya da yara ya amsa da lafiya mun samay ku lafiya yaya Addah ta iso kwanaki.
Ta amsa da lafiya tazo tana godiya sosai Allah ya kara arziki mikewa nayi a daidai lokacin ya dago kai yana fadin ina kuma zaki.
Ban shiga wurin Amma ba na bashi amsa ina kokarin gyara gyalen kaina dake sabulewa a lokacin gashina da ya kwanta lub lub a kaina yana baiyana a fili.
Amma kin san yaran nan sun gaji hutu suke so yanzu don haka kizo mu mayar dasu gida su huta hakana.
Ya idan ban shiga gurin Amma mun gaisa ba kasan ban kyauta ba yara ai nan ma gidane su zauna mana su huta a nan.
No ya fada yana mikewa tsaye yanayin shi yana nuna shima a gajiye yake lokacin ko kuma yana cikin wani yanayi mara dadi a lokacin.
Ki shiga ki fito muna mota muna jiran ki Sultana fa ya tambaya tana gun Fauziya ta goyata tayi barci sai yayi shiru ya rigamu fita part din.
A gurguje na shiga wurin Amma din muka gaisa take tambayana yaya kuma taga ban zauna ba na bata fuska ina fadin yaya ya matsa in fito tafi yaran sun gaji wai.
Shi umarun yace haka yana ina mara kunya wa zaiwa iya shege ne yanzu da rashin kunya shi a ina yayi wayau ba a gidan nan ba ?
Yana mota na bata amsa ina hade rai nan na barta na shiga wurin mama hadiye saiga yara sun zo kirana da gudu wai ance in fito mu tafi.
Raina kara batawa Amma ta mike tsaye tana fadin wanan wanan sadauki akwai iya shege dashi kabar yarinya mu ganeta saboda diyan ka zaka takura ma yar mutane.
Amma na biye dani tana masifa a bayana a gurguje na sallami mamu fauziya ta biyoni da yarinyar a bayanta .
Ina sadaukin yakene tana kokarin gyara daurin zanin jikinta dake banyewa a lokacin.
Ina ja,irin yaron yake ka hana yarinya zama taga iyayyenta don iya shege ko ?
Amma may kuma nayi yayi tambaya cikin natsuwa yana zaune gaban mota ya sakewa yara Ac suna zaune a baya.
Yo ka matsawa yar mutane tafito tafito ku tafi daga zuwanta kamar ba gidan su tazo ba .
Amma dai Amma kinsan matatace dai ko ko wani lokaci ina iya sata ta fito yaran nan sungaji basu huta ba tun shekaran jiya da muka taso dasu.
Kaga ja,iri mara kunyar banza ni kake fadawa matarkace yo ai basai ka fada ba tunda gashi ka nuna muna iko da ita.
Ya dan sake murmushin dole fuskan shi ya nuna gajiya a lokacin yana fadin Amma zancen kike so idan kina son zama da mune sai ki shirya inzo in daukeki mu tare can gidan mu huta tare ko ?
Da sauri nace daga inda nake wallahi daya fi muna sauki yaya mu zauna muna kallonta ko kuda ba zan yarda ya taba min ke ba Amma.
A, a karya kukeyi ja,iran yara ku daukeni ku kaini gidan ku ku wahal dani ina zaune kalau yace min don Allah shiga mu tafi na kalli murja nace murja ku shiga muje keda Fauziya don Allah.
Baice muna komai ba suka bude baya suka shiga har lokacin Fauziya tana dauke da Sultana data banye a bayanta.

Sallamu Alaikum ta fada daga kofa tare da fadin hjyn salma na dakine tana tambaya Nafisa dake zaune da waya a hannun ta tace tana ciki ta kwanta ne.
Ta juya zata koma maryam banyi barcita fada daga kofa kinzo tsegumin ganin abin mamakin da yaran nan sukayi ko ?

Wallahi kamar kin sani hjy wai dama ashe sun haihu ni ban taba jin labari ba a gidan nan yadda kika gansu haka na gansu maryam.
Maryam dani yaron nan yake wasa harni zai rainawa hankali akan yarinyar idan nayi mai magana yace indan bashi lokaci karatu takeyi idan ta kare zai turota.
Da zan ganta sai ganin su nayi da iyalinsu abinda banson akai sai da ya kaimu gare shi ta fada tana hade zuciya.
Hjy yarinya ta koma kamar wata sarauniyar mata a gurin gwajin kyau ai shike nan dama burin Alh ke nan ya kuma cika.
Shigowan salma ke nan gida da goyon yarta wani kallon mamaki tayi masu lokacin da ta samesu tare suka gaisa take tambayan may ke faruwane mama na ganku haka ?
Uhummm salma ke dai bari yayan ku ne suka zo wai ashe har yarinyar nan ta haihu har uku amma ba wanda ya sani.
Wai wani yayana kuke magana hjy maryam dake fada mata tace umar mana da yarinyar nan Fatima kinko ga yadda yarinyar nan ta koma kamar haihuwan larabawa.
Salma ciki murnanta tace lah ashe sun zo don Allah maman ikilima har sun haihu da yaya kike fadi.
Sun haihu wallahi salma sai ma kinga yaran kamar ki sace su don kyau da daukan ido wallahi bazakice yaran kasan nan bane.
Na banza inji hjy jummai ta fada cikin kunan rai dani yaron nan yai wasa sai na nuna mashi ni ba sa,arshi bace .
Don sai na raba wana tsinanen aure na kuma rabashi har ita da yaran mugata tsiya.
A,a mama don Allah don Allah mama ki barshi da matar shi tundai yana son abinshi kinga har da zuria a tsakanin su kuma yanzu.
Mama abu batun yau ba kina nuna adawan kin wanan auren gashi yanzu har ankai ga hayayafa haka yara kunce har uku don Allah dai mamaki barshi da iyalin shi dai.
Ke rufa min baki marasa kinshin zuciya sakarai da bata taba wayau naki na barsu din aiduk ku dinne barayin na tsunta dake dashi.
Salma ta dago kai ta kalli uwar tare da fadin ni gaskiya nake fada maki mama kin dai san rabo yana kashewa yana rayawa kuma.
Da yanzu rabon yaran nan su fito ta tsatson fatima da yaya ya kashe ki fa mama idan kwananki suka kare kana jayaya da Allah ne mama ?
Lalai salma ke sakaraice karan ma ta karshe a daidai lokacin Nafisa ta dawo falon tana fadin anty salma don baki ga yadda fatima ta koma bane wallahi ko ke da kinji wani iri a ranki.
Tace wani iri namay nafisa bayan nasan Allah bai raba daidai ba tun farko kowa rabon shi yake ci ke nafisa wallahi in wanan halin zaki dauki zaki samu matsala a rayuwan ki kuwa.
Nan su ukun suka haye salma da fada da zagi karshe ma bata zauna yinin da tace zatayi ba tayi masu sallama zata tafi.
Har takai kofa uwar tace wallahi naji wana magana ya fita sai na saba maki fiye da tsanmanin ki bata dai ce komai ba tayi dariya tana fadin ni mama ba sune gabana ba yanzu kowa ya iya gidan shi dai ta fice.
Hjy maryam ta dade suna mayar da zance da sarakuwa har da basu labarin irin matsa min da yayi in fito mu koma gida don yara.
Shike nan maryam yanzu kin fara fahintar abinda nake hangowa a cikin auren yaran nan ko ?
Duk da hjy maryam bata fahince taba sai dai tace kwarai kuwa hjy ai na dade da gano manufarki ba yau .
Hjy Jummai tace yadda maimuna ta sakani bakin ciki nata sai yafi nawa don ita ga saki kuma in saka ya karbe yaran muga ta tsiyan cin arziki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button