NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Muna shiga gida yaya ya kwalawa maria kira ta fito da sauri daga part din su tana zuwa yace ta ba yara abinci suci tai masu wanka su kwanta.
A daidai lokacin muka karaso ciki tare da su murja part din shi naga ya shige bai ko waigomu ba.
Nan falo muka zube muna hira da murja sosai inda a wurin ta na ji wasu abubuwan da akayi a bayana wanda take ban labarin su.
Ban lekashi shi kuma bai fito ba saida naga lokacin sallah yayi na mike na shiga wurin inda samu bai daki yana bandaki a lokacin.
Kara budan kofan shi ya dakatar dani daga juyawan da nayi zan bar dakin na juyo ina fadin na dauka baka tashi bane ai kana kwance.
Yanzun kika tuna dani kina can kin samu yan uwanki yau kin manta dani na danyi murmushi ina fadin.
Haba yaya yaya zan manta da kai yau dai kawai ina bata lokacinane da yan uwa saboda farin ciki yau gani a gida duk da ka hanani zama da Amma muyi hira yaushe rabo da juna.
Sai gyara hannun jallabiyan jikin shi yakeyi yana fadin zaki jamin masifan fadan ta akaina da zagi idan ina cewa kiyi abu gabanta kina mun gardama ya fada lokacin da ya dauki tasbahan shi zai fita.
Bayan na fito na samu murja a dakina har tayi alwala nima alwalan na shiga nafito nayi sallah muka dawo falo muka zauna don cin abinci.
Lokacin ne ba nemi Fauziya dake can leke da Sultana tun yarinyar na mata kiuya har ta dan fara sakin jiki da ita don daukanta da takeyi da goya ta.
Murja ta kira mukaci abinci a tare duk yadda tayi yarinyar taci abinci taki ci saima kukan da tasa a karshe na karbe ta daga hannun fauziya din.
Ya shigo ya samu muna leke da Fauziya data bar abincinta ta dawo inda yarinyar take saman jikina sai daya shigo ya karbe ta daga hannu na fauziya ta rabu da yarinyar don bata iya zuwa gurin shi.
Ya dan zauna a falon sai dai bai kulamu ba din ya kula su murja sun sha jinin jikin su dashi tun lokacin daya zauna wurin yana rarashin yar shi.
Mikewa yayi da yarshi a hannu ya nufi dining ganin hakan na mike daga inda nake zaune ina muna cin namu abincin a kasa saman kafet.
Abincin na bude ina tambayan shi abinda zan zuba mai yaci sai da ya lumshe ido kamar baison magana lokacin yace ke may kikaci ?
Tuwo naci don shi nave suyi mun ya lumshe ido yace zubamin irun shi kawai yaran fa suna barci har yanzu na bashi amsa ita wanan ma goyon da ta samu wurin fauziya shine taki kwanciya.
Ya sake lumshe ido tare da mika hannu ya dauki cup din dake aje yana tsiyaya ruwa kadan ya kurba da bisimilllah yasha.
Yaja abincin bayan ya wanke hannu ya fara diba yana kaiwa a bakin shi har lokacin Sultana tana a jikin shi naso in karbe ta ya daga min hannu na barshi da ita.
Daga inda nake zaune wayana yai kara na dauka nasan mamu ce don ita kadai keda sabon layina ina dauka take fadin kin tafi min da yarinya bayan kinsan tana zuwa hadda.
Mamu a barta yau mana mu wuni a tare da ita don Allah gobe sai ta tafi idan Allah ya kaimu kinsan halin karatu nan ba wasa a cikin sa ki dawo min da ita kafin lokaci tafiya karatu yayi.
Murja kinji mamu wai Fauziya ta koma gida barta idan na tashi tare zamu koma anji ai daga inda yaya yake zaune ya miko min murya yana fadin ba tace akaita gida ba ta tashi in sauke ta fita zanyi yanzu idan nagama.
Mikewa nayi na shiga dakina na fito da wani babban jakka nace ki kaiwa mamu ki ce zamuyi waya murja ma na mika mata ledan ta nace kafin kayana ya iso ki fara amfani da wanan.
Fita yayi suka bishi baya har bakin mota na rakasu suka wuce ya sauke su a daidai get din gidan bai shiga ba yace akwai inda zai tafi yana sauri.
Kamar mai jiran tsamani hjy maryam ce zaune da yaranta sun zubawa kofan shigowa get ido suna hira sama babban tabarma idan tana son yin wani gulma haka sukan wuni zaune waje don ganin kwam.
Ganin fauziya tafe da babban jakka tana ja saida murja ta bude get ta shigo ta kama mata sukaja zuwa dakin mamu suka aje.
Daga inda suke zaune suka zuba masu ido saida suka shige da jakkan mai kamar jirgi part din ga tsawo ga nauyi da alama kayane masu yawa a cikin sa.
Wanan abinda ta gani ta tafi ta tseguntawa hjy jummai abinda idon ta ya gani aiko nan hankalin hajiya ya tashi sosai dole ta nemi kannenta tana labarta masu zancen zuwan mu da abinda hjy maryam tazo mata da tsegumin shi da yamma.
Ranan kamar hjy zatayi hauka a gidan hankalinta a tashe yake sai yamma kawu ya dawo daga kauyen dayaje dauri aure yazo ya samu labarin zuwan mu daga bakin yaran shi dake tasowa yan samari.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:31 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMIN RAHIM IHDINAS SURATAL MUSTAKIN, , ,

Mun zo mun gaida kawu da imani da mamaki mu ya cika mai zuciya har ya kasa boye mamakin shi gare mu yana fadin wai kai Umar akidar turawane ka dauka ko ra,ayin kane haka nakin fadan komai wa kowa saida a ganka kwatsam da abu daga sama.
Yata harda ke kin koyi wanan akidar tashi kuma yanzu yana kokarin mayar dake haka da irin halinsa ace har zaki haifi yara har uku amma bamu da labari a nan?
Ayi hakkuri kawu na bashi amsa a cikin ladabi sai ga su hjy sun shigo falon gaida su na fara tayi kamar bataji ba saida kawu tace baki jin suna gaida ke jimmai .
Ta dan juyo tana amsa min ta juya wurin kawu tana fadin dama yaran nan nake son magana dasu a gaban ka na shigo.
Da sauri ya umar ya dago kai yana kallon ta da mamaki yana son sani abinda aka kawo mu kara wurin mahaifin shi a kai .
Ya akai haka daga zuwan ku har kun batawa mahaifiyar ku rai Umar ya akayi haka ya faru kuma ya fada yana mai kallon fuskan dan nasa cikin yanayin nuna damuwa.
Kai yaya Umar ya dukar batare da ya furta komai ba sai da yaji mahaifin nasa ya kara maimaita tambayan shi gareshi ya dago kai yana fadin .
Daddy a iya sanina bansan nayiwa mama komai ba tun zuwa asalima tunda nazo bamuyi wani maganan kota arziki a tsakanin mu ba balle ince ga wanin abinda ya hadamu da ita.
To ke kinji kawu ya fada yana kallon mama tare sa canza yanayin fuskan shi yana fadin jimmai bana son haka ga yaran nan.
Ki bar yaran nan suyi rayuwan su babu tsagwama a ciki haka kwanaki habbib ya kawo min kara ki akan iyalin shi .
Wanan dalilin yasa nayi karan wana yanzu gurin ka don ina son a tambayar min shi ko yanzu ya samu wasu iyayyen da suka fimu ne ban sani ?
Da har wana yarinyar zata tara iyali haka ban sani ba kuma banko ji labari a gurin wani ba sai kawai in gansu kwatsan da yara sunzo muna don may raina ba zai baci ba Alh ?
Kawu yace wanan kina da gaskiya don yanzu haka zancen da mukeyi da su kenan kika shigo falon nan.
Sai abinda nake so dake ya kamata yanzu ki fahinci halin Umar don halaiyanshi sai hakkuri don na fahinci haka Allah ya hallice shi yadda yake shiru shiru hakama komai nasa yake tafiya.
Ni dai ina daga gefe nayi shiru na kama bakina tunda ba wanda ya ambace ni a cikin zancen nasu.
Banga laifin shi ba ai tunda ita wace yake bare baren akanta ta kama uwarta ai shidai ne ake kokarin rabawa yanzu da tashi uwar .
Yaya ya dan murmusa tare da fadin bare bare kuma mama akan me zan dinga wani bare bare har in manta dake ?
Tace gashi kuwa wai har kaine da shiga dakin maimuna ka kasa shiga dakin maryam ka gaida ita don kawai kana auren yarta ko mai ?
A natse ya dago kai yace mama koda na shiga part din ai yanzu ba laifi bane don gaisuwa dai kawai saboda akwai nauyi mai girima a tsakanin mu .
Don yarta tana a matsayin matata kinga dole munzo in shiga in gaida ita.
Ko mama ta manta a gaban kawu take tace da dan bata babawo a gabana kake kiran wanan yarinyar da matarka ?
Jimmai ba matarsa bace ko zaki raba abinda Allah ya hadane gaisuwa a tsakanin su shine abin tashin hankali kuma yanzu?
Kin manta har gobe ina zuwa gidan yayaki gaida shi da sauran yan uwan ki girmana sukayi ko haihuwana da nake zuwa gaidasu da girmana.
Don haka ban son irin maganan nan kin bar yaran nan yadda sukazo a cikin farin ciki su gama su koma lafiya hakana.
Nan mama ta fara fada cikin tashin hankali tana fadin abinda ke cikin ranta a lokacin tana cewa dama abinda aka kulla ke nan don kawai a jaye mata da daga gare ta.
Da kawu yaga tashin hankalin yai yawa ga yaran har sun fara rudewa da masifan mama suna kuka suna make muna a jiki.
Fatima dauki yaran nan ki tafi dasu idan na gama zan shigo in dauke ku mu tafi nan na dauko yaran muka fito daga part din kawu zuwa wurin su mamu don ban shiga ba da muka shigo.
Na shiga muka gaisa har lokacin yaran basu bar kuka ba nima idona da hawaye a rude mama ke tambayana na kasa fada mata komai.
Murjace tace ya wuce hjy ce don naji muryan ta a gurin kawu yanzu da zan shigo da sauri mama tace may kuma kukai mata daga zuwan ku.
Sai an mata wani abu tunda neman nayi takeyi dama a hankali nace wai don may yaya ya shiga gaida mamu da muka shigo bai shiga wurin maman su ikilma ba.
Yau naji kitihi a gidan nan yau kuma har turashi ake ya gaida maryam a gidan nan har ta manta da ita da bakinta tace ba wanda ya haifa mata diyan.
Har ya fito muka tafi ban samu shiga wurin mamu ba ranan sau murja naba sako ta fada mata mun tafi.
Kwana biyu bamu shiga gidan ba gani ina son zuwa mu zauna da ita in mata bayanin kayan dana tura akai mata kafin inzo har zuwa lokacin ban samu bayani da ita ba.
Nafisa da salma suka zo gidan saidai basu samu yayan su a gida ba ya fita tunda safe maria suka samu a falo da yar aikin mu tare da yara suna hira.
Ina kwance a daki saiga maria tazo tana fada min anyi baki suna falo a zaune nace gani fitowa yanzu ki basu abin motsa baki tace na umurci su Asiya su basu ko.
Na mike da kyat don duk jikina banjin dadin shi yai min nauyi haka kawai ranan koda na fito ina jawo kofana sai nayi arba da Nafisa tana bude bude kofofin gidan ga Salma na mata fada a bayanta ta bari haka baida kyau.
Ki shigo gida kina masu bincike sai kace an turo mu muzo mata rashin mutunci sai naji tace wa yar uwar .
Halan gidan tane da sai da izinin ta zamu yi komai gidan dan uwan mu ne fa ba nata ba kuma kin dai san dole in duba abinda tazo dashi tunda taki ba kowa tsaraba sai yan dakin su kawai ta aikowa katon jakka maman su ikilima ta gani take fadawa mama ranan.
Don haka wanan shegiyar sai mun nuna mata gadara da isa akan dan uwan mu zata shiga hankalin ta.
Jin hakan yasa raina ya baci nasan ba zuwan girma da arziki sukai min ba ke nan ina shine bada Nafisa ba da take wanan magana haka .
Don haka ina jin abinda ta fada tana shirin bude kofan dakin yaya nace wanan wani irin rashin tarbiyane haka kuma Nafisa ?
Gaba daya suka juyo don basu san ina tsaye a wurin ba da suke magana nace ya haka zaki shigo min gida kina bincike kamar an turo ki kiyi min hakan ?
Gidan ki fa kikace ta fada tana min wani irin kallo a wullakance nace kwarai kuwa ko gidan ki ne wanan ke na tambaye ta ?
Tace magana barnan baki amma dai kin san gidan dan uwan mu ne na jini daya ko don haka zan iya yin komai fiye dake a gudan nan ma tunda ke auren ki kawai yakeyi .
Nace mijinane tare muke kwana muke tashi tare a shimfida daya muyi komai tare a gidan nan dani dake yanzu wafi kusanci dashi cikin mu.
Au har wani gadara kikeyi dashi na kuna kwana tare kuna tashi tare dashi kwana nawa ya rage maki kuyi tare dashi.
Nafisa kinsan abinda kike fadi kuwa kizo gidanta kina fada mata maganan banza haka kamar wata sa,ar yin ki matar yayan mune fa yanzu.
Kyale ta anty Salma dama abinda tazo yi mun ke nan dadin abindai itama mace ce kamata gidan wani zata tafi ba zata tabbata a gida wurin mama ba.
Sannan da kike fadi kwana nawa ya rage mina gidan nan ko yanzu dai na bar gidan nan na riga da na shamci kowa don ko yanzu aka kashe biri, biri yai barna don tun ba yau ba aka so ya sako ni bai sake ba .
Yanzu ko ko ya saka ban saku ba don mun riga da mun zama daya dani dashi yanzu rai uku ba wasa bane Nafisa koma ki fada wa wanda ya turoki da ya makara wallahi yar zakanya ta girma.
Nafisa tace da mamaki wanan magana ke nan nace mama ba sa,ar yina bace kin sani kedai da kikazo fada min baki da baki dake nake zance yanzu.
Nafisa dama saidana fada maki ki bari yanzu gashi kuna kokarin haddasa tashi wani sabon tashin hankali kuma.
Fatima don Allah ku bar wanan zancen haka kada yai maku nisa yakaiku inda ba a so kuma yakai nace Anty salma ya kai mana dama da gaiya tazo gidan nan don ta fada min abinda taga dama a gamay dani.
Iya kadai ace yaya ya sake ni ko badai raina zai rabani dashi ba ai kuma rabamu akayi da karfi da yaji bada son ranshi ba kinga ashe ba ni kadai zanyi wahalan ba.
Salma tace haba Fatima don Allah ki daina biye mata kuna wanan abin haka bai dace a tsakanin ku ba gaskiya.
Nagode anty salma insha Allahu nagode bazan kara tanka mata ba kuzo mu zauna a falo.
Anty salma idan kin fito ki samay ni gida tace ta fita tana bakaken maganganu na rakata da harara .
Fatima kun zo lafiya ta fada tana kallona sai lokacin na juyo na kalleta da kyau tunda suka shigo ban mata kallon kyau ba.
Anty salma mun samay ku lafiya ya gida yaya yara da maigida na tambayeta cikin nuna mata kulawa.
Ta danyi murmushi tana fadin kun shige England kuyi shiru abin ku haka har kun tara iyali haka masu yawa ?
Nace kai anty salma nice dai ai aka kwara da ban zuwa gida shikan ai ko yaushe kuna ganinsa a kasan nan.
Mun zauna munyi hira sosai da ita take ban labarin tayi karatu baya auren mu sai dai takardan ta baiyi kyau ba mijin ta kuma yace ba zai sake barin taci gaba da karatu ba.
Mun tashi munyi sallah muna cin abinci saiga yaya ya shigo gidan ranshi a bace ganin salma a gidan bai hanashi ya tambayeni ba a cikin fushi.
May ya hadaki da Nafisa kuma don kawai tazo gidan nan zaki mata rashin mutunci har kina mata gori.
Ni din nan dai yaya ita baka tambayeta ko mai ya kawo har nayi mata gorin da tace nayi mata din ba.
Shiru ya danyi na wani lokaci kamar mai nazarin magana na a lokacin kafin ya bude baki cikin natsuwa da kwantar da murya yana fadin.
Na fada maki ki kara da hakkuri ga duk wani abinda za ai maki ki daure ki shanye amma baki dauki magana ta da muhinmanci ba kika biye mata kuka saida hali keda ita.
Har mama ta kirani sai abinda ya bace mata a baki yau shine bata fada min ba a kanki.
Kayi hakkuri yaya don Allah Nafisa bata da gaskiya don a gabana akai komai wallahi don tare muka shigo gidan nan da Nafisa.
Sai kayi hankali dasu yanzu akan matar ka tunda kasan komai basai na fada ma ba.
Amma ba hujja bane ace mun shigo gidan nan da gadara don kawai muna takama gidan dan uwan mu ne nan muce zamuyi abu cikin gaba gadi.
Mumafa matane muna da yan uwan miji bazamu so suzo suyi muna yadda nafisa tazo tayiwa Fatima gaba gadi ba gaskiya.
Salma ita ba zata koyi hakkurin zama da yanayin su ba har lokacin da Allah zai sa wanan abin ya lafa tunda tasan yanzu mama tana da cikin mu a ranta.
Wanan abi yasa nake ta gudun zuwan mu gida tuntuni na dauka zuwa yanzu Zarah tayi wayau sanin irin halin da muke ciki na barazanan mama a kan mu.
Na gaji dajin maganganun shi nace yanzu yaya mai nayi cikin wanan maganan da kake ganin laifina don Allah ?
Yanzu daidaine ace Nafisa ta shigo gidan nan ta dinga shiga wurare har dakin kwanan ka wai tana duban abinda muka zo dashi.
Dakina fa kikace ya fada a fusace nace ga anty salma nan tana mata magana tace wai sai taga komai da muka shigo kasan nan dashi.
Nan anty salma ta kwashe komai daya faru ta fada mai yace shine daidai nafisa ashe bata da hankali haka ban sani ba ?
Jin yana fadin haka na mike na bar su zaune na shige dakina sai da anty salma zata tafi ta aika maria ta kirani na fito nace anty salma zaki wuce ke nan tace eh fatima.
Daga nan gidana zan wuce don yanzu nasan hardani mama tana can hake dani idan naje yau ba zan shata da dadi ba.
Ledan dana fito dashi na mika mata ina fadin anty salma ga wanan kiyi hakkuri dashi kafin kayan mu yazo don Allah a gaida sauran yaran da maigidan ta amsa da ta gode shima ya ciro kudi mai yawa ya bata yana fadin sai mun shigo wurinta.
Bayan tafiyanta na juya na nufi hanyar shiga dakina yace ina zaki baki ban abinci ba ?
Ban dauka kana jin yunwa yanzu bane na fada ina kallon shi yanayin fuskanshi ya sauya.
Yace kina nufin bazan maki fada ba har kike nuna ban isa ba a gaban mutane da wani kike son inji Zahrah da maganganun su mama koda naki yanzu ?
Ni yanzu wani abin kuma na kara yi bayan wanda akace maka nayi kuma ka yarda dashi.
Dole in yarda zahra tunda na fada maki tun farko kema kuma kin sani auren mu da zaman mu ba son shi mama da wasu a cikin gidan mu sukeyi ba.
Gashi har mama yau tana kirana da wai ina bare bare akanki da yan uwan ki na watsar da nawa yan uwan na kama naki.
Don Allah zahra ina kara rokon ki ki kawar da kanki ga duk wani abunda mahaifiyata da yan uwana zasuyi maki ki bari in rabu lafiya dasu kamar yadda ko wani da yake son rabuwa da mahaifiyar shi lafiya.
Ta hanyan ki kadai zan iya samun haka wurin kawar da kanki da toshe kunuwan ki ga duk wani fitina ire iren haka da zasu tayar nan gaba don kawai su samu dalilin fakewa ta hanyar tuzuraki bukatan su ya biya.
Aurena ya samu tangarda wanda bazan taba son hakan ya faru ba tunda kinsan kece dai ba a son zaman ki dani ko ?
Ya kawar da zancen yana fadin ki ban abinci inci banci komai tunda safe na fita gidan nan.
Banyi magana ba sai nufar wurun cin abincin danayi ina dubawa kafin ya tako a hankali zuwa wurin ya zauna har lokacin banyi magana ba.
Ina son mu koma lagos don zama garin nan naga kamar zai iya jawo muna matsala da mama.
Nace in dainice ai ba wani abinda yanzu zatayi wanda ban san manufar yin shi ba don haka ba sai har munkai ga barin garin nan ba ai.
Ko yan uwa bamu zagaya ba yaya zakai maganan komawa wani kasa kuma yanzu duka duka har yaushe muka sauka garin nan ko kwana goma bamu cika ba fa.
Gobe ina sa ran Amma zata bakunce mu gidan nan kuma idan tazo ba zan barta ta koma ba sai ta kwana biyu damu nan gidan .
Aiko wanan zancen yai min dadi sai in hada ita da murja mu zauna kwana biyu nan din in samu ta sake jikin ta da dakyau a gidan nan.
Yadda duk kikayi nadai fada maki gobe zanje in dauko ta in Allah ya kaimu da safe.
Ranan nasa aka gyara dakin da Amma zata zauna aka kara saka komai da zaiyi daidai da rayuwan ta babu takura sai jiranta kawai muke zuwa washe gari.
Sai dai duk abinda nake fadab mu da Nafisa bai fita raina ba ina nazarin maganganun data yaba min a cikin fadan sai da dare na kira mamu ina sheda mata yadda duk mukayi da Nafisan.
Sai cewa mamu tayi dama mai kike nufi ai kadan ke nan ma kika gani indai dangi mijine da kanne miji ake farawa kafin akai ga maya gaba daya.
Saidai idan ka iya hakkuri kana shanyewa sai abin yazo maka da sauki a rayuwa komai yazo ya wuce kamar ba,ayi ba haka rayuwa take.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button