SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:32 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM SIRRATAL, LAZINA AL,ANTA ALAIHIM, , , , , ,
Washegari bayan ya karya ya fita ya ja gida saida ya shiga suka gaisa da kawu suka dan taba hira duniya dashi ya mike yana fadin zai shiga ya gaida su mama.
A falo ya samu mahaifiyar shi tana waya tana ganin shi ya shigo ta katse wayan suka gaisa ya samu wuri ya zauna saman kujera.
Dan shiru ne ya biyo baya kafin hjy tace dada jiya dai matar ka ta nuna min ta isa ta samu wuri a gidan nan har da kora min ya tayi daga gidan.
Dan murmushi yayi kafin yace mama har zarah ta isa ta kori ko dan aikin gidan nan gida balle Nafisa yar uwata.
Gashiko ta kora din an gani ta nuna yanzu suke da kai da komai naka yar uwanka bata da iko da abinka yanzu.
Mama Nafisa dai ita ta kori kanta don na samu salma a gidan ta fada min komai daya faru Nafisa itace bataje da gaskiya ba.
Ya isa ta daga mai hannu tana fadi rai bace na fahinci ka goyi bayan matar ka kaida salma ke nan .
Yanzu basu da ikom zuwa gidan ka suyi abinda ransu ke so saboda ka auro yar gwal ka aje a gidan ko kada ranta ya baci.
Mama ayi hakkuri don Allah da Nafisa da Zarah duk yarane dukkan su ya kamata a tsawata masu jiya nayi mata magana ba zata sake wanan halin ba insha Allahu.
A,a tamayi ai wurin yi ta samu don haka tana da daman da zatayi duk iya shegen da taso a gidan ka.
Dan kasa munafuncin da ka kulla lokacin da nake bugama waya akan ka sako masu ya cewa kake dani kana jiran ta gama karatu da mahaifin ku yace ka sakatane a can idan kunje.
Ashe kasan munafuncin daka kulla da kai da mahaifin ka don kawai ku bakanta min rai babawo har ka yarda ka hada zuria da wanan matsiyatan mutanen.
Tau yau dai zaman ta da kai ya kare ina son ka sallamar mata yarta ta dawo gun uwar ta suci tsiyan su tare.
Mama me tayi da zan sallame ta ya bukaci sanin dalili cikin natsuwa tace tun yanzu tana ganin ta kafu a gidan ka don ta haifa maka wa yan nan yaran masu zubin zabaya yan ruwa biyu take ganin sawun ta ya doke na rakumi a wurin tsayi har zata iya gayawa Nafisa irin maganganun data fadamata kuma wanan sakaran salma na tsaye tana ji bata iya daukan mataki akan komai ba.
Haba mama ai diniya sai ta zageki keda Nafisa ace nazo da matana lafiya kan Nafisa na saketa .
Ni nafison a bari sai idan tayi wani abinda ya shafeni ko ya shafe ki wanda kowa idan yaji yasan muna da hujja mai karfi ba za,a zargeki ba kan hakan.
Amma yanzu idan na saketa kan Nafisa ai mutane ba zasu gamsu da hukincina ba karshe ma in dorawa Nafisa baki jini kan hakan .
Ko mai mutane zasu fada su fada bai damay ni ba ba zan taba yarda maimuna da yarta suci galaba a kaina na muddin ina raye koda hakan na nufin komai nawa zai kare akansu kuwa.
Da sauri yace mama may wanan maganan naki yake nufi hakan mama don Allah akan wanan dan magana kada ki yarda shedan yai galaba a kanki ki kaucewa Allah.
Ya juya wurin da Nafisa take rakube yana fadin ke kuma ki fita harkan Zarah na fada maki ku barmu namu ya hadamu da ita idan ma zan saketa ne a lokacin zan saketa ba wanda zai zargeni akan komai.
Amma yadda kuke nufin inyi abu a cikin rashin tunane haka kowan ku nan sai wanan abinda kuke so in aikata yanzu ya shafa gaba dayan mu.
A yanayin da yake magana cikin bacin ran da basu taba ganin ya nuna ba sai jikin mahaifiyar tasu da Nafisa yai sanyi lokaci daya.
Nafisa ta matsa da sauri lokacin da yake shirin tashi tace yaya kayi hakkuru nima daga baya nasan ban kyauta ba kamar yadda Anty salma ta lurar dani daga baya.
Mama kan dago kai tayi tana fadin anya babawo mutanen nan basu gama da kai ba duk da shawaran daka bayar yana da kyau amma ni sai ina hango kamar sun gama da kaine.
Ina tsoron yadda uwarta tamayar da mahaifin ku idan ba kaima haka ake son mayar da kai din ba ji yanzu yadda ranka ya baci ka rufe ido kana fadawa kanwarka magana akan yarinyar nan.
Mama ni ba wanda ya isa ya gama dani sai Allah dayayini kawai dai raina ya bacine yadda Nafisa taje gidana tana rashin mutunci ko yaya take da zarah ai dai matatace a yanzu ko ?
Don haka ba zan zura ido suna wullakanta min aurena ba duk da irin kyautata masu danake don may ni zasu so su muzantani.
Hjy ta rasa baki magana kanta ya daure don a lokacin bata son wani yasan abinda Nafisa taje tayi min a gida.
Don haka ta rasa yadda zatayi ganun ya tubure mata a karo na farko yana fada a gabanta kan matarshi da ta tsana.
Ya sake kuma ya kafa mata wasu hujjoji yaki ya saka wai saida hujja mai karfi bai kara second ba bayan ya gama magana da Nafisa ya bar falon mahaifiyar tasu.
Mama bata taba tsinkewa da lamarin danta ba sai wanan ranan don gaba daya ya juye mata ya zama kamar na mijin zaki lokaci daya.
Part din Amma ya nufa yana shiga ya samayta zaune tana shafa mai ya zauna ba tare da yayi magana ba bayan sun gaisa tunda tsaye kafin ya kai zaune.
Jin shirun yasa Amma ta dago kai tana fadin lafiya kake ko sadauki ya danja tsuki yana fadin ba komai Amma ke nazo dauka muje gidana yau.
Yau din nan yace eh ina son kije ki dan lekamu kiga yaya muka sauka ai na gani tunda naga iyalin daka tara da idona a duniya.
Yayi murmishi yana fadin ki shirya muje na sa zarah ta shiryawa zuwan ki tun jiya zuwa na dai Amma tace ?
To barin tashi tunda naga da gaske kake daukana din kazo yi yace ba matsala muje dai .
Haka ta fito ba tare da ta dauki komai ba tabi dukkan matan gidan tana fada masu zata leka gidan mu ta ga saukan mu.
Allah ya tsare a fili kowa yai mata saidai na ciki na ciki a zuciyar kowa da yadda yake fassara zuwan nata gidamu din.
Tsab na shirya komai na shiga nayi wanka nabar yan aiki da yara suna karasa abinda ba,a rasa ba.
Shiya shigo dakin a daidai lokacin da nake kokarin saka riga a jikina ya shigo yace sai ki fito gata nan ta iso yanayi shi kawai na kalla nasan baya cikin dadin rai a lokacin .
Juyawa yayi zai fita lokacin nace yaya wani abin ya faru ne kuma yau dan girgiza kai yayi kamar karamin yaro.
Tausayi ya ban lokaci guda na karasa wurin shi ina fadin yaya nasan nayi kuskure kan biyewa Nafisa danayi jiya sai dai lamarin zuciyane da bata da kashi yasa har na biye mata don furucin data furta min lokacin.
Zarah na dauka zuwa yanzu kinyi hankalin da zaki gane matsalan da nike ciki a kanki da mahaifiyata zaki tayani yakar wanan kudirin nata mu zauna lafiya sai dai ashe nayi kuskuren fahintar hakan gare ki zarah.
Hawaye ne suka zubo min a idona lokaci daya nasan banyi daidai ba tun farko ya rokeni da inshaye duk wani abinda suka bijiro min da shi na dauki alkawarin hakan gare shi.
Nasan kin hakkuri da duk abubuwan da akeyi da kuma wanda ake nuna maki a zahiri kina gani saidai ina son ki sani saida hadin kanki zan samu burina ya cika akan kudirina.
Zarah ya kamata yanzu kisan kina da darajan da za,a iya hasada a kanki har yakai mama tana furta min wai nazo ina bare bare a kanki da mahaifiyar ki.
Nasan dole mama tace haka don ke din matatace kuma uwar yayana da nake alfahari dasu yanzu a duniya.
To idan banyi bare baren da mama ke fadin inayi daku iyalina ba akan wa zanyi hakan bayan duk rabin samuna akan yan uwanane da mahaifana.
Koku iyalina din da suke fadin ina bare bare akanku nasan bakuci ko kwatan kwacin abinda nakeyi yan uwana ba daga cikin abinda na mallaka din yanzu.
Don hakane nake son ki natsu ki ban hankali ki wuri daya mu samu mu shawo kan wanan matsalan a cikin ruwan sanyi kamar yadda na shirya a tsarina.
Ya kamata ki san darajan ki da kimar ki yanzu ya zatar wace zata tsaya ana kananan maganganu irin wanan kin sani zarah ban son yawan magana a rayuwata.
Shiyasa nake komai nawa a dunkule sai bayan nayi wanda duk zaiyi magana daga baya ya furta abindake zuciyar shi gamay dani wanan yafi mun sauki a rayuwata.
So ki shirya hajiya tana zaune a falo tana jiran ki da fatan zaki amfani da magana ta nan gaba yana fadin haka yasa kai ya fita ina jin su daidai zan fito Amma na fada dashi wai ina ita yar gwal din naka munafukan banza da wofi har kun manta da lokacin da kuka dagawa mutane hankali a baya kan auren ku damun bi ta naku da yanzu ina zaku kai wanan alhakin yaran naku ?
Amma gani wanka ya samu na shiga yanzu don kada kizo ki sameni hakana ki dauka haka nake zama a gidana ta dan harareni a daidai lokacin da nake karasowa ina kokari rungumar ta.
Shikani karki karasa ni don Allah yadda kika koma din nan kamar ke kadai mijin naki ke kiyo a gidan .
Su maria ne suka fara fitowa da abinci suna mata sannu da zuwa tana amsawa tare da binsu da kallo tana nazarin su.
Maria daki zaku kai mata komai zatafi sake jikin ta a can na kamo hannun ta ina fadin taso muje daki ki huta kagin lokacin sallah ya karasa sai mu zauna asha labati yaushe rabo.
Nanma yayi min ai har wani daki zan shiga in zauna ina dai wuni kawai zan maku in koma anjima to ai kyaso ki dan kishingida dai ko ?
Don na fahinci bai mata bayanin yana son zata dan zauna damu bane na kwana biyu na samu tashiga dakin da aka gyara mata tana sallama tana fadin a, a a ikon Allah.
Ta kai zaune saman kujeran dakin tana bin dakin da kallon mamakin irin tsara shin da akayi da haduwan shi.
Abincin na fara gabatar mata a gabanta bayan na gama ne na tuna ai murja bata zo ba tare da Amma ina tunane a raina yaya akai hakan kuma bayan ga yadda muka shirya dashi kuma.
Don hakane zai kara kwantarwa Amma da hankali saboda shakuwan da sukayi da murja din wanan lokacin da su kadaine a gida tare da ita a gabanta a matsayin jikan da take gani a gaban ta.
Waya na dauka na fita lokacin danaga Amma ta fara cin abanicin layin murja na kira nake fada mata ta daukowa Amma duk wanin abinda tasan zata bukata a kusa da ita tazo mata dashi muna son su kwana muna biyu nan ita da Amma.
Cikin dan lokaci kadan sai ga murja ta hado mata goron ta tasbaha da wasu kaya kala uku don bukatan ta.
Mamaki ya kamata tana fada da murja don may ta hado mata kayanta kamar wace zata kwana a nan tace yaya yace na hado maki na kawo.
Zai dawo ya samay ni nan abinda zai mun ke nan yaje ya daukoni ina dakina zaune kalau ya kawoni nan inda ko rana bana gani balle lokacin ibada.
Sai dariya nake mata ina fadin muma munada bukatan ki a nan ai yaya bai dawo gidaba har dare har ta kwanta bai shigo ba sai dare sosai ya dawo gidan lokacin har tayi barci ya tayar da ita yace taci nama da abin sanyi daya kwaso mata din.
Sun dade daki zaune suna tatauna matsalolin shi wanda yana daga cikin dalilin dauko ta gidan shi da yayi.
Da wanan tunanen Amma ta kwana a ranta ranan mamaki da tunanen duniya ya cika mata zuciya.
Tana tunanen yadda uwa zata matsama farin cikin danta akan iyalin shi ta matsa sai ta daga mashi hankali.
Gasu su ba irin iya shigen da basuyi mata a gidan a gabanta ko bayan ta tana shanyewa don kawai kawar da kai a zauna lafiya suda mijin su take kawar da kanta.
Donme hjy zata kasa tunanen haka ga yayanta ta lura akwai kishin diyan ta a cikin zuciyar ta .
Hjy saidai addua kawai don ta kula da abinda bahaushe kecewa idan uwa ta faye saka matan diyan ta gaba to walau ta ci fitsarin danta ko ta faye saka son diyan ta a zuciyar ta har yakai tana kishin matan diyan nata.
Ta kula da abindake damun ta ke nan a zuciya don ta tuna da yadda aka kwasa da habbib da ita da matar shi har yakai habbib din yayi fushi tun tafiyan shi har lokacin bai kara leko kano ba tun lokacin.
Wanan abin na hajiya da mai ya kama ko Aisha matar Aliyu haka suka kwasa lokacin haihuwan ta sai da akai jidali da ita da yan uwan mahaifan Aishan kamar Auren zai mutu a lokacin gashi kuma yanzu Umar yazo mata da wani zance na matsin da take mai kan lalai sai ya sakeni na koma dakin uwata da zama .
Washegari ina idar da sallah na fito don in duba Amma da yara sai masu aikin da zasu hada abin karyawa kada suyi wanda bai gamshi Amma ba wurin ci.
Na samesu zaune suna hira da murja a dakin hakan yai min dadi sosai don naga murja tasa ta sake jikin ta.
Saida na zauna na fara gaida ita da kwana na juya nagaida murja don ko banza murja ta girmay ni ita da nafisa gurin haihuwa.
Amma ya dare nace bayan mun gama gaisawa da murja na juya wurinta ina tambayan ta.
Yar mijin ki yazo min da wani magana wanda ya tayar min da hankali jiya gyara zama nayi ina fadin wani magana yazo maki dashi kuma ?
Zancen ku da uwar shi yarnan jiya banyi barci daren jiya ina tunanen wanan hali na uwar ku yaya zaki turo yar ki da batai aure cin mutunci gidan dan uwanta don kawai kiyayya ta batawa yarta kurciyarta.
Dadin da nakeji na salma ke nan yanzu da salma ta kama auren ta ta fita zancen duk wani ingiza mai kantu da uwar zatai mata akan auren ta tun lokacin da sukai wanan takai kan satan data turata taiwa mijin ta kara kama kanta da yake tana son zaman auren nata.
Sata kuma amma na tambaya cikin mamaki tace mu bar zancen nan don baki sanshi ba yanzu dai na fahinci dalilin daukoni gidan nan da mijin ki yayi.
Fahinci wani abu daga cikin magana nan ki mijin ki yana bukatan kulawan a ciki wanan lokacin yana bukatan wanda zai zauna ya dan fahintar daku wasu abinda ku ba zaku iya ganowa ba a cikin zancen nan.
Abinda nake so dake da farko natsuwa mu fahinci inda zamu fara dosowa wanan zancen don ba karamin fitina daga ke har shi kuke ciki ba.
Shiru nayi lokacin da amma ke min bayanin kaina ya kulle sosai ga abunda take fada min wanda da farko ban dauke shi wani matsala ba a wurina.