NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:32 – ????????????: Salma ta wuce ta barni cike da tunane haka naja kafa na koma falon na samu murja zaune tana kallon film a falon.
Ta juyo tana fadin ta tafi na amsa a wani yanayi ina zama nace ta wuce taci gaba da kallon ta sai kuma can ta juyo tana fadin .
Yanzu salma rayuwan ta ya sake gaba daya kamar ba salma ba wallahi ta hadu da mijin daya natsa mata daukan kai da izzan nan nata gaba daya.
Gashi tana mutuwan son Ahmed a rayuwan ta da bata son shi da tuni maman su tayi sanadin da ta kashe auren su wallahi.
Murja inda Allah ya tsara ma rayuwan ka idan kana da tunane sai kayi hakkuri da hukucin ubangiji ai.
Dashi Allah yayi zata zauna tace ai gara salma ma in fada maki don ita ikilima raguwace ta karshe ga aukin haihuwa kamar wata akuya.
Haba murja dudu yaran su nawa yanzu ki duba fa diya uku suka haifa fa kike fadin haka .
Nima ba gashi diyan nawa uku bane yanzu tace aike Allah ne yai maki kyauta da kari kowa ya sani kedai murja a fada a hankali kada duk shekara ki taramu gidan dan batta suna da cewan wanda zata aura.
Tace wa ni baki daiji ba da kyau fatima, waneni da rayuwa irin nasu sun mayar da kansu wani iri kowa na fada dasu kan kama jiki kamar ana kara zugasu ne suyi.
Yanzu wa zaice wai salma ta hada takarda don Allah ko karatun saida kawu da mijin ki sukai tsaye suka mayar da hankali ga karatu.
Karatun ko baka aiki yana da amfani sosai na bata amsa ba wai da niya suka bar kansu haka ba murja akwai rashin waddata yana damuwan rayuwan su.
Don kinga yanzu da zasu fara aiki ko wani sana,a mai karfi suna dan fita ko kuma kudi yana shigo masu zaki ga sun dan walwale cikin dan kankanin lokaci.
Tace amma ai kawu yana kokari dasu sosai wallahi ke dai kawai akwai battalanci a cikin harkan su.
Tun farko fa kin san komai basa iya yi da kansu yanzu sai abin ya zama masu sabo a wurin su ga lalurar yara da dawaiyarsu duk ya taru a kansu lokaci daya yai masu yawa.
Na amsa da fadin kinga ke nan dole a taimaka masu ashe tunda Allah ya hore masu yan uwa masu shi da zasu iya tallafa masu din.
Fatima yanzu ke da kanki kike wanan magana har kin mata da irin muzancin da salma da mahaifiyar ta suka dinga maki don kawai kawu ya dauko rikon ki ya kawo gidan har ya aura ki ga dan dakin su.
Murja dane wanan yanzu salma yar uwan maigidane kuma yar uwatace nima ta jini idan ba don lalacewan zumuci ba ai ni jinin su ce dama.
Ki dai bi a sannu kada kiyi zurfi da yawa don su din ba abin yarda bane da sauri.
Nace Allah yasan dalilin sakani a cikin su murja don haka da zuciya daya zan zauna da kowani su.
Kusan wanan hiran muka wuni munayi a ranan sai wani lokaci ka dan fito haraban gidan muna shan iska.
Yara kuma suna wasannin su a inda aka tanada don su suyi wasa karan budan get din gidan da akayi ya mayar da hankalin mu wurin mai shigowa gidan lokacin.
Bamu gane mai shi ba saida motan ya tsaya mukaga mata suna fitowa daga cikin motan data shigo gidan lokacin.
Gaba daya mun mayar da hankalin mu gurin su da farko ban gane su ba sai daga baya na gane ashe.
Hjyn su yayace tare da yan uwanta suka shigo gidan wallahu galibun ala amrihi na fada lokaci daya don nasan da wuya wanan zuwan idan na lafiyane haka.
Tun kan su karaso kusa damu na mike tsaye hakan yasa murja mikewa muna masu sannu da zuwa sai shan kamshi ko wacen su keyi su duka ukun.
Murja data gaida ita karshe tace a,a yar gidan hadiya kema kina nan ne ashe tace hjy nazone dazun tace kwarai naga alama ai don yanzu kowa inda yafi maski ake dafewa a lakaci arziki.
Dayan yar uwar tace yo indai za,a lakata a barka da danka aida sauki amma ina dadin a rabaka da uban dan a kumayi kokarin rabaka da dan ka don samun wuri.
Dan kallon juna mukayi a fakaice nida murja lokacin da dayan ke fadin abindai ma a filin Allah akeyin sa don kawai kwadayi da samun wuri irin na wasu matan .
Yaya zaki aure uba kiba yarki kuma dan kishiya don samun wuri na sake fadin sannu ku mama ina dan dukawa.
Tace yau fatima nice uwarki ko may ko dan mawa ya tilasta maki da ki kirani da mama ban sani ba.
Kamar ban fahinci irin maganan da suke sake min ba a lokacin sai dan murmushi nake a fuska ina nuna masu ban damu ba da abinda sukeyi sai ma na juya wurin maria dake can nesa damu da yara ina fadi cikin harshen turanci kawo su su tari grandma din su maria.
Kowa kallon yadda nake turanci zakace ko wata haihuwar America ceni lokacin.
Maria ta riko hannun yaran tana fadin oya come great her samun wuri ita wanan din wacece hjy Rakiya ta tambaya.
Aidai kin gani da idon ki idan ma ji kikeyi da yanzu ganau kike rainon ma harda maiyin shi akazo tundaga can don samun arzikin banza.
Gaba na fara yi na tura kofan falon daketa kamshi yasha gyara kamar ba mutane ke zama a cikin shi ba duk da yawan mu gidan.
Suma shigowa sukayi suka suna bin gidan da kallon yadda yasha gyara ga haduwa wai ni yaya zancen dayar matar gidan ne anty kanwar ta tambayi hjy.
Yo ina zan san inda yasa gaban sa yanzu an fitar mashi da raiga kowa yanzu ai saidai a tambayi sabbin iyayyen shi kuma.
A daidai lokacin na fito kitchen dauke da katon tire a hannuna dake shake da abin sha dana motsa baki nake jin suna wanan zancen.
Kallon kayan da na aje a gaban su sukayi tanaci gaba da maganan ta tana fadin ya barta can ke nan yazo nan da yar gwal dinsa ganin gida.
Ta sake kallon kayan tana fadin ba wanan ya kawo mu ba mu zuwa mukayi mu duba gidan nan muga inda yar mu zata zauna itama kafin lokaci.
Dan murmushi nayi tare da fadin ko zaku dan zaga kuga gidan da kyau har ta baya ga hanya can da zai iya sadaku da ko ina ai.
Wanan yar a kwaiki da shiga hanci da yawa barta kawai karyan su da kadarin su ya kusa karewa a gidan nan ai .
Amma mama sai ina ganin wanan ba girman ku bane da kimar ku zuwa gidan dan ku kuna sake irin wanan magana haka duk da ita fatiman naga bawai zancen ya shigeta bane.
Murja ni kike kokarin fadawa magana komay a,a hjy gani dai nayi hakan bai dace da girman ku ba gaskiya aida sai ku bari idan yaya yana gari sai kuzo ku duba ya nuna maku nata bangaren don mu bai nuna muna ba kafin ya wuce.
Murja na fada a cikin wani irin murya na bacin rai ta juyo tana kallona nace ban son rashin kunya ki barsu suyi abinda ya kawo su tunda sunce ba gurin mu sukazo ba .
Gidan dan tane tana da ikon yin duk wani abinda take so a gidan nan idan ma yau tace bata kaunar ganina gidan nan ya zaunu don haka ki kyale bakin ki don Allah.
Eh lailai anty yanzu na kara tabbatar da komai da idona yar nan kafanta ya tsaya a kasa har take iya fadan magana a gaban idon mu haka.
Abu kamar a mafalki haka nake kallonsu suna fadin magana babu girma ko sanin ya kamata a cikin zancen.
Kamar kananan yara dasu saida zasu tafi hjy rakiya ta dawo wurin tire din dana aje masu abinsha tana fadin ba,a barin mugu da makami akace.
Ke kuma murja uwarki hadiya tayi min kadan balle ke idan aure yana da dadi taje tayi aure mana ai bata wuce aure ba yanzu.
Ina zatayi tana nan zaune tana aikin saka ido da gulma tana batawa kanta lokaci a gida sai hana masuyi su zauna lafiya take kokarin yi.
Da ace zan bi ta murja ranan da mun masu rashin kunya saidai ni na sani dama bakina suka zo ji don i masu rashin kunya a kafe a nan.
Allah ya taimakeni yanzu ba da bane kuma na riga da nayi mai alkawarin ba zan taba mayar da martani ba again koda dukana hjy tayi kuwa.
Suna fita murja ke fadin girma dai ya fadi wallahi wai banbarakwai uwa a gidan danta take sake wanan maganan dako mu yara ba zamuyi shi ba.
Ki koma gida ki fadawa uwar ki dana baifi karfina yadda ake tunane ba don aure zan mashi da yar uwar haihuwan shi kwanan nan.
Gidan nan ba na yar agola bace da zata cika min gidan da da haihuwan yuyuyun diya masu zuben ruwa biyu.
Tsit nayi har suka fita don ni abin sai ya koma ban mamaki a waje ma sai nake jin yayan su kamar basu tafi ba.
Fatima wai yaushe kika koma hakane don Allah wanan ba abin kyalewa bane hjy fa ta wuce sanin ki yanzu sai kin zare kema.
Duk maganan da takeyi ban samu bakin bata amsa ba sai ajiyan zuciya da nakeyi a zaune.
Ashe aure yakan canza mutun haka ban sani ba yau nice ake fadawa maganan daya dace in bada amsa amma na share don darajan aure kawai ban bada amsa ba.
Ina zaune zuciyata takai matuka wajen baci sai tunane nakeyi mainayi wa hjy haka har take nuna min wanan hali haka a fili.
Ban san lokacin da hawaye suka fara bin fuskana ba a lokacin kuka na somayi sosai a lokacin.
Ganin haka yasa murja mikewa ta bargidan ba tare dana sani ba sai maria ce tazo tana ban hakkuri.
Zuwan murja gidane ya harzuka Amma sosai ashe ban sani ba murja tayi video komai daya faru a gidan takai ta nuna ma Amma.
Amma bata zauna ba tasa aka kira mata su kawu dukkan su su uku tace murja ta nuna masu video din.
Amma dai anyi hasarariya a nan hjy ko wai tana cikin hankalin ta kuwa ki wanke kafa zuwa gidan matar yar ki da yan uwanki kuyi irin wanan hauka haka ?
Kawuna dai yana zaune ya rasa abinda zai fada ranan don idan yace zaiyi magana lokacin ba furci mai dadi zai fada ba.
Kyale kowa yayi bai tanka ba har suka gama fadan su yana zaune kurum.baiyi magana ba a wurin.
Kwana hudu yaya yayi a can bayan hjyn su ta kirashi ta fada mai cewa sunje gidan nayi masu rashin mutunci ni da murja sai abinda na manta a bakina ranan.
Hakkuri ya bata sai ya dawo zai dauki mataki kan maganan don bata san da cikin gida sun san da zancen ba.
Kafin ya dawo ya turo motoci guda hudu masu kyau gida kafin yazo tare da Aliyu suka dawo wanan karon
Ranan da ya dawo naga alaman bacin rai sosai a tare dashi baiyi min magana ba ni kuma ban nuna mashi na gane yanayi ba.
Ban yarda na nuna mashi komai ba duk da na zargi zancen ne hjy kila ta juya mai shi yake ma fushi hakan bai hanani shiga wurin shi ba da dare.
Kamar yadda shima bai fasa kulani ba don yana fushi dani saida babu sakewa har lokacin a fuskan shi.
Da safe muna karya gaba dayan mu har yara da Aliyu wayan shi yai kara ya dauka jin ya ambaci sunan kawu yana gaida shi yasa na dan dago kai ina kallon shi.
Dan shiru yayi yana sauraren kawu din sai naji yace gamu nan zuwa insha Allahu yanzu daddy.
Yana aje wayan yace daddy ke neman mu a gida dukkan mu yanzu zamu tafi na tambaye shi.
Yanzu yace muje ya bani amsa yana cigaba da cin abincin shi nina fara tashi na koma daki na kara kimtsawa na fito na samu ni suke jira muka dauki yaran zuwa wurin mota.
Haka kawai naji gabana na faduwa shike magana da Aliyu jefi jefi naji Aliyu yace ashe madam din namu dai zaman turai ya karbe ta sosai haka wanan tsaleliyar motar haka sai matan manya ai dama.
Ya juyo ya dan kalleni na danyi murmushi don yadda shi yakan jani da wasa ni har yanzu ban faye sake jiki in mayar mashi da amsa irin na wasan kannin miji ba.
Mun shiga gidan tun daga nisa na hango takalma a kofan dakin daddy wanda hakan yasa na gane akwai mutane a falon nashi lokacin.
Muma falon muka nufa direct a lokacin ina shiga yadda na gansu zaune jugun jugun yasa gaba kara faduwa.
Gaidasu mukayi muka samu wuri muka zauna dukkan mu kawune ya bude taro da addua aka shafa ya mika hannu gefen shi ya dauko wayan shi.
Dan tabe tabe yayi a wayan ya fara mikawa hjy dake zaune ta hakince don bai fadawa kowa dalilin kiran nasa ba lokacin.
Tana gama gani tace to shine may dama ai nasan zakuji komai tunda gaban yar leken asirin ku akayi koda ita fatima bata fadi ba ba karya na fadi ba abinda nace aure zan masa wanan ba fashi tunda kayi mai nasa ikon nima yanzu zan masa nawa tunda tare muka haife shi ai.
Yace kwarai dankine ba wai ba jimmai ya juyo gareni yace Fatima ga uwarki nan ki tashi ki bita dakin ta ke kuma ga danki nan da yaran sa ki dauki abinki na raba wanan gardaman da jidalin yau kowa ya rike nasa.
Da farko nayi wanan hadin ne na dauka zaki fahinci manufana kan hakan tunda har yau Allah baisa kin gane ba a zauna lafiya Allah ya bada zama lafiya ga wace zaki aura mai .
Saidai kema ki shirya barin nawa gidan a ranan ko kafin ranan don kafar wace zaki aura mai fitar kafarki a gidan nan ke nan.
Ciki kaduwa yaya yace daddy kana nufin raba aurena da fatima zakayi kan laifin da bamu mukayi shi ba.
Murmushi kawu yayi yace Umar wanan abin yayi yawa kowa yayi hakkuri ya dauki danshi fitina ya kare hakana.
A daidai lokacin na mike don barin falon don ba zan iya kara wasu mintina a gurin ba kuma .
Ina fita a daidai lokacin da yake fadin mama menayi maki baki son farin cikina a duniyan nan ?
Nazo da merry nayi ba daidai ba kun nuna min kuskurena ta hanyan aura min yar uwata tunda na auri fatima ni kaina nasan Allah ya kubuto dani daga halaka.
Fatima bata taba wuce inda na ajeta ba tana min biyayya yadda ya dace mama shin shine baki kauna gani a gare mu ?
Tace kai babawo ka shiga hankalin ka ka natsu kasan may kakeyi don ya rabaka da wanan gaiyan tsiyar bawai haka na nufin mata sun kare ba a duniya mamaka Ramatu ta baka yar gurin ta data dade tana jiran ka yanzu haka amincewan ka kawai muke jira don mahaifin ta yace saida amincewan ka za ,ayi.
Amincewana mama tace kwarai yafi mun kwanciyan hankali don nasan yar yar uwatace kecin gashin kanta ba yar wasu ba.
Mama ban amince ba kamar yadda nasha fada maki Fatima da merry sun isheni a rayuwata ba kuma zan taba amincewa da bukatan ku ba ko may zakuyi min kan hakan .
Ya juya wurin mahaifin shi yace daddy kaika hadani da fatima yanzu kuma kake kokarin rabamu ba zanyi wani korafi ba a nan don kai kasan dalilin yanke muna wanan hukuncin nida ita saidai ina son fada maka bazan taba sakin fatima ba sai dai muyi ta zama a hakan dani da ita.
Kai sadauki a gaban iyayyen ka ke don haka idan rai ya baci hankali ke nemo shi ka bari mubi maganan nan a sannu.
Yace nagode Amma daga fadin haka ya mike tare da kallon Aliyu yana fadin taimaka min mu dauki yaran nan don Allah.
Hjy tace ina kuma zaka dasu can tunda uwarsu ta koma wurin uwarta da zama ?
Yace gidana ni zai raini abina da hannuna don ni Allah yaba hakkin kula dasu bayan uwarsu tace cikin tsawa kai babawo ni kake fadawa magana haka kan wanan yar banzan yarinyar don sun karbe abinsu shine me yafi nono fari a gurina.
Mama duk wani biyayya ina maki shi a duniya saidai wanan karon ba zan yarda da kudirin ki ba akan iyalina me fatima tayi maki matsalanki da daddy ne da mahaifiyar ta banga abinda Fatima tayi maki na son ki rabani da ita ba da karfi da yaji.
Ya fice falon yana jan yaran shi kowa na falon yai shiru yana binshi da kallo sai can Amma ta nisa tace yau saiki zuba ruwa kasa kisha jummai Allah ya cika maki guri ki kan yaran nan.
Biyan bokaye da malamai sai ya kare ki bar kurwan su ya zauna lafiya Allah ya baki da dake maki biyayya kishi da gajin hakkuri yasa kin kasa hango hakan.
Daga kofan mamu ya tsaya ya kira wayana naki dagawa sai gashi ya fado falon ina kwance saman dogon kujeran falon yace.
Ke fatima ina son ki kwantar da hankalin ki kada haka yasa ki daga hankalin ki wanan yana daga cikin abinda yasa ban son zuwan mu kasan nan.
Nayi murmushi lokacin da nake juyowa gare shi ina fadin nace kawu yayi gaskiya yaya don yanzu ya fahinci ban dace da kai ba don nasaban mu ba daya bane.
Dama shi ya daukeni yabaka ni kuma yace yanzu ya fasa kyautar dani gareka dani dakai yanzu sai muyi hakkuri do maganan iyayyen mu shine gaba da namu.
Ina maman twices take idan ta shigo kice nace ina rokon ta da ku rike min sultana don yanzu itace kawai matsalana don bata yarda da kowa sai ke sauran maria tana nan kafin ki dawo.
Dariya ma ya bani dana kalleshi idanuwan shi sun kade sunyi ja nace kaima kasan wanan ba zai taba yuyuwa ba jinikace sultana don haka jinin mamace sai ka kaiwa mama ita ta rike kada ka kara shafawa mamu wani laifi a gidan nan kuma.
Ya juya fita bansan ya akayi ba don ni tun ina tunane cikin bacin rai har barci ya daukeni sai dana tashi naga sultana goye a bayan fauziya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button