SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:34 – ????????????: Falon yayi tsit bayan fitan shi kowa na wurin kamar ruwa yaci shi lokacin sai Amma ta fara fadin wanan abin dame yayi kama don Allah.
Kina yar musulma diyan hausawa kike kokarin bata auren ahalin ki ko taysayin wa yan nan yara bazaki gani ba jummai.
Duk wani biyayya da ya kamata diya suyiwa mahaifan su Allah ya hore makishi yaran nan suna iya kokarin su akai.
Ba a hakkuri da lamarin diya ke aka zauna dake da halin ki har wanan lokaci yanzu bukatan ki ya biya an raba auren sai ki zuba rowa kasa kisha.
Hajiya ainayi kokari da bansa ya sake taba fin karfin da aka nuna min a gidan yasa nake son gwadawa kowa nina haifi abina ba wani ya haifa mun su ba.
Kwata kwata ni yarinyarce tun farko banso da watace aka bashi kila zan iya hakkuri kamar yadda na hakkura da auren habbib da Aliyu.
A,a ko su baki hakkura ba baki da dai yadda zakiyine dasu don su ba irin halin sadauki ke garesu ba yasa bakici galaban su ba.
A daidai lokacin mamu ta mike ta kalli kawu tace shike nan zan iya tafiya yace shike nan aina gama magana ta.
Allah ya sauwaka tace ta fita suka amsa mata da Amin suna barin falon a daidai lokacin ne ta hadu da murja dauke da sultana dake wani iri kukan tashin hankali irin na yaran da suka rikice.
Kamar bata gansu ba zata wuce dukda kukan yarinyar har kasan zuciyata take jin shi a lokacin.
Mama yaya yace in rike ta har Amma ta fito gashi kuma tana kuka bata yarda dani kaita gurin hjyn shi tana ciki ta bata amsa tana wucewa kamar bata san inda sultana ta fito ba.
Tana shiga falon da yarinyar dake ta wani irin kuka gaba dayan su take tambaya nan murja ke mayar masu yadda yarinyar tazo hannun ta da abinda mamu tace mata a kofa.
Aikin banza ke nan bani ita nan da batayi kuka ba lokacin data fito aida bata kai haka ba yanzu tana mikewa zata karbe ta .
Kada ki karbi yarinyar nan Amma ta daka mata wani irin tsawa taci gaba da fadin ya ganki yace aban ita idan na fito yasan kina gidan ai.
Ba a dai raba anta da jini duk inda akaje aka dawo dole ace jikanane ita mama hadiye tace ashe kin san da hakan ke nan yanzu ?
Fita tayi daga falon ba tare da ta tsaya bada amsa ba don tasan halin mama hadiye wurin masifa yanzu zasu rikice akasa rabasu.
Mamu ta samay ni a dakinta kwance tace min a nan kika kwanta lokacin barci ya fara daukana nace eh nan ma yayi min ai.
Naci gaba da barcina mai kama dana tashin hankali bata kara kulani ba sai dana tashi naga Fauziya goye da sultana dataji kukan yai yawa kowa na lalashi taki shiru ta karbeta ta goya sai barci.
Lokacin dana tashi mamu bata falon nake tambayan Fauziya meyasa ta daukota a cikin wani yanayi irin na mamaki ta kalleni.
Nace maida ita inda kika daukota yanzun nan lokacin mamu ta fito tana fadin barta harta tashi ta maida ita kukan nan zai iya ja mata wani ciwo kuma.
Jin haka yasa na kyale ta da yarinyar a bayan ta kewayawa nayi ban dakin su Fauziya na fito na kara kwanciya a falon a daidai lokacin murja ta shigo falin mamu din.
Zama tayi fuskanta ya sauya ta kalleni tana fadin da nasan hukuncin da kawu zai dauka ke nan daban gwadawa Amma abinda ya faruba wallahi.
Na dauka idan sun gani tsawatawa hjy kawai za ayi da gidan ki sai gashi kuma matakin da aka dauka yayi muni sosai.
Murmushi nayi nace murja koda baki nuna wanan ba ai tunda tace bata sona da danta babu inda zamu hakan da kawu yayi Allah yasa shine mafi alheri garemu baki daya.
Ranan dai haka muka kwana kowa ransa abace yake gidan idan ka debe hjy da bansan abinda ke ranta ba a lokacin sai kuma hjy maryam dake sintiri part din ta dana mama a ranan.
Sultana ta hana su barci da kyat suga asuba kukanta ya karde gidan gaba daya da asuban farko masifan Amma ne ya tayar da mutanen gidan ga baki daya.
Wanan wani irin daukan alhakine haka ku raba yara da uwarsu da karfi da yaji wanan ke nan da muka kwana da ita a nan ina ga su wayancan tagwayen dabamu san yadda suka kwana ba tayi masifa sosai kafin ta fito zuwa part din mamu tana dukan kofan da karfi saida mamu ta taso daga inda take zaune tana lazimi ta bude kofan.
Ina yar nan take ta tambaya a hasale tana ciki mamu ta bata amsa ta wuce fuuu zuwa dakin sai mamu tace tana dakina a nan ta kwana.
Ina kwance bayan na sallame sallah na kara kwanciya ina jiran ayi asuba ta shigo da sultana tana fadin karbeta nace wanan daukan alhakin yayi yawa wallahi.
Amma dai Amma kinji abinda kawu yace kan yaran nan ki kaita wurin hjyshi kawai don Allah bana son kawu yaga na saba mai Amma.
Ba kawu ba kawulle nace tana min dakuwa ta kara fadi a hasale ba kawu ba nace maka wuya.
Dariya ne ya kubce min nace Amma kawun nawa kike zagan min tunda asuban farko haka an zageshi ko zaki rama mai ne nace wace ni hajjaju Ammalle na rama a fakaice.
Tare da mika hannu na karbi yarinyar a hannun ta da sauri sultana dake ta miko min hannu tazo wurina tana sauke ajiyan zuciya har lokacin bata bar kukan da takeyi ba din.
Kada naji ko in gani kin kaiwa wanan mara imanin yar nan a gidan nan dani take zance wallahi.
Ta fita tana fitina a tsakar gida ita kadai ba wanda ya lekota har taci ta sude ita kadai.
Baya nayi sallah nayi wa sultana wanka nima nayi banzo da wasu kaya ba dole na saka dogon rigar mamu a jikina lokacin.
Na koma muka kwanta zuciya ba dadi nasan yadda akai fama da sultana ko su Abdul haka zaiyi fama dasu a gidan duk da ga maria gashi suna ganinshi amma nasan sai sun taba rikici sosai a gidan.
Da tausayin mu a raina ina muna addu,a sosai don Allah kadai yasan halin da kowan mu ke ciki a ranan har mahaifan mu.
Har kawu dayai sanadin auren dashi nasan ranan baiyi barci da dadin raiba shima a nasa bangaren .
Kamar yadda kawu ke bin dakuna yauma haka ya shigo part din mamu da dan sandan shi dake karamai karfi yana dogarawa .
A falo ya samemu zaune muna karyawa muka shiga gaida shi da kwana ya samu wuri ya zauna yana fadin.
Fatima ina son ki saka hakkuri a ranki nasan mun cuta ma rayuwan ki mun bata maki lokacin kurciyan ki banyi hakan da niyar cutawa a gareki ba ko kadan.
A hankali na dago kai na dan kalli inda kawuna yake zaune yana magana nace a a ha kawu wallahi ni baka cuce ni ba don uba bai taba cutar da yarsa ai.
Yace na gode da wanan fahintar da kikai min Fatima hakan da nayi yanzu shine mafita gareku damu duk a barta ta aura mai wadda take so.
Abinda nake so dake ki kara kwantar da hankalin ki ki natsu kina dai da takardan ki ga hannu zan duba inga abinda ya dace ayi nan gaba kan aikin ki.
Na gode kawu nace a fili a ciki zuciyata kuwa sai wani irin harba min takeyi ina fadin yanzu shike nan an rabani da aurena ina ji ina gani ko may ?
Muryan mamu ya dawo dani ga dan tunanen dana fara tana fadin yanzu yaya yaran nan ba,asa makomarsu ba tunda, , , , ,
Hannu kawu ya daga mata ya hana ta karasa fadin abinda take son fadi a lokacin mikewa yayi yana fadin hajiya ta sameni kan zancen yar nan ita mace ce kuma karama zaku iya riketa a nan don kada a jawo mata wani matsala kuma.
Daga haka ya fita nasan part din mu shine karshen shigan shi a zagayen da yake yi don haka muna gamawa na mike na dauki sultana zuwa part din Amma don in gaida ita.
Hjy maryam ce na hadu da ita ta fito part din kawu muka gaisa da ita ta dan make murya tana fadi sai hakkuri fatima iyayye suna gaba da komai ba komai hjy nace mata tare da mata godiya na wuce abina inda zani tabini da kallon munafunci.
Na samu Amma a zaune falon su kamar yadda na zata ta tasa abin karyawan ta a gaba tana kallo .
Jin sallamana yasa ta dago kai tana kakaro murmushin dole a fuskanta tana fadin yanzu muka gama waya da mijin ki yace zasu yi tafiya shida yaran yau.
Gabana ne ya fadi sosai dan jin abinda Amma tace min yanzu ina kuma zasu tafi na tambaya a dan mamaki.
Bai fada min ba yadai kirani yana tambayana kwanan ku nace kuna lafiya yace min sai idan yazo zamu magana dashi.
Fitowan murja daga dakin su yasa na kalleta nace dama ina son in turaki ki dauko min kaya don ko yanzu na mamu na saka a jikina kina gani.
Ta kai zaune tana fadin wa ni ai in kin gani kasuwan maza gulma ya kaini yanzu ban ko son hanya ya hadamu da yaya don sai inyi zaton zaiga nice duk na jawo mai wanan abin.
Haba dai yaya zaiyi zaton hakan gare ki tunda yasan baki da laifi shi ba haka yake ba ai kawai dai baki gama fahintar shi bane.
Muna tsaka da hirane muke dan jiyo hayaniya a tsakar gidan sama sama shiru mukayi muna sauraren hayaniyar meye kuma akeyi.
Muryan hjy ce ke masifa da alama wani ya tabata a lokacin inda take shiga ba nan take fita ba.
Wai ashe yayane ya turo Aliyu ya kawo kayan abinci part din mamu shine hjy taji ta fito tana masifa hakana .
Saida fauziya ta shigo muke ji a bakin ta wai tana masifa da Aliyu bai kula ba sai kai kayan abincin tare da abin sha da suka jibgo mota dashi yake shiga dasu part din mamu abinshi.
Zata ko mutu da bakin cikin akan dan yau, idan tace bakin kishin matan diyan cikinta ta saka a ranta haka wanan abinda mai yai kama kiri kiri ta hana yaran nan zuwa garin nan saboda tashin hankali ana zaune a kasa daya amma ya dauke kafan shi da gidan nan.
Nace wanene Amma ta kalloni hasale tana fadin habibu ma da yarinyar nan Rakiya matar sa su ai sun fita iya iskanci indai fulanin dajine suna daidai da uwarta ai.
Jin hayaniyar yayi yawa yasa murja da Fauziya har mama hadiye fita da sauri sai Amma dake kokarin mikewa irin na tsofi ta rage a falon tana kiciniyar tashi tsaye.
Daga inda nake zaune naji muryan yaya kamar diran mikiya a kunnuwa na yana fadin don may ba zan kawoma matana kayan abinci ba tana matsayin matana har yanzu ?
Mama banso mukai haka dake ba a gidan nan na fada maki ba zan yarda ki rabani da matata ba don banga abinda ya shigo da fatima cikin tsabgan ku ba da kukeyi.
Ba zan yarda darajan aurena ya tabu ba a garin nan matana da yarana nike da hakkin ciyar dasu a kaina.
Don haka ba zan yarda wani ya ciyar min da mata ba alhalin ina dashi zamanta a nan wanan ra,ayin kune keda daddy wanan ni bai shafeni ba all what i know aurena yana bisa kanta.
Da hjy tana da kunya ranan data jishi a gidan nan don yadda yaran sukai mata a gaban kowa ta rasa abinda zata fada.
Sai Ammane ta amsa mai da fadin wanan kayi gaskiya tunda har yanzu a matsayin matarka take wurin ka.
Ya juya yana tambaya ina ina ne ?
Da sauri murja tace tana wurin Amma.
Ya nufo part din Amma din rai a bace a kwance ya same ni sultana tana saman ruwan cikina tana ramuwan barcin da batayi ba daren jiya.
Tsaye yayi yana kallon mu kafin yace ramuwar barci wanan keyi ko don Amma tace jiya bata barsu sunyi barci ba da dare .
Na amsa mashi da kai.
Ya dan kai zaune gefena yana fadin ke naga kamar zaman gidan yayi maki dadi sosai a ranki.
Nace to yaya zanyi wai yaya idan ban zauna ba so kake in binka in butulcewa iyayyen mu ko may ?
Dama su suka bakani na fada maka yanzu kuma sunce in dawo gida in zauna ai dole ne in dawo yace good may kuke bukata yanzu don yau zan bar garin nan ni.
Ina kuma zaka na tambaye shi saida ya dan furzo da iska a bakin shi yace lagos zan koma in na kwana biyu Abuja may zan zauna inyi garin nan kuma yanzu tunda sun kwace min ke ?
Nayi murmushi nace yaran fa da maria yace dasu zan tafi duka yau zamu bi jirgin karfe biyu zuwa Abuja motar ki yana nan kofan gida saidai ban son yawan yawo ki natsu wuri guda don Allah zarah kafin komai ya lafa.
Idan ka tafi auren naka fa sai bukin ya tashi zaka dawo ke nan wani kallo yayi min yace kina tsoron auren da ake fadin zanyi ne ?
A,a ha kan me zanji tsoro tunda ba a kaina zata zauna ba in tazo hanyar jirgi daban na mota daban kaima ka sani.
Mikewa yayi tsaye a lokacin Amma ta shigo dakin nace zancen tafiya na gida fa in duba su ?
Wani kallo ya jefa min yana fadin haba zarah muna ciki wanan halin kike wani zancen tafiya gida yanzu ?
To may nakeyi a nan din ai gara inje gidan mu asan ina da gida agolaci ba zama shegiya bace yafi yace good kina da gaskiya cikin bacin rai.
Wurin Amma ya juya yana fadin Amma zan tafi ba lalai bane in dawo ta nan kafin in tafi yana mika mata kudi tace wai ina zakane yace gani nan dai Amma.
Tunda yace hakan na gane baison kowa yasan inda ya dosa a lokacin naja bakina nayi shiru ya sake cewa ga amanan su nan na bari a hannun ki Amma don Allah a kula da su ban son yawo ta sani ita.
Babu ma inda zata insha Allahu harka dawo tace nace da sauri a,a Amma kada kice mai hakan idan fita ya kamani fa ?
Wani kallo yai min a daidai lokacin ya duka ya shafi kan sultana yana kiran sunan ta yarinyat dake cikin nauyi barci tayi firgigit ta bude ido kuka tasa tana mika mashi hannu ya dauke ta.
Dan dagata yayi sama ya sunbance ta sai kuma ya rungumay ta a jikin shi yana sauke ajiyan zuciya a hankali.
Abincin ta yana nan nasa an kawo mata don Allah zarah ki ba yarinyar nan kulawan daya dace sosai kallon shi nayi ina mamaki komai da yake kai kasan a cikin karfin hali yake yin shi.
Kudi ya ciro ya aje min gefena yace ki rike wanan idan na samu lokaci zan turo maki ki kara rikewa a gurin ki.
Yana fadin haka ya mike tare da kallon Amma yana fadin to Amma zanyi niya Aliyu zai kawo yaran nan suyi sallama da maman su kafin mu wuce.
Da sauri na furta masu ka barsu karsuzo su damay ni nan daga shi har Amma wani irin kallo sukai min lokaci yace don may kikace hakan nace haka kawai a cikin daure fuskana.
Barsu kawai sadauki Allah ya saukeku lafiya ka kula da kanku ka kuma kwatar da hankalin ka komai yayi tsanani maganin shi Allah ne.
Hakane Amma yace yana sauke ajiyan zuciya ya juya ya tafi ba tare daya kara min magana ba ko kallon inda muke.
Wani iri naji a raina saidai hakan shine saukina duk da nasan ban kyauta ba hanashi kawo min yaran danayi muyi sallama.
Bayan na idar da sallah ina zaune wurin da nayi sallah a falon Amma nake tunane duk inda suke yanzu suna shirin dawa su bar gari ke nan.
Biyu daidai na kalli agogon falon na sauke ajiyan zuciya a hankali na kai kwance a kasa ina lumshe idanuwana.
Muryan Amma ke fadin ni na taba ganin wanan bala,in haka kace kai baka kaunan kowa a rayuwan ka a dole sai ka mayar da kowa bawa a gurinka.
Ban dai yi magana ba ina jin ta tana maganganun ta na share abinda ya damu zuciyana a lokacin ya dameni.
Ban kira shiba shima ranan bai kirani ba sai washegari sai ga kiran shi a wayana na dauka lokacin muna zaune tare da mamu a falon ta.
Dauka nayi da sallama sai ya hauni da fada zahra may kike nufi da hakan da kikeyi ne wai ?
May kuma nayi yaya na tambaye shi kamar ban gane mai yake nufi ba ga maganar shi.
Yaci gaba da fadin kina ganin don sun daukeki daga gidana hakan na nufin sai ki shareni aiko ba don niba zaki kira kiji lafiyan yaran ki ko ?
Saida na dan saci satan kallon gefen mamu naga ta kura min ido don ta gama tambayana na kirasu naji saukan su nace na kira ban samay shi ba nayi mata karya da hakan don nasan zata iya min fada kan hakan.
Nace nakira bai shiga bane yaya sai naji ya kashe wayan shi na bata rai ina aje wayan a gefena cikin bacin ran kashe min waya da yayi.
Ya kamata ki tausayawa halin da bawan Allah nan yake ciki don dake dashi duk ba yin kan ku bane yana zaman zaman shi aka ja mashi magana.
Shi kanshi yaya yasan halin matar shi dalilin da tun farko naki wanan hadin naku ke nan amma sai ba a duba min ba.
Yanzu ga abinda ake soncin mawa kara lalacewa yayi bai yuyu ba don haka banga abinda zaisa kiga laifin bawan Allah nan ba duk yadda akeyi yayi muna halarci a rayuwa don ba haka mahaifiyar shi taso da shiba kowa ya sani shi dalilin yin wanan haukan haka da takeyi.
Su basu gane irin kiyayyan da hjy ke min da duk wani nawa cikin gidan nan don haka duk wani hanyar da zataga ta kuntata min shi take nema ta gasa min kwakwa a hannu na.
Ta manta Allah ne mai yin komai bawai ra,ayin ka ba yanzun da mun dage akan ba za,yi auren ki dashi ba ina rabon yaran nan zai kai mu.
Sai Allah ya dauke dayan mu ayi ba dashi ba shi yasa wani lokaci jayaya da hukuncin Allah baida kyau mutum ya rugumi kadara duk dayazo mashi maikyau ko mara kyau ya barwa Allah hukuncin sa nayin hakan.
Har yau sam ban taba badaman auren ki da umar ba don yadda duk ake halarci bawan Allah nan yayi muna shi a rayuwa .
Yadda yake aikowa uwarshi kudi duk wata haka nima yakan turo min da kudi ta account dina duk wata kuma yace kada in fadi don Allah.
Nasan halin umar tun muna kanana ba mutum bane mai son magana haka Allah yayi rayuwan shi shi tun farko.
Mamu ni bawai naga laifin shi bane kawai dai ina kaucewa bacin ran kawune don kada yaga yana kokarin min gata ni ina kokarin watsa mai kasa a idanu ga idon jama,a.
Zaisan kuyi waya dashi ne ko kuma koda ace rabuwa kukayi ai yanzu kun zama daya don ruwa ya dade da gaurayewa da jini ko.
Mamu zan kula insha Allah ni bawai ina ganin laifisa bane ni mai yayi min da zanga laifin shi may ye yaya bai mun ba na ingata rayuwa na da zan manta da hakan.
Zuwa yamma na fara jin ba dadi a jikina haka yasa nasha magani na kwanta ranan ban fito ba ga fitinan sultana da takeyi min ga ciwo sannan kuma zuciyana ba dadi lokacin.
Washe gari ne na tashi da zazzabi sosai don tun cikin dare nake dan jin jikina sama sama har yakai na fara amai sosai .
Ganin haka yasa mamu zuwa fadawa kawu banda lafiya yace subbahanallahi may ke damun ta ga mijin ta ina ganin kamar baya gari tun shekaran jiya rabona dana ganshi gidan nan.
Ko uwar shi naji tana tambaya wai munyi waya dashi bai shigo ba harshi har Aliyu tun ranan .
Mamu tace ina ganin kamar baya garin nan fa yaran fa suna ina su kawu ya tambaya cikin dagowa yana kallon ta.
Duk dai inda yake yana tare dasu ai tunda kaji baiyi magana ba bai kuma kawo su nan gidan ba.
Yanzu barin baki kudi kuje asibiti taga likita asan abinda yake damun ta yafi tace dama kabar kudin don tace akwai kudi a wurun ta yayi saurin fadin a, a karba dai ki kaita don nauyina ne yanzu kula da ita.
Ina kwance na rufe har kai sai naji muryan mamu tana fadin ki tashi murja ta rakaki asibiti ko maman ki hadiya.
Don ni ba zan kaiki ba kada kuma yazama wani abin magana a gidan nan yanzu suna ganin mun fita tare za a dauko wani zance a dora muna kuma.
Ina fadin ba sai naje ba zan iya treating din kaina ai tace a, a ku dai je asibiti zaifi a auna ki asan abinda ke damun ki muryan mama hadiye ne a falon mamu tana fadin ina take nai yar gidan gwaggo.
Mamu ta amsa mata tana fadin gamu nan dakina ai ta shigo tana fadin fatima ba lafiya haka kuma ?
Nayi karfin halin tashi zaune ina fadin mama jikin nawa ne banjin dadin shi yau.
Tashi muje asibiti tace min dole na mike ba wani complain na shirya muka fita da motan ta muka fita tare da murja hjy maryam ce ta ganmu take fadin uwa da yarta sai ina kuma haka da safe asibiti ta bata amsa nayi karfin halin gaida ita da kwana ta amsa min tana bina da kallon kurulla.
Munje anyi min dan gwaje gwaje result ya nuna ciki ne dani dan sati biyar ma,ana dai a nan gida na samu cikin ke nan zuwan mu.
Nike fadin abinda ya dace aban saura nace su bari zan rubuta in sayo idan na koma gida.
Maganine kawai ba aimin allura ba muka tsaya muka saye a hanya muka dawo gida a lokacin har hjy maryam taje part din hjy sarakuwana ta fesa mata fitan mu da mama hadiye.
Sukace karya muke ba asibiti zamu ba wurun biye biyen bokayen mu zamu tafi tunda yanzu bamu ga zama ba ai sai abinda ya turewa buzu nadi kan dan ta.
Allah sarki sha daya da wani abu muka dawo gida itace dai still taga dawowan mu na tsaya ina amai a waje daidai shigowa get din gida.
Wani sabon gulma ta kara gundawa a cikin ta lokacin bata samu zuwa ta fesawa sarakuwana ba don kawu ya kirata part din shi.
Saida nasha magani na kwanta koda Amma tazo har na samu barci yadan daukeni lokacin din haka bansan shigowan ta ba.
Ta dawo shiyanta cikin ikon Allah sai gashi ya kira Amma bayan sun gaisa tayi mai yaya hanya yake tambayan ta ko muna lafiya yakira bai samu wayana ba.
Tace yanzu daga wurin ta nake sun dawo asibiti bata da lafiya naje na samu barci ya dauketa ko .
Cikin wani irin murya yace da sauri subbahanallahi Amma may ke damuwan ta kuma har asibiti tace wallahi jiya uwar tace daren jiya basuyi barci da dadi ba.
Amma idan ta tashi akai mata wayan ki ko ta kunna nata wayan ya fada tare da yi mata sallama ya dan shiga tashin hankali don shi yana tunanen ko damuwane na saka a raina yaja min ciwo.
Don maganin dana sha na samu yin barci sosai a lokacin ban falka ba sai uku na rana na danji dadin jikin nawa lokacin saidai nauyin da yaimin ke damuna irin na wanda ya kwanta ciwo.
Lokaci daya na danyi fayau dani bayan na sallame sallah ne mamu ta shigo da kofin shayi yana tururi ta aje a gabana tana fadin ki daure ki sha wanan ko hanjin ki zai dan warware maki ki samu kici wani abu mai nauyi anjima.
Mamu ba kunu insha shi nake son sha yanzu kawai tace akwai da kamu sai a dama maki yanzu.
Barshi idan babu nace mata ina kokarin kaiwa kwance kasa a wurin da nayi sallah.
Tace sanyin kasan ba zai maki yawa ba idan kin kwanta a nan nace sanyi sanyin kuma nake so bata ban amsa ta juya ta fita daga dakin .
Ba a dauki wani dogon lokaciba sai ga kunun an dama min shina samu na dan kurba sama sama na aje cup din sai ga Amma ta shigo dakin tana fadin sannu yarnan .
Jikin ya kiya haka kuma ina dai ba danuwa kika saka a ranki haka ba Aruwa babu mai rabaki da mijin ki kinji muddin ina raye.
Shima ja,irin tun dana fada mai baki da lafiya ya hani zaman lafiya a gidan na ya bugo waya yafi a kirga yau yace ki kuna waya ko ki karbi wanan.
Kawun ki ya dawo nayi mai magana ya mayar dake dakin ki in ba so yake sadauki ya tare muna a gidan nan ba .
Maganan mamu ya katse Amma mama ta koma ina kuma ai gara dai kowa ya rike nasa kuma zaifi saukin wanan fitina na hjy.
Maimuna ki fita min a idona tun ranki bai baci ba jin abinda mamu tace yasa na gane nufin ta nace cikin karfin hali Amma bazan koma gidan yaya ba idan kuma kin matsa in koma gidan mu bauchi da zama.
Shike nan ku kasheni ku huta zaifi min saukin wanan bakin cikin da kuke sakani a gidan nan kan auren yaran nan.
Karan wayan tane ya hanani magana ta miko min wayan na dauka da sallama zahrah me yake damun kine haka Amma ta fada min har asibiti kuke yau.
Muna fara magana sai mamu ta mike ta bar dakin zuwa falo kusan tare suka fita ita da Amma a lokaci daya daga dakin.
Banjin dadin jikina na bashi amsa a sanyaye ya yace asibiti may sukace nace sun dai dubani sun ban magani.
Ko kinsa damuwa a ranki ne haka zahra da sauri nace damuwa akan may kuma yaya kawai dai ciwone sukace dani na bashi amsa.
Kina amai ne nace nayi daga dare zuwa safiya har lokacin da muka dawo gida sai lokacin na samu barci.
Kinci abinci nace na dai sha koko yanzun dana tashi komai naci baya zama a cikina sai kokon dana sha yanzu banyi amai ba.
Yace zahra na amsa anya ba ciki kika samu ba kuwa da sauri nace ni banda ciki dawa kukaje asibitin nace murja da mama hadiye.
Ok ina maman twices nace yanzu ta fita falo ita da Amma bata wayan zan yi magana da ita.
Da kyat na iya mikewa na kaiwa mamu waya ta karba na dawo dakin na kwanta lamo banji yadda sukayi da mamu ba.