NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:34 – ????????????: Ina zaune a inda nake ina tunane naji muryan mamu tana fadin kina son tayar da hankali kan auren da mijin ki zai kara ko ?
Na dago kai nace mamu auren shi bai damay ni ba sai dai nasan auren gaiyya ake son mashi a kaina.
Don murja ta gano ko wace yarinyar ce ashe diyar hjy sabuwace da sukai zama lagos ance idanun yarinyar a bude yake sosai zata girmi anty salma na a wurin haihuwa sosai.
Sayadi ba zaman lagos ba ko zaman turai tayi karewan bude ido mai zai dameki indai kin rike gaskiyar ki da amanan mijin ki a ranki kina kuma aiki da hankalin ki aiko tsakiyan faransa ta tashi karewan bude ido zata barki ne.
A yadda Murja ke fada min taji wai ashe zancen nasu ya dade sosai yarinyar taki da farko da hjy taso ayi hadin sai yanzune suka aminta da ayi suna bin hjy sauda kafa har ta yarda.
Mumu tace kamar nasan da zancen nan a baya saidai aikin mantuwa kawai ashe zancen nasu yana nan har yanzu ai da farko na dauka diyar Rakiya ce ko Ramatu dan suma suna son auren shi naji wurin hjy maryam.
Ashe yar wurin hjy sabuwa ce kuma yanzu idan wanan ce aiki barsu kawai zai fita a tsakanin su don bata da hakkuri ko kadan kowa yasani.
Ba mutunci ne da wanan matar ba su kansu suna tsoron masifan ta shine kuma yana zaune zaman zaman shi zasu dauko yarta su bashi kai hjy bata lissafi kafi ta aikata abu wallahi.
Mamu ai duk saboda nine nake gani zasuyi wanan hadin .
Tace a wurin hjyn gidan nan ba amma su wurin su aiba hakana bane mijin ki kamilin mutum ne da yasan kansa ga zati da kyau da cikkaken ilimi uwa uba arziki wanda ko wace mace yanzu take gurin samun mijin irin shi.
Haka ya tashi da farin jinin mata tun muna yara duk da koda yaushe fuskanshi shi a daure yake bai hana mata suce suna son shi ba harda wa yanda suka girmay shi lokacin.
Shiya banyi mamaki ba lokacin da yazo gidan nan da matarsa merry don nasan irin nacin da mata ke gwada mai ta gwada mashi har ya yarda da ita.
Ni dai abinda nakewa gudu da tsoro shine asiri tun dawowan hjy sabuwa garin nan da zama gaba daya hjy ta fada harkan bokaye da malamai inma da tanayi dai a boye take abinta amma yanzu a filin Allah take lamarin ta.
Saidai ni abinta bai faye damuna ba tunda ina bin dare ina fadawa Allah matsalolina ya kuma amsa min na gani.
Mamu nidai idan abin zai zama fitina gara in tsira da rayuwana kowa ya kama gaban sa .
Da sauri tace kina ko da hankali sayadi mai yasa kikaji manya na fadi anyi hakkuri da yanayin aure mai dadi ko mara dadi duk a kan yarane fa.
Kan yaro sai ke mace ki danne komai naki kiyu hakkuri ki barwa Allah al,amarin sa komai da zai faru da bawa Allah yasani.
Don yara wasu mata ke zaune gidan mazajen su suna cin boni gun kishiya da miji don sun kwamace da wata ta ba yaron su tarbiyan banza garasu suba abinsu mafi ingancin tarbiya tun zamaninda da ake da sauran imani balle yanzu da imani yai karanci ga zukatan mutane.
Idan kinyi hakkuri komai yazo mai wucene a gurin Allah sai a koma kamar ba,ayi ba daga baya.
Mamu amma aini nayi karanta da shanye irin wanan abinda kike lissafo min na fada ina kallon fuskanta.
Tace kaiyya sayadi hakkuri ga yaro da babba aka san shi balle ban sa a raina cewa don mijiki ya auri yar wurin hjy sabuwa zai juya maki baya yadda kike tsamanin zaiyi ba duk dako itama yar uwasa ce kuma iyayyen su zasu tsaya sosai a kan auren na sani.
Kedai ki kwantar da hankalin ki Allah ya saukeki lafiya ayi a zauna lafiya ba shike nan ballema shida baida ra,ayin aje mata a guri daya irin namun nan may zai damu mutum .
Ba zama wuri daya ke sakawa mata kyashi da hassadan junan su ba haka abu yakici yaki karewa ko yaushe.
Ranan mun dade da mahaifiyata muna hiran abu daya saida likacin sallah yayi muka tashi mukai sallah da cin abinci na shiga wurin Amma.
Washe gari na tashi da niyar zuwa gidan Anty salma da tazo tana min korafin naki zuwa wurin ta dama ina da niyar zuwa wanan matsalan yazo muna na dawo gida.
Sai ranan nayi waya da drivern gidan yaya akan ya kawo min motana zan fita dashi kwalliya sosai muka sha dagani har sultana fauziya da murja.
Rigan dake jikina basai an fadawa mutum an kashe naira a gurin sayen shi ba dayai wani tafiya Dubai ya sawo min shi ga sultana da ta kwaso farin mu kamar yar turawa kwaliyan dan riga pink da wando dogo har ribon da ta kalman kafatan adon pink ne da fari a jikin ta.
Daidai mun fito ke nan daga wurin Amma da muka shiga sallama aka turo get din cikin gida za,a shigo.
Ban damu da kula matan da nagani suna shigowa gidan ba a lokacin don hankalina yana ga wayan da nake da Aisha muna dariya ina tafiya salo salo kamar da kamar da gangan nakeyi banko san inayi ba.
Wani irin kallon kishi da tsana suke aika min daga inda suke suna kallon yanayin shiga na a cikin rudewa.
A hankali tacewa uwar wanan kuma a gidan nan take ne tana magana kasa kasa kamar rada ga uwar.
Wata kila bakuwa sukayi wanan motar da muka gani waje muna magana kai amma dai wanan ta hadu wallahi.
Taji ina ace haka ta samu haduwa koda rabin nawa ne aida tasan dole mijin da take muradi ya so ta.
Ga mace kamar balaraba sak da ganin ta yar wani ne ko matar wani a kasan nan irin yaran nan ne da suka taso a cikin hutu kinga fatarta wani irin luf luf dashi kamar wace bata shiga rana dan cikin jikina daya turo ta kalla tace ciki dai yanawa wasu mata kyau wallahi.
Ita kadai take zancen ta a zuciyan ta sai taji duk irin kwalliyan data fito dashi suna yauki daga ita har uwarta duk sun muzanta a gurin.
Ganin sun danzo kusa damu yasa na dan barwayan ina fadin sannun ku da zuwa ina wunin ku.
Mun saba da gaisuwa irin na tura da zaka hadu da mutum baka san shi ba ku gaisa.
Tana mamakin jin muryana daya dan girgizata sosai bamu kara kulasu ba mama hadiye ne ta fito tana fadin Fatima ku biya gidan saratu don Allah ku gaisheta na amsa da to mama da cewa gidan kanwar mama hadiye din.
Bari na dan riko abin da zamu kai mata nace ina sake hannun sultana zuwa part din mu da sauri.
Ba yar ba har uwan saids gaban ta ya fadi uwar tace kardai nace wanan ce matar yaron nan dama ?
Da wanan mamakin suka shiga wurin hjy da sukazo dubawa don tun maganan su Nafisa ta kwanta ciyo.
Shine suka zo dubata don yanzu zumuncin su ya taso sosai a tsakanin su idan ba a hadu ba ana makale da waya.
Hjy dake zaune tana ta dago tana dan murmushi tana masu sannu da zuwa.
Suka amsa da um kedai hjy muna shigowa muka hade da wata mace data dauke muna hankali yanzu gidan nan.
Hjy tace a gidan nan kuka ganta Nafisa dake gefen ta zaune tunda tayi masu sannu da zuwa ta kawar da kai gare su tace Fatima ne fa suke fadi yanzu da zan shigo na gansu zasu fita ita da murja.
Na,ima tace na shiga uku itace fatiman matar Umar dama anya kuwa kuwa Umar zai soni yana da wanan matar haka ?
Da sauri hjy jummai tace inkiji soma ai daya ke nan ai sai yayi maki so da kaunar da bai taba yiwa wata mace irin shi ba indai ina raye.
Mu zuba dani dasu zaki sha mamaki ke dai kawai mu samu yanzu mu shawo kanshi a samu ayi wana abin gida bai koshi balle in barwa daji ganima .
Iya gudun shi nake kallon nan gaba bausan sanda zai kawo kafan shiba gidan nan da kansa yana rokon gafaran mu.
Hjy sabuwa tayi dariya tace tun yaushe wasa yake damu ai don dai kawai ma ya zama namu ana daga masa kafa.
Mikewa Nafisa tayi ta bar falon zuwa daki waya ta dauko tana tsegun tawa salma zancen da sukeyi a falo tana jan tsuki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button