SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Muna fita gidan muka shiga mota nida murjane a gaba fauziya da yarta suna baya zaune suna dan hiran yara.
Wai fatima kin san wa yan nan da suka shigo gida yanzu nace wasu mutane ke nan don ni har na manta dasu a raina.
Tace wa yanda kika gaiyar mana da zamu fito nace OK matan nan ai ina ga wurin hjyn su yaya suka zo ko ?
Itace fa Na,iman da ake fadi yaya zai aura din ta fada tana kallona wanan din da suka shigo yanzu fa murja na tambaya ina kallon ta.
Ita face da uwarta ina fada maki kaina girgiza ina runtse idona duk da ban masu kallon kyauba amma na danyi tunanen kamanin su.
Ban taba zaton zanji abinda naji a raina ba lokacin da sauri nace innalillahi ina kallon hanya.
Suma bakiga irin kallon kurullan da suke maki bane da suka shigo ba lokacin kila suma sun gane ki ne suke kallon ki.
Suka sani na bata amsa ina kallon ta tare da fadin sai fa kin mun kwatance don ban iya kai kaina gidan yanzu gaskiya.
Tana mun kwatance muka isa gidan tun a waje na gane salma na cikin wani yanayi don har yanzu gidan na a yadda na san shi a baya ba,a gyara komai ba daga gidan.
Nan dai muka shiga bayan nasa Fauziya ta riko abinda muka kawo mata sallama mukayi daga kofan shiga tana ciki ta amsa muna.
Tana fito da gani girki takeyi a lokacin mamakin ganin mu tayi wanan lokacin yau a gidan nan nace gidan ki kuwa yau dai gamun zo falo ta kaimu tana kame kame aiki yai yawa bata samu ko gyaran falon ba yau.
Muka zauna muna gaisai tana tambaya mu mutanen gida ranan mun sha hira tanayi tana duban girki har yayi ta zubo muna mukaci tare bayan azahar sai ga maigidan ya shigo cin abinci dama tace muna kila ya dawo don ba kullun yakan samu dawowa gida ba.
Allah ya taimaka sai gashi ranan ya dawo tundaga waje yake kallon bakon motar daya gani kofan gida haka ya daure ya shigo gida da sallama tare da zullumin wanda zai sama a gidan.
Kasa nake zaune na sake jikina muna hira dan kwalina yana saman kaina na rufa ya shigo da sallama.
Muka karba tare da mai sannu da dawowa da mamaki yake kallona tare da fadin wa nake gani haka kamar Fatima gidan yau nace nice yaya.
Duk cikin mu ni kadai ke masa wanan karan kiran shi da yaya tun farko kuma yana jin dadin hakan har cikin ran shi.
Gaisawa ya zauna mukayi sosai yana tambayana yara nace suna lafiya baban su ya tafi dasu suna gurin shi.
Kefa may kikeyi a garin nan har yanzu sai nayi mai dariya kawai anty salma tace kamanta na fadama tana gida yace amma na dauka laluran cikine ya tsayar da ita aiko ?
Shiru yayi na dan lokaci kafin ya mike yana umurtan ta takai mai abunci a daki tunda muna gurin .
Nan ta barmu ta shiga hidiman mijin ta muna dan hira da murja sama sama a gurin na lura da akwai biyayyan aure sosai da salma take mai don yana shigowa gaba daya sai naga ta daburce min .
Sai da ya gama na mike ina tambayan ta ya kare cin abinci ne ina son magana dashi taje ta fada mai yace in shigo tashi yayi saman kujeran da yake zaune ya koma bakin gado ya zauna.
Na shigo da sallama muka kara gaisawa yace banji dadin jin kina gida haka zaune kuma ban sani ba don yanzu na rage shiga gidan tun bayan auren mu da salma bana shiga kamar yadda nake zuwa dacan.
Nace yaya dole na zauna gida abubuwa sunki canzawa ta bangaren hjyn su salma har yanzu dani nan dai na kora mai dan bayanai da suka faru.
Yace ni abin yana ban mamaki wanan hali na hajiya har kullun ita bata amfani da girman ta da shekarun ta.
Yanzu shi Alh dayace ki zauna gida yana ganin hakan shine mafita ga zancen ku ?
Nace yaya ni hakan yafi mun sauki gara kowa ya zauna a matsayin shi zai fi abinda ke daga min hankali shine kullun dan zance kadan tayiwa mamu gori da zagi da cin mutunci.
Zuciyata ta fara gajiya da wanan abin yaya don ba zan yarda ina ganin mahaifiya ta ko yaushe a cikin tashin hankali yaya meye laifin mamu a cikin barin ta da mahaifiyar ta tayi ?
Yace ni yanzu ba wanan ba don in da sabo ai hjyn ki ta saba da halin wanan matar hakana zaman ki gida shine bangane nufin Alh ba.
Nace yaya koma dai maye ni ba zan koma gidan yaya Umar ba taje tayi mashi auren gatan da tace zatayi mai din kowa ya gani ba shike nan ba.
Yanzun gida nake son zuwa kwanan nan tunda nazo banje gida na dubasu ba idan na dawo zan fara maganan aiki tunda ina da takarduna zaman nan ba zai fitar dani nan gaba.
Yace a,a Fatima kada kiyi haka ki bari a zauna ai magana zan tuntubi Alh da zancen nasan ba zai boye min komai ba daga ciki in yaso sai mu san abinyi daga baya.
Yaya ba zanso kai mai magana ba don ni abin yanzu ya fita mun a rai ba zan iya daukan cin fuskan da akewa mahaifiyata ba yaya a kaina.
Fatima shi aure da kike gani ta wuce nan ya fada yana murmushi shi umar din ai badashi kike da matsala ba yanzu don mahaifiyar shi sai kice kin hakkura da mijin ki da diyan ki ga baki daya.
Zamu zauna da Alh duk abinda ake ciki zan kira hjy muyi magana itama hakkurin data saba shi zatayi.
Kin gani nan sai da na nuna mata nima na iya ta barmu muka zauna lafiya da salma gidan nan yazu ta fita batun yar nata wai ta yafe min ita.
Yakai inda nake sin zuwa nace kai hjy ho dama yaya zanso muyi magana sai ga sultana ta shigo tana kuka a dakin tana nema na.
Saida na lalashe ta tayi shiru yace wayan can yaran su ance mazane kika haifa da farko ko ?
Nace mazane yaya kafin ince dama zancen Anty salma nake son zamuyi dakai idan mun samu lokaci don naga yanzu kamar kana saurine ?
Yace wani abinne tace nayi kuma haba yaya me zakai ma anty salma harta kawo karanta gareni kawai dai ganin dacewan abin yasa nace tunda dai ni zaman kanwarka nake a gare ka zan ma magana ko za a samar mata aiki ko wani sana,a mai karfi wanda zata rike kanta kamar yadda mata sukeyi a zaman nin ba sai mace ta dogara ga abin namiji ba .
Dan murmushi yayi kafin yace Fatima nasan da wana gata nan ki tambaye ta kiji nidai ga tsarina ba zan yarda da aikin gwaunati ba.
Ko karatun da tayi mijin ki shi yazo ya rokeni alfarma naji nauyin shi na yarda taje karatu.
Salma bata da wayau fatima da kike ganin ta ga kazanta da ace ni mai ra,ayi tara matane da yanzu na dade da kara aure don halin salma.
Nace abin ko bai mata kyau ba nayi mata magana dazun da muka shigo kuma ta dauku alkawarin zata gyara.
Yanzu dai naji yaya ba zaka barta tayi aiki ba zaka barta tayi sana,a mai kwari koda a cikin gidane don ta huta zaman banza .
Da alama zancena yana bashi dariya don murmushin da yake sakewa a fuskan shi idan nayi yasa na gane hakan.
Fatima yanzu shahon mu ba kamar da bane can baya kuma ni kin san a karskashin wani nake har yanzu dukiyan mutanene amana a hannu na na fada mata tayi hakkuri har Allah ya bani wani dama in samu dan kudi in bata tasamu abin yi dashi.
Na sani yaya ba wai ina nufin kai kaimata a yanzu nasan yanayin da kasan nan ke ciki da halin da kuke ciki dan uwan ta dai ne zai mata idan ka yarda.
Fatima kin san halin hjyn su sarai yin wani abu ga yarta yana iya jawo muna matsala daga baya mussanman ma idan abin ya fito daga bangaren su.
Nace yaya kada ka dubi wanan yanzu idan ana dubun halin hjy komai ba zaiyi ma yan uwan shi ba ita ta kwammace yai ta bata kudin tana bin wani hanya dasu.
Yace Allah dai ya kyauta Fatima halin hajiya sai ita muyi ta hakkuri tunda Allah ya hadamu dasu.
Wayan shi da yai kara ya katse muna zance ya tsaya daukan waya a daidai lokacin na mike ina fadin yaya na gode zamu tafi gaba har gidansu mama muke son zuwa yau din nan.
Na fito na dauki jakkana na suba kudi a ciki yana fitowa daga dakin naji yana fadin ke barin baki dan wani abu a saya maki biscuit ko yana kokarin lalaben aljihun rigan shi ta gefe.
Da sauri nace a,a yaya don Allah ka barshi ni ga wanan dama na riko maka lokacin da muka zo ban samu kawo maka tsaraba kayi hakkuri da wanan ina mika mai kudin daga cikin daki da yake tsaye a kofa.
Yace Fatima kamar abin bin bashi ni ko wanan mutuncin da kike min keda mahaifiyar ki kun maidani tankar dan uwan ku na jini ai ya isheni daku .
Babu komai yaya don Allah ka karba ina dashine aina baka da bandashi gurin ka ai zanzo nima in samu yaji dadi yana fadin kwarai kuwa fatima yasa hannu ya karba yana min godiya.
Sai bayan ya karba yace kai kai kai Fatima kudine fa masu yawa kika miko min nace yaya ka wuce nan a gareni idan inada wanda yafisu sai in baka babu kyashi.
Godiya yai min sosai ya fita yana mun sallama sai bayan ya fitane na kalli anty salma da ido nace ko dan rakiya baki mai kiji ko yana da wani maganan da zakuyi tunda gamu a wurin.
Mun zauna da ita munyi magana sosai bayan la,asar muka fito gidan zuwa gidan mama saratu da kanwar mamu mama saude duk mun kai masu ziyara ranan kuma sunji dadin zuwan mu.
Sai gap da magariba muka dawo gida a gajiye part din mu na wuce direct don nagaji sosai a lokacin tun a falo na fara kokarin cire kayan jikina.
Mamu tace kin bar wayan ki a gida ana ta kiran ki na dauka ban gane yaren da matar take min ba yare kuma mamu na tambaya ina kallon ta.
Tace ni kan yare naji tanayi mun ai don ban fahinci may ake fadi ba nace koma waye ai zai sake kira idan wayan ya damay ta.
Har na juya na fara tafiya wani tunane yazo min a raina na juyo ina fadin mamu kodai wanan matar da muka kirane ta kirani yau.
Da sauri tace kuma fa yana yuyuwa gaskiya nace bari na duba na shiga na dauki jakkar da wayan ke ciki ina dubawa daga daki nace wallahi mamu itace kuwa ga sunan tanan da nayi serving.
Ikon Allah mumun kira ranan bata daga ba yau kuma ita ta kira har sau uku ba a daga ba may wanan abin yake nufi ne wai haka ?
Dare yayi yanzu sosai a can zai kai karfe goman dare ko ya dan fi amma dai barin gwada kiranta mu gani ko zata dauka yanzu.
Tace shiyasa mijin ki yace idan zan kira na dinga kiran ki goman safe ko zuwa shaday haka yafi a same ku.
Kiran sunan yaya da tayi yasa na tuna da zancen mu da Ahmed nake tunane sai dai ban mata magana ba duk da an fara kiran sallah hakan bai hanani kiranta ba a lokacin.
Nayi sa,a aka daga wayan da sallama na karba muka gaisa tace kwana biyu nace eh ban dawo ba ina Nigeria har yanzu.
Zancen da mukayi dake ne na kira don nazo ga mahaifiyana na tambaye ta tace min sunan mahaifiyar ta halimatu sadiya amma mahaifan ta suna kiran ta da Siyama a lokacin .
Sai naji tayi wani irin kanbbara da karfi tana fadin nasani nasani kamar yayi yawa wallahi itace itace wace muke nema shekara da shekaru bamu gane ba.
Da gudu na fito falo zuwa wurin mamu sai na sameta zaune tana kuka da alama taji wayan da nakeyi da matar a lokacin.
Ban damu da kukanda takeyi ba na fada mata ina ihu da murna ina rike da waya a hannu na lokacin .
Munyi magana sosai da ita na fahinta ta fada muna mu saurare ta zuwa safe zata kirani ta fada min yadda sukayi da mutanen ta.
Mamu ki bar kuka godiya ya kamata muyiwa Allah da ya karba muna adduan mu a lokacin da mukafi bukatan hakan a tare damu.
Sayadi dole in kuka yau ta fadi tana share fuskanta jin zancen nan nake kamar mafalki nakejin sa yau ubangiji Allah ka tabbatar min da wanan abin ya zama gaskiya a gareni.
Ba zan kara sati ba a gidan nan zan tafi zuwa neman mahaifiyata tunda na gano a inda take yanzu.
Tashi muyi sallah mu godewa Allah lokaci yana shigewa kada muyi wa Allah butulci da halin mu na yan adam a lokacin da ya amsa muna addu,an mu.
Mikewa nayi ina tafiya duk jikina ya mutu da maganan mamu da tace sayadi abubuwa suna damun rayuwana da zancen rashin ganin mahaifiyata zanji koda rashin kwanciyar hankalin gidan nan kullun nike nan a cikin gori da takala da habaici iri iri.
Yanzu idan mahaifiyar mamu tazo yaya hjy zatayi da take yawan mata gori kan hakan irin tunanen da nakeyi kenan ina alwala a ban dakin.
Na fito na tayar da sallah muna idarwa kuma muka dasa maganan ta yadda zamu bullowa maganan don haka zamu yi shiru tukun na sai mun gama tabbatar da komai da gaskene kafin ta tunkari kawu da Amma da zancen.
Barci nayi sosai ranan don a gajiye nake sosai kamar nayi wani aiki dan fitan da mukayi ya saukar min da kasala a jikina.
Washe gari ne da safe muna karyawa sai ga kira kawu a wayan mamu yace ta turo mashi ni falon shi.
Da mamaki a raina na mike zuwa amsa kiran kawuna a falon na samay shi zaune tare da hjyn su yaya tana cika tana batsewa ganun hakan yasa nasan ba lafiya bane wanan kiran.
Gaida su nayi na samu wuri na zauna daga kofa a kasa ina fadin gani kawu yace Fatima yanzu uwar ku ta kawo karanki wurina.
Kan kin sa drivern mijin ki ya dauko maki mota a gidan mijin ki kin fita dashi jiya alhalin ba a gidan sa kike ba yanzu kin sani.
Dan kallin hjy nayi cikin mamaki nace kawu ban taba motar yaya ba motanace dana bari a can nasa driver ya dauko min da zamu tafi gidan Anty salma jiya.
To kinji jimmai ya fada yana nuna ta da hannu yace jimmai wai may kike nema da wanan yarinyar ne haka a gidan nan ?
Shiyasa ban maki magana sai da tazo don muji dalilin ta na daukan kayan danki bai gari ita kuma a matsayin matar shi.
Motar ta ni bai sheda min cewa tana da mota ba da zai tafi don haka dole inyi magana akan kayan dana don ba kayan banza ya ajeba da kowa zai dinga dauka yadda yaga dama ko wani lokaci.
Kawu bai dago kaiba hankalin shi naga waya sai daya kira aka dauka yasa handfree yana fadin kana lafiya ya yara.
Ya amsa mashi kawu yace yanzun ina zaune mahaifiyar ka ta shigo min da wani magana wai Fatima ta aika gidan ka an kawo mata mota ta fita jiya.
Shine na kira fatiman yanzu gata a gaban mu take fadin motar tace ta dauko ba naka ba ita jimmai bata yarda ba shine na kira muji a bakin ka.
Innalillahi yace munajin shi yanzu daddy don Fatima ta taba kayana shine abin magana wurin mama motar nan nata ne tun a London na saya mata ba fita take nan ba yasa na turo mata dashi gida.
Kai mara kunya inada daman da zanyi magana akan kayan ka idan naga za,a wullakanta maka dukiya tunda ba,asan zafin shi ba.
Mama matatace fa ta taba kayana tana da iko da duk wani abinda yake mallakinane a garin nan yanzu don tare muka same shi a nan.
Lalai babawo ka nuna min an gama da kai har kake fadin haka a kunnuwana yau komai tsiyar ka sai ka rabu da yarinyar nan na fadama.
Mama daga yau nabada baki duk abinda Fatima zatayi da kayan gidana a barta tati natane na mijinta na yaran ta final ya kashe wayan.
Kawu yace tashi kije abinki na dago ido na kallesu tare da fadin nagode kawu na fita daga falon zuciyana ba dadi abinda hjy take min yayi yawa sosai yanzu.
Tayi min tayiwa uwata duk muna daurewa muna shanyewa anya kuwa zan iya nan gaba da halin hjyn su yaya.
Na shigo part din mu mamu ta bini da kallo banyi magana ba son banda niyar fada mata wanan magana.
Lafiya yake neman ki nace lafiya mamu ganin ta kuramin ido tana son jin akan may ake kirana din nace wai hjy ce takai karana na dauki mota jiya daga gidan yaya na fita dashi.
Matarnan tana da hankali kuwa wanan wani maganane haka babu dadin ji ko yaro ai ba zaiyi wanan abinba.
Ta dai daukeni matsiyaci dagani harke tana muna kallon wullakantatu a idon ta.
Mamu hassadane da ne da kyashi ke damun hjy rashin kaunar ki da batayi ya kawo haka garemu .
Niko nasan da hakan don hjy ko kasheni tayi idan ba ta cire min kai taga bana motsi ba hankalin ta baya kwanci.