NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:13 – ????????????: Na dauka ya fita daga gidan ne ashe suna part din mahaifin su sundan dade dashi suna ganawa kafin su fito su shiga wurin Amma.
Ana nan sun dade wurinta shi da yan uwanshi tana magana kan fushin da habbib keyi na rashin zuwa gida daya dauke kafan fashi don dan matsala da suka samu da mahaifiyar su.
Amma tace ashe da kaine dan uwan ka yaya ke nan zakayi kiri kiri sun rabashi da matarsa don kawai wani dalili na su can .
Jin haka ya umar ya mike tsaye yana fadin ina sauri ne fa suma yan uwan suka mike daga inda suke.
Tare suka fita daga gidan ya Umar da yan uwan shi duk da basu inda zasu tafi bi a lokacin ido kawai suka sawa yayan nasu.
Lokacin ina gyaran falon mamu da ya sha gyara sai kamshi yake bayan na gama don kannena sun tafi school lokacin.
Part din Amma na koma muna hira don ranan murja tana gida bata fita ba zuwa school bata zama yanzu suna final year din su ke nan.
Amma ne da tai shiru tana tunane can ta juyo tana fadin hankalina baya kwanci idan ba naji kiran yaron nan akan maganan komawan ki gidan shi ba.
Allah yasa dai wanan karon a shirya don kamar karfin maganan wurin hjy yake ai kawu ya zuba mata idone ko zata sauko daga kudirin ta nayi mai auren da tace ai.
Sallaman mamu dake rike da hannun Abdulsalm tana fadin ga baki kunyi fa.
Mamakine kwarai ya kamani ganin yaran don yaya bai fada muna cewa tare suke tafe da yaran ba dazun daya shigo ya fita yana fushi dani lokacin.
Na mance a gaban mamu da Amma nake na rugume yarana a cikin murnan ganin su suma kankameni sukayi suna murna tare da tambayana cikin harshen turanci may yasa na tsaya nan na barsu su kadai ?.
Kowa yayi shiru a falon yana kallin mu ashe kuna da aiki idan jiran komawar uwarku kukeyi gidan ku mamu ta fada da hausa tana juya zata fita.
Mekike nufi da wanan maganan da kike yawan yi ne maimuna tace gwaggo gani nayi dai mahaifiyar umar bata da niyar saukowa ga kudirin ta har yanzu ai.
Kudirin tana banza da wofi ita ba zaune take a gidan mijin ta ba lafiya iya shegen da takeyi a gidan nan idan ba yaron nan bane wazai daukan matashi haka .
Juyawa nayi aurin maria muna gaisawa na fita zancen su ina tambayan ta bayan robon mu.
Maria ta hade hannayen ta guri daya tana rokona inyi hakkuri mu koma tare wanan karon.
Murmushi nayi mata kawai ina dan kwantar da yaran a jikina ina jin wani yanayi mara dadi yana sauka min a zuciyana lokacin.
Ido na lumshe ina ci gaba da tunanen halin da rayuwan aurena ya fada cikin matsala saboda uwar mijin da ban mata komai ba a rayuwana.
Ranan dai tare da yarana na wuni a gidan sai dare ya aiko aka dauke su hakan kuma shi ya jawo magana wurin hjy.
Cewa tayi yara sunzo na hana suje gurin ta na hana su santa a matsayin kakan su na hana mata shakuwa da jikokin ta su saba da ita tun yanzu.
Zance yakai har wurin Amma don kawu yanzu ba a son yawan bata mashi rai sosai haka yasa Amma tayi masu iyaka da tayar mai da hankali.
Bayan ta gama magana Amma ta juya wurin mamu tana fadin maimuna da yaran sukazo basuje gurin ta bane jiya ?
Gwaggo bansan ko an kaisu ba ko ba akaisu don ni jiyan ina hidima da Alh ban zauna ba.
Yanzu kunyi min adalci ke na maimuna kina kokarin rabani da yaran nan
Ida ba baki kaddaran daya hada dana da yarki ba da babu ta jnda zasu hadu ko ki taba gani inda aka hada tsiya da arziki a wuri daya. .
Kada kiga nai wanan maganan kice ko yaran yarki sun dameni ne a raina a, a idan ma kun rike abinku duk dayane don dama wanda bai gajiya arziki ba ko sashi a baitalmali duniya tsula zai fito daga cikin shi.
Baki san zafin uwa ba maimuna haka ma yar ki yasa a kullun kuke kokarin kuga kun rabani da dana mafi soyuwa a gareni.
Hjy inda kece ke bayar da arziki ba Allah sai ince na debe rai ga wanan arzkin da kike kira kullun har yau ke kuma banga arzikin da kika tarawa kanki ba a gidan nan.
Kai da kun bar wanan magana haka hjy maryam tace yara ko anki ko anso yanzu sun zama na mutum biyu ai a gidan nan irin wanan fada kan yaro ko fili sai Allah ya dau ran guda daga cikin ku a zauna lafiya.
Maryam ni kike kokarin fadawa magana a fakaice hjy tace don taki jin azo magana hjy maryam ta dan kauce mata yanzu zata nuna mata bacin ranta a gurin.
A, a hjy akan me zan fada maki magana kamar ina jirake dake gani dai nayi abin bai kaiga kallo ba.
Hjy amma dai da kike fadin wanan magana kin san na shiga dasu su gaida ke kika barmu a falo zaune.
Irun wanan ba jiya kika fara yi mun haka ba idan na shiga part din ki sanan ina son ki sani mamu dai ba shegiya bace da uban ta a duniya kuma yana raye.
Duk magana ya tashi ke kenan a cikin zagin kaddaran da ya sameta don kawai mahaifiyar ta tana kasan su .
A laila ba mamaki yarinya wuyan ki ya isa yanka a gidan nan ni kike kokarin yiwa kashedi akan uwar ki ko mai a gidan nan.
Ai ba tafiya zakice kakar taki tayi ba kice tana wurin yawon dandin da suka shigoyi dama a kasan nan.
Allah sarki hjy gara da yau kika fadi manufan ki kowa yaji a gidan nan mamu tace sai dai saukin abin asalin kowa a tafin hannun kowa yake yanzu.
Amma dai kin san mun san mahaifin ki su suka fara budewa karuwai gidan clubs a garin nan a fili yana yawo da betil da mata da rana suna shan giya suna rawan yawon siyasan NPN duk da tsufan shi ko kin manta da hakan duk da ban sani ba kunne ya girmi kaka ai.
Wani irin kukan kura hjy tayi mamu ta mike tsaye nan fitina ya murtuke sosai a tsakanin su tana fadi tana fadi duk suka rikita gida mamu na fadin na gaji kullun ina daga maki kafa baki daukan girman ki.
Aliyu ne ya samu wanan fitinan a gidan ya juya ya fita rai bace in auren yarki yayi dubu da babawo ya mutu a gidan nan .
Mamu tace sai me don kin kashe auren danki naki nakima ai baki damu da yamutu ba balle na wani hjy wani girma da kimar da nake baki duk ya kare a gidan nan daga yanzu yadda baki kaunana da jinina haka nima ban kaunar ki har cikin raina.
Kawu da yaji hayaniyar yayi yawa ya fito basu daina ba yace wace ta kara tankawa a wurin a bakin auren ta fadan malam bashe a gidan shi hakan yasa kowa taja kafanta ta koma part din ta cikin kunan rai.
Nikan har cikin raina banji dadin hakan daya faru tsakanin su ba don nasan abu zai kara rikicewa a tsakanin mu ke nan.
Saidai kuma naji dadin amsa mamu sosai don ta rama cin fuskan da hjy ke mata tana ganin bata san nata zancen ba na fada.
Ashe yaya baya garin anyi haka da kwana biyu ya dawo tun yana can Aliyu ya buga mai waya yana sheda mai cikin bacin rai.
Koda ya dawo bai nuna yasan komai a kan zancen ba sai hjy ce ta fito mai da zancen karin auren shi yace ban shirya aure yanzu na fada maki mama.
Zaman Fatima a gidan nan da daddy ya zaunar da ita nake son ta koma don ban fahinci may hakan yake nufi ba don.
Kai dakata kaji idan itace autar mata babawo ka gama zama da wanan yarinyar diyar marasa tarbiya diyar wa yanda basu da mutunci.
Mikewa yayi ya bar part din ba tare da ya tsaya sauraren ta ba sai da dare ya kira mamu a waya.
Yace ina son Fatima zata koma dakinta cikin jikin ta yana girma zamu koma tare wanan karon.
A,a umar ya kamata ku hakkura hakana da kai da ita kasan mahaifiyar ka har yanzu tana kan bakanta ga zancen nan zaifi don Allah idan haka yafi zama alheri a gare ku Allah ya tabbatar muna da hakan.
Nagode yace ya kashe wayan shi ina zaune ina jin yadda sukayi dashi a wayan .
Kaina na dukar lokacin da take aje wayan naji tace kai bawan Allah nan shima yana cikin wani hali wallahi.
Wanan al,amari yakai min inda yakai wallahi tun farkon wanan hadin abindana guduwa ke nan don halin hjy sai ita.
Al,amarin sai addua wallahi naji ta fara jero addua,a tanayi sai kuma tace ni yaran ma suke ban tausayi kullun idan sun shigo nakan shiga wani hali wallahi.
Ni idan ma auren zatayi mai tayi masa kowa ya huta tunda ba,a kan ki zata shigo ta zauna ba kowa da halin sa ake zama dashi ai.
Washe gari ina barcina sa goma zuwa shadaya dake min dadi a yanzu naji mamu tana tayar dani wai kawu suna neman ta a falo ga yaranan zaune falo.
Nafito ina tunane kan me kuma su kawu suke neman mamu fitinan gidan nan dai baya karewa wallahi.
Mamu tana zuwa falon Amma ta samu falon a cike yake kawu balarabe yace ina ita Fatiman take tace ina daki tabashi amsa.
Ka barta tukun sai idan an fara magana a kirata zai fi kawu yace a dai kirani kusa yanzu zaifi dole mamu ta fita ta kirani muka dawo tare da ita falon Amma din.
Lokacin da na shiga nayi mamakin ganin mutanen da aka tara a falon na samu wuri kusa da Amma na zauna na fara gaida su.
Wanda naji kawu balarabe ya kira da liman ai muna addu,a kafin mu fara abinda ya kawo mu ko ?
Sai mutumin yayi addua ya kara da fadin duk abinda za,a tatauna ya zama alheri a garemu baki daya suka amsa da amin.
Kawu balarabe ya kalli yaya yace jiya ina gida Faruq ya sameni da wani zance akan matar shi wanda ni duk dadewan nan basan da wanan zancen ba gaskiya.
Yanzu dai gashi muji daga bakin shi don kowa yaji wanan maganan dayazo min dashi shiyasa na taraku a nan gaba dayan mu don samun mafita ga zancen.
Yaya dake kasa gefe shida habbib ya gyara zama ya fara da sallama yace akan zancen matanane Fatima da daddy ya aura min har mukai haihuwa uku da ita gana hudu a cikin ta yanzu.
Don muna zaune daddy ya kirani ga waya muna zuwa ya bada umurnin itata koma dakin mahaifiyar ta ni kuma mama ta rikeni da yayana tun wanan lokacin ban kara jin wani magana a kan zancen ba.
Yanzu ina son matana ta koma dakin ta don ina son mu tafi tare saboda cikin jikinta da ke girma ba zanso barin ta nan ta haihu bana nan ba.
Hjy bata bari yakai zancen ba ta bude baki tace karana ke nan kakai wurin iyayyen ka ko ?
Hjy kiyi shiru nan ai yanzu ba karan ki ya kawo ba inhar kina da laifi zancen Alh dai muke son jin manufarshi nayin wanan hukuncin daya yanke ?
Kawu ya dago kai yana sallama kafin ya fara fadin lalai nayi hakan ne kan a zauna lafiya don banyi wanan abin da wani manufa a raina ba sai don karin zumuncin dake tsakani na da yan uwana koda bayan bana raye ne.
Sai kuma wanan yaron da ya dauko muna yar ahalulkitabi a matsayin mata yazo min da ita na duba gaban sa hakan ba zai haifar mashi da alfanu ba a rayuwan shi nan gaba
Liman yace haka Allah yace ayi Alh hakkun kayi gaskiya sai kawu yace ashe ni ban sani ba ita hjy yin hakan har wanan lokacin bai mata dadi ba.
Kai balarabe da mustapha ga baba nan zaune da ranshi tsohon yana jingine da sandan shi baiyi magana ba har lokaci kai kawai ya kada masu.
Ba zabi da baki na basu ba takarda na watsa da sunayen yarana mata da nake da niyar basu a lokacin diyan ya uwana.
Koba haka akayi shi a falin nan ba ya sake tambayan su suka amsa da hakane.
Yace daga baya jimmai ta tuma ta kafe bata yarda da auren shi umar ba da yarinyar nan tun kafin in basu takarda saida na kafa sharadin idan jummai tayi korafi akan auren nan a bakin auren ta.
Subbahanallahi liman ya furta kawu yace kwarai anan falon na fade shi gaban kowa jin haka jimmai ta yarda da hakan ta amince.
Saidai ashe bansan da manufa ta amincewa hakan ba azuciyanta na dauka daga ta fahinci abinda na hango nayi wanan hadin daga baya.
Saidai ashe ita a wurin ta ta dauki wanan abin gaba tsakanin ta da maimuna gata nan.
Yakai bayan yaron nan ya wuce da mayarshi ashe ta kafa mai sharadin banza kan idan yaje ya sako muna yar mutane da akai min alfarma aka dubi mutuncina akabamu.
Ita mai diya mace da aka cuta tana karama sosai a lokacin aka ba danta batayi koraglfin haka ba sai jummai ne zata kasa hakkuri ta rugumi kaddara har yakai yaran nan sun haifi diya uku acan batare da sanin mu ba anan .
Kullun na kira saidai suce suna lafiya yana zuwa kasan nan ya koma ba tare da ita ba duk bai fada muna sun samu karuwa a tsakanin su ba .
Ashe duk gudun mahaifiyar shi taji wanan yakw boye muna hakan koda suka dawo hakkurin hakan kawai ya bamu a lokacin nayi fada sosai dashi daga baya na fahinci abinda yake nufi da hakan.
Sun dawo gida fitinan mahaifiyar shi kan yarinyar nan sai karuwa yakeyi bata bar masa mata ta zauna lafiya ba haka kuma bata bar kishiyan ta sun zauna gidan nan lafiya ba.
Har takai ta kwashi yan uwan ta zuwa gidan yaran nan tayi tataki kan ta shirya zata aurowa danta mata da take bukatan shi da ita a duniyan nan.
Ba wani ya fada mun ba ya ciro wayan shi yana laluben yace kai balarabe shedane tare tsohuwar mu ta kiramu ta nuna muna video nan da yarinyar nan murja ta dauko na cin mutuncin da sukaje sukayi a gidan wai sunzo duban dakin da zasu saka yarsu.
Wanan dalilin yasa na kira yaran nace kowa ya dauki dan shi a zauna lafiya duk da na fada mata kafar yarinyar a gidan umar gashi fitan ta gidan nan nawa har abada ke nan.
Naga alaman ta amince da hakan kuma a zuciyar ta tunda zaman yarinyar nan gidan nan ba wani sauyi da suka samu kullun fitinane da uwar yar nan.
Har yau ban taba kiran su da sunan maimuna takawo min karan jimmai ba gata zaune amma ita a kullun cikin korafi take anmata dai an mata a gidan nan.
Kawun hjy ya nisa a lokacin yace jummai amma baki biyo halin mu ba wallahi tir da Allah waddai da wanan halin naki.
Keda kanki zaki hana rayuwan danki zaman lafiya don wani kudirin ki na baza can da kika sa azuciyar ki gareki wai farau kishiya jummai ?
Kawu da kubar wanan zancen don yarinyar nan ba zata koma gidan umar ba har abada shine abinda na yanke akan maganan nan mamu tace.
Kowa na falon ya kallo ta don jin abinda ta fada tace kwarai kawu hakkurina ya kare a kan hjy tunda kan auren nan yakai har hjy ta kira min da mahaifiyata da yar yawon duniya.
Subbahanallahi hjy da girman kike wanan furcin ga yar uwan ki ya kasance hakan gaskiya ne ai ba fade yakamata ki mataba illa shiryuwan Allah gareta.
Kawu balarabe yace a ina wanan zancen ya fito haka mara dadin ji kuma ?
Liman ne ya katse su da fadin salamu alaikum suka amsa masa yace da farko wanan al,amarin baiyi dadin ji ba ace babban gida irin na Alh mutumin da duk unguwan nan yaro da babba ake ganin mutuncin sa yau ace a halin sa ne ke wanan irin rikicin kamar gidan da babu adini a cikin sa.
Alh kaima kana da naka laifin a wani bangare a ina ka taba jin iyayyen sun samu ikon kwatar yarsu a hannun mijin ta ?
Wanan sai idan shi mai auren ya bude bakinsa yace bayayin auren ya fasa wanan ba sauran abin yi sai a raba auren.
Yanzu duk mu bar wanan zancen tunda ga ma,auratan a zaune gaban mu ya juya ya kalli yaya yace Umar Faruq kazo tafiya da matar kane a yanzu ?
Cikin ladabi yaya yace abinda nake so ke nan idan hakan zai samu a yanzu.
Amma idan zai tafi da ita sai an bani dama ya karbi nawa bukatan auren yar wurin sabuwa da nake son yayi.
Da sauri kawunta yace bukatan auren diyar sabuwa jummai kina da hankali kuwa a rayuwan ki son kan ki har yakaiki ki halaka kan ki da kan ki yaro suna zaman lafiya da matar shi zaki dauko zancen yar sabuwa da basu da tarbiya ki jefa a cikin ahali ki ?
Kawun nata yai mata tas a wurin yayan ta yana taya shi dole taja bakin ta tayi shiru don babu hanyar yin magana a wurin gareta kuma.
Yace ka dauki matarka ka tafi wanan magana ya kare a wurin nan yanzu don haka idan ka shirya daukan matar ka ka dauketa ku tafi.
Mamu tace ta bishi kuma a haka kawu ku tuna fa ba daku zata zauna ba dasu ne hjy kuma ba fasa abin nan zatayi ba ga yarinyar nan tana fadin haka ta fashe da kuka.
Jikin kowa a falon sanyi yayi a lokacin ganin mamu na kuka nima na fashe da kukan lokaci guda falin yayi tsit ana sauraren sautin kukan namu.
Kawun hjy yace kuyi hakkuri ansan an cuta maku ana makan cutarwa din don wanan bata da alaman fasa halinta tunda ta kulla da sabuwa.
Yanzu ai ga yarinyar nan a zaune itace ke zaman aure ba wani ba yana da kyau muji ra,ayin ta idan zata bi mijin ta su tafi a yanzu din.
Da sauri yaya ya dago kai kalli kawun hjy da idanuwan shi da suka kada sukai ja a cikin natsuwa yana fadin malam kada kuyi haka yanzu a lokacin nan da suke jin zafi da ciwo a zuciyar su don furcin mahaifiyar dataji kuma.
Kawun hjy yace umar ka kwantar da hankalin ka ba zabi bane hakan hakkintane itama za a bata don muji ra,ayinta a kanka yanzu.
Ya juyo gareni yace Fatima kiyi hakkuri ki daina kukan nan kiyayya a filin Allah da tozarci haka baida dadi ko kadan .
Fatima kindai ji hukuncin da muka yanke a gaban ki yanzu shin zaki bi mijin kine ku tafi koko wani shawara kika yanke a zuciyar ki ?
Kaina a duke ban dago ba sai hawaye nake yi ina tunane a zuciyana ra,ayin uwata da take kokarin kwato min yancina a gurin hjy zanbi koko tausayin mijina da yayana da suka koma kamar marayu zan bi yanzu.
Jin malam ya kara kiran sunana yana fadin Fatima ke muke saurare muji ra,ayin ki yasa na dago kai a hankali na kalli inda malam din yake a daidai wurin kuma yaya Umar din shima yake zaune a kasa.
Karab idanuwa na suka sarke a nasa ni yake kallo da jajayen idon sa da suka kade ko kiftasu bayayi a lokacin bashi kadai ba duk wanda ke falon a lokacin ido ya zuba min don jin me zan fada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button