NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:16 – ????????????: Na sake dukar da kaina a kasa ina dan sheshekan kuka kowa a wurin ya zuba min ido suna saurarena a lokacin.
Azuciyana sai faman tunane nake ba zan yarda in bi yaya a wanan lokacin ba don kwatar wa uwata martsnbata a gurin hjy dake ganin don abin hannun danta mamu ta zuga kawo ya cusa ni gareshi a nata tunanen ke nan ita.
Kowa yasa tsakanina da mahaifiyata akwai shakuwa da yawa wanda har mutane ke ganin bata kawaici a kaina irin da akewa dan fari don shakuwane sosai da aminci a tsakani na da mahaifiya ta.
Don shi kanshi yaya idan muna waya wani lokaci da mamu ya kance min shike nan kun koma aminai dake da mahaifiyar ki don na lura a cikin ki babu wanda take so kamar ki.
Nakan ce mai kasan banda Amma mamu bata da wani wanda suka shaku a baya yanzu ko Amma girma ya kamata dole wani shawaran dani zatayi shi.
Sannan ina tuna da namiji ba dan goyo bane in watsawa uwata kasa a ido yanzu a gaban jama,a yazo uwarshi ta tursasa shi yai auren da take so da wani ido zan kalli mahaifiya ta daga baya.
Kai Allah waddan naka ya lalace kan yar nan duk kabi ka susuce kanka a banza kamar itace autar mata a duniya.
Na rasa mai kagani a wurin yarinyar nan ka juye a lokaci haka babawo har suna daukan kansu su wata tsiyace yanzu muryan hjy ce kewa yaya fada a wurin lokacin.
Wanan ai da gani sun gama da kaine don bayin kai sake bane wanan abin don anga wurin cin banza an mayar da kai shanuwar tatsa.
Kawun hjy yace jummai wanan wani irin kalamai ga danki kike furta wanan magana nan haka a gaban kowa babu dadin ji.
Kawu bari na fada mai gaskiya don Allah idan ba an gama dashi ba zai zaunar damu a nan haka kan wanan diyar makaskanta har ana son a fada min magana akanta.
Don kawai suna kurin sun rabani dashi zaiyi kokarin ya kunyatani a gaban jama, a haka yasa ai min dariya nan gaba kan bijire min da yayi.
Tana aje maganan ta lokacin zuciyana ya gama tafasa da kalaman ta mai daci a garemu tana ganin don abinnhannun shi yasa nake zaune tare dashi ke nan ko me ?
Nace malam ba zan bishi ba gara kawai mu rabu kowa ya huta da wanan fitinan ba don kuma shi yaya yai min komai a zamun yasa na yanke wanan hukuncin ba don kawai hjy tasan koda dan ta ko babu zan iya rayuwa a duniya .
Amma ko yanzu mahaifiyata tace in bishi a shirye nake da in bishi don ni bai taba kasawa dani ba a zaman mu tare ko yanzu ba nayi mashi haka don gazawan shi bane sai dai kawai don kwanciyan hankalin mu gaba daya har shi.
Aikin bamza ke nan inji hjy don kin san ba wani kadari zakiyi ba koda kin koma din gare shi.
In banda abin dan yau har me yaron nan ya gani ga wanan kodadan yarinyar haka da zaka nace mata kamar autan mata.
Kaiyya jummai dadin me kikaji ga hankan yau dan kin raba auren yaran nan da hannun ki saboda mugun halin ki na baza.
Da kina da hankali da tunane dan zaman wurin nan da mukayi yanzu ya isheki darasi a rayuwan ki amma babu komai gaki ga dan naki sun bar maki shi kan mugun nufin ki na banza sai ki aura mai wace kikeso ya zauna da ita mu gani.
A a kawu meye laifina a ciki zancen nan yanzu sun gama dashi ne tunda sun samu abunda suke so gare shi yanzu baida sauran amfani a gare su.
Gaba daya wurin ya hargitse a lokaci guda masu ganin laifin mamu na fadi na hjy kuma sun fi yawa.
Na dago ido na saci kallon yaya Umar dake zaune ya kura min ido makwal din wuyan shi yana zuwa yana dawowa saboda bacin rai bai iya furta komai ba a lokacin.
Wani iri naji a raina na rashin amincewan da banyi in bishi hakan yana nufin na watsawa yaya kasa a idone a bainan yan uwan mu yanzu .
Banda abinda da zanyi don kimar uwata da martabanta a gurin hjy dake ganin abin hannun danta muke so nake zaune dashi da sauri na dukar da kaina kasa ina sauraren kalami kowa a lokacin.
Muryan mamu ne ya katse ma kowa maganan shi a wurin da tace Umar ya dago kai ya kalleta ba tare da ya iya amsa mata a fili ba.
Yau kake son tafiya da matar ka ko sai ta shirya zuwa gobe ko jibi ku tafi kowa yayi shiru yana sauraren su a falon.
Yaya yace idan ta shirya yau din sai mu tafi ba wani matsala bane tace to gata nan na danka maka ita amana a hannun ka.
Kayi hakkuri da komai da ya faru ita din mace ce yar uwata tasan irin kuncin da nake fuskanta ga auren ku yasa ta zabi in bada zabi a kan ku yanzu.
Insha Allahu nayi maki alkawarin rike ta amana kamar yadda na rike maki ita a baya maman twices.
Take falon gaba daya aka dauki kabbara lokaci guda sai lokacin kawu sani yai magana tunda aka zauna kowa na magana baice uffan ba a gurin.
Alhamdullahi anzo gurin da nake son akai kawu ya furta kowa ya mayar da kallon shi gare shi yace da farko dai niba umar Fatima a matsayina na kawun ta kuma mijin uwarta.
Wanda hakan yana daga cikin rashin zaman lafiyan auren nan ga baki daya sai gashi yanzu a karo na biyu uwarta ta kara mika maka nauyi da amanar yarta da hannun ta kuma ka dauka.
Aikin banza inji hjy tace tana jan tsuki kawu yai murmushi kafin yace ba bako a wurin nan da baisan halin ki ba jimmai don haka na baki zabi daga yau ko ki bar yaran nan su zauna a cikin salama ko rayuka su baci a gidan nan.
Gashi nan a gaban ki idan baki zaki masa ya lalace a kan auren yar uwanshi da baki so sai ki masa a gaban kowa muji.
Shidai daya nuna ma duniya matarshi tafini gare shi zai fada ya yafeni a matsayin uwa a gare shi yau.
Yaya ya dago kai a hankali cikin halin shi na natsuwa yace mama ban ki kiba don Fatima kina nan a matsayin uwa a gareni kamar yadda Allah ya halat min fitowa ta tsatson ki.
Amma mama wanan halin mu kike barwa abin fada a gari ace duk kan mu gaba daya babu mai jin dadi a gurin ki daga mu har iyalin mu mama ?
Yau yaya kike son wanan bawan Allah yayi da rayuwan shi ne a lokacin da muke tunanen samun natsuwa da inganta a tare dashi lokacun ne kuma ke mahaifiyar mu kike kokarin tarwatsa mashi rayuwan shi dana iyalin shi.
Ina mama kin sha fada muna don mu kike hakkuri da daddy da zaman gidan nan a yanzu don mama kike kokarin sai wata tabar nata iyalin ta tafi.
Shin mama idan anyiwa Salma wanan hukuncin ko Nafisa zaki ji dadin abin nan ace sarakansu suna muzanta maki diya a gaban ki suna aibanta su haka.
Nan rikicin Nafisa daya taso munji bawai bamuji ba mama Fatima ita ta kwato maki inci ga wullakancin da dan iskan yaro nan yazo har gida yai maki da iyayyen shi Fatima ita ta hana a dauki kayan a gidan nan tare da basu amsan maganan banzan da suka zo dashi.
Mama may kike so damune wai a rayuwan mu mu bamu ji dadin ki ba hakama iyalin mu basuji dadin ki na kasancewa sarakuwa a garesu ba kaf din su babu wace kike so da zuciya daya a cikin su.
Shin gatan da daddy yai muna a yau muke jin dadin shi hakan laifine ke a gurin ki mama.
Mama na rokeki ki bamu salama da iyalan mu mu zauna lafiya don Allah yarinyar nan fatima iya biyayya tana maki yau har yakai ta fara baki amsa ga maganar ki.
Mama ina kara rokon ki kiba bawan Allah nan salama duk a cikin mu yafimu karfi ya fimu kulawa dake yadda ya dace babu a binda Fatima ta isa tasa shi kota hana shi aka abinda yake maki da sauran yan uwan shi don Allah wanan abin ya wuce hakana ki barsu su zauna lafiya na rokeki mama habbib ya kare fadi da hada hannayen shi gurin daya lokaci guda.
Wani irin kuka hjy tasa tana fadin Habbib ni zakaiwa rashin kunya tunda kaine isashe marakunya wanda ya isa.
Mama ni ban maki rashin kunya ba gaskiya na fada don ni ba zan dauki hakan ba shima dai hakkuri yake yasa kika samu nasaran kokarin rabashi da matar shi.
Zatai magana liman ya tareta da fadin watau hjy shi musulunci yazo da sauki ga wanda ya fahince shi.
Diya da kike gani amana ne a garemu iyayye haka ma diyan suma rashin biyayya ga iyayye wani babban gibine garesu a wurin Allah.
Abindana fahinta a nan shine yaran ki kaf dama abokan zaman ki duk hakkuri suke da ke kenan.
Shin hjy baki tunanen mutuwa yana iya riskan bawan shi a kowani lokaci a cikin ko wani irin hali.
Hjy me kika tanadarwa zuwan wanan lokacin yanzu ace mutanen da Allah ya halatta zaman ki dasu duk korafin su dayane a kanki babu dadin ji haka ?.
Malam liman baka san komai ba a nan kiran ka akayi kazo kayi sulhu a gidan nan don haka kayi abinda ya kawo ka kawuce.
Assha magana ya kare jummai Allah ya shiryeki ku tashi mu tafi banga fanin zaman mu wurin nan ba kawu ku barta dantane idan taga dama yau ki tsine masa dan ki daine.
Bana wani ba zaki iya duk abinda kikaga dama gareshi saidai ki sani kamar yadda malam Liman ya fada su diya amana a wurin mu.
Mu dai mun sheda danki yayi maki biyayya yadda ake so don ga shedun haka ya samu habbib yace kwarai kawu.
Don ni shedane duk wata yana bata sama da dari biyar na bukatan ta wanda ni din nan in nayi wuta da kyat zata iya samun dubu hamsin zuwa kasa dashi a wuruna.
Lokacin hjy tace ina wuta ta saka habbib don tonon asirun da yai mata a bainar jama,a tana kokarin tsine mai yana fasin babu abinda zai same ni da yardan Allah mama don nafadi gaskiya Allah shi yace mu fadeta komai dacin ta ai.
Ina ga yanzu ya dace a bar wanan zancen tunda akai ga manufa shi umar zai dauki matarshi su tafi shike nan magana ta kare a nan.
Ke kuma hjy Allah ya huci zuciyar ki inji malam liman ya katse maganan yana tashi zaune.
Kuka Amma ta saka tana fadin Jummai ubangiji ya saka min a kanki ba zan taba yafe maki lalata min zuria da kikayi ba.
Ya umar yace kai haba Amma abin da da uwa yaji haushin maganan Amma kuma zuwa ga mahaifiyar shi.
Dole in fadi haka umar wanan bata da mutunci ko kadan bata san Annabi ya faku ba a zuciyar ta.
Umar tashi kuje kawu balarabe yace yana umurtan umar din sai yaya umar din ya juya wurin hjy yana fadin kiyi hakkuri mama da abinda ya faru ki yafe muna.
Yana fadin hakana ya mike yana kallona yana fadin tashi muje kaina na dukar kasa idona yana fitar da hawaye.
Ya duka inda sultana take barci a jikina ya dauke ta tashi kibi mijin ki Mamu tace min a hankali haka yasa na dago ido ina kallon ta ina hawaye tace jeki ubangiji Allah ya albarkaci auren ku da Albarka aka amsa da amin muka fice daga shiyan Amma.
Kuka nake wiwi a kofa muka samu hjy maryam zaune saman dan dakalin shigowa wurin Amma ta zauna.
Ki bar kuka Fatima haka yafi maki zaman gida kai kuma sai ka kara hakkuri da mahaifiyar ku kundai saba da halin hjy.
Mun gode yace mata muka wuce ta bimu da kallo ita tasan abinda take tunane a zucuyanta lokacin.
Part din mamu na nufa yace ina zakije kuma abu zan dauka na bashi amsa yace ki barshi ko menene har gobe zan dawo in daukar maki dare yayi yanzu banson tukin dare garin nan.
Wayata zan dauko na bashi amsa a cikin kuka barshi nace maki haka yasa dole na bar wayan muka fice daga gidan.
Tun kan mu isa wurin motar yasa remote ya bude motar bude min gaba yayi na zauna ya dora min sultana a jikina ya zagaya ya shiga motar.
Har lokacin kuka nakeyi ban bari ba cikin natsuwa naji muryan shi yana fadin ina son ki Fatima kin sani ba zan iya rabuwa dake yadda mama take nufin inyi ba.
Ban zabe ki na bar mama don in bata mata rai ba na zabi zama da kene don hakan shine alheri a garemu baki daya har maman da bata gane ba a yanzu.
Don na gane zafi da ciwon rashin ki a tare da mu yanzu don nagane rasa ki a tare dani wani matsala zai haifar muna nan gaba dani da yarana.
Ban taba zato ko tsanmanin zaki zabi mahaifiyar ki ki barni ba koda yake kinyi hakan a cikin hikima da basira irin naki kike gani hakan kuma da kikayi baisa naji wani abu game da ke bs don ni namiji ne nafiki tunane da hangen nisa saboda nasan haka kawai zan muna in samo muna kwanciyar hankali a tare damu.
Don haka ki share hawayen nan na banza da kike zubarwa kada ki shiga min gida da hawaye tunda ba satoki nayi ba wallahi.
Jin abinda ya fada yasa na dago kai na dan kalleshi ba tare da ya juyo inda nake ba yace eh abinda na bada ke nan kika ji.
Wai kin manta cewa nidin nan namijine da nake dagaro da neman na kaina kuma ina fatan in gama lafiya da iyayyena .
Kin san ina son ki Zahra barazanan mama gare mu na kara min wata mata ma kada ya daga maki hankali ko ki rike haka a ranki.
Ni nayi maki alkawarin babu wata mace ko wani mutum insha Allahu da zai iya juyani daga gareki.
Zahra nasan kin min abinda ba kowace mace zata iya hakkuri da jure irin abinda nayi maki a baya ta iya matashi a lokaci guda.
Na raba ki da iyayyen ki da kowa naki alokacin da kikafi bukatan su a tare da ke ban dubi maraicin ki ba lokacin gangan shedan da zugin mama yana min aiki a kaina.
Na gwadaki da dama baki san da hakan ba a lokacin na hanaki hurda da mutane kinyi rayuwa ke kadai a haka kika hakkura da hukuncina har yau .
Yanzun kuma a shirye nake da in gwadawa duniya ke din mace ce data cancanci a nuna a cikin mata muddin ina raye a duniyan ba wani wanda ya isa ya sha gaban ki a gurina ke kin sani bawai da baki nake fadi ba.
Don me mun kai ga mafita zaki nuna min baki bukatana a tare dake don yanzun kin fahinci ina bukatan zama a tare dake da mallakan wanan jikin naki kike son nuna min din ba kya sona a yanzu ko kuma baki bukatan zama dani.
Dago kai nayi ina kallin shi a lokacin don jin abinda yake fada min.
Azuciyana kawai nake iya bashi amsa da ina amfanin zama da mutumin da mahaifiyar ka bata son ka tare dashi.
Ina amfanin zaman mu a tare mahaifiyata tana cikin bakin ciki da gori a wurin taka mahaifiyar a kullun don nasan ba fasawa hjyn su zatayi ba kan abinda takewa mamu.
Don may ba zanyi kuka ba na bar mahaifiyata a cikin kunci da bakin ciki babu ko sallaman daya dace a tsakanin mu.
Goran ruwan dake gefe ya miko min tare da fadin karbi ruwan nan ki sha ko zakiji sanyi a zuciyar ki.
Saiki wanke wanan fuskan naki da kika bata kada ki shiga gida haka ki dagawa yara hankali don nasan idon su biyu yanzu suna jiran isowan mune kawai.
Karban ruwan nayi kamar yadda ya umurceni a daidai lokacin da yake horn a bude masa get ya bude mota yana fadin wanke fuskan ki kafin mu shiga.
A cikin lalashi yake magana dani a lokacin kamar karamar yarinya ana lalashin ta.
Duk yaga maigadin ya bude get bai shiga gidan da mota ba saida yaji na sauke ajiyan zuciya yaja mota muka karasa ciki.
Kamar yadda yace mun samu yaran a falo har yan aikina a zaune falon jin horn din mu maria ta fito da sauri tana muna sannu da zuwa.
Tana kokarin karban Sultana dake barci a jikina yace ta tafi zai shigo da ita .
Mun shiga suna min sannu da zuwa yaran suka taso da gudu suka rugumay ni haka yasa na rage tsawona daidai su na rugumay su a jiki.
Saida yai masu magana su barni in je daki suka sake nina mike amma basu yarda sun barni ba tare dasu mukaje dakin nawa.
Nan ma basu barni ba don sun baibaye ni sun hanani sukuni da tambayoyin su a lokacin.
Da kyat na samu na mike naje yayi alwala kafin na fito na tayar da sallah na dade zaune ina ta addua a wurin yayin da yaran ke wasa su uku saman gadona sai abin ya kara bani tausayin kan mu dana yaran ya kara kamani a wurin .
Sallaman da akayi daga kofanane yasa na dago kai ina kallin kofan inga mai shigowa dakin nawa.
Tani ce mai abinci tana tafe dauke da katon tire da kuloli a cikin sa sai da ta aje ra gayar dani take fadin hjy barka da zuwa ya mutanen gida.
Ga abunci Alh yace a kawo maki nan dakin ki ta fada nace Tani gida lafiya na gode yaya bayan rabo ?
Tace hjy munyi kewar ku sosai wallahi kullun sai tambaya nake yaushe zaku dawo ne ashema wai kina garin nan ni ban sani ba aida nazo na gaida ke.
Nace ba komai ai nagode ko yanzu shine yayi sallama da alama wanka yayi a lokacin ganin Tani gurfane a gabana ya juya wurin yaran yana magana dasu Tani tayi saurin mikewa ta fita daga dakin.
Ki ci abinci ki watsa ruwa ki kwanta ki huta don idan ba kwanciya wa yan sukaga kinyi ba yau ba zasu barki ki hutaba da cewa yaran dake ta murnan dawowana gidan.
Ban jin cin abincin don bakina bai min dandano na bashi amsa amma kuma kinsan ba zaki kwanta haka ba dai da yunwa a ciki.
Dan ya mutse fuska nayi ina fadin banjin cin komai yanzu ne shiyasa ya kalleni ya gyada kai yace sai ki tashi ki watsa ruwa don kin san dai ba zasu je gun maria ba yau suna ganin kamar zaki iya barin sune ki koma inda kika fito.
Na kalleshi cikin natsuwa nace nifa ina ganin bawai hjy ta yarda da dawowa na gidan nan bane ?
Yace nasan da hakan nima sai dai meye matsalan ki ke ina yanzu rikicin a tsakanin nida itane kuma.
Amma yaya kasan ba zanso ace sabodani ka samu matsala da mahaifiyar ka ba gaskiya don nima ba zanyi fatan diyan nan suyi muna haka ba watarana.
Zahra mama uwatace na fiki sanin halin ta ciki da waje kamar yunwar cikina don haka ki kyalemu kawai muyi abin mu babu ruwan ki ya yanzu a maganan mu.
Ki tashi kije kiyi wanka ki samu ki huta hakana ya juya ya fita daga dakin na sauke ajiyan zuciya.
Ya dan jima da fita kafin in mike na shiga na watsa ma jikina ruwa na fito na shirya cikin dogon rigan barci gyarawa yara kwanciya nayi kafin in hau gadon tsakiyan su na kwanta ina sauke ajiyan zuciya a hankali.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button