NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:16 – ????????????: Washe gari ban fito da wuri ba saida rana ya fito ko ina ya haska sosai har ranan ta dan fara zafi don ban san lokacin da maria ta shigo ta kwashi yaran tafi dasu daga dakin ba.
Ko yanzun ma yunwa dana tashi dashi a gigice yasa na fito daga dakin zuwa falo don in samu abin da naci.
Wurin dining na nufa kai tsaye ban kula da mutanen a falon ba a lokacin na fara bubude kayan abincin dana samu a jera saman dining din.
Fersun kifi ne anyi mai yanka mai kyau sai kamshin kayan yaji ke tashi a cikin sa na kara bude kula na biyu wanda ke dauke da irish soyayyen karamin kulan na bude wanda na zata kwaine sai naga source din kabeji ne da anty da za,a ci da soyayyen dankalin sai kayan tea a gefe guda da ruwan sha dana tea a flask.
Zaune nakai ina jawo dankalin na dan zuba kadan tare da zuba source din da zanci dashi ruwa na jawo na daureye hannayena.
Ina shirin kai abincin a bakina naji muryan Yaya Aliyu yana fadin uwar gida ina kwana a lokacin .
Da sauri na juya inda nake jin muryan nasa sai ganin su nayi su uku a tare lokacin guda dan nauyi da kunya ne ya kamani a wurin haka yasa na taso zuwa gare su don in gaida su.
Ki koma kici abincin ki tukun ki gama yaya yace min don nasan dama da yunwa zaki tashi tunda jiya bakici komai ba kika kwanta yau kuma kinkai har wanan lokaci kina barci.
Ki daina wasa da cin abunci Fatima yaya habbib yake fadin haka ba tare da ya dago kai ya kalli inda nake tsaye ba.
Ban yarda na koma na zauna ba saida na karaso inda suke na gaida su a cikin ladabi babu zancen wai kannen miji a wurina har yaya Aliyu da kan dan jani da wasa wani lokacin.
Bayan su amsa min ne tare da tambayana yaya gida na amsa da lafiya na daga zan tashi naji yaya habbib na fadin amm, fatima ina son ki kara da hakkuri a zuciyar ki.
Kada ki dauki wanan abin da daya faru tsakanin ku da mama wani abinda zaki rike a zuciyar ki .
Mama dai uwa take a wajen ki kuma mahaifiya ga mijin ki don haka nake son kada ki dauki wanan kiyayyan da take nuna maki a matsayin wani abu cikin zuciyar ki har ki riketa a rai nan gaba.
Da sauri nace yaya ban fatan hakan ya darsu a zuciyana nima don mama uwa take gareni na sani don yau mama tace bata sona bawai hakan yana nufin in fasa mata biyayya a rauwana a matsayin ta na uwa a gareni ba.
Zan dai gujewa duk wani abinda zai iya haddasa muna fitina a tsakanin mu nan gaba insha Allahu.
Don Allah ku kara hakkuri da taimakon ku zamu samu mu rabu lafiya da iyayyen mu.
Don jiya bayan tafiyan ku abin yaso ya baci tsakanin mama da daddy mun Allah ne ya gyara magabatan su suna gurin.
Allah ya tsare nace ina kokarin mikewa don barin wurin zuwa wurin abincina dana rigana zuba kada yai sanyi.
Zam nayi na basu baya don akwai tazara a tsakanin mu sosai da inda suke zaune din don haka ba lalaine inji abinda suke tataunawa ba akai.
Har na gama na shige daki suna wurin a nan na barsu na koma daki ina tunanen maganan da mukayi da yaya habbib din don nasan ba karya ya fada sai mun basu taimako wurin shanye duk wani abin da hjynsu take nuna muna zasu zauna lafiya da ita.
Har wani barcin ya kara daukana ban sani ba sai da sultana ta tayar dani daga barcin shigowan ta dakin nawa tana kuka na tashi.
Falo muka koma muka zauna da yaran suna kallo nima dan kallon catoon din nakeyi jefi jefi a lokacin sai dai raina yana tunanen ko yaya ya fitane a lokacin.
Sallaman Amma ne tare da murja ya dauki hankalin mu zuwa falon tana shigowa da sallama tare da fadin shi daga anbashi matar shi sai kawai ya dauke muna ita ya gudu.
Dariya na danyi ina ce mata ya sani ko ki kawo shawaran da bai gamsheshi ba a wurin .
Aini jiya yar nan kun barni da mamaki danaji ance ko sashen uwarki bai bari kun shiga ba ya wuce dake.
Nace uhumm Amma ni yaya na iya da rigiman yaya ko wayana fa a can na barshi ban dauko ba yace da safe zai sa a kawo min su.
Ai ni hakan da yayi naji dadi sosai a ruwa don kafin ai wani magana ace a kiraku har kun tada mota kun bar gidan daba haka ba jiya Allah kadai zai hana auren dayan ku tsakanin keda jummai bai mutu ba sai Allah ya gyara kawai hakan bai faru ba.
Da sauri nace subbahanallahi har abin yakai ga haka Amma ta girgiza kai tare da fadin ban taba tunanen akwai mace shu,uma irin jummai ba don dai karshe zage malam Liman da kawun nata tayi suka tashi da kunyar su nina hana yaro nan ya saketa a daren jiya.
Allah ya sauwaka mata a gaban kowa take aiban ta maimuna da munanan kalamai na ba gaira ba dalilin ban san a ina ta samu wanan banzan labarin ba haka ?
Amma wani gori yana zama alheri ga bawa muddin dai baka rama mai zafi ba irin wanda akaima sai Allah yai ma sakaya da abinda baka zata ba a rayuwan ka.
Haka tace tare da fadin ina roko Allah ya baiyana muna uwar yarinyar nan kowa ya huta duk nice naja mata wanan gori da na barta a lokacin tabi uwar ta da hakan yafi sauki gaba daya a gare mu.
Amma bar fadin hakan rabon mu nida su fauziya ne ya tsayar da ita kasan nan har aka samay mu insha Allahu indai tana raye Allah zai baiyana muna ita bada dadewan nan ba Amma.
Yanzu ina mijin naki yake ta tambaya tana kallon kofan dakin shi da idanu.
Nace sun fita tare da yan uwan shi ina barci ban san fitar su ba jiya yaron nan habbibu yaci min goro a rayuwana don tsab ya fadawa uwar gaskiya duk ko da dacin ta.
Hjy bata da masu fada mata gaskiya a rayuwan ta duk yan uwanta kara izata sukeyi ba masu lurar da ita hanyan daidai murja ta fada.
An gama abinci aka kawo muna nan munci mun sha muna hira akai sallah muka tashi zuwa sallah.
Bamu dade da fitowa daga sallah ba yaya ya dawo gidan yana shigowa sukai arba da kakan tashi yace may kikazo yi min gida kuma jiya jiya da dawowa da matana ko kin dawo ku kara dauke min itane kuma ?
Ja,iri tunda na gama aikina ko dole kace min hakan daba don dabaran dana koya ma ba aida yanzu matar taka tana dakin uwarta zaune su basu damu da zaman nata ba hakana.
Ya kai zaune a saman kujera daya da Amma yana fadin Amma ni abin yana daure mun kai sosai wallahi na rasa gano inda mama ta dosa haka ?
Aure take son ka kara sadauki idan ba auren nan ka karaba ba zaku taba zaman lafiya a yanzu da mahaifiyar ka ba.
Da sauri na dago kaina na dan saci kallin shi don jin amsan da zai bata a lokacin .
Karab idanuwan mu suka hade da juna ya dan sakar min malalacin murmushin shi daba kowa ke iya gane hakan ba sai wanda ya sanshi sosai zai gane hakan .
Amma na fada mata matana biyu sun isheni a rayuwana ba zan iya kara aure a yanzu ba bandai sanar ma nan gaba don mai rai baya debe tsamani a rayuwa tunda ni din namijine.
Kwarai kuwa Amma ta bashi amsa tare da fadin ita waccan matar taka kafiran dauka take baku da aure da ita yanzu ai.
Haka take gani shima ya fada yana mikewa tare da fadin Amma zan dan shiga in watsa ruwa tsohuwar tace har yanzu dai wanan dabi,an yana nan maka sadauki na wanka akai akai.
Yana shiga na kalli Amma ina fadin Amma naga kamar kema yanzu kina bashi shawaran ya kara wanan auren ne ko .
Abinda uwarshi ke so ke nan A ruwa indai zata barshi ya zauna lafiya aisai yayi nagani.
Nace shi zai zauna lafiya kan ammani nasan ina kofan fita ga niyar hajiya yadda take kuma sakawa a ranta.
Zata iya amma ni hanka yanzu baya damuna tunda har ba ta iya rabaku a yanzu ba hakan ya nuna ko nan gaba ba zata iya ba.
Amma idan ya fito ina son ki mashi zancen zuwa na bauchi kwanan nan don Allah murmushi tayi kafin tace kin masa magana yace ba zaki bane.
Amma ko nayi mai ban samun wani amsa mai dadi a gurin shi kullun sai yawo yake min da hankali Amma hankalina yana gun manjo karfin hali kawai nake ban nuna damuwa a kan hakan.
Ki gwada mai magana kafin ku tafi idan zai bari saiki tafi don dai ba zaki shigo kasan nan ace harkin koma baki lekasu kinga lafiyan su ba, suma suga yaran nan don basu sansu ba.
Bai bar Amma ta koma gida ba saida dare ya mayar dasu gida ita da murja kafin ya dawo nayi wanka na kwanta don ya tsaya gaisawa da mutanen gidan duk da dai ya samu hjyn su a cikin fushi sosai har lokacin dashi da yan uwan shi.
Dakin ya shigo ya same mu a kwance tare da yaran suna wasa ya samu bakin gado ya zauna yana fadin yau ma wa yan nan a nan zasu kwana ke nan ko ?
Nace ai in sun kwana nan ba laifin sukayi ba tunda suna kewanane yace amma nima kin sa ina da bukatan ki a kusa dani ko ?
Ba tare dana dago kai ba na kalleshi nace gara ka saba da hakan tun yanzu ai zaifi ma sauki nan gaba.
Wani sabone banyi ba da rashin ki a kusa dani yanzu bayan wata biyun da kikayi ba tare dani ba nace nan gaba idan kayi aure zaka iya yin fiye da hakan ma ba bakon abu bane ai ga maza yin hakan.
Yace may kike nufi da hakan nace kaida zaka kara auren yar uwanka ina zamu samu kulawan ka kuma lokacin ?
Naki tunanen ke nan kan hakan ban taba tunanen zaki iya wanan tunanen haka ba a kaina.
Kai ba namiji bane daba zan tuna haka gareka ba yaya kaifa da bakin ka fadin hakan dazu gaban Amma.
Yace shine kika rike a rai har yanzu ai gaskiya na fada ni din namijine kin sani niko na sani don da wanan kalamin kayi winning din anty merry ai.
Yace oh realy nace kwarai kuwa don ina da labarin komai ai ashe kinyi nisa ne ban sani ba ya fada yana mikewa tsaye tare da dan ja min kafana sai sultana tace mai daddy tana dariya.
Ya kada kai ya wuce yana mata bye bye da hannu tana mayar mai da martani sauran hankalin su yana wurin wayana da suke game dashi.
Tsab na shirya bayan yaran sunyi barci na same shi a daki zaune yake saman kujera ya tasa laptop din shi a gaban shi yana aiki dashi nayi sallama daga kofa ina dauke da flask din ruwan zafin dana dauko mashi.
Don wanan kullun ne sai ya sha ruwan zafi kafin ya kwanta barci har ina tunanen lokacin da ban tare dasu ko yaya yakeyi da wanan halin nasa na baude gashi har yanzu bai sakewa maria fuska ko kadan.
Ranan ba zan iya bayanin gamuwan mu da yaya ba don an dade ba hadu ba mun nunawa junan mu kulawa da kewan juna a tare damu.
Ban mashi maganan tafiya ta bauchi ba sai washe gari bayan mun karya ne nake tambayan shi yaushe ne zan tafi inga mutanen gidan mu.
Bai ban amsa ba haka ya gama abinda yake har abokin shi Nasir yazo suka fita sai lokacin na samu sukunin kiran mamu a wayata data kwana tana caji lake.
Bayan mun gaisa ne take tabayana ba dai wani matsala ko nace ba komai mamu aikin san halin shi ko abu yana damun sa baya fada.
Sai dai nasan akwai damuwa sosai a tare dashi don jiya ya dawo naga damuwa a tare dashi sosai.
Sa,an mu daya sayadi yana sonki tsakanin shi da Allah har zuciyar shi da kuma yaran nan da kika haifar mashi karin abin ke nan.
Mamu idan ma bai ra,ayina ni hakan bai dame ni ba wallahi tunda baka ba namiji amana ga baki daya karshe ke mace ce zaki kwana a ciki.
Wanan magana ya fita a bakin ki daga yau kiso mijin ki yadda yake kaunar ki shima hakan zai jawo yarda da amincewa a tsakanin ku.
Nan har take ban labarin irin cin mutunci da gorin da hjy tayi mata a gaban bainan jama akan wai don kawai kwadayin arziki aka likewa danta da mahaifin shi.
Mamu ina fada maki sai hjy tayi data sanin fadin kalaman ta gareki wata rana in Allah ya yarda.
Mun dade muna waya take kara tambayana matar bata kirani ba nace bata kiraba har lokacin .
Bayan yaya ya dawone yake fada min akwai aikin da zaiyi a kasan nan wanda hakan zai daukeshi lokaci mai tsawo a kasan nan.
Shi kuma ba zaiso ace na haihu a nan ba dole in koma nida yara don yana son zasu fara karatu da mun koma din.
Ba damuwa na bashi amsa zan koma don ci gaban yarana nima sai in samu inci gaba da karatuna lokaci.
Yace shima yayi min tunanen hakan sai dai bai sani ba ko banda ra,ayin yin hakan yasa ya kyaleni don baiji na masa magana ba.
Bayan kamar kwa biyar da dawowana ina kitchen tare damasu aiki don nakan bushi iska in shiga gurin su muyi aiki a tare duk da yaya baison hakan yace meye amfanin mai abuncin daya dauko min wace keda takarda a kan girki.
Mace bata cika mace saita hada da aikin gidan ta da kanta amsan da nake bashi ke nan idan yana fada sai yayi shiru.
Mummy your phone is ringing Abdul yake fada min yana miko min wayan a lokacin na karba da sauri saidai bakuwar lambace aka kirani dashi a lokacin na wani kasan.
Na dauka ina sallama yare naji anayi kafin a amsa min da sallama kuma ana fadin nice Fatima bayan mun gaisa nace eh a cikin harshen turanci ake magana.
Nace nice waye a layin zaki magana da mahaifiyar muce aka bani amsa nace ok wani murya naji ana sallama dashi na amsa.
Da hausa take fadin an ban layin kine don akwai tambayoyin da nake son zan maki nace Allah yasa na sani na bata amsa.
Hausan ya hade da harshen su ba fita yake sosai ba a lokacin saidai ina gane mai take fada da nawa hausan da nima ake fadin wai hausana ya canza yanzu.
Menene sunan mahaifiyar ki ta tambayeni kai tsaye na bata amsa da maimuna mahaufin ta fa nace Adamu.
Yana da yar uwa mace ta tambayeni nace eh muna ce mata Amma kakarmu ke nan wace ta rike mahaifiyata bayan wucewar mahaifiyar ta don na fara fahintar inda tambayan ya dosa a lokacin.
Her realy name please ta fada a cikin harshen turaci nace mata Amamatan sai naji tayi kabbara har sau uku ta kashe wayan idan ba kunnena ya rudeni ba zan iya cewa harda guda irin na larabawa naji kafin kashe wayan.
Zaku gama ku kawo kan ku na fada ina aje waya don ba zan yarda mamu ta bisu ba sai dai su su kawo kansu gare ta badan komai nake son haka ba don hjyn su yaya kawai nakeson haka ya kasance din.
Ranan haka suka wuni kirana suna min tambayoyi muryoyi daban daban ina basu amsa dake sasu nishadi da alama zancen yana masu dadin ji don kowa nason ya tabbatar da hakan a cikin su.
Nayi masu kwatancen komai da yadda zasu iya kawo kansu garemu idan sunzo garin kano din har address din gidan duk na basu.
Washe gari na shirya naje gida da dakin hjyn su yaya na fara saidai ban sameta gida ba ta fita a lokacin na fito na shiga na gaida hjy maryam dake son jana da hiran abinda ya faru ranan.
Ban yarda na bata wani amsa ba saidai na bata amsa mai kama da sako nace shi mutum ai ba a debe rai gare shi idan ba ya mutu ba don wata rana wanda kake gani banza shine wani abu gare ka.
Na barta na fito zuwa wurin Amma mun dade muna hira kafin in shiga wurin mamu don kawu bai gida a lokacin ranan ya fita kasuwa.
Mun dan dade muna hira kafin ince mamu gobe zaki kwashe kujerun nan a saka maki sabbi da duk wani abinda baida amfani a part din nan don zakiyi baki cikin kwanan nan ba zanso suzo su samu wurinki a haka ba.
Sayadi da gaskiya zasu zo na kwashe duk yadda mukayi dasu na fada mata addua naji tanayi a lokacin kafin in mike ina duban abinda ya dace ace an kawar a lokacin.
Na fita tare da murja zuwa wani shagon dake decoration din daki mukayi cinikin wasu set har da gado na gani mai kyau na hada dashi da labulaye masu kyau mukai jinga na biya su yaran shangon suka biyomu da kayan a take har gidan.
Lokacin marance yayi saidai hakan bai hanasu aikin su ba kafun dan wani lokaci har sun hada komai don nan na barsu suna aikin don kiran me nake a gida har wanan lokaci da yaya ke min a waya.
Washe gari muna barcin safe sai ga kiran hjyn su ya tayar damu daga barci inda na fahinci zancen take mai lokacin da naji yace kaya kuma mama wallahi ban san zancen da kike min ba yana kallona.
Tashi nayi na shiga ban daki a lokacin ban fito ba sai da nayi wanka na tsane jikina na fito ina goge ruwan a kaina yana zaune a bakin gado naji yace min.
Wani gyara kikaje gida jiya kika sa akawai maman twins a part din ta ne ?
Nace ina kallin shi cikin rashin tsoro ko darr din shi gyaran part din kawai nasa ayi mata don zatayi baki kwana nan .
Ba zan so azo a samu maxaunin ta a haka ba yasa nayi wanan shawaran na gyara mata part din don yanzu kawu baida karfin hakan garesu ita kuma kasa ba aiki takeyi ba ai.
Ya danyi dan shi kafin yace mai yasa baki fada min ba kafin ki aiwatar da hakan don gashi yanzu kin ja min magana wurin mama aida kin fada min sai in saka ai masu gyaran yadda ya dace ga baki dayan su.
Kayi hakkuri banyi tunanen yin hakan ba don naga hakan kamar ba komai bane shiyasa.
Baiyi magana ba illa idon daya tsura min na dan lokaci kafin ya mike ya shiga bandaki hakan ya bani daman fita daga dakin nashi na kuma nawa part din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button