SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:16 – ????????????: Bamu bar gidan Atika ba sai dare muka koma gida mun dawo mun samu abincin da babbafa ya saka ai muna yana jiran mu a dakin manjo.
Mukace mun koshi ba zamuci ba munci abinci a gidan Atika sai yaran gidan, ana fita dashi yaran shi suka zauna sukaci .
A daidai lokacin Umma lami ta dawo daga unguwar da ta fita tun da magariba tana arba da yaran zaune suna cin abincin ta doka wani uban salati lokaci daya.
Hankalin kowa ya koma gareta suna mamakin ta nan ta fara fada dasu tana fadin abincin dana dafawa Fatima da yaran ta kuka zauna kuna ci shike nan.
Umma tace ba zasuci ba kada ya lalace ta fito muna dashi fada take wanda duk mai hankali zai fahinci akwai wani abu a kasa.
Jin sababin nata yayi yawa har muka gaji muka fito daga dakin manjo a lokacin.
Lami wanan fadan haka halan wani sheri kika karbo kika zubawa wanan yar marainiyar Allah da iyalin ta manjo ke tambayan umma Lami a hasale.
Ganin kowa yana kallon ta taci gaba da fadin wanan fada naki duk mai hankali yasan bana lafiya bane .
Gabana ne yayi wani irin mugun faduwa tsikan jikina ya tashi don sam wanan tunanen baizo min a raina ba da farko.
Tsohuwa wanan wani irin magana kikeyi haka kuma gaskiya na fada ina dai wanan abincin na yarnan ne.
Kuma tace akoshe suke yan uwanta su dauka suci kada ya lalace kinzo daga baya kina wanan fada anya lami ba wani sheri kikai niyar yiwa yarinyar nan ba kuwa Allah ya kamaki da hannun ki.
Ai dama bana abin kwarai a gidan nan sai a dauko sheri a sakawa mutum don kawai kiyayya.
Allah ya kyauta manjo tace tare da duban inda muke a tsaye cirko cirko tana fadin maji ma gani ita dai ramin karya kurarane dama sheri karene mai shi yake bi.
Har muka koma dakin mu jikina bai dawo daidai ba sai maganan manjo nake ji a kunnuwana lokacin da take tambayan umma lami kan abinda yasa take fada haka tana kumfan baki don kawai diyan ta sunci abincin data girka muna da rana.
Jikin kowa a cikin mu yayi sanyi a lokacin don haka muka nemi wuein kwanciyar mu muka kwanta saidai barci bai daukeni ba a lokacin sai zuwa dare sosai.
Don nayi iya tunanena banga laifin da nayiwa wa yan nan mutanen biyu ba a duniya watau umma da hjyn su yaya da suke nuna min kiyayya irin haka.
Yanzu da munci abincin wani abu ya samemu ko ya samu yaran mutane yaya zanyi da kakar su da mahaifin su nake nanatawa a raina.
Can barci ya dan figeni nake jin motsi sama sama a gidan tunda na bude idanuwana na kasa rufe su tun ana wanan motsin kadan kadan har abin yayi yawa sosai ina jiwo hayaniya.
Da kuka manjo ne ta mike tana fadin dama na san za a rina akwai abinda ke faruwa a gidan nan duk yadda akayi.
Nace ashe baki barci ba kina jin su manjo tace najisu ai kokarin tashi zaune takeyi tana fadin hakan.
Kofa ta nufa tana budewa zuwa waje inda na taso na mara mata baya muka fito tare bayan na saka hijabi a jikina.
Dan gidan umma lami ne dan matashi sanusi ke faman wulle wulle a kasa ciwon ciki ya turnike shi lokaci guda.
Salatin da manjo ta saka tana fadin dama nasan fadan nan Lami dazun ba a banza kikeyin shi ba.
Dama yar nan kika so ki kashe da yan uwanta da yaran ta ko me Baffa yace haba babba wanan wani magana ne haka kuma ?
Gatanan tsaye ka tambayeta ta baka amsa nan dai cikin fada fada take mayar mai da abinda ya faru.
Mutuwan tsaye babffa yayi a gurin tare da nazari a ranshi yace tabbas akwai kamshin gaskiya a maganan nan naki babba.
Ihun da Sanusi ya yanka ne lokaci guda yasa mukayi kanshi a gigice dukawa nayi ina kallon shi kafin in ce da sauri mama akwai manja a gidan nan a bani da sauri.
Da sauri mama ta wuce zuwa dauko manja zuwa lokacin har ya fara zubar da wani kumfa a bakin shi mai kauri.
Tana kawowa na bude bakin shi na dura mai manjan sosai a ciki kafin in ce madara fa akwai madaran ruwa a gidan nan a bani.
Akwashi yana nan cikin kayan shayin dana shigo dashi dazun yake cewa mama ta juya da sauri zuwa dakin shi.
Madaran na bashi sai kuma ga amai ya biyo baya nace Alhamdullahi yazo akaishi asibiti insha Allahu ba abinda zai same shi sai dai don Allah duk wanda yaci abincin nan a bashi manja da madara yasha.
Ruwa ruwa aka kwashe shi sai asibiti ranan umma tasha tsina da zagi wurin manjo da babffa .
Nikan ban bisu asibitin ba daki na koma mukayi zugun ni da murja kowa da abinda yake rayawa a zuciyar shi.
Can murja ta nisa tana fadin Fatima kina tare da kariyan Allah wallahi duk sanda wani sheri yake tunkaroki sai ubangiji ya kareki daga gare shi.
Yau da badon Allah ya tsare mu ba baza,ayi wanan tunanen ba sai ace kwanan mu ne ya kare a nan ai.
Murja kin san plain din wanan matar idan anyi magana sai tace unguwar da muka fitane dai mukaci wani mugun abin don ba za a taba dora mata laifin ba.
Kiran sallah ne ya tayar damu daga zaman da mukayi son muna zaune mun kasa komawa mu kwanta barci.
Bayan mun idar muka ja kofa muka rufe barci sosai mukayi sai hayaniyar mutane dake shigowa ne ya tayar damu daga barcin.
Ban bude kofan dakin manjo ba don kada yarana su fita tsakar gida muna dakin don ban bar kowa a cikin mu ya fito waje ba saboda tsaro duk da nasan Allah yana tare damu.
Bugun kofan da akeyi tare da sallamane yasa na mike na bude kofan umman Atikace take buga kofan .
Ina budewa tana fadin Fatima barka da arziki ashe wanan matar tana nan a bakan ta akanki har yanzu.
Umma na rasa mena tare wa umma take bina da wanan nufin haka ko yaushe idan nazo garin nan.
Baki mata komai ba Fatima illa hassada da kyashine irin na dan adam idan bashi ba ya kamata yanzu ace matar nan ta saduda da wanan abun a kanki.
Muna tsaka da hira wayana yayi kara na dauka ina dubawa wanan matar daine ta sudan take kirana inda take kara tambayana address din dana basu na kara maimaita mata shi yadda ya dace.
Murja na dan kalla ina fadin ina ganin yau zamu koma kano don muna da baki a gida zuwa gobe ko jibi.
Da sauri murja tace nima tun dazun naso in sheda maki haka mu koma gida kawai zai fi don wanan abin ya firgitani wallahi.
Umma dake zaune tana jin mu tayi saurin cewa a, a kada kuyi haka don Baffan ki bazai ji dadi ba a ransa.
Ku bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu sai kuyi sammako ku tafi abin ku shike nan nace ba tare da nuna wani damuwa to umma.
A gidan ta mukai wanka muka shirya don ban yarda yarana su matsa kusa dani ba a nan Atika ta same mu gidan nasu ranan dai wuni mukayi muna magana kan abu daya a gidan.
Sai dare sosai muka dawo dakin manjo don mu kwanta tare da shirya kayan mu ba wanda yasan cewa zamu koma a washe gari sai umman Atika da Atika din suka sani.
Washe gari tunda nayi sallah na fito dakin babffa na nufa nayi sallama daga bayana ya amsa min yana dawowa daga masalaci.
Har kasa nakai ina mashi ina kwana yana amsa min yanayin shi kawai ya nuna yana cikin damuwa sosai a lokacin.
Na dan kara kwantar da murya ina fadin baffa yau muke son mu koma din an bugo min waya zamuyi baki daga kasan waje a yau din nan ko gobe .
Yace Fatima kada ince wanan abinda ya farune ya daga maki hankali kike son komawa kano yau.
Da sauri nace a, a baffa wallahi dalilin ke nan na fadama idan bado baki ba ai kwanakin daya bani zancika a nan.
Wuri kawo ya samu ya dan tsuguna yana fadin Fatima bansan irin kalamin da zanyi maki amfani dashi ba wurin baki hakkurin abinda ya faru.
Da sauri nace baffa akan me zaka bani hakkuri akan laifin da bakai ka aikata min shi ba ya nisa tare da fadin ba zanso ki rike wanan zancen a ranki har kizo ki gujeni Fatima daga karshe.
Idan kin muna haka baki dauki sakkayan da Allah yai maki ba ke nan a zuciyar ki da wanan tunane na kwana a raina Fatima ina tsoron sherin Lami ya rabamu dake nan gaba.
Baffa idan banzo wurin ka ba wa nake dasu nan duniya da zan nuna a matsayin yanuwana na jini idan baku ba ko kadan wanan tunanen baizo min a raina ba baffa na bashi amsa.
Allsh yai maki albarka Fatima dake da iyalan ki banda abinda zan baki sai addu,a a tsakanina dake Fatima.
Saidai ina kara rokon ki da ku boye maganan nan ga mahaifiyarki don idan taji maganan ranta ba zaiyi dadi ba ina kunyar kawun ki Fatima da mijin ki na rasa wani irin hukunci ya dace in daukawa Lami a gidan nan da raina zai min dan sanyi ba.
Baffa tunda Allah ya mayar mata da abinta ta gani ka barta da Allah Alhamdulillahi dai tunda ba wanda wanan abin yaiwa sanadi a cikin su.
Mun dan dauki lokaci tare da baffa har rana ya hasaka muna wurin tun inatsugune har nakai ga samun wuri na zauna yana koro min irin hakkurin zama da umma lami da yakeyi.
Nace a karshe zamu biya wurin Addah mu gaida ita kafin mu koma gida yayi murna da jin hakan.
Mun shirya tafiya manjo tana asibiti ita da su yaya hashimu suna jinyar Sanusi bata san da zancen tafiyan mu a ranan ba saida na tura driver ya dauko ta.
Tana zuwa ta saka muna kuka wai umma lami ta rabata damu ke nan kan abinda tayi muna.
Hakuri na bata tare da kebewa gefe da ita nayi mata bayanin komai yadda zata fahinta dani akan ba saboda wanan maganan zan tafi ba a ranan.
Mun rabu kamar kada in rabu da yan uwana a lokacin musanman kaka ta mafi soyuwa a gare ni na tafi ina tausayawa halin rayuwar da na barta a cikin shi.
Saida muka biya kauyen da Addah take muka dan dade kafin mu kama hanyar kano sai dare muka isa kano din.
Mun samu baya gari ya tafi Abuja a nan muka kwana tare dasu murja gidana sai washe gari nake warning din su kan su boye min sirin gidan mu kan abinda ya faru kada su fadawa kowa wanan zancen.
Sai dana dan hada masu tsaraba da zasu kai gida cikin dan abinda muka samo da wanda muka sayo a hanya na kaisu gida a muna sannu da zuwa .
Na shiga wurin mamu mun dan dade muna hiran gida da ita kafin in fito in koma gida duk da yamma ya soma ina sallah la,asar na kwanta a wurin.
Maria ce ta shigo min da jakkata dana bari a falo da wayana a ciki yana ringing na dauka nomban Baffana ne daya bani ya kirani dashi.
Naji nauyi da kunyar rashin kiranshi da banyi har ya kai ga kirana a wanan lokacin.
Na dauki wayan da sallama na fara gaida shi yace mun iso lafiya lafiya Alhamdullahi ya jikin sanusi ?
Sanusi sai dai muyi hakkuri Allah ya kira abinsa jiya da dare ya kare yanzu ma na kirakine ki kira babba ki mata magana kin san mutumin tane tana nan ta tayar da hankalin ta mun rasa gane kanta.
Banji sauran karashin maganan da kawu yake min ba don tashin hankalin dana shiga a lokacin ya wuce musali.
Gaisuwa nayiwa Babffa mun dade muna magana kan mutuwan Sanusi inda jikina yayi sanyi sosai wanan maganan dolene in fadawa mamu shi babu zancen boyewa a nan.
Gani ni kadai a gidan haka yasa na fito falo muka zauna da su maria ana hira har zuwa lokacin da akai sallah magariba duk bani cikin yanayin dadin rai a lokacin.
Sallah nayi na shiga daki nayi ban kara fitowa waje ba waya mukayi da yaya nake sheda mashi dawowan mu.
Yace yana hanya shima yanzu haka bai samu jirgi ba mota ya shigo zuwa gida shida Aliyu nayi masu Allah ya kawo su lafiya.
Haka yasa danayi sallah isha,i na fito don tanadar mai abinda zaici idan ya isa na koma dakin shi don nice mai gyara na kara gyara ko ina na fito bayan komai ya kammalu na shiga nayi wanka na dan kwanta.
Basu shigo garin ba sai goma da wani abu na dare suka iso gida ina kokarin daga sai gashi a dakin nawa hakan bai hanani mikewa ba ina taron shi da zuwa.
Ya rungume ni a jikin shi yana fadin wanan kara girma da kikeyi haka kamar kin kara dauko biyu a wanan karon ?
Da sauri na daga daga jikin shi ina fadin haba yaya baka tausaya min kake min wanan fatan ina zan kaisu yanzu idan na dauko su.
Ina tausayin ki yace yana kallon cikin nawa tare da ci gaba da fadin wanan cikin duk yafi sauran cikin da kikayi a baya girma.
Nace kasan yanzu tunbina ya kara budewa abincin can kuma ba mai nauyi bane irin wanda nake ci yanzu a nan don yanzu tuwo shine abincina tunda na samu cikin nan.
Tare muka fito zuwa dakin shi saida naga ya shiga wanka na fito zuwa falo lokacin ne maria ke fada min tsaraban da yaya yazo dashi nace ba matsala zan gani da safe idan Allah ya kaimu.
Saida yaci abinci nake fada mai zancen rasuwan da akayi a bayan mu baiji dadin jin hakan ba yai min gaisuwa tare da fadin da safe zai kira baffa su gaisa.
A lokacin ne kuma nake mai godiyan irin dawainiyar dana samu yayiwa iyayyena a gidan mu hannu ya daga min alaman in bar zancen kawai.
Washe gari tunda na tashi da safe na kara kiran Baffa nayi mai gaisuwa nace ina son akaiwa manjo wayan an dan dauki lokaci kafin akai mata waya ta karba tana fadin.
A ruwa da nasan Sanusi ba zai rayuba dana biki kin tafi garin ku dani a daidai lokacin yaya ya shigo dakin tana fadin A ruwa ke kin tafi sanusi kuma mai kula dani a madadin ki ya tafi ya barni yanzu.
Wa zai kula dani yanzu a gidan nan wanan yaron shine idona shine kafata yanzu kuma bashi.
Zama yayi a kusa dani yana sauraren mu tana fadin kizo ki daukeni tun basu karasani ba A ruwa idan baki zo ba zaki dawo ki samu bani.
Manjo kiyi hakkuri zanyi magana da mijina musan yadda za ayi da hidimar ki amma ki bar kukan nan tunda kika iya rabuwa ni kikai hakkuri a baya.
Bayan munyi sallaman na dago na kalleshi zuciyana ba dadi a lokacin .
Ki kwantar da hankalin ki ya kalleni yana fadin rudun tsufane zan saka koda kin tafi can azo maki da ita ta zauna maki idan kin haihu haihu zata dan debe maki kewa.
Kana ganin idan mun dauki kakata hakan ba zai zama matsala ba a gurin hjy matsalan me har taje ta dawo tunda ba kasa daya kuke ba ina zata san taje.
Mikewa yayi yana fadin muje ki ban abinci fita zanyi yanzu sai na biya gida na gaida su zamu tafi wani unguwa da Nasir.
Mikewa nayi zuwa falon na bashi abinci nima na zuba nawa muka karya ya fita daga gidan dan kwantawa nayi a falo ina kallo yara suna min hira sai barci ya dauke ni.
Can a cikin barcin wayana yai kara firgigit na falka ina daukan wayan tare da duban mai kirana a lokacin.