NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:16 – ????????????: Da sauri na mike tsaye don jin abinda ake fada min a wayan da mamaki nake kallon wayan dake hannuna ina ayyana lalai idan ina duba aikina zaici.
Na riga dana nasa hakan dama kuma gashi yanzu hakan ya tabbata hasashena ya zama gaskiya garesu sune din suke fada min gasu a garin kano.
Sai dai girma da fadin garin yasa sun rude sun kasa fahintar kwatancen da nayi masu shine nace su jira a airport za a zo a tafi dasu.
Dakatar da tunanen danakeyi nayi lokaci daya don tunawa da nayi suna dakon mu a lokacin a daidai lokacin da nake shirin kiran yaya a wayana sai wayan ya sake daukan kara lokaci guda.
Take sheda min cewa na bari kawai mijin ta ya kira za,ayi amfani da addres din dana basu a samu gidan nace ba matsala.
Murja na kira ta dauka nake fadin kije dakin mamu yanzu ki gyara duk wani abinda bai dace ba dakin cikin awa daya ki tabbatar da kin gama komai nima gani nan zuwa a lokacin.
Ban hakkura da kiran yaya ba don kada in fita yazo bai sameni a gida ba don bansan ko ba zasu dade ba inda sukaje.
Yana dauka wayan yace zahra yaya akayi ne nace yaya mutanen nan iyayyen mamu sune suka kirani yanzu wai gasu a kano .
Yace what nace wallahi yanzun suka kirani suna sheda min shine nike son muje can su samemu a gidan kafin su zo.
Ok ku tafi yace kafin inzo da sauri na shirya bayan mun gama wayan daga ni har yan aikina gaba daya muka nufi gidan kawuna.
Ban shiga dakin mahaifiyata ba saida na gaida kowa na gidan a gurguje kafin in fito zuwa wurin mamu .
Na samu murja ta gyara part din na mamu duk da dai a gyare yake tana zaune suna hira da mamu tare da fauziya nayi sallama.
Ban kai ga gaisheta ba take fadin kin dauka ni irin kine zakice wai azo a gyara min daki kuna daukan kowa zaune yake sai an mashi abu mutum da karfin shi ya zauna jira.
Dariya kawai nake mata ina zama tare da fadin yau ba ranan fada bane gareki mamu don tukwaici ya kamata ki bani babba kan hakan ba kuma tukuicin komai nake so ba sai fauziya zan tafi da ita idan zan wuce.
Wai hauka kikeyi ko me haka Sayadi yau gaba daya kin wani zare min kafin in kai ga bata amsa wayana yayi kara na dauko ina dubawa yaya ne ya sake kirana yana tambaya na su nawa ne sukazo nace ban sani ba yaya don basu karaso ba tukunna.
Ok kawai yace ya kashe wayan shi na dago ina kallon mamu data tsareni da ido tana son jin bayanin wanda zasu zo muke magana.
Nace a hankali mamu yau dai Allah yayi wanan jumma,an zaki gana da mahaifiyar ki in sha Allahu wace zuwa yanzu suna cikin kasan nan ko sun sauka dazun da safe.
Ban rufe baki ba mukaji diran motoci har da jiniya sun tsaya a kofan gidan kawu wanda hakan yayi daidai da fitowan yan gidan kawu gaba daya a daidai lokacin da murja take kwalawa Amma kira ta fito yau ga mahaifiyar mamu tazo.
Hjy dake kokarin fitowa daga part din ta a daidai lokacin tace haukan banza ina wanan magana ya fito haka kuma ga yarnan.
Har kawu sun fito da sauri shida hjy maryam suka tsinkayi muryan murja dake shela a gidan na zuwan bakin.
Kowa mamaki ne ya cika shi a lokaci daya suna tsaye suna kallon juna ba wanda ya iya magana a cikin su a lokacin.
Tabbatar da lalai a nan motar ya tsaya yasa kawu kokarin fita waje ya duba ko su waye wajen don ya tabbatar.
A lokacin na fito zuwa kofan gidan nima mukai arba da wanan matar mai suna sumaiyya wace ke zaune a London.
Ko wacen su na cikin shiga irin na al,adan su nace sai dai ko ba a fada maka ba kasan ko a can din manyan matane sudin.
Don zinare na sarka ne zuwa awarwaro ke nuna kanshi a jikin su sun kai su shidda mata sai maza dake da kama mutum hudu.
Bayan dan bayani da wanda akasa ya rakosu daga gidan gwaunati yayi wa kawu ya basu daman shiga gidan lokaci guda.
A daidai lokacin da Amma ta fito tana fadin da gaskene yau Sadiya ce a garin nan ko kuwa.
Ai kuwa arba sukayi da ita tace hjy kece itama amma tana fadin tsarki ya tabbata ga Allah halima ce kuwa da kanta nake gani nan.
Sai ta fashe da kuka a lokaci daya wanda hakan yasa matar hamshakiyar da aka kira da maimuna itama ta fashe da kuka tana rungume Amma.
Ga yaran maza kamar su dauke uwar don manne mata da suke a jiki lokaci guda.
Mamu tana kokarin fita aka turo get din gaba daya da sauri kawu yake kokarin bude kofan na karba nida murja muka wagale get din gidan suka fara shigowa ciki.
Sai bin gida da kallo suke suna yaren su har lokacin Amma da matar suna rungume da juna basu sake dan uwa ba.
Ji nayi an dafa ni na juya dayan matar wace take yar matashiya a cikin su ne ta dafani na juyo ina kallon ta.
Tace min a harshen turanci kece Fatima ko nace eh sai ta rungume ni tana fadin kamarmu daya dake yasa yar uwarmu ta baiyana ta dalilin mu don ni kika kwaso sak .
Nace harda mahaifiyata don kamartane na kwaso sosai tace da gaske nace kwarai kuwa zaki ganta da ita kuke kama har na kwaso ku.
Muna tafe ake dan fira a tsakanin mu murja dake bayan mu ta rada min Fatima duba hjy kiga ikon Allah yau.
Da sauri na dago na kalli hanyar part din ta tana tsaye a cikin imani da al,ajabin abinda idon ta yake gani muka shigo gidan.
Gaba daya suka ja suka tsaya don ganin mamu dake masu wani irin kallo lokaci guda da sauri matar ta sake Amma tana mikawa mamu hannu alaman tazo gare ta.
Da sauri suka hade lokaci guda har yan mazan dake bayan matar tafe suka rungume mamu suka sakata a tsakiya.
Kowa na sharan kwalla a fuskan shi suna yaren su na can daya bayan daya suke rungumar ta suna mata gaisuwan su na larabawa na sumbata.
Duk wanda ke wurin sai da yai kuka in ka debe hjy jummai da hjy maryam dake tsaye kamar an dasa su a wurin.
A daidai wanan lokacin yaya ya shigo gidan shida Aliyu suna masu sannu da zuwa kafin su dawo inda mahaifin su ke tsaye su tsaya suma.
Can yace min nazo na dan zo yake fadin yaya zamu barsu a nan a waje mu shiga daga ciki mana zaifi.
Nace kukan ne basu kare ba ai yaya sai faman runguma sukeyi suna yare yace shiga dasu ciki don Allah yana gama magana dani ya daga kai suka hada ido da mahaifiyar shi dake mashi wani kallon tuhuma a lokacin.
Don a zaton hjy shine mussababin tono inda mahaifiyar mamu take har suka zo din inda take yanzu.
Mun shiga ciki har lokacin suna bin part mamu da kallo ina kokarin dauko masu ruwa saiga murja na sallama da katon din ruwa da drinks tana shigowa dashi ita dasu Fauziya.
Abinci abinsha da sauran abin baiwa baki duk sai gashi ana shigowa dashi part din na mamu kamar dama an tanadar masu shine.
Banyi mamakin hakan ba dana gani don nasan aikin yaya ne wanan dawainiyar sun sake sosai suna cin abincin ba tare da nuna bakunta ba a gidan ba.
Dakin Amma na nufa don can nakai yara da yan aikina dana zo dasu sai maria ne ke part din mamu tana ba baki abinci.
Hjy maryam tazo har dakin gaida su da zuwa ta dan zauna na dan wani lokaci kafin ta fito suna gaisawa.
Su yaya na fitowa daga gun kawu suka shiga dakin mahaifiyar su don su gaisa sun gaisa din duk da ya fahinci yanayin ta bai hana ya dan zauna tare da ita ba a lokacin.
Muryan ta yaji tana fadin Babawo makirci da sallon yaudara har da kai za a hada baki ayishi a gidan nan .
Subbahanallahi mama mai kuma akace maki na aikata yanzu kuma tace meye baka aikata ba din don yanzu na gaskanta komai dana gani da idona.
An hada baki dakai wurin neman uwar maimuna har wani kasa ka nemota wama yasani ko mai kama da ita kukayo haya a wani kasa.
Aliyu yace haba mama wanan zancen ai bai dace ace anjishi a bakin ba wallahi don Allah mama ki rufa muna asiri ki daina wanan halin haka ?
Yaya za,a yo hayan mutane haka zuwa nan da sunan karya irin wa yan nan mutane har kike tsammanin za a dauko da sunan haya.
Da ganin su kaf yan babban kasa don babu yadda za ayi gwaunati ta turo ayo masu rakiya haka idan basu da mukami a gwaunatin su nacan.
Koma menena dai bai shafeni ba ko duniya zasu zo dashi don kaina na sani to mama sai ko ki kyale don Allah wanan abindai kowa ya nuna masu farin cikin shi.
Kin san kuma dole shi yaya yayi wani abu akai tunda dai yana auren jikan ta yanzu ko ?
To ubana saika tsareni kana min fada tunda kun rainani akan matan ku kun fifita matayen ku yanzu a kaina kowa kuma yasan da hakan.
Shiru sukayi gaba dayan su babu wanda ya kara magana a cikin su taci gaba da fadin idan bashi yaje ya nemo masu ita ba ai bata taba tunawa tabar diya a kasan nan ba wullakance.
Ko ita maimunan da yarta suna da halin zuwa har wani kasane neman mahaifiyarta watau ka nuna min ka gaji da gorin da nake mata ko ?
Mama kiyi hakkuri idan kince na nemo masu ita kamar hakane tunda ni nakai ita fatima kasan waje har suka hade da wace tasan mahaifiyar maman ta a can ta hadasu da ita.
Tace bakaji zancen ba ta dalilin ka komai ya faru idan ina magana sai a dinga ganin laifina abinda nake gudu ya faru ke nan yake faruwa dakai an mayar dakai wani binan sai abin da suka tsarama kakeyi a gidan nan.
Haba mama koda ace kudi na kashe wurin nemawa maimuna mahaifiyar ta ai ba zai zama laifi ba don na sama masu martaban su ko ?
Martaba wani martaba ga matar data tafi ta bar yarta shekara da shekaru a wullakance nan wata kila ma zaman banza takeyi a can don ba abin mamaki bane hakan ya kasance .
Innalillahi yace tare da fadin Aliyu tashi muje Nasir yana jirana yana kokarin tashi tace kada inji kada in gani ka saka bakin ka a cikin wanan karyan da za ai muna gidan nan.
Basu ce komai ba suka fita cike da kunnan rai suna maijin zafin halaiyar mahaifiyar su da ta kasance halinta a hakan .
Mata hudu da mazan muka kwasa muka tafi gidan mu dasu zasu sauka a can don zasu fi sakewa a can inda kakata tace a wurin mamu zata sauka ita da kanwar ta guda.
Sun yaba da gidan namu sosai don komai a wadace suke yinsa ko wani daki mutum bibiyu suka sauka a cikin sa.
Inda na shiga dawai niya dasu a gidan kamar yadda ake karrama ko wani bako idan yazo maka bakunta a gidan ka.
Sai washe gari ne bayan sun huta anty Summaiya take min bayanin su kamar haka.
Kakan ki itace babba a gidan mu bayan iyayyen mu sun bar kasan nan da mu muka koma gida a cikin bakin ciki take da kyar aka samu tayi aure a cikin dangin mu.
Ta aure dan wan baban mu a lokacin wanda ya dawo karatun likita daga kasan waje lokacin dashi ne ta haifi wa yan nan yaran da kike gani tazo dasu dukan su diyan cikinta ne su biyar maza hudu da macen nan da kukai kama muke kiranta da Binta.
Da yake yan gidan mu duk gaba dayan su suna ilimi muma komawan mu can yasa aka sakamu a makarantar mukai karatu mai zurfi har ita yayan namu dake da aure bata zauna ba.
Mijin ta shine tsohon minister lafiya na kasan mu da tare dashi zamu zo sai dai aiki yai mai yawa yasa ya hado mu da yan rakiya kawai mukazo.
Ni dai kin san a London nake zaune mijina ne ke aiki a can shine nima zamana ya koma London din sai dai muna zuwa gida lokaci lokaci don hakane baki faye ganina a shagona ba kowani lokaci.
Binta batai aure ba har yanzu saidai tana da wanda zata aura Family din mu daya dashi kin san mu bama auren bare sai dan gida wanan ka,idan gidan mune hakan.
Na tausayawa halin dana samu mahaifiyar ki a ciki dama wanda ta shiga a baya don muna zaune a cikin daula ita tana nan tana zaman hakkuri.
Saidai ke Alhamdullahi da gani baki da matsala a rayuwa don jikin ki bai nuna hakan ba a kullun wanan ne damuwan kakan ki a can tana yawan magana kan rayuwan mahaifiyar ki.
Kin san tsakanin da da uwa akwai motsi na jini dake yawan halin da dan uwa yake a ciki .
Sai dana lumshe idona na fara koro mata matsalolin da muka fuskanta a rayuwan mu nan dama wanda muke a cikin sa yanzu.
Har rana yayi sosai bamu sani ba muna zaune muna hira a wurin sai kiran sallah azahar daya karade unguwar muke danji lokacin muka kalli lokaci muka san rana yayi sosai ashe.
Sallah mukayi mazan suka fita zuwa masallacin don suyi sallah wanan zuwan da sukayi shi ya dage muna tafiyan mu a satin mun shirya zuwa can gidan kawu wurin su kakan tawa don su gaisa da ita.
Da sultana kawai naje nabar sauran a gida wurin maria busy muka samu mamu tana faman dawainiya da bakin nata.
Tubewa nayi na karbi aikin nata naci gaba dayi sai mamakina sukeyi wai da cikina tsoho ina aiki haka.
Bayan magariba muka samu kebewa da mamu na tambaye ta ko hjyn su yaya tazo gaisawa da bakin ta ?
Bata shigo ba ta bani amsa tare da fadin kuma hakan ni bai dameni ba tunda Allah ya karba mi addu,a na wankeni daga sherin da ta dade tana min ga mutane.
Da ranan nan tagama fada da Alhaji wai yana rawan kafa saboda uwata tazo inda Allah zaisa naji sai gashi na shiga wurin shi kai mashi tsaraban da suka zo mai dashi.
Nan ta kama fadan karya tana wani kame kame don tasan naji abinda suke fadi lokacin.
Mamu wanan matar tayi nisa sai dai addua ga lamarinta kawai yanzu don abin yafi karfin kishi sai kiyayya a tsakanin mu da ita.
Dazun da kawun ki yazo gaishe su naji suna fada mai suna rokon idan zasu tafi zasu tafi dani inje inga yan uwa yan uwa su ganni.
Da sauri nace meyace mamu ta dan bata fuska tare da fadin yace sai ya zauna yayi shawara da gwaggo .
Da alama ba zai bari ki bisu ba mamu tace ai ba zan yarda da hakan ba kada kiyi wani magana idan ya hana nace mata.
Amma kin san za a tauyeni da yawa idan yai min haka don yasan suna bukatana can ke nan hakan kuma shi zai sa kowa ya fahinci karyan da hjy ke masu na cewa uwata ta gudu ta barni idan har na bisu din.
Wanan gaskiya nasan kawu ba zai hanaki ba idan kun fahinci juna sai dai ban son ki tayar da hankalin ki kan wanan magana kada yaga kin manta da halatcin da yai maki a baya shi da Amma.
Mamu naso fada maki abinda ya faru lokacin da mukaje misau sai dai hakan bai samu ba nan nake bata rabarin abinda ya faru naga hankalin ta ya tashi sosai tana fadin .
Ni maimuna na rasa me muka tare wa wa,yan nan mutane suke neman rayuwan mu haka mu bamu damu da al,amarin kowa ba amma sun sakamu gaba haka ?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button