NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Rayuwan gidan Alh sanj haka yake gudana a cikin iko da nuna isa a gurin hjy jummai don takaman da take itace mai gida ko banza yaranta sun kawo jiki.

Hjy maimuna bata biyewa duk wani barazanar su da suke son janta da tashin hankali don ganin sun hanata jin dadin gidan mijinta.
Ranan wani laraba tsotsayi yakai tagwayen hjy maimuna wurin motar da yaron hjy jummai ya aiko mata dashi a cewan ta data fada ma yayan nata wai mota daya Alh ya aje mata ita da kishiyoyin ta duk wace zata fita sai a ciki zata fita ita kuma bata son hakan da akeyi tunda yana da karfin da zai sayawa kowa motar hawa .
Jin haka dan nata yace kada ta damu indai don mota hawa ce ba matsala zai saya mata mota har ta mance da sunyi hakan kwatsam sai ga mota ranan ta iso wace ta dauke hankalin kowa a gari.
Shine yau yaran suna wasa sukaje gurin motar ba tare da sanin kowa ba suka shafa farin kala wa motar da sukai rubutu.
Ai kuwa da yar ta ta fito ta gani ta koma ta fada mata ga yaran can a gurin motar ta suna rubutu ta mike a sukwane salma na kiranta amma bata tsaya ba ta fice.
Kallon yarinyar salma tayi tare da fadin may yasa kika fada mata bayan kin dan halin hjy da rashin hakkuri.
Hjy maimuna da sauran mutanen gidan suka jiyo ihu yaran cikin tashin hankali suna tafe tana bi tana shadi da zagin su.
Uwar su suka zo suka rungumay a gigice hakan baisa ta barsu ba sai fada take tana kokati dukan su a gaban uwar.
Muryan Amma ne ke fadin amma wanan matar baki da tausayi wanan duka hakan ga wa yan nan yara kananu ko mutuwa na tsoron idon mahaifa.
Maganan tsohuwar bai sa ta daina abinda take shirin yi ba ga kowa tsaye cirko cirko yana kallon su ta sake daga hannu da niyar takai masu duka a jikkn uwar .
Lokacin ne hjy maimuna tace kada ki soma ki kara taba min yaya don abin naki da biyu kike dukan su .
Turus tayi tana kallon ta da mamaki don jin kalamin nata tace ni zaki gwadawa haihuwan yaya a gidan nan tunda kafin kizo na haifi yayan da ake cin moriyan su.
Don wa yan nan yaya naki yayan baya taka kushewa har yayane a gidan nan tun kan kizo duniya nasan haihuwa nasan da hakan ai hjy sai dai yanzu ai kowa ya sani ko ?
Ke ko don maganan wanan tsohuwar ai ke barsu haka komay sukai maki tunda ta haifa maki mijin da kike kurin kin haifi yayan naki dasu.
Maimuna ni kike fadawa hakan kan wa yan nan yayan naki to bari kiji ko kadan ni din nan a cikin gidan nan dake da yayan da kike ganin kin kutso kin haifa ba abakin komai kuke gare mu ba .
Kuma ki kiyaye rashin kunyanki gare ni, don ba zai haifar maki da alheri ba nan gaba shiga tsabgata fitanane gare ku dake da diyan ki.
Don haka doso ni ba abinda zai haifar maku sai karin bakin jini da kiyayya a gidan nan ba ruwana da yayan ki don dake har su baku a gabana don baku tsare min komai ba a rayuwa ta don haka duk ranan da suka kara shiga tsabgata dukan dayafi wanan zan masu.
Tabe baki hjy maimuna tayi tare da fadin a baki ke nan ba amma kowa nan yasan da mun tsone maki ido a gidan nan duk da suna diyan taka kushewa.
Don da kin san da zuwan su a baya da baki bari sun fito duniya ba da kina da ikon yin hakan tana fasin haka taja hannun yaranta zuwa part din ta don ta yi masu wanka saboda kukan da sukayi duk sun yi zufa ga majinan wahala yana tsiyayo masu a hancin su.
Sai bayan shigewan hjy maimuna ne Amma ta matsa da tambayan abinda yaran sukayi take fadi yara kanana sun san hassada da kishi idan ba turasu akayi ba may ya kai su wurin motata su zane min ita da rubutu.
Amma tace yanzu akan mota yar nan kikaiwa yaran nan dukan a kawo ruwa haka waye baisan halin yaro ba tunda duk nan mun haifa mun sani.
Idan kuna magana ku dinga sanin abinda kuke fadi kada zafin zuciya ya sa ku aikata abinda ba daidai ba tace yanzu hjy kada in hukunta su ke nan gobe ma su koma ko ?
Wanan irin hukunci naki yayi tsauri da yawa yaran nan har guda nawa suke su ina suka san wani abu ai tsawatawan yafi wanan duka don in yaro ne gobe ma komawa zasuyi wurin.
Salma ne ta fito tana fadin haba hjy tunda kin dauki mataki ki bari hakana mana tana jan hannun ta don su bar gurin.
Amma tayi kwafa bayan tafiyanta tace aidaiyi hasara a nan babba bai san girman shi ba haka nina taba ganin hakan.
Alh sani daya dawo sai baiga yaran shi sunzo taron shi ba yake tambayan ina yan biyu sai dan gurin hjy maryam yace mama ta dukesu tun dazu suna barci.
Duka kuma mai sukai mata ta duki su kuma ya tambayi yaron da mamaki yaron yafara fadin don sun rubuta A ga motar ta.
Kuma akai fada da mamu da Amma da mama akai tafada daddy wani iri yaji a ranshi ya kama hannu yaron suka shige.
Bai leka ba sai lokaci da ya gama abinda yake ya shiga part din hjy maimuna din yaran suna kwance har lokacin suna barcin wahala don ba,a taba dukan su irin haka ba tunda suka zo duniya.
Hjy maimuna dake zaune a gefen su tana duban wayan ta ta dago kai tana amsa mashi sallaman shi tare da mashi sannu da dawo wa ya amsa yana fadin yanzu samir ke fada min wani magana yana kai hannun shi ga jikin yaran yana dan tabawa a hankali zafin da yaji jikin yaran yayi ga kuma shartin bulalan a jikin su yasa yace wai yanzu a kan mota tayi masu wann dukan ?
Hjy maimuna tace akan mota tayi masu duka ashe ni ba ko tsayaji abida sukai mata tunda da biyu ta doke su tunda tana da manufa akansu ta fadi kowa yaji.
Murmushi irin na manya yayi tare da fadin amma jikin yaron nan ya kamata a kaishi asibiti don jikin yayi zafi sosai gaskiya amma ina zuwa.
Sai ya daga waya y kira Ahmed daya dauka Ahmed din na gai da shi bai tsaya amsawa ba yace kana ina ya bashi amsa da gani nan hanyar gidana .
Yace in ba damuwa don Allh ka biyo nan ka dauke ni mukai yaran asibiti basu da lafiya Ahmed da sauri yace subbahanallahi gani nan zuwa Alh.
Ba fi yan mintina ba ya bugo ma Alh waya gashi a kofar gida yace ya shigo ya kama mai yaro guda zuwa waje sai gashi ya shigo yana gaida hjy maimuna tare da mata jajen ciwon yaran.
Lokacin da zasu fita da yaran yar guri hjy jummai ta gansu itace taje tana fadawa uwar tace su dai suka sani duk abinda zaiyi ya dade bai yi ba.
A asibiti sun duba yaran inda suke son bayanin abinda ya samay su bai boye ba yace dukan su akayi likitan yace ayyah yara kanana haka da duka irin wanann yana kara duba jikin tare da tausaya masu.
Sai baya an gama basu treatment ne sun fito Ahmed ke fadin Alh wa yai masu wana dukan haka kamaf ba tausayi dan murmushi Alh ya sake a fuskan shi tare da girgiza kai yace Jummai ce da wana haukan don sun taba mata mota wai .
Innalilahi Ahmed ya furta shima yana girgiza kai tare da fadin dukan yayi yawa wallahi Allah ya sauwaka ranshi ya baci sosai da hakan daya ji yana mai tausayawa hjy maimuna da yaran ta kan matsin da suke gani a gidan.
Basu dawo gida ba sai da suka biya da yaran ya sai masu abubuwa suka juyo zuwa gida suna lafe jikin mahaifin su don wahala.
Shigowan su bai kai su gurin uwar su ba dakin Amma suka wuce da yaran nan ya samu Amma da tunda abin ya faru take cikin bacin rai ganin shigowan su da mahaifin su take fadin gaku kamar fita kukayi man ?
Yace daga asibiti muke da yaran jikin nasu ne ya dau zafi sosai yana kokarin zama yake kuma ciro wayan shi daga aljihunn shi.
Wayan matan ya kira daya bayxn daya su samay shi a part don mahaifiyar shi zan iya cewa kowa yasan kiran da ake masu din don haka ko wace tazo da shirin ko ta kwana a cikin su.
Hjy maryam yar sari ka noke ta fara shigowa sai hjy maimuna hjy jummai itace tazo karshe tans cika tana batsewa.
Yana zaune da yaran sun lafe a jikin shi don basu da walwala shi mara lafiyan har yayi barci a lokacin rike da goran yought da aka saya masu.
Wuri ko wace ta samu ta zauna akan kushin sai maimuna dake kasa can gefe daga kofan shiga kuryan dakin Amma.
Kallon inda take zaune yayi yace kira min hadiya ba tare da ta amsa ba ta mike daga dakin zuwa kiran hadiye dayace tayi.
Sai gasu tare da hadiyen sun shigo falon kowa ya samu wuri ya zauna kamar yadda sauran sukayi.
Dan gyaran murya yayi tare da fadin Amma na dawo gida dazun banga yan biyu na tambaya sai Samir ke fada min wai hjy ta doke su yau.
Shine ban gane kan dukan ba hjy nake son karin bayani ga abinda ya faru don ban fahinci maganan yaron ba sai kuma gashi naje parr din ita maimuna na samu yaran akwance ba lafiya yanzu haka daga asibiti muke dasu shine kikaga mun shigo nan .
Hjy takatse shida fadin nina duke so kan barnan da sukai min a motata kuma uwar su ta nuna min niba kowa bace a gidan nan tunda na daki yayan ta.
Akan mota kika dake su haka jummai kashe su kike son yi komai don dukan yayi yawa ko ni na taba kama wani yaro a gidan nan nai mashi makamancin dukan nan.
Nan aka fara cacan baki da ita don cewa tayi kan dan dukan danai masu kake kokarin kare su ko ?
Ko banda halin da zan dauki mataki akan yaro a gidan nan ne in sani don ban gane manufarka na tara mu a nan ba in wani abu ne muyi shi daga ni sai kai mana don in akwai abinda taki jini shine fada gaban wani.
Don suba yayan mai ke nan bari kazo nan ka turke ni ko tunda ta zama yar gwal ita da yaran shine hjy maimuna ta saka baki suka fara musayar kalamai a tsakanin su.
Tsawa ya daka masu tare da yima jummai kwakwaran kashedi akan duka irin haka yace ya kafa hujja ne a gaban mahaifiyar shi.
Wanan fadan yana daga cikin abinda ya kara saka bakin cikin maimuna da yaranta gurin hjy jummai da duk wani nata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button