SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:18 – ????????????: Kwanan bakin mu hudu a kano tare damu wanda yaya umar ke faman dawainiya dasu don fitar damu kunyan su.
Dukko da irin hattaran shi da hjyn su takeyi saidai ya nuna mata shi baida ko lokacin su aikin gaban shi ya sha mai kai don ya bar gari shida dan uwan shi.
Don kada tace lalai shidin ne kuyin abubuwan da take ganin ana shigowa dashi gidan don su.
Sai dai kafin ya tafi ya barwa Nasir abokin shi yin komai don bakin a hannun Nasir wanda yake kawowa ta gidana ni kuma sai inba driver ko in kawo da kaina.
Sai kuma ta koma zargin kawu tana fadin shine mai hidima da bakin yake nuna masu shi baida hali yanzu amma gashi saboda zuwan yan uwan mamu yana fitar da kudi yana kashe masu don kawai a yabe shi.
Yace idan nayi laifine yin hakan don kafin in masu da naki yan uwan nasha dawainiya a baya kika kuma manta da hakan da nayi maki yanzu.
Gori zakai min don kawai na fadi gaskiya yace babu zancen gori a ciki sai amsa daidai da maganar ki kinga kenan baga yan uwan maimuna na fara rawan kafa ba ashe ?
Wasa wasa saiga muryan su yana tashi har yakai sauran sassan gidan ana iya jiyo abinda sukeyi wanda hakan baiyiwa kowa dadi ba a gidan.
Bamu dade da shigowa gidan ba wanan abin ya faru da dabara na dauke hankalin su ta hanyar kara karan tv dake aiki ina masu bayanin abinda mai wanka yake fadi.
Hakan ya dauke hankalin su saidai ita kakantawa dake jin hausa tasan abinda ake fadi sarai a gidan kallon mamu tayi tana tambayan ta tace maigidan ne da uwar gidan mu suke dan hatsaniya .
Tace har yanzu ana irin wanan halin a kasan nan da addinin nan daya zaga ko ina ana wa,azi akan hakan mai yai mata haka take wanan daga muryan haka ?
Nace wanan halin tane mama kamar yadda naji diyan ta suna kiran ta nan na fara bata labarin irin gorin da hjy take wa mamu ita kuma tanawa yan uwanta bayani har ga zuwa aurena da danta har rikicin da mukeyi da ita zuwa yanzu.
Suyi da yaren su suyi da turanci ko da dan hausan da sukeji kadan suna kara bamu shawaran yadda zamu zauna da ita.
Kawu ya yarda dasu tafi da mamu don taga yan uwa da wuri koshi sai da Amma tasa baki a maganan ya yarda don yace sai daga baya zai shirya sutafi tare da ita.
Amma tace sam ba zai yuyu ba yaushe zai samu lokaci yadda yake fama da jikin nan nasa yanzu.
Don haka muka fara shirin tafiyan mamu kasan mahaifiyar ta ta dubosu ba karamin kudi muka kashe ba wurin hada tsaraba irin wanda ya dace suje dashi wanda basu dashi can suna bukatan shi .
Da muka fitar da tsaraban ba karamin fada kakan tawa tayi ba damu kudin data bamu yafi kudin da muka kashe yawa .
Da farko munki karban kudin data bamu din saida ta nuna bacin ranta ga hakan kafin in yarda na karba tayiwa kowa na gidan alheri na bajinta saida kowa ya girgiza bayan tsaraban da suka zo dashi aka raba inda hjy ba kunya ta karbe komai da akabata tana cewa ta rage zagin dukiyan da danta ya barar masu itama.
Mamu zata tafi da su yan biyu da mansur karamin danta nan aka shiga zancen ina fauziya zata zauna mamun tace wueun Amma.
Da kaina nayiwa kawu magana zan tafi da fauziya don ta kamamin idan zan haihu a can yaso ya hana saida ya danyi tunane kafin ya barmu mu je da ita.
Yau dai mamu sun daga muna tsaye muna kallon har jirgin su ya daga saida ya bace muka dawo gida inda kusan gaba daya yan gidan kawu mukai masu rakiya zuwa airport din inka debe hjyn su yaya .
Ta daiyi banjin ta ta rakosu har kofan gidan kawu da zasu wuce saidai kana kallon ta kasan naciki na ciki lokacin.
Bayan tafiyan sune muka hau shirin namu tafiyan don komawa London din dan karatun yara dayace lokaci yana kurewa yasa muka bar kasan, sai dai bamu samu tafiya dashi ba don aiyukan dayace yayi mai yawa a nan.
Kusan yanzu watana takwas rabona da london saidai komai ban canza min ba sai dan kara kawata kasa da kullun suke cikun yinsa su.
Muna komawa akakai yaran makaranta harda yar sultana na sai ya zamanto yanzu fafitikan nemawa Fauziya makarantan da zata shiga nakeyi duk da alkawarin wata uku nayiwa kawuna zatayi don nasan idan na fada mai gaskiya ba zai yarda muzo da ita ba.
Yaya ya bugo waya yana sheda min bude ma,aikatar su da akayi a kasan guda lagos guda Abuja na tayashi murna jin komai ya kammalu bayan fafutukar dayasha na shekara da shekaru wurin neman yayunwan abin.
Tuni nayi mai akan zancen mijin Atika yace bai manta da zancen shi ba ai tunda takardun shi suna a hannun shi .
A cikin hiran namu yake fadin yana son ya samu daddy akan maganan Ahmad don yana son suyi aiki a tare dashi tunda kasuwan nasu yanzu baija sosai kuma sabbin yan kasuwa matasa masu amfani da tecnolagy a yanzu.
Sai zancen salma da zai budewa gidan buga ruwan leda na sha ban san lokacin da dadi yasa na sake dan ihun murna ba a lokaci guda don dadin danaji na hakan har kasan raina.
Bayan kwana biyu sai ga salma ta bugo min waya tana min godiya wai yaya yazo da kanshi har gidan su da abin alheri gare su.
Mun dade muna hira har zamu kashe wayan tace wallahi Fatima yaya har tausayi yake bani hjy ta daga mai hankali akan karin auren shi da ta matsa mai yayi.
Ashe su har sun saka rana ba wanda ya sani sai da zancen yaje kunnen daddy akeji a cikin gida koshi saida baban ita yarinyar ya kira daddy don yace baiga kowa har lokacin daga bangaren mu ba kan zancen ga lokaci sai karasowa yakeyi na bukin.
Gabana ne ya yanke ya fadi lokaci guda nace kai lalai kuwa hjy takai wallahi itako salma sai zubamin labarin takeyi tana fadin.
Kin san halin yaya bai nuna abu ya dameshi saida daddy ya kirashi ne yana tambayan shi yake fada mai yadda mama ta tursasa shi har tana batun yi mai baki idan bai yarda ba.
Yace ma daddy yana son a dage bukin har zuwa lokacin da zaki haihu idan kin haihu sai ayi bukin.
Da salma tasan yanayin da nake ciki lokacin da bataci gaba da fada min wanan bakin labarin datake tsegunta min ba a lokacin.
Duk da ina da kishiya amma sunan ta dai ne nake ji na amfani dashi don nida ita tunda ta samu labari bamu taba ido da ido ba har wanan lokacin.
Ban yarda ta fahinci irin halin da nake ciki din ba a lokacin don kada in katse ta da jin labarin idan ba haka ba sai dai inji wanan labarin daga sama.
Wai kin san wani abin haushi ba naje gidan mama saude ba sai ga yar iskan nagani wai tana yawon nuna anko ga yan uwa na bukin.
A raina nace Allah yasa kada yaya ya aminci muga ta tsiya wani iri nake ji gaba daya jikina ya dauki rawa a lokaci guda har abin cikin cikina saida ya juya lokaci daya.
Nace dama ashe zancen yana nan salma amma kinga yaya bai fada min ba don munafuncin maza.
Haba dai Fatima na fada maki ai bada son ran yaya ba fa wanan shirin duk daga mama da yan uwata masu zugata yake fita.
Ke mama fa kin dai san uwatace wallahi lamarin mama sai addu,a kawai don har tana ikirarin idan kun kama yayane keda maman biyu ita a tsaye take kwana kan danta sai dai idan babu boka ko malam a duniya.
Fatima wanan magana ya kamata mama tana fadin shi kan matar danta don Allah duk da take uwata shi gaskiya ai dayace.
Yanzu ya kamata ace mama ta mayar da lamarin ta ga Allah tana istigifar din kuraren tana bayane ba wanan shirmen ba da ake zugata akai ni nasan sai mama ta dawo tana dana sanin wanan abin daga baya wallahi don ba mutanen arziki ta debowa kanta ba.
Allah dai ya sauwaka nace mata don na kasa furta komai akan maganan don idan nace zan furta din zan iya fadin abinda ba daidai ba ga mahaifiyar nasu dake son ganin tarwatsewan rayuwana a kowani hali.
Ita bata ko tausayin halin da nake ciki da tsohun ciki haka a jikina take kiran ai min kishiya jin nayi shiru ban tanka ba tace amma fa tunda nace ban sani ba don Allah in rufata a gurin yaya kada yaji ita ta fada min yayi fushi da ita kuma.
Nace baki da matsala kan hakan anty salma indai nice ba zan mai maganan ba sai idan shi yayi min.
Ajiyan zuciya na sauke bayan mun gama wayan ina mamaki a raina na wanan halin na hajiyan su .
Haka na wuni sukuku saukina ma yaran da basu gida sai hudu suke dawowa har na samu lokacin yin tunanen mafita akan maganan.
Koda yaran suka dawo hakana suka sameni cikin rashin walwala a tare dani.
Ga wani irin bushewa da makogorona suna faman surtun su haka na zauna kamar mutum mutumi ina kallon su.
Gaskiya akace ciwo ya mace sai mace yar uwarta don Fauziya ta fahinci ina cikin wani hali na tashin hankali ita ta dauko ruwa da abinci ta kawo min gabana wai inci.
Dago kai nayi na kalleta sai lokacin na dan sake murmushi kada yarinyar ta daga hankalin ta akaina.
Ruwan na dauka na dan kwankwada na aje kofin ina lumshe idanuwana tare da bin kujera na kwanta har lokacin na kasa aje magana daya a kan zancen da yau salma take fada min din na tabbacin zancen karin auren yaya din.
Bayan kwana biyu ya sauka kasan bai samu zuwa wurin mu sai washe gari da yamma ya shigo gidan hakan kuma ya bani tabbacin gane merry tana kasan ke nan.
Ya shigo gidan daidai yaran na gidan sun dawo da murna suka tare shi sultana ta sheko zuwa dakina tanayi min albishir din dawowan daddy nasu nace naji kawai.
Ya gama da yaran a falo har lokacin ban fito zuwa taron shi ba ina dakina kwance na lumshe idona.
Can naji ya murda kofana ya shigo daga kofa ya tsaya yana kare min kallo ni kuma har lokacin ban dogo kai na kalleshi ba.
Sai da naji motsin shi zuwa inda nake kwance na dan bude idanuwana da sauri nace sannu da zuwa a kasalance ya bini da kallon yadda na tare shi yana mamakina a ranshi.
Bai amsa min gaisuwan ba yace meya sameki ko baki da lafiyane kuma yana tambayana tare da kokarin taba jikina yaji.
Lafiyata kalau na bashi amsa kawai ina kokarin tashi zaune ya hanya na kara fadi.
Tambayan ki nake kina kin bani amsa meke damun ki ne na ganki haka kamar mara lafiya ?
Lafiyata kalau sai dai idan za a lakaka min ciwon dai a yanzu kallon mamaki ya bini dashi yana fadin wani irin magana ne wanan kuma kike fada min.
Ai ba,a damu dani ba tunda ana ganina banda galihu tunda mahaifina baya raye kamar na kowa dole azo nan a yardani kamar banza.
You are very stupid da wanan magana da kike min zahra daga dawowana zaki tareni da wani shirmen magana taki mara dadi haka.
Ya mike ya fita a fusace ya bar dakin rai bace bai sake shigowa ba nima ban fita ba ina dakina kwance a lokacin ban leko falon ba.
Yayi wanka yana cikin shirin shi da alama fita zaiyi a lokacin fuskan shi a daure yace ni zan tafi merry na gari nazo duba kune dama.
Ban tanka mashi ba ya juya ya fita abinshi ya bar dakin cikin tafiyan shi mai kama da kasaita sai daya dan jima naji tashin motar shi a lokaci.
Haka na kwana ina hadiyan zuciya dagani sai yarana da maria a gidan don ko washe gari bai shigo gidan ba sai da dare lokacin har yara sunyi barci ya shigo gidan.
Ban san ma shigowan shi gidan ba don haka na wuni akwance sai maria ne ranan take komai a gidan don a zaton ta banda lafiyane ni.
Kofana ya murda yaji ta a rufe ya fara kiran sunana ina jin shi ban amsa mashi ba ya kara cewa dani ki bude kofa nace cikin tsawa jin tsoron shi da nake har yanzu yasa na mike na bude kofan lokacin.
Wanan wani hali kuma kika dauko na kule kofa da key banyi magana ba na juya in koma bakin gado naji ya rikeni yana fadin.
Wai wanan wani hali kika daukone hakane zahra ban fa gane maki ba zahra tun dawowana garin nan.
Ka tambayi yar uwanka da kake boye min auren ta don a yaudareni ne aka turoni nan aka barni da yara ai da ka sani baka turoni nan ba don ba zan tareka da komai ga auren ka ba.
Hakan baiyi ba sai da kazo ka watsar damu kamar mu ba mutane bane a nan ka shigo garin nan yaya baka damu ka fara zuwa nan kaga lafiyan mu ba sai ka tsaya wurin merry da yarta.
Zama yayi bakin gado yana murmushi yace har an samu wanda ya kwarmata maki wanan zancen tun daga Nigeria har nan duk taka tsam,tsam da nake kada kiji ?
Ban tanka shi ba don haushin da nake ji a raina a kwana kin nan yasa na kyaleshi kawai bayi magana ba.
Karamin filon dake gefen shi ya jawo ya rugume a jikin shi yai shiru har wani lokaci na bashi baya yana zaune sai ajiyan zuciyana yakeji daga inda yake zaune.
Bai taba tunanen ina da zafin kishi haka ba don ban taba nuna mai kwatankwacin halin dana nuna mai ba wanan karon.
Sai ya danganta abinda harda laluran cikin dake jikina ya hademin jin zafin don ace zuciya sai mace mai tsohon ciki dama.
Baiso inji wanan zancen ba a yanzu sai idan na haihu shi da kansa zaimin bayani yadda zamu fahinci juna don shi kanshi auren biyayya ga mahaifiyar shi zaiyi yanzu bawai don so ko kaunar auren ba.
Sai gashi wani da bai sani ba ya bata mashi tsarin shi ya kwaramata min zancen a lokacin dabai so hakaba gareni.
Yanzu kallon mayaudari nake mashi wanda ke shirin ha,intana ko cin amana nakenan na dauke shi.
Can naji ya gyara kwanciyar shi still dai dakin shiru yayi ba wanda ya iya magana a cikin mu a hankali kuma yaji sheshekan kukan da ya fara zo min a lokacin.