NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:18 – ????????????: A hankali na sauka daga kan gadon na wuce bathroom nayi alwala na fito har lokacin bai falka daga dan barcin daya samu ya dauke shi ba don ya kwana da tunane a ranshi.
Mata biyu ke nan bai iya da halin su ba inaga kuma ya kara na uku yanzu wace ba bakin arzikin dayaji yabon ta a gurin su.
Ya bar gidan merry data zo bukin yar uwanta tun yana Nigeria ta ishe shi da kira saida ya dawo akan dole da fitina da komai sai da yazo wurinta karshe ma kuma suka kare da fitina don yanzu yar tsarguwa ya rigada ya shiga tsakanin su ko.
Komai yai mata sai taga rashin kyautawan shi gare ta zatace don ya aure illiterated din yar uwan shi yake kokarin wullakanta ta yanzu.
Har ya kai ga fada mata wanan din data raina tafita da komai yanzu gareshi don tasan kimar shi da darajan shi tare dana yan uwan shi.
Ran merry ya baci da wanan kalamin nasa sosai tace dama an fada mata su musulmai basu da tabbas ai gashi ko ya fara nuna mata hakan.
Saida sukayi tsiya tsiya dashi yabar mata gidan rai a bace ya nufo wanan gidan namu .
Sai gashi yazo ya samu wani fitinan dake shirin taso mashi kuma wanda yake ganin zaifi na merry idan bai dauki mataki a kan hakan ba.
Ashe gaskiyane da akace mace ba abin yabo bane sai idan an mata kishiya bata tada hankalin ta ba za a yabeta.
Ina abin tayar da hankali akan wanan auren da yake shirin yi yanzu yarinyar da sau daya ma ya ganta kuma a duhu don samun su tayi zasu tafi bayan sun gama ganawa da mahaifin ta da mama ta tursasa mai yaje ko ta saba mai .
Hakan yasa dole ya shirya shi da Nasir da Aliyu suka tafi akai magana suka bada komai.
Allah ya gani zaima mamane biyayyan haihuwa kawai don ya gane auren shine salama a gare shi don a zauna lafiya.
Ina za,a hada zahra da sauran matan shi don dai kawai halin mata da basu raina abin kishi har may wanan mai zubin mayunwatar daya gani zata ja da zarah ne ?
Koda ya aure ta baiji zai iya zuwa da ita ko ina ba bayan Nigeria shiyasa tun farko ya fadawa mahaifiyar shi wanan magana akan ta sani ba zai fita da yarinyar ko ina ba idan ta yarda zata zauna a Nigeria shike nan .
Suka yarda da wanan sharadin nasa don su bukatan su kawai ace anyi wanan auren su shiga cikin rigar arzikin su suma a dama dasu kawai.
Nan hjy ta kawo zancen Fauziya da taji mun tafi da ita daga baya tana fadin zakace ba zaka iya kai yar yaruwata inda kake ba.
Amma ka iya daukan diyan maimun har biyu don ka inganta masu nasu rayuwan suci gaba wanan ba maganan da zai yuyu bane yadda kakai wanan yar matsiyatan itama ya zama dole ka kai wanan din can .
Habibb yace ki gyara zancen k mamai don yanzu sun wuce akirasu ahalin tsiya kamar yadda kuke kira masu a baya.
Don kowa yaga arziki yanzu a tare dasu har sun zartamu don shi wanda uwar maman twinces ke aure ake sa ran shugabancin kasan nan gaba.
Saida na bincika naji komai nasu a kasan ita kanta uwar wata babban ma,aikaciyace a kasan basu da alfaharine kawai yasa baku san wanan ba yanzu haka idan kin shiga kinyi saching din sunan shi zakiga komai masu in deteils.
Arzikin su na banza da wofi tunda danashi suka fara karya a gidan nan kowa kuma ya sani in badon arzikin nasa da sukabi ba ina zata taba ganin uwar nata nan a tauye.
Kai barin fadama ba wani abinda zaka fada min wa yan nan mutanen su burgeni a duniyan nan na tsane su kamar yadda na tsani ranan mutuwata.
Amma mama uwar diyan shine fa bai dace kina aibanta masa mata da take matsayin uwar garken gidan sa ba haka a gaban shi.
Tace ko zaka rama mashine marata ido da bai san inda duniya ya dosa ba uwar garken sheri da ba,ayi hakan tsakani da Allah ba tun farko.
Da kyat ya samu barci ya dauke shi lokacin saboda tunanen irin abubuwan da suke faruwa dashi duk sabodani wanda kuma a karshe sai baiga laifin nuna kishi na din ba gareshi don ta haka maza ke gane irin son da mace ke masu ai saidai kishin idan yai yawa cutane wani lokaci don ya gani ga mahaifiyar su wanda zafin kishin ta yasa yanzu bata sanin abinda ya dace da ita na daidai.
Shine gabanin asuba ya samu barcin yayi gaba dashi har na tashi nayi sallah bai sani ba yana kwance ya dukule a wuri daya kamar yadda yara ke kwanciya idan suna barshi ya dan dora hannu yayi filo dashi.
A hankali na bar dakin har lokacin bai falkaba da alaman bai dade da fara barcin nasa ba don nasan ba kasafai sallah asuba yake wuce shi ba tundai wanan unguwan da musulmai keda yawa har jam,i yake zuwa wani lokaci don akwai mosque da sarauniya ta gina don musulmai.
Ban wani dade da fita a dakin ba ya falka a razane yana furta subbahanallahi yaya akai haka ya faru dashi baiji karan alarm ba ya tashi.
Kallon inda nake kwance yayi bana dakin a zaton shi ina bayi ne lokacin sai da ya saurara yaji bana cikin bayi tashi yayi ya koma dakin shi bathroom ya nufa don dauro alawa.
Maria na samu a kitchen tana aikin hadawa yara abincin tana ganina ta shiga gaidani da kwana na amsa mata cikin sakin fuska tare da tambayan ta mai take girka masu ne ?
Tace madam burgur ne nake tosting don ko sunje da abincin basa ci har su dawo dan murmushi nayi don tunawa da baya wai yau nice har rayuwa ya nuna min nawa diyan cikina sun fara daukan darasi a duniya.
Maria tace in koma kawai in kwanta zata gama komai a cikin lokaci nace ta barshi in karasa sai in dora abinda zamuyi breakfast dashi.
Daki ta nufa don yiwa yara wanka da shiyasu naci gaba da aikina a kitchen din hankali kwance.
Saidai aikin nake don ya rage min zafin danake ji a raina baiwai a cikin dadin zuciya nake ba lokacin.
Ni kaina nayi mamakin kare aikin abin karyawan danayi da wuri koda na fito falo na samu yaran suna fitowa daya bayan daya dakatar dasu nayi sai sun karya tunda maria tace min basucin abincin da ake dan saka masu a jakka suje dashi naji hankalina bai kwanta da hakan ba sam.
A daidai lokacin yaya ya fito a cikin shirin shi na da ya saka kwarjin shi ya kara fitowa sosai yana rike da labcoarth din shi sagale a haban hannun shi.
Morning dad yaran ke fadi daya bayan daya daga inda suke zaune saman dining table din ina basu abinci.
A hankali na dago kaina dan kalleshi tare da fadin ina kwana yaya kun tashi lafiya ya ban amsa yana shafan kan Abdulsamad dayakai inda yake tsaye.
Nice ke fadin suyi sauri su shirya kada su makara bus ya wucesu sai naji yaya na fadin ni zan kaisu yau ina da abinda zanyi can.
Suka shirya ya fice dasu gidan bayan ya zauna shima ya karya kummalo a lokacin ya fice da yaran.
Na dan dade a zaune wurin da suka barni kafin in mike in shaga daga ciki wanka nayi na shirya na kara kwanciya don nima ban samu barcin kirki a daren jiya din ba.
Ina tsaka da barci ya shigo dakin ya dan dade tsaye saman kaina yana kare min kallon yadda na dan koma don na dan fada ga cikin jikina da alama ban nisa sosai da haihuwa yanzu yace a ranshi.
Ke zahra yace daga inda yake tsaye yaga ban motsaba haka yasa ya dan bubuga min kafa na bude idanuna dake tattare da barci a lokacin.
Kallon shi nayi a cikin dakewa nake mashi sannu da dawowa lokacin na mayar da kaina saman filon da nake kwance.
Yayi karfin halin hade fushin shi a kaina yace ki tashi asibiti nake so muje a dubaki, da sauri na bude idona nace a dubani banda lafiya ne halan.
Yace ina son a duba ki don nasan bakije asibiti ba tunda kika dawo kasan nan ?
Nace ni lafiya ta kalau banjin komai balle inje asibiti wani dube dube yanzu kuma .
Kin dai ji abinda nace maki ban son raini hankali ana maki magana kina share mutum kamar wace bata san ciwon kanta ba.
Dole na tashi ba don naso ba na shiga bandaki na kewaya na fito na sameshi a falo yana jiran fitowa na.
Tunda muka dauki hanya ba wanda yai ma dan uwa magana a cikin mu har muka shiga haraban asibitin .
Katina ya bika suka dauko file dina sai can aka kirani wanan karon ma likitan mace ce muka sama asibitin ta karbemu kamar ta san mu da farko.
Bayan dan dube dube tana rubutu take fadin in rage yawan tunane kada yai min yawa ya shafi abinda ke cikina in dinga samun isashen barci ina yi sosai lokaci lokaci.
Mukai mata sallama ta fada min lokacin haihuwa na muka bar office din don zuwa sayen magani.
Muna cikin tafiya kamar yadda mukazo din na ba wanda yai magana a cikin mu sai naji yaja tsuki yana fadin.
Haka kawai don sakarci mutum yajawa kansa ciwo a banza kiyiwa mutane hasara kallon shi nayi nace injawa mutane ko in jawa kaina.
Tunda yanzu ba batun mu kakeyi ba kana zukin sabuwar amaryan da kake shirin daukowa inma wani abu ya sameni aikaina najawa ba wani ba.
Eh ai kinsan lokacin dana aure ki nayi rawan kafa sosai ba dole yanzu itama wanan din in mata rawan kafa kan zan shiga inda ban taba shiga ba.
Kashi ga mana yaya meye sabo a wurin da zai dameni ga wace tayi rayuwa lagos kowa ya sani ba abune boyayye ba idon ta ya bude da mazan lagos .
Karki soma aiban ta min mata don ba zan lamunci hakan ba ga kowa kowa ya zauna a matsayin sa.
Raina ya kara baci da wanan magana bace basai ka fada min yar uwaka bace don nasan dama nice bare a cikin ku ai.
Zaki iya fadan komai yanzu lokacine zai nuna kasan idan muna da rayuwa daga haka yai shiru bai kara magana ba nima na juya na bashi baya na bar zancen.
Muna shiga gida dakina na wuce ban tsaya falo ba ko gaisuwan da maria ke min sama sama na amsa mata shi.
Shigowa yayi dakin dauke da ledan maganin da muka sayo yana miko min amsa nayi ba tare dana yarda na kalleshi ba.
Zuwa yanzu ma dariya nake bashi don daukan abinda nakeyi a shirme yake kallon shi niko iyakar gaskiyana nake masa hakan.
Ban kara fitowa falon ba sai bayan magariba na fito don yunwan da nake ji a lokacin.
Yara na falo suna assingment tare da fauziya nake tambayan ta ko sun biya karatun da take koya masu saboda ban son su rasa karatun addini tare dasu don zaman mu a kasan turai da mukeyi babu daman kaisu samun karatun addini din.
Sun biya a gurin yaya dazun da yamma kafin ya fita ta bani amsa daga hakan na wuce zuwa dining don jin ambatan sunan shi da tayi.
Ina cin abinci ne sai ga kira a wayana nomban kasan sudan dana gani yasa ni daukan wayan da sauri.
Mamuce a layin take kiran mu a lokacin gaisawa mukayi tare da tambayan kowa a bangarena nima na tambaye ta zaman sudan da mutanen su.
Tace suna lafiya fauziya fa ta tambayeni nace gata naba yarinyar waya suka gaisa take fadawa mamu ta fara zuwa school a nan london.
Bayan ta gama gaisawa da yaran har maria tace su ban wayan na karba ina fadin yaushe zaki koma Nigeria ne mamu ?
Ba yanzu ba ta bani amsa sai naji tace Sayadi mai ya hada ki da mijin ki kike neman tayar mai da hankalin shi ?
Shiru nayi a lokacin na kasa magana saida naji tace ashe baki da wayau sayadi ban sani ba ?
Wani abin yace nayi masa ne mamu kada ki kawo min shegantaka tace min kishi haukane da har kike nema ki zubar da mutuncin ki a idon mijinki.
Sayadi mutumi yana faman kokarin shi a kan ki dama mu duka shine zaki daga mai hankali don wani magana can da bai shafeki ba .
Har kina kokarin jawa kan ki matsala bayan kin san halin da kike ciki akan kine farau kishiya koke ba wata kika shiga kika samu a gidan ba.
Ke mace ina ruwa ki kin san donke za,ayi wanan auren shine don shirmen ki na banza zaki bari har a gane takon ki tun yanzu ?
Me zai dameki da auren shi da zai kara koda shi ya gani yace yana so dame ya rageki dashi a zaman ku.
Ba,a aure ke aka aureki ina wata kika shiga kika sama ta hana ya baki kulawa idan kika nuna rashin damun ki kece da pawer a wurin shi indai kin iya hakuri da gyara da ba mijin ki da yayan ki kulawa.
Namijin bahaushe ana hana shi yawan aure aure ne idan yana da hali yin hakan .
Shiru nayi ina sauren ta tace ki kwantar da habkalin ki Allah ya saukeki lafiya shine adduan mu.
Tadai ta min nasiha karshe kakata ta karbi wayan itama nasiha tayi min kan in kwatar da hankali ina haihuwa in koma makaranta kamar yadda nace.
Idan kin haihu zan ba kakan ki sakon mu na yan nan ta kawo maki ki dinga amfani dashi tace nace na gode grany kamar yadda muke kiran ta dashi.
Muna gama wayan nayi shiru kafin in mike naji abincin dana zuba ya fita min arai ba zan iya cinsa ba kuma a lokacin saboda yadda nake jin zuciyana yai min nauyi.
Na kalli maria da fauziya ina fadin maria kada su wuce tara basu kwanta ba ni zan shiga daki bana jin dadi jikina yau.
Sannu suka fara yin mun ina amsawa da kyat don yanayina daya sake a lokaci guda ina shiga daki na fada saman gado da karfi saida naji dan cikina ya motsa min lokacin .
Wani irin kuka na sake zuciyana cike da tsaban tunane kan sarakuwa da irin kiyayyan da take nuna min haka.
Ina kwance ina kuka sai gashi ya shigo dakin ya dan tsaya yana kare min kallin yadda nake kwance na kifa cikina kamar babu komai a jikina yadda nake.
Zama yayi a gefena yana fadin kin manta kina da mutum a cikin ki ne kika kwanta haka zahra yana magana in a cool voice kamar mai lalashina.
Na dago fuskana dake jike da hawaye nace mai nayi maka haka kake son hadani da mahaifiyata yanzu kuma ?
Don naga kina son wasa da rayuwan kine na kirata tayi maki fada saboda ni yanzu kin rainani .
Don kina ganin muna mu,amula tare ko mai ban sani ba don ban taba tsamanin haka daga gareki ba wallahi.
Eh zakace haka ai tunda kasan abinda kuke shiryawa kuyi min don kawai aga bayana a gidan nan.
Yanzu hardani kike tunanen za a hada baki aga bayan ki idan naga bayan ki in gane me a cikin yin hakan.
Kuka na kara wiwi yaja tsuki yana fadin to meye abin kuka a nan tunda kina ganin zaki kwatowa kanki yanci kuma.
Ko zaki iya fadin wani laifin da nayi maki a cikin wanan magana ke kanki kin sani ban sanda wanan zancen ba sai ta sanadin ki na fara sani.
Don dai kawai ki tayar min da hankali zaki tsiro da wasu halayen da bansan ki dasu ba a baya.
Don wata can da dukkan mu bamu santa ba bamu kuma san halinta ba har yanzu ko tazo mai zata gane a wurin ki yanzu tunda kin gama min da zuciyana ke kadai na sani a matsayin mace ta gari da zanyi alfahari da ita.
Shiru nayi ina sauraren shi don jin abinda yake fada yaci gaba da fadin ko mama ta matsa min sai na aureta ba a wuri daya zaku zauna ba don ba zan hada zuria,ana da wace ban gamsu da tarbiyanta ba.
Dadin kalaman sa da watan kurciya yasa na yarda da kalamin shi na dan dinga sauke ajiyan zuciya a hankali ina rage sautin kukan da nakeyi din.
Hakan ya bashi daman kai hannun shi ya rugumoni yana fadin zaki tayar min da hankali ga banza har yara sun fara maraicin farin cikin ki a cikin gidan nan.
Haka dai yayi tayi min dadin bakin su na maza har na manta da komai na sake jiki dashi muna dan hira sama sama har ya samu ya biya bukatan shi.
Washe gari ban iya fitowa ba har zuwa goma da wani abu ina daki sai danayi wanka na shirya na sauko kasa na samey su zaune tare da yara suna kallo yana zaune a tsakiyan su.
Fauziya da mariya suna kitchen kasancewa yau ranan satine babu aiki ko ina fitowa yaran sukayo kaina suka dugumeni suna gaidani.
Kansu na shafa daya bayan daya ina karba masu dan zama nayi muna hira dasu sai ga fauziya ta kawo min abin karyawa a inda nake zaune .
Lokacin cikin jikina yayi girma sosai ya turo na kara zama wata mace abun kallo da alfahari ga wanda ya mallakeni.
Na jawo abincin na fara ci kenan door bell din mu yayi kara da sauri maria ta mike a inda take ta nufi kofan zata bude .
Gaba dayan mu mun mayar da hankalin mu ga kofan don ganin wanda ke shigowa gidan don bamu faye yin baki ba kasafai sai lokaci lokaci mukanyi bakin.
Dan tsayawa tayi tana magana da wanda ke wajen haka yasa na mayar da hankalina ga abinda nake sha lokacin.
Merry ce da yarta queen sai wata mace da fuskanta kamar na taba ganin ta saidai na manta a inda na san matar.
Wanderful merry tace lokacin da ta karaso taja tsaye tana karewa falon namu kallon har yara da kowa lokaci guda.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button