SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:18 – ????????????: Yadda take tsaye tana kare muna kallon daya bayan daya nima haka nake kallon ta yayin da yaran suka mike suka nufi wurin shi sai sultana ne tazo inda nake zaune tana kokarin shige min a jikina.
Daddy who are those kids ?
Queen take tambayan shi tana karasowa gare shi ya dan shafa kan yaran ya kalleta yana fadin they are my kids allso.
Wani irin buga kafa ta kama lokaci daya tana fadin No no no dad i am d only kid you have mummy said.
She just say it to you she know a have those kids also, meet your twin’s brother,s and your sister yana nuna mata sultana dake wurina ta haye min jiki don shigowan su.
Da kyat na taushi zuciyana nace masu you’re welcome anty have a seat ina nuna masu kujera daga gefen su suna tsaye har lokacin tana karewa yaran kallon mamaki don bata taba sanin yaran sun kai haka ba ashe.
No ba zama ya kawo mu bayi na biyo mijina ne da kike kokarin kwace min daga gareni yanzu.
Murmushi na dan sauke a fuskana ina nuna mata shi da hannuna cikin ko in kula ina kokarin tashi da kyat tace .
What a surprise zan kara gani wani cikin ne kuma a jikin ki again ?
Lalai kun kai macuta na kwarai dake da wanan mayaudarin daya cuceni sai kuma ta kasa karasa maganan da takeyi don hawayen da yazo mata a lokaci guda.
Murmushi yayi a fuskan shi yace you can call me with any name you like na fada maki dama zan baki mamaki ai lokacin da kika tsiro yi min iskancin kan kin gama haihuwa dani .
Fadane sosai ya kaure a tsakanin su lokaci guda ganin haka nayi wa maria data sume a tsaye wuri daya signal da ido ta fahinci mai nake nufi.
Yaran ta fara kokarin ja ita da Fauziya zuwa dakin su don abin nasu yayi nisa sosai kada tazo suyi wani abinda ba daidai ba a gaban su.
Abu kamar wasa karamar magana yana shirin zama babba don hayani sosai sukeyi tun bai daga murya har yakai yana daga muryan shi fiye da nata sunawa juna tonon asiri.
Wani iri nake ji a raina don sai nake ganin hakan kamar rainin wayau ne zata zo har gida tana min wanan haukan haka .
Ya kamata nima in nuna mata nima mace ce don haka ina da yanci kamar yadda take da yancin yin hakan har gidana.
Nan da nan wani courage yazo min yadda nake jin kululun bakin ciki yana rufe min zuciyata lokaci guda.
Look madam merry wanan abinda kika zo dashi ki bari sai idan ya koma can gidan shi kuyi shi can na fadi with full confidence a fuskana.
Gaba daya suka juyo har shi suna kallona da mamaki fuskana babu sauki da gaskiya nake magana ina fadin.
Merry duk wani girma daya dace in baki ina kokari inga na baki daman ki na wace ke gaba a gareni .
Saidai yanzu na gane daga maki kafan da nakeyi yasa har kike kokarin cimun fuska har gidana.
Banje gidan ki ba, ban sakaki a rayuwana ba kamar yadda kema baki sakani ba bani kadai banw kuma kishiyar ki a yanzu da zaki matsa min dani da diyana kina tayar muna da hankali haka.
Na hade hannayena ina fadin na rokeki ki fita mun a rayuwa kamar yadda na fita a naki tun muna ganin mutuncin juna dani dake anty merry.
Ki bincika kiji dagani har shi ga yanan auren mu ba auren son kan mu bane mukayi aurene na hadin iyayyen mu gare mu don haka nake daga maki kafa don nasan mun shiga rayuwan ki a lokacin da bai dace ayi maki haka ba.
Kallon da take min ta mayar gareshi lokaci guda tana mamaki tare da fadin you have another woman again Omar ?
No no no sai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai lokaci guda ta juya da sauri ta bar falon da sauri queen da dayan matar suka mara mata baya lokaci guda.
Yana tsaye ya huci don bacin rai na dan kalleshi kawai na bar wurin zuwa dakina ba tare danayi mai magana a yadda nake jin zuciyana a lokacin.
Ina shiga dakina kuka ne yazo min mai taba zuciya sai faman tunane barkatai da nakeyi kan wanan rayuwan da muka tsunci kan mu a ciki.
Rayuwane garemu na tsaka mai wuya daga ni har yaya din da yaran mu sai yaushe salama zai samu gare mu wai a hakan.
Ga hjy data sani a gaba ga merry da nata kalan matsala duk kaina ita da mijin ta yanzu kuma ana kokarin jefo muna wata ita kuma ban san da wanda zata zo muna ba dashi .
Ga mama lami can gidan mu da ban san laifin da nayi mata ba take neman halakani ko wani lokaci ta samu sa,an yin hakan gareni.
Da wanan tunanen har barci ya daukeni inda dagani har shi banga laifin mu ba a karshe don rayuwan mu mukeyi ba tare da hassadan kowa a tare damu.
To mu me muka tsarewa mutanene suke kin mu haka wai saboda kawai munyi aure da yaya ne kome haka ke faruwa damune wai ?
Ban fito daga dakin ba sai bayan sallah la,asar na sauko yana zaune tare da yaran suna tula karatun addini.
Mummy you wakeup Abdulsalam yace min dan shafa kan yaron nayi ina fadin karatu kukeyi da daddy ?
Zama nayi dan daura dasu ina sauraren abinda sukeyi muryan Fauziyane ya dawo dani daga tunanen dana fara a lokacin.
Anty kici abinci tace lokacin da take aje min abinci a gabana na dago kai na kalle ta ina fadin na dai gane fauziya kina son ki batani dan kwanakin nan.
Dan dariya tayi tare da fadin naga kamar kina kiuyan zuwa dining kwanan nan kici abincin sai nan yasa nake kawo maki nan din.
Nace ashe kin gane fauziya bana jin dadin zama saman kujerun yanzu ban san me yasa hakan ba wallahi.
Ta juya zata koma kitchen ya kira sunan ta ta juyo da sauri tana amsawa ta nufo wurin shi.
Gani yaya tace tana dan rage tsayin ta don girmamawa Fauziya idan lokacin cin abinci yayi ki dinga kawo mata nata nan .
Da tau yaya ta karba tana tashi daga inda ta dan rage tsawon gare shi a lokacin.
Bude abincin nayi na fara zubawa a plate kafin inji yace dani zaki iya fita zuwa unguwa mu duba su Ramla kafin su tafi Nigeria bukin kannen Ahmed.
Zan iya na bashi amsa ina kai abincin dana diba a bakina don in kawar da komai kamar yadda mamu ta koyar dani nace buki zasu ashe kwanan nan ?
Yace eh bukin nasu ya zama na gidane ya kama dole yaje tunda shine babba kamar ni a gidan su.
Ashe muma in bukin su Nafisa da murja ya tashi zamuje kenan ko yace gaskiya banyi alkawari ba don ba dole bane sai ku kunje.
Dan kallon shi nayi kamar zanyi magana sai kuma na share naci gaba da cin abinci na a hankali mikewa yayi yana fadin zamu dan fita da yaran muje yawo.
Allah ya dawo daku lafiya nace mai ina nuna mai ba komai a raina don har lokacin yana cikin dan guiltynes dani kan zuwan merry da yake dauka zanyi magana a kan yadda tazo muna har gida da cin fuska.
Bayan fitan sune maria ta fito daga dakin su ita da fauziya da har yanzu itama bata iya sake jiki idan yana gidan.
Zaman su a falon ya dan kara sani sakin zuciyana don hira muke sosai dasu don yanzu maria ta zama na jikin mu sosai.
Nan nake masu hiran merry da dalilin da yasa nake dan daga mata kafa kan irin halin da take nuna min wani lokaci.
Basu dawo gidan ba sai da dare wuraren karfe takwas har sultana tayi barci shine ya shigo dauke da ita a kafada ya shimfideta a falo saman kujera.
Ya juya ya fita sai gashi yana shigowa da kaya niki niki a kwalaye da sauri su maria da fauziya suka tashi suna karba a hannun shi suna ajewa.
Daga inda nake zaune na idar da sallah nake mai sannu da dawowa ya karba yana fadin wanan bataci komai ba taki sakin jiki a can.
Wanan kan sai idan da maman ta aka fita take yarda ai fauziya ke fadi ku bata abinci taci yace yana kokarin hayewa sama zuwa dakin shi.
Saida yayi wanka ya fito falon lokacin dagani sai Fauziya a zaune maria taje ta kwantar da yaran a dakin su.
Dining ya nufa ya zauna yaci abinci yana gamawa ya mike yana fadin shi zai shege ke nan muka amsa mai da Allah ya bamu alheri ya shige.
Ban dade ba na mike inawa maria dake kawar da kayan daya shigo dashi kayan yaran ne sai ciye ciyen yara daya kwaso masu.
Wanka nayi na dan dade a dakina kafin in nufi dakin shi na tura na shiga da sallamana yana zaune yana duban computer har lokacin baiyi barci ba ashe.
Samun wuri nayi na kwanta ba tare da nayi magana ba saman gadon shima bai tankani ba sai da ya dan dauki lokaci naga ya mike ya kashe laptop din ya nufi ban daki.
Ya dan jima ya fito ya danyi abinda ya saba yi kafin ya kwanta kafin ya hawo gadon lokacin har barci ya dan fara daukana ko naji hawan shi saman gadon haka yasa na bude idanuna a hankali.
Jinayi yace dani nasan baki barci bako zanso zuwa safe kimin list din abubuwan da kike bukata don zanyi tafiya next week.
Maiyuyuwa koda zan dawo lokacin haihuwan ki ya matso ko ko kuma idan kina iya fita sai na baki kudin ki sayo abinda kuke bukata kafin ki kara nauyi.
Ina jinsa ban yi magana ba shima bai jira na bashi amsa ba yace zanso ki hada da kayan yarinyar nan fauziya da maria don an dade ba a sai mata kaya ba tun tafiyan mu gida.
Sai yanzu na gane nufin shi na fita da yaran da yayi dazun don ya sawo masu suturu ne ya fita dasu kasancewa ranan weekend ne.
Zan duba ida na samu lokaci sai mu fita tare dasu na bashi amsa ina gyara kwanciyana.
Nasan halin shi baya daga min kafa idan muna tare ranan ma kokarin lalabata yakeyi sai nace banjin dadin jikina tun rana nake jin marata yana min ciwo.
Shine samun saukina dashi ranan amma idan ba haka ba komai bacin randa yake ciki bai hana shi sauke laluran shi gareni.
Kwana biyu yayi a gidan mu kamar yadda yake a sharia muna zaune bayan karfe biyar sai gashi ya fito yana gyara agogon hannu shi yana fadin zanje wancan gidan.
Ko bai fadi ba nagane gidan merry yake nufi zai tafi lokacin Allah bamu alheri na iya fada a fili na kawar da kai.
Bai shigo gidan mu ba washe gari ga yaran suna tambayana yayi tafiyane nace masu eh baya garine.
Hakan ya dan sa zuciyana kara jin babu dadi da zamana a gida yafi mun wanan zaman nake gani a yanzu da a gida muke zanyi baki koni kaina i fita zuwa unguwa.
Ranan daya dawo duk yadda naso in boye bacin raina kan shere mu dayayi kwana biyu yana gari na kasa boye hakan gareshi.
Don yana magana da kyat nake iya budan baki ina bashi amsa karshema ya sherini kawai ya kama harkokin gaban shi.
Yana zama wayan shi yai kara ya dauka jin ya ambaci mama yasa na dan dago kaina na kalleshi kadan.
Bayan sun gaisa naji yayi shiru yana sauraren wayan kafin ya mike yana fadin idan ta haihu din ai zan bugo makune mama wallahi bata haihu ba sai wanan watan da zai tsaya idan Allah ya kaimu.
Yana fita falon yake fadin haka zuciyana ya ban don auren yarsu hjy ke tambayan idan na haihu badai don kulawa ba kam.
Ya jima bai shigo ciki ba har lokacin dana bar falon zuwa dakina don ban iya kara jimirin zama falin lokacin.
Bayan na gama komai na kwanta zuciyana ba dadi gareni sai faman tunane da nakeyi barkatai a raina kan hjy dashi yadda za a kwashe nan gaba ga zaman mu.
Ni tsorona shine kada hjy ta aura mashi yar uwanshi ta saka ya fita batuna nida yaran don yarsu.
Inzo ina ganin wullakanci don kudirin ta ke nan kawai a kaina yasa ta matsa da sai yayi wanan auren data lakaka mai yanzu.
Duk da banda niyar zuwa wirin shi haka bai hanani shafe jikina da lotion ba da kamshi a jikina kamar yadda na saba yi kullun koda baya gari hakan yanzu ya zama min dabi,ata.
Jin motsin an shigo dakin yasa na dago kai ina kallin wanda ya shigo min dakin.
Shine yana saye da dan three quarter da farar singileti a jikin shi ya nufo bakin gado inda nake kwance yana fadin.
Lafiya kike kikai saurin shiga barci yau lafiyata kalau ina dai son kadaicewa ne kawai na bashi amsa.
Zama yayi bakin gadon yana fadin zancen haihuwan ki mam ke tambayana kokin haihu ban fada masu ba.
Yaya ko ban haihu ba zaku iya yin bukin ku ai tunda sun damu in haihu kuyi bukin .
Murmushi ya danyi yana fadin naki tunanen ke nan kuma don ta tambaya ?
Kuka na fashe dashi ina fadin laifina guda yanzu wurin hjy don ina auren ka yaya da ban auren ka duk wanan kiyayyan da bai kai haka ba tsakani da ita sai dai ya tsaya iya su da mamu.
Zahra me yasa haka kina a wanan halin kike kokarin daga min hanka kan maganan da bashi ba a kullun.
Yaya dole hankalina ya daga da duk wani mai kaunata ina a wanan halin kuma ba,a barni na huta ba sai kokarin akeyi aga durkushewana ko yaushe.
Idan don auren kane ba hannun hjy a cikin sa hakan bai taba damun rayuwana ko kadan don ba,a kaina zata zauna ba idan ta shigo.
Amma kirkiri hjyn ku ke nuna min cewa tafi bukatan zaman ka da yar uwanka dani .
Ni dai rokona gare ka shine kada ka wullakanta ni kana rawan kafa yadda akeson kaimin don samu sabon wuri ni yanzu mai tsohon wuri a wullakantani yadda akeso a ga kayi min.
Magana ta ba karamin dariya taso bashi ba saidai ya daure kamar bai fahinci mai nake nufi ba ga zance na.
Zahra yaushe kika zama hakane wai ban sani ba duk kinbi kin daga hankalin ki a banza kan wani magana da baida tushe can.
Wani rawan kafa kikags inayi kan mace da zaki fara tunhumana kan wata can tun bata shigo ba.
Ke kinfi kowa sanin wanan auren zanyi shine don cika umurni kawai ba don son raina ki koyi hakkuri kina danne fushin ki tunda har kin san da manufa aka sharada min auren nan.
Kuka naci gaba dashi ins sauraren yana fadin wanan halin da kika dauko hakkuri ya kusa karewa a kanshi ina daga maki kafane don halin da kike ciki ba don komai ba.
Idan sakarcin ki ya kaiki kika bada wani kafa da za,a sameki wanan kuma ke kika jiyo don’t blamed me yana fadin hakan ya tashin ya fita daga dakin.
Washe gari ina daki naji sako ya shigo min a wayana ban duba ba sai dana gama abunda nakeyi kudine ya turo min masu yawa na sayayyan da zanyi lokacin.
Tambayan kaina nayi ni mai zan saye kuma kayan yarana ma wasu banyi amfani dasu ba.
Koda na fito ya fita kai yaran shi makaranta sai maria me ke gyaran gidan lokacin .
Mun gaisa da ita take fada min sun fita shida yaran ya kaisu makaranta.
Na dauka da yai muna kwana biyu gidan zai koma gidan merry ne kamar yadda yayi a baya sai naga sabanin hakan.
Haka yasa na gane merry bata garin kenan ta koma inda ta fito shima kwana biyu yayi tafiyan da yace zaiyi din.
Mun fita gaba dayan mu zuwa sayayya mun sayo kaya mai yawa kamar ban taba kudin ba daya ban .
Har watan haihuwana ya kama a lokacin ya dawo ya dawo da sati a wani dare na kuda ya kamani muka tafi asibiti abin mamaki sai gashi na kasa haihuwa kuma da kaina.
Saida aka kara yi min aiki ake cire min yaro a cikina wanan dana haifa duk yafi sauran yaran kyau da girman jiki.
Tuni wanan haihuwan ya mantar damu wani zancen kishiya can da muke badakala akai kowa hankalin shi a tashe sai yake ganin kamar zan mutu ne don wahalan da nasha a wanan haihuwan.