NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:20 – ????????????: Sai washe gari na dan san a inda nake a hankali na dan bude idanuwana da sukai min nauyi saboda wahala ina karewa dakin da nake kwance a ciki wanda babu motsin komai saina na,uran dakin dake aiki a lokaci.
Sannu a hankali na gane a inda nake kwance dakin asibiti ne kokarin daga hannuna nayi ina shafan cikin jikina sai naji wayau.
Hakan yasa na gane aikin aka sake min wanan karon ma ke nan shike nan ya tabbata ba zan iya haihuwa da kaina ba kenan ko me ?
Turo kofa akayi alaman wani zai shigo dakin ke nan lokacin haka yasa na dan mayar da hankalina ga kofan.
Nurse sai yaya dake bayan ta dauke da yaron a cikin showel ya rugume shi a jikin shi.
Suna kallona nurse din ke fadin thank god ta tashi ma before time din ya cika da sauri yaya ya matso bakin gadon yana min sannu da jiki na amsa mai da kai kawai.
Bayan hakan na dan kara lumshe idanuwa yace bude ido kiga baby din ki zahra namiji kika kara haifo muna wanan karon kuma.
Dan murmushi nayi ina bude idon nake kallon su shida yaron daya karkato min shi yadda zan ganshi da kyau daidai fuskana.
Zahra kinganshi kece ya biyo sak a kyau da fari ba ta inda wanan ya roki har yafi sultana kwaso kamanin ki sosai.
Dan murmushin na sake yi ina rufe idona daga kallon yaron ba tare danayi magana ba.
Nurse din ne ke fafin alluran bai gama sake jikina ba har yanzu su barni har nan da zuwa anjima idan na falka.
Ban kara sanin kaina ba sai goma na dare lokacin na tashi da wani irin matsakaicin yunwa lokaci guda.
Kokarin tashi zaune nakeyi naji muryan maria a kusa dani tana min sannu madam ya jikin nace da sauki maria sannu da kokari ashe kina nan ke nan tace eh oga ya koma gida don yara yace in zauna a nan.
Zaune nakai ina fadin maria yunwa nake ji sosai da sauri tace me zakici madam tea kawai zansha na bata amsa.
Da sauri maria ta tashi ta hada min tea mai kauri ta miko min a inda nake zaune tana kara yi min sannu har lokacin.
Na amsa sai nake fadin ba zan iya sha ba ban wanke bakina ba maria da sauri ta karbi tea din a hannu na ta aje tana kokarin mikar dani tsaya nace ta bari zan iya ai
Saida na wanko bakin na dawo na zauna na dan kurbi ruwan tea ban wani sha sosai na miko mata cup din da sauri ta karba ta aje gefe.
Ban kwanta ba don na gaji da kwanciyan tace madam kina da sa,an haihuwa yaran ki duka masu kyau kamar ku wanan har yaso yafi twins kyau sosai.
Oga yana ta murna sai bugama yan uwan ki waya yakeyi kin haihu murmushi nayi don jin abinda take fadi a raina kuwa cewa nayi wata kila ya gyara halinsa ne yanzu.
Ko kuma ya bugane don asan na haihu don su fara shirin bukin su da suke jiran sai idan na haihu din suyi kamar yadda ya roka a bari har na haihu ayi.
Tabe baki nayi da wanan tunanen yazo min a rai nace maria yaron yana lafiya ko tace lafiya yake sosai madam kullun sai an kawo shi nan ya dan sha dumin jikin ki.
Duk hiran da take min sai dan murmushi kawai nake iya mata a lokacin saboda yanayin jikin da nakeji ba dadi.
Kwana daya na kara aka sallameni daga asibitin bayan sunga na samu lafiya muka koma gida a gida duk wani kula da gidan yana kan maria da fauziya.
Don ni ko falon bana fitowa ina daki ko wani lokaci don yanayin jikin nawa inda muke samun yan barka jefi jefi yan kasan mu da muke hurda dasu can suna shigowa barkan samun karuwan mu.
Ina da sati daya da dawowa asibiti kwatsam saiga Nafisa a garin kamar daga sama don bai fada min zuwan ta ba.
Ban yarda na nuna komai garesu daga shi har ita kawai dai na mata taro yadda ya dace aiwa bako idan yazo kamar babu komai a tsakanin mu dama.
Zuwan ta yasa nake dan fitowa falo yanzu muna zaune muna hira take fada min aida hjyn su suka so zuwa saidai saboda zancen bukin yaya da za, ayi kwanan yasa basu zo tare ba.
Ban yarda na nuna mata ko wani re,action ga maganan ba sai cewa da nayi gaskiya kan dole sai hjy tana kusa zaifi.
Ta kara fadin ai mun dauka zaku zo sai yaya ke fadin sai kin kara jin sauki zaku shigo gaba dayan ku.
Don shinema hjy tace ai in shirya inzo tunda ita ba zata samu zuwan ba kuma nace kin ko kyauta muna aida kikazo don ba wanda ya taba zuwa wurin mu sai yaya Aliyu koshi sau daya yazo kasan nan.
Zaman mu ba wani matsala ina sati biyu cif da haihuwane ranan da dare hjy ta kira yayaa waya tana fadin Nafisa ta iso lafiya ko don naji baka kirani ba sai kuma zancen auren ka yaya najika shiru lokaci yana kara karatowa.
Yace da wuri haka mama tace a fusace a wurin kane yake da wuri kada ka mayar dani wata bi can nina haifaka bakai ka haufeni ba umurni na baka dole kazo don karshen satin nan ne daurin aure.
Don yanzu haka har an fara sha,anin buki kazo ko kada kazo yanzu ya rage naka kuma aure dai ba fashi na fadamaka.
Amma mama har yaushe Zahra ta haihu haihuwan nan kuma fa kinsan aiki akai mata da za, ace na tsira buki yanzu ko suna bamuyi ba na yarin anan suna kawai aka rada mashi.
Fatimar tafi wanan da taketa jiran kane bukatan ka kome na fadama wanan karon ba zan daga wanan ranan ba.
Tana fadin haka ta kashe wayan ta tana huci shima kanshi ya dafe yana fadin innalillahi a fili.
Sharan kiran Amma yayi koda abinda zata taimaka mashi a daga wanan auren har zuwa wani lokaci nan gaba.
Amma na daukan wayan sun gaisa yake fadin Amma kinji fitinan da mama ke shirin jefani kuma a ciki yanzu ta kirani wai daurin aurena karshen wanan satin za,a daura.
Yanzu mai mama take kokarin yi min a rayuwana ya take inyi da yar mutane da nake jinyar ta a nan ?
Amma tace cikin yanayin damuwa muma haka wanan zancen yazo muna dazun nan mahaifin ku yake sheda muna zancen wai ashe bukin ya tashi.
Kayi hakkuri tunda haka shine farin cikin uwarka aure in anyishi a tafarkin Allah ai alherine sadauki.
Indai da zuciya daya sukai wanan hadin Allah yasa hakan shi yafi zama alheri ga rayuwan ku ga baki daya.
Idan kuma bada zuciya daya ake shirin yinsa ba don wani kudiri nasune, Allah ya tarwatsa aniyar su.
Ka kwatar da hankalin ka kai mata biyayya yadda sharia ya tanada muna tsaye gareku da addua akoyaushe insha Allahu sai alheri aruyuwan ku kaida iyalin ka.
Yace yanzu Amma matsalan ai shine yadda zan tunkari Zahra da wanan zancen tana fama da kanta duk a sanadin haifar min yaro datayi.
Kada ka zamo umar din mata mana mai sunan ka da jarumta akasan shi ko a inane kuwa balle kaida matar ka.
Yace Amma na gode don dole yau in fada mata saboda kwana biyu kawai ya rage min ke nan in zo Nigerian.
Amma tace hakana zaka daure ka fada mata Fatima inba ta canza ba zata fahince ka ai yace Amma na gode Allah ya shige muna gaba tace Amin ya kashe wayan.

Saida ya gama duk abinda yakeyi ya shigo dakina ina zaune rugume da Abbana don sunan mahaifina Abubakar ya sakawa yaron.
Muna kiran shi da daddy yayi sallama na dago ina amsa mashi ya tako har zuwa inda muke yana lakatan bakin yaron dake zukan nono hankali kwance.
Fauziyace ta mike da sauri zata bar dakin yake fadin aida kin zauna abinki ba dadewa zanyi ba bata dai tsaya ba ta fice daga dakin kawai.
Zama yayi dab da inda nake zaune yana fadin wanan kamahin fa haka yana kai hannunshi don karban yaron a hannuna.
Murmushi nayi kawai banyi magana ba a lokacin yace zan shiga Nageria zuwa jibi zahra don mama ta kirani dazun da magariban nan nadai yake fada min wai zancen bukin shi ya taso zai tafi Nigeria ayi bukin.
Allah sanya alheri na fadi ina kokarin dauko abu bakin gadona yadda na bashi amsan kai tsaye ya tsaya yana karemun kallo da mamaki a fuskan shi.
Na juyo ina fadin munyi waya da mamu tace zatazo kafin ta koma gida ba wani nuna damuwa a fuskana yadda ya zata nake magana na freely dashi.
Yace har yanzu ashe bata koma gida ba nace ko yanzu ina ganin ba maza ba don ko zata koma ina ga ba,a wanan gida na kawu zata zauna ba don tace gidan da zata koma ana gyaran shi a yanzu haka.
Kara mayar da hankalin shi yayi wurina sosai yana mamakin abindana fada nace eh iyayyen ta wai sun turo an saya mata gida kano tace unguwa dayane dana kawu a nan cikin old GRA ne gidan yake.
Amma ina ganin ko daddy baisan da wanan zance ba balle mama yake tambayana nace wallahi ban sani ba yaya.
Yaji dadin yadda yaga ban nuna damuwana da auren shi ba a yanzu tun bayan dawowana asibiti ban kara tayar da wanan zancen ba muna zaman mu dashi lifiya yana kuma bamu kulawan daya dace mu samu a wurin shi.
Don haka na tatara zancen na watsar a raina bayan zurfin tunanen da nayi tun zuwan merry gidan mu naji kalaman bakin yaya din naba kaina lafiya.
Ya dan jima dakin muna magana kan zuwan Nafisa wanda sai wanan lokacin ne yake fada min yadda akayi tazo din.
Don hjy ce ta nace kan dole sai wani nata yana gurin wanan karon don asan shima yana da yan uwa a duniya.
Ai hakan yana da kyau na bashi amsa kaga yanzu tasan inda muke zaune ai yace gaskiyane hakan nagode da baki nuna komai akan hakan ba don nasan ba ku wani jittuwa a tsakanin tun gida saboda hakan ina kara baki hakuri ku rabu lafiya har lokacin da zata koma din.
In dai nice yaya lafiya zamu rabu don kowa yasan halin kowa a cikin mu don haka zanyi hakkuri da ita insha Allahu.
Kamar Nafisa tasan munyi wanan magana a kanta sai gashi ta fara tsiro da wasu halaiyan da zai iya kawo muna matsala a tsakani mu.
Da yara ta fara a gidan mussanman ma fauziya da nasu baizo daya ba don kamar yadda basu kaunana harda su da suka fito tsatso daya haka suke nuna masu ko yaushe .
Dan abu kadan zatayi yanzu zata hauta da zagi kamar zata duketa ina kokarin kawar da idona kan hakan don na kula da yarinyar har ta fara tsarguwa da hakan yasa idan tana falo sai ince mu koma daki tare da ita idan suna gida.
Sai kuma abin nata ya koma ga yarana har dukan su takeyi da sunyi dan abu kadan zata kwashe yaro da bugu ko zagi.
Ina iya kokarina wurun tausan zuciyana kan hakan don ba zanso taga wani bacin rai a wurina ba ko kadan don nasan da gaiya take hakan.
Ban nuna mata hakan yana min ciwo sai kuma ta tsiro yi min hiran da auren da yaya zai kara kan irin shirye shiryen da gidan Amaryan sukeyi na bukin.
Nan ka na bata amsa da fadin ana gabas suna yamma ke nan sai wanan uban shirin daga bangaren Amarya kawai ba ango.
Kin sani ko duk shi bada kudin da ake wanan facakan haka nace balle kinsan ai dole ya basu tunda yana dashi.
Don ko bai bayar ba hjy saita basu a matsayin shi tunda baza a bari aji kunya ba Allah yasa ya tura masu kudin dai.
Haka nake biye mata mu zauna muyi ta hira kan bukin ina nuna mata ni ko a jikina hakan bai dameni ba.
Ranan muna zaune take ce min wai ke Fatima ba zakuyiwa yaron nan suna bane kome ?
Don naga har yana batun cika sati uku da haihuwa ba suna nace kinsan nan ba wani taron suna akeyi ba ai tunda ya je masalci aka rada ma yaron suna shike nan.
Tace cabdi jam ina na taba ganin haka a rayuwa namiji ke nan fa yana can yana bushashan shi da amarya ya fita zancen sunan yaro da aka haifa mai.
Balle samira tashin binni ne ita ta waye har ta gaji duk iya bude ido idanun su a bude yake tar.
Shiyasa da akace wai a gida daya zaku zauna nace ashe akwai aiki don zama da irin su sai ka shirya don ba barin kishiya ta zauna lafiya da miji sukeyi ba.
Nace Nafisa ke nan yaro ai gida yazo itako amarya ai bakuwace yanzu a ciki mu kinga gara dai a fitan kunyan bakin ido ko ?
Sanan budewan idonta ai ga iya mijinta zai tsaya shida ya aje ta all what ni wayen ta bai taba damuna ba a yanzu fatana mu zauna lafiya dai.
Wai ke fatima wata irin mace ce haka baki ko dan gwada kishi irin na mata ko kadan duk inda aka fito da zancen sai ki tare.
Mezanwa kishi Nafisa mijina yana tsaye a kaina da diyana harma da yan uwana idan nayi haka ai na zama butulu ke nan .
Sai naga tayi shiru ta bata fuska ta shigo dogon nazari kamar mai tunanen wani har muka bar wurin bata kara wani magana kwakwara ba a ranan.
Ta dauka maria bata jin hausa don ban dadewa a falin nake shigewa saboda jegone a jikina don falon ko yaushe a cikin sanyi yake sosai.
Waya ta dauko bayan shiga na tana waya da hjy su maria na kitchen tana jin duk abinda suke fadi a falon.
Maria ta labarta min duk abinda taji Nafisa na fadawa uwar ta a waya game damu har da irin daulan da yaya ya sakar muna a gidan da yadda mukejin dadin rayuwa a nan.
Tace komai tayi min cikin abinda ta kitsa sai inyi kokarin kare yayan da kalamai masu dadi sam ban yarda naga laifin shi ba balle ta samu kafan kulla min shirin su nagaba.
Saidai bataji abinda hjyn ke fadi a nata bangare maria tana fada min wanan magana hankali a tashe.
Maria kin san Ogan gidan nan zai kara aure gobe shine plain din su na zuwan Nafisa kanwarshi nan don ta tayar min da hankalin da zan samu sabani da mijina.
Shine hikimar hjy na turo min nafisa a nan a matsayin ta na yar leken asirin hjy don tazo taga irin rayuwan da muke anan asan hanyar da za,a samu nasara a kaina.
In Allah yarda saidai suyi kunya nowarder take muna abinda taga dama da izza a gidan nan wanda koke matar gidan baki min shi.
Zataci abinci tabar plate ko cup a wurin kamar ba mace ba zata cire kaya ta barshi sai idan nina shigo dakin na dauke a kasa ko saman gado.
Ba karamin dadi najiba da kika raba Fauziya da dakin nan yanzuma yaran nake son kwanan su ya dawo nan wurin ki har lokacin da zata koma.
Duk da na kula da hakan nima yana bata min saidai don alkawarin dana dauka a raina harta koma inda tafito.
Tunda maria ta fadi hakan nasan akwai abinda takewa yaran wanda bai dace don haka zanbi shawaran maria din a cikin hikima kada ta illanta min yara wurin hakkurina .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button