SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:20 – ????????????: Yadda hjy taso hakan bai samu ashe don yaya bai samu isa ba sai bayan sun gama shagalin bukin su wanda haka yaso jawo matsala a tsakanin su da uwar samira amarya.
Hjy ita tai uwa tayi makarbiya ga komai sai yan uwan shi da suka tsaya mai dan dole da yan abokai kamar su Nasir suna tsaye a wurin bukin.
Hjy bata samu dawowa gida don can ta tare a gidan namu duk da part din mu na ainihi yana rufe sai wanda aka gyara daga baya don Samiran ta zauna a ciki.
Wanda hjy bata so haka don cewanta namu part din yafi kyau da tsaruwa da komai dole a ciki samira zata samu daki itama.
An buga da yaya yaki yarda da hakan yace haka ya tsara abinsa babawa anya kana da niyar adalci a tsakanin iyalin ka ?
Hjy ta tambaya yace muddin zanwa sauran adalci har suka zauna dani zuwa yanzu itama zan mata ai kamar yadda nakewa kowa saidai idan halinta ya bambamta dana sauran wanan kan ba zata ji dadina ba.
Duk wanan a waya sukaita musayan yawu da mahaifiyar nasa hakan yasa ba,a bude wanan part din namu ba.
A gajiye ta dawo gida washe gari koshi tana gudun ta kara kwana kawu yai fada don taso sai ya Umar din ya iso gidan taga zaman su zata koma gida.
Da hjy maryam suka ci karo tana kwasan shaya a waje tayi mata sannu da zuwa ta amsa tana shan kamshi kamar yadda ta saba a kullun.
Tun daga nesa ta hango kofan a datse da katon kwado abin ya bata mamaki sosai na ganin hakan a kofan part din ta.
Bata yarda da abinda idon ta yake ganan mata ba sai data karaso kusa ta taba kwadon taji kofan a rufe .
Juyawa tayi tana tambayan hjy maryam daga nesa wa ya rufe min kofa haka da wanan kwadon ko Nura ne da cewa dan autan ta.
Wallahi ban san an rufe ba sai yanzu da kike magana Nuran baya ciki ke nan hjy maryam.
Yana ciki za,a rufe dashi muryan kawune ya katse masu magana yana fadin nine nan na rufe kofana .
Sai ki koma can inda kika fito tunda kin cika burin ki na kimin bakin ciki akan taimakon danki da nayi kike dauka da wani manufa nayi mai aure da fatima.
Har kika dauka yimai aure ta fanin ki shine zaisa ki fashe zafin abinda nayi maki .
Banyi tsamanin zaki manta da alkwarina ba akanki ko har kin mantane nace Amaryan ki na shiga dakin Faruq ke kuma kina fita naki dakin da sunan aurena.
Alhamdullahi Allah ya cika maki alkawarin ki nima kuma ya cika min nawa Allah yaba da zaman lafiya yana fadin haka ya dogara sandan da yake bashi kariya ya bar wurin.
Kallon mamaki duk wanda ke wirin yake bin kawu dashi ya wuce abinshi cikin halin ko in kula garesu.
Wanan mutumin mai yake nufi da yin haka dayan kanwar hjyn da suka kwaso ganiman bukin sunzo dashi su raba take fadin haka.
Duk abinda yake nufi a shiye nake da shi tana fadin hakan ta juya ta nufi kofan Amma a hasale.
Ta samu Amma na ggugan goro a jikin wani dan kwanko a hannun ta ta shigo da sallama a hasale.
Bayan karba mata da Amma tayi tana fadin kun dawo ashe bata bata amsa ba sai cewa tayi na dawo na samu Alh ya rufe min kofan part dina yanzu.
Garin yaya kuma ya rufe maki kofa dakin ki takai zaune don yadda take ji kafuwan ta ba zasu dauke taba a lokacin kamar ba ita bace ta dawo da farin ciki yan mintutukan da suka shude.
Wanan halin naku da girman ku kuna abinda yara ba zasuyi ba a gidajen su yau lafiya gobe fitina wanan hali naku ya isheni a rayuwa.
Tana kokarin yunkurawa take wanan magana tana fadin ina shi yaron nan yana gidan tace yana nan yanzu ya gaya min shi ya rufe kofan don haka yai alkawari.
Amma dake shirin fita taja ta tsaya wuri daya tana fadin ke nan alkawarin ku kowa ya ciki kuke nufi.
Shiru hjy tayi don bata da amsan da zata ba tsohuwan a lokacin sai kuma Amma taci gaba da tafiya ta nufi waje.
Mama hadiye ta biyo ta a baya tare da hjyn part din kawu ta nufa yana ganin ta yana zaune a kasa saman kafet ya hada hannayen shi yana fadin don girman Allah hajiya kiyi hakkuri ki barni da matan nan tunda iyakana take son nunawa duniya.
Jin da Amma tayi ya hadata da Allah yasa takai zaune daga inda take tsaye tana fadin wanan rayuwa da kuka dauko dame yai kamane haka a gidan nan.
A haka rayuwan yayan ku da iyalin ku kuke son suyi koyi daku kuna wanan halin kullun a cikin tashin hankali irin haka ?
A daidai lokacin hjy ta shigo dakin ya kalleta yana fadin me kike ma har yanzu a gidan nan na fada ba zan sake fada ba na yanke igiyan aurena daya a kanki wanan abin ya kare hakana tsakanina dake jimmai.
Alh kana dauka idan kaimun haka zan damune yace don nasan baki damuwa na tabbatar maki da hakan yanzu.
Hajiya wanan ba yar mutunci bace ki koma part dinki zaifi don bata sam Annabi ya faku ba har yanzu duniya sabuwace a gareta ita.
Sam bata tunawa da mutuwa a tare da ita har abada yana fadin haka Amma ta mike tana Allah ya kyauta don bata iya tsayawa wurin kuma.
Tun Amma bata karasa fita ba hjy ke fadin yadda ka sakeni akan wanan yarinyat nima haka zan saka dana ya sake yar taku inga ta tsiya.
Kawu yace bissimillah karki fasa abinda kikai niya ki gani da ita da danki wanda zai wahala a yanzu.
Wanan magana da kawu yayi shi yakara konawa hjy rai sosai tana fita a kunyace tacewa yan uwanta biyu suzo su fice a gidan.
A,a anty kada ai haka gara dai kiyi hakkuri ku sasanta zaifi ace kinyi fushin zuciya kin tafi tare damu.
Rakiya kina son in zauna inga wullakanci a gidan nan fiye da wanda Alh yaimin a yanzu gaban mahaifiyar shi.
Gaban wanan tsohuwar Alh ya furta ya yanke igiya daya a tsakanin mu ni Alh zai furtawa hakan saboda yar agolan gidan shi.
Yasakeki sukace cikin mamaki hanyar fita gidan ta tanufa kai tsaye suka mara mata baya hankali tashe duk jikin su yayi sanyi ga abinda ya faru.
Suna fita take fada masu yadda yayi alkawari tun farko idan har tasa Umar yayi wanan auren ranan itama zata bargidan.
Ajiyan zuciya hjy Rakiya ta sake kafin tace yanzu ina muka dosa daga nan don dai ba zamu nufi gidan yaya ba ko kawu da wanan magana mara dadin ji haka.
Don gaba daya laifin mu zasu gani kan hakan a karshe don sai su dauka da zugin mu hakan ya faru yanzu.
Nima tunanen da nakeyi ke nan yanzu gidan babawon zamu koma in zauna har ya iso garin nan .
Saidai yadda sukai min ko su haka zan saka sadauki yaiwa yar tasu da suke ganin ta kafu a gidan.
Sai naga bayan wanan yarinyar ina fada maku dani Alh ke wanan wasa bai karkare sanin halina bane har yanzu.
Yan uwan duk abin duniya ya ishe su a rayuwa don basu ji dadin kalman sakin da kawu ya furta mata ba haka kai tsaye.
Gidan sukaje kamar yadda tace saida sukai horn yafi a kirga kafin maigadi yazo ya bude masu kofa su shiga.
Samira da ke zaune da kawayen ta da yan uwanta sai ganin hjy sukayi sun dawo tayi saurin mikewa tsaye tana tambayan hjy lafiya naga kun dawo kuma ga kaya haka.
Bude muna wancan dakin mukulin shi yana cikin keys din dana baki hjy tace kai tsaye.
Ba musu samira ta dauko key din tana gwadawa dakin ya bude suka shiga nan suka barta tsaye tana mamaki su kuma.
Sace jiki samira tayi zuwa daki ta kira mahaifiyar ta tana fada mata zuwan hjy gidan tana fadin da alama umma a nan take shirin zama tare damu don da gani babu lafiya.
Wani ashar hjy sabuwa ta lailayo ma hjy jummai tana fadin jummai fa bata da wayau sai na gyara mata zama idan hakane.
Ta kamanta dai gidan dantane ko shiyasa ta kwaso kafa tazo maku gida gotai gotai da ita don bata san kunya ba.
Shima shashan dan nata mai daukan kan tsiyan banza me yake jira har yanzu bai shigo kasan ba mu fara dashi.
Samira tace nima umma abinda ke damuna ke nan rashin zuwan shi har yanzu kasan .
Hjy sabuwa tace zai gama kwanaye kwanayen shi ai yazo hannun mu kwana nawa zamu gama dashi .
Karamin kudi na kashe kan wanan auren kafin in samu ya yuyu na uwarshi mai sauki ne ban dauketa wata tsiya ba can.
Aiko zargin su ya zama gaskiya don sai gashi hjy ta kwana daya biyu a gidan sai rana na uku yaya ya iso Nigeria a cikin dare .
Idan ranshi yayi dubu a bace duk suke saboda labarin abinda ya faru da mahaifiyarsu da Aliyu ya kira yana labarta mashi.
Shiko habib cewa yayi gwada Alh ya nuna ma mama hakan don ni banga laifin shi ba tunda ya fada mata tun farko taki ji.
Itama hjyn sanin halin habbib din yasa bata kirashi sunyi maganan ba sai Aliyu don tasan ba zataji kalman dadi a bakin shi ba.
Don shi a tsatsaye yake tun farko gaskiya komai dacin ta baya gudun fadan shi ko ga waye.
Direct part din mu ya nufa yai wanka ya samu wuri ya kwanta bai ko tsaya neman wani abu da zaici a cikin shi ba yana Allah Allah gari ya waye mai ya fito.
Samira bata tashi sanin yazo garin ba saida safe yarinyar da suke zaune tare take fada mata taga sabbin motoci a gidan kuma wancan dayan shi a bude yake yau.
Da mamaki samira ke kallon ta tace ki koma ki gani ko waye ya bude idan ba wanan yar hawan jinin data zauna muna bane nan.
Samira uwarta ta kira take fada mata abinda yarinyar tazo ta fada tace ke me kike jira baki fita kin gani ba.
Barin gaya maki kada ki tsaya wanan shegen sanyin jikin naki yanzu har su samu sallon takaki a gidan.
Ita wacan jikan bakaken larabawa mai shegen wayau an gaya maki haka takeyi dashi data mallakeshi ko uwarshi bata iya kwabashi akanta.
Don idan ba kinyi da gaske ba kinyi da gaske kika mallake kowa tun yanzu ba sai kin zama bora a gidan in fada maki.
Gida dai tunda mun samu kin shigo da karfi da yaji don haka saiki dage ke kuma yanzu kiyi duk abubuwan da muka karbo mu samu mu mallake yan baza ga baki daya.
Haka dai uwar tayi ta zugata da mugayen shawara har taji wani karfin gwiwa yazo mata lokaci guda .
Suna gama waya da uwar ta mike cikin karfin gwiwa ta nufi hanyar fita daga part din ta suka hade da yarinyar data turo din.
Da sauri yarinyar ke fadin wallahi anty ins ganin maigidan ne don naga yan aikin gida suna ta shiga gaidashi.