NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Nafisa dake zaune ta kurawa tv dake aiki ido tun zaman ta a wurin take faman tunane a ranta.
Gaskiya ita yanzu gida take muradin zuwa wanan zaman kadaicin haka ya ishe ta ace mutum ko rana baya gani balle dan adam kana cikin gida a kulle jiddadun alaina baka ganin komai a garin.
Tana mamaki na yadda bata ga mun damu da fita ba dagani har maria dake wuni a tsaye tana muna aiki a gida.
Na fito daga daki ina daye da wani bakin wando da ya dan zarta wuyan kafana kadan sai dai bai sauka min ba kasa.
Sai rigan daya dan sauko min har kysan gwiwa mai umberal sai dai ta kare min kallon yanayin shigana take fadin.
Wai ke fatima haka kuke zama wanan garin zugu zugun ba fita ba komai kullun mutum a gida.
Har mama wai tana ganin wani daula da jin dadi kuke ciki nan ashe abin ba haka yake ba ma ashe .
Yawo kike son fita tace min tun zuwa na garin nan baki fita ya kai sau biyu ba gaskiya idsn mutum ba yazo yaga yadda kuke rayuwa ba dole idan ya ganki yayi zaton duk komai na yaya yana hannun ki ai…

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:20 – ????????????: Sauraren maganan nafisa nakeyi kamar a mafalki don azaton su ashe a cikin daula nake sai abinda naga dama nake a gidan dan uwan su.
Ke nan wanan zuwan ya fara wankeni daga zargin da suke min ke nan a baya ni dai nasan su matane dole gidan wani zasu su zauna kamar yadda nake zaune a gidan dan uwan su.
Tabbas ko wace mace sai tayi irin wanan rayuwan da yan uwan miji wata rana dan dama ma ni nawa dangin mijin yan uwanane amma basu raga min ba a cikin zaman mu don wani dalili nasu can da suka ratayawa zaman namu.
Hakane kuma suma nasan ko wace zata fuskaci irin nata kalubalin daga yan uwan mazajen su kamar yadda suke min suma.
Don hakane na nake hakkuri da komai ina danne abinda duk Nafisa take min na takalan bakina don kawai ta samu madogara ga kudirin ta gareni.
Kallon ta nayi bayan gama tunanena ina fadin Nafisa ke nan ai kin san dama idan mace tana zaune kalau da mijin ta hakan mutane kanyi zato gare ta.
Sai su dauka tana zaune tana juya mijin ne ita son ranta sai abinda taga dama takeyin shi a gidan basu dauka hakkuti da jarircewan wasu matan ne yake kaisu ga hakan.
Nafisa idan kinyi wa zaman mu da yaya adalci ni ko shi har yau ba wanda ya taba korafin wani a gidan mu da sunan rashin jin dadin zamantakewa da dan uwan shi.
Nafisa ke kin sani ba wai bamu samun sabani bane a tsakanin mu kwarai muna samu saidai hakkurin da Allah ba kowane a cikin mu ya hana har mu bada kafa a fahinci hakan.
Ke dai yanzu ganauce kinzo kinga rayuwan da muke a gidan nan daga ni har yaran mu ba wai wani abin duniya da kuke tunane bane yaya yake sakar muna, muna yadda mukaga dama a gidan nan .
Rayuwa muke na sese wa sese da zama rufawa junan mu a siri yadda ya dace duk wata macen kwarai ake bukatan samu hakan a wurin ta.
Yanzu kinga ke nan zaki koma gida da hujjan kan abunda idon ki ya gane maki a zaman mu gidan nan .
Wanda kuke ganin kamar wani daulan duniya nake cikin shi zaune a nan tace da sauri wa kike tunanen zan fadawa hakan ?
Bawai ina nufin ki fada kai tsaye bane ai Nafisa kawai na tabbatar da idan magana makamancin haka ya taso a kan mu kina wurin zaki bada shedan abinda kika gani wa idon ki ai.
Sai lokacin naga ta danyi murmushi kadan a fuskanta tana fadin kwarai kuwa don ni din dai ganauce don ban zaci hakan ba gaskiya a zaman ku.
Duk da dai ba a gane tsakanin miji da mata sai Allah amma dai duk da hakan na fahinci dan wani abin yanzu kan zamantakewa na aure wanda a baya ba haka na dauki abin bani.
Mun kai wani lokaci muna jefawa juna magana a dunkule da sunan hiran salma wanda kowan mu ya gane nufin dan uwa.
Rashin dawowan yaya har sati hudu yasa na fara shirya yadda zan fara karatuna don dama mun gama magana dashi haihuwana ne ya tsayar dani kan hakan amma na dade da applying anyi komai.
Nafisa kan iya gajiya ta gaji da zama wuri daya don bata saba da hakan ba ita ni har mamaki take bani don idon ta yanzu ya matukar budewa kamar ba yar gidan kawu bace ita.

Muryan hjy sabuwa ce ya tayar dasu ranan daga barci don kamar a hanya tayi sallah asubahi a yadda tayi sakkon zuwa gidan cikin rashin mutunci.

Bada kowa take wana jidalin ba saida hjyn su yaya tana fadin yo jummai ai bansan makira kike ba sai yanzu.
Haka kawai kin wanko kafa kin dawo gidan yara cikin ki kin zauna don kawai ki batawa Samira jin dadin auren ta.
Ashe kin yarda an hada wanan auren ne don ki yaudaremu ki samu daman da zaki dawo gidan danki ki zauna ki kasa ki tsare don sheri.
Budan kofan da akayi yasa ta tsaya ta dan dakata da maganan ta don ganin wanda ke fitowa a part din lokacin.
Hjy jummai ce ta bude kofan tana kallon hjy sabuwa da mamaki hakan bai hana hjy sabuwa fasa fada abinda take fadi ba a lokacin.
Tana fada ta nufi cikin part din a hasale tare da fadin tabbas kuwa na sheda don ga zahiri nagani yau hjy jummai kinsan kunya kuwa ?
Ki rasa inda zaki tare sai a gidan yarinyar dake ganuwan amarci da mijin ta kinzo don rashin ta ido kin zauna masu a gida kin hanasu rawan hantsi a gida don kawai kina takama gidan danki ne nan.
Hjy sabuwa irin sakkaiyan da zaki mun ke nan bayan duk abinda ya faru sanin kanki ne a dalilin auren yarki ya faru dani.
Ni zakizo ki watsawa kasa haka ga ido tunda farar safiyan nan haka a gidan nan .
Naki dai ki daina cewa sanadin samira hakan ya faru dake don Allah kada makiya suji su canfa min yata ga banza.
Yo koma hakan ne yanzu ke daidaine ki dawo nan ki tare masu nan ne kawai gurin zama a cikin gidan nan kome ?
Wallahi jummai kinban kunya don ban zaci hakan da wuri a gareki ba koma me kika shirya ai kya bada lokaci ko ?
Hjy da imani da mamaki ya cika lokacin kasa magana tayi don jin abin take kamar a almara wai duk gwagwalmayan da take sha duk akan auren yar sabuwa irin sakaiyan da zatayi mata ke nan da farar safiyan nan.
Samira da bata son auren ta ya balgace ne takewa uwar nata magana kamar a fada haba umma yakamata abi abin nan a tsanake bada tashin hankali haka ba.
Ta juya wurin yar tana fadin barni in fada mata gaskiya idan bakanta ya kamatane ?
Mama wai me ke faruwa hakane a gidan nan muryan wa nakeji cikin rashin kamun kai zai shigo muna gida da safen nan da masifa haka ?
Wanan wata irin bakuwace haka mai kaifin harshe mara tunanen gidan mutane tazo da safen nan take wanan nuna tarbiyan haka gareki.
Aliyu ne da sauran yan uwanshi da dawowan su ke nan daga masallaci basu dade da shiga ba suke jin muryan hjy sabuwa komai da take fada a kunnen sune.
Allah ya nufa za,ayi wanan abun a gaban su yayan su yace su kwana a nan don da safe zasuyi sammako zuwa gurin wani dan uwan su daddy su a kauye.
Gaba dayan su juyowa sukayi a inda suke jin maganan suna kallon su da mamaki.
Dan kame kame hjy sabuwa ta farayi don batayi tsamanin gaba dayan su har shi umar din yana gidan ba a lokacin.
Au kuna ciki ashe tace ba wanda ya amsats sai shi umar din ne cikin sanyin murya yake fadin mama meya faru ne haka wai da safen nan ?
Wanan matar tazo muna da jidali gida babawo sarakuwan kace fa mahaifiyar samira amaryan ka .
Wani kallo yaiwa hjy sabuwan don harga Allah matar ta sake mai ga baki daya don ba haka yasanta ba a baya gaba daya yaga ta sauyamai ga gani.
Wani kallo yai mata bai iya magana ba ya juya zai bar dakin ba tare da yace da ita uffan ba sai jin muryan ta kowa dake falon yayi tana fadin .
Babawo ko ban baka mata ba a matsayin uwarka nake balle na wanke diya na baka do dole alakan mu dakai ya karu a yanzu.
Ta fada a gadarance tana kallon shi kamar mai bashi umurni tace ban san matsayin daka dauki yata ba a wurin ka don har yanzu kwanan ka nawa a garin nan tana cikin gidan ka tace ko gaisuwan ka bata samu.
Ban san dalilin hakan ba tunda ba mutum mutumi na kawo maka ajiya ba a gida mace ce lafiyaya na dauka na baka aure.
Tunda ta baci sunan shi yaja ya tsaya wuri daya yana sauraren maganan da take fada mai ba tare daya juyo inda take ba har zuwa lokacin data tsayar da maganan ta.
Sai lokavin ya juyo gareta jin ta tsaya da maganan da take koro mashi ya dan murmusa kafin yace hjy zanso ki gyara kalaman ki kan komai nan gaba ko abin zai zo maku da sauki.
Yar ki bata fadi karya ba don har yanzu ban san tana gidan nan ba don bamu je an muna gwaji ba a tsakanun mu a tantance lafiyan ta.
Me kake nufi da fadan hakan gwaji gwajin me kake nufi zakuyi tuhumar yar nawa kake dawani cuta ko me kuma ?
Eh a ka,idana sai anyi wanan gwaje gwajen an tattance tsakanin mu kafin in tabatar da komai a gare ta.
Uwarka jummai gatanan za, a gwada ka kalli tsaban tsakiyan idona babu kunya kake furta min wanan maganan gwajin ko me ?
Nasaran da kake koyi dasu sunci abu kazan kazan su wa zaka kawowa wanan bakin akidar naku na nasara a nan sale sale salin ka batawa yata suna ko me kake nufi.
Kiyi hakkuri mama haka ka,idana yake ni don haka zan samu lokaci muje a auna mu ta kara fadi a tsawace a aunaku akan me ?
Nace cuta gare ka ko ita kake tuhuma da cuta da sai an aunaku zaka fara takata kamar wasu arnaku can da basu yarda da Allah da kaddara ba.
Sorry yace ya juya ya fara tafiya yan uwan suka mara mai baya yayin da hjy sabuwa ke fadin wani sabon kullin da kukayi da dan naki kenan hjy don ku tozarta mu kome ?
Sabuwa mamakin wanan dabian da kike min a yanzu nakeyi nima yadda kikaji wanan maganan yanzu a nan nake jinshi yanzu don baiyi wanan zancen wani gwajin dani ba.
Koma me kuka shirya samira ba zatayi wanan gwajin ba waya sani ko kun shirya da wani likitane ya bata mata suna ga banza.
Kuma bari kiji samira ba zata zauna dake gotai gotai haka a part daya ba ga dakuna birjit a gidan nan baki zauna ba sai wurin ta don sheri irin naki kawai.
Idan har kika bari auren Samira ya samu tangarda a dalilin ki jummai ina mai sheda maki tabbas auren ki ya tabu kema a gidan nan.
Umma ni banji dadin zuwan nan naki ba gaskiya don kin kara bata wanan abin ne hakan da kikayi .
Da ki barni in gyara komai da kaina basai kinzo ba saida nace dake kada kizo ki bari zansan yarda nayi amma umma baki ji ba saida kikazo gashi yanzu abinda zuwan naki ya jawo min kuma .
Ke rufamin baki ke me kika sani cikin halin wanan matar nida ita kar yasan kar idan tana tunanen zuwane ni a hanya na kwana wurin sheri.
Hjy jummai da tun fitan diyanta part din ta kasa zaune ta kasa tsaye a dakin da take har nan din tana iya jiyo murya hjy sabuwa da yarta da suke magana a daki game da ita.
Sai lokacin da taji fitan hjy sabuwan wani kukan mai cike da nadaman yarda da dadin bakin da hjy sabuwa ta dinga mata a lokacin da take son wanan hadin yazo mata.
Bata san lokacin da hawaye masu zafi suka dinga zubo mata daga idanuwan ta ba yaune rana na farko da ta fara nadama kan abinda take aikatawa ga mijin ta da yaranta da basu gazawa da al,amarinta ta sani wani lokaci tana tauye su da yawa amma saboda son zuciya irin nata tana ganin har yanzu su yarane basu san daidaiba.
Yau da a gaban wani ba diyan cikin ta bane sabuwa tayi mata wanan tujaran haka ina zata saka kanta taji dadi a duniyan nan.
Do ita abinda taki a rayuwan ta shine taji kunya ko nauyi a gaban wani saboda girman kai irin nata da take dashi.
Yau sai gashi sabuwa ta wanko kafa har gidan dan nata tazo taci mata mutunci saboda yarta har tana ikirarin sai taga bayan auren ta idan na yarta ya mutu.
Ashe haka mutum yake saida Asma,u kanwarta ta rabata da wanan maganan hadin auren amma ta rufe ido tayiwa kanwar nata tas da gangan.
Can falon mu kuma bayan sunyi wanka sun shirya mai girkin shi ya jera masu abin karyawa ne a dining sun fito.
Ba wanda ya kalli abincin don rayukan su da suke jin ba dadi a lokacin saboda abinda hjy sabuwa tayiwa mahaifiyar su a gaban su dazun.
Shine ya fito karshe yana daura agogo a hannun shi ya nufi wurin abincin kallon yan uwan yayi yana fadin ya baku fara ci ba kun san ni ba wani abu zanci ba ai yanzu.
Bros wake zancen abincin nan yanzu wanan matar ta cazawa mutane kai tunda safe haka duk da dai banga laifin wanan matar ba ai don basu da laifin komai a nan kansu sukewa faiting.
Wanan maganan kun daukeshi wani zance ne can mai muhinmaci kune baku san halin sabuwa ba har zaku wahal da kanku don ni na rigada na gama shirin komai.
Zancen zuwa kauyen ma mun fasa ba inda zamu fita yau zamu zauna gidane akwai abinda nake so mu gane kan shirin wanan auren da suka kulla min.
Na fara gane akwai wani manufa cikin wanan hadin wanda ita mama kanta bata fahinci hakan garesu ba.
Zuwa gobe zan kawo karshen maganan kowa ya huta idan suna ganin sun kamani a hannu ne yadda suke tunane tun yanzu.
Da hjy tana da gaskiya ba zata ce bata yarda aje asibiti da yarta ba wanan kawai ya ishe mutum mai tunane ya gane .
Aliyu yace abinda nake faman tunane ke nan tun dazun ai tayi zaman lagos tasan amfanin gwaji kafin aure bawai dole sai ciki ko wani abinda take tunane ba za a iya ganowa a wurin gwajin ba har ma abinda mutum baiyi tunene shi ba sai ya bashi amsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button