NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:20 – ????????????: Fadan hjy sabuwa ya komawa samira matsala don gaba daya ya fita zancen ta a gidan bata ma ganin dawowan shi ko sanin fitan shi gidan daga ita har hjyn su yanzu.
Tafiya yayi duba company shi na farko daya kafa lagos dashi da Aliyu hakane ya kara harzuka ran hjy sabuwa ta addabi hjy jummai da masifa na rana daban na dare daban.
Sai shige shige ya tashi abu ga wanda addini bai zaunawa kai ba dama sai fadi take wai ba a banza hakan yake faruwa ba da yar ta.
Saidai ta tafi tsirara amma sai taga bayan mai shi a duniyan nan gaba daya da farko sun dauki laifin sun dora min ne .
Daga baya kuma suka komawa merry don wayan da Nafisa tayiwa uwar cewa ita bataga wani abin da nake samu na jin dadi ko kulawa daga gareshi wanda zai tsonewa mutane ido .
Don ta gama fahintar ko nan ba ganin shi muke yi yadda ake tsamani yana muna ba don ta binciki mai aikina ta fada mata komai a yadda ta fada masu.
Don hakane suka juya akalar su zuwa gun merry kuma wace bata san hawa ba bata san sauka ba kan maganan.
Shiko a nasa bangaren ya kudurta cewa muddin mahaifiyar shi bata koma dakin ta ba da sunan aure ba zai taba kallon samira da sunan mata a gareshi ba.
A cewan habbib bai dauki auren samira wani aure ba can don babu waliyi daga bangaren mahaifin aure ko yana wajabtane daga bangaren ma,aurata biyu.
Sin bar hjynsu a cikin dibin tunane don ko ganin su ma su duka ukun batayi balle ta sauke masu sababinta a kansu.
Abu ya taru a lokaci daya ya rikicewa hjy wace bata taba zaton hakan ba da farko daga can lagos ya juya ya wuce zuwa united state of America inda ya samu wani kira na gagawa a can kan aikin su.
Sai bayan Aliyu yazo kano ne suke jin cewa baya kasan a baki daya lokacin .
Samira tana jin haka saida ta kwanta ciwo aka kaita asibiti nan ran mahaifiyar ta ya kara baci sosai tana fada wai zatayi karan Umar da mahaifiyar shi kotu.
Mijin ta yace akan may da kukai auren ku kinga kafan shi ko wani nasa gidan nan da sunan aure ?
Dama abinda nake fada maku ke nan kuka kasa gane mai nake nufi saida kika san dabaran da kikayi kuka kulla wanan auren yanzu kije kotu ki tonawa kanki asiri ko yar ki.
Duniya ta san halin da kuke ciki idan ma baki sani ba ki sani wanan yaron ba zaku iya juyashi ba yadda kuke nufi saidai kuyi ta barnan kudin ku ga banza.
Don irin su kansu ya riga da ya waye wani asiri ko jefa da kira ba zai shige shi ba don a tsaye yake a kafan shi.
Shi wawane da zai yarda auren mahaifiyar shi ya lalace ya gyara auren yarki bayan yasan furcin mahaifin shi kan wanan auren .
Idan zaki natsu ku bi komai a sannu ki tarkato yar ki da kayan ku zuwa gida zaifi don shidai ya nuna ba zaman shi takeyi ba a gidan yanzu haka.
Samira wace ke kwance saman gadon asibiti ta sakewa iyayyen nata wani irin kuka lokaci guda.
Mahaifin yace dama ai daga kin gaskiya sai bata tun kina da mutuncin ki nake baki shawaran ki natsu ki fitar da mutum daya wanda zaki aura saboda kinga kina da daurin gindin uwarki tana zugaki kika kasa yin haka.
Tace daddy ni wallahi in yace ya fasa aurena mutuwa zanyi wallahi ka taimakeni kasa baki a cikin wanan magana don naga umma ta kasa wanan aikin ita kadai.
Yace samira yanzu kuma ni din da kuka mayar ba komai ba ke da uwar ki yin abinku kukayi ba ku dauki shawaran dana bayar da muhinmanci ba kun mayar dani wani makiyin ku.
Asiri ba a ko ina yake tasiri ba haka asiri yafi aiki kan wanda yake sakaci da adfinin shi yanzu na kara fahintar hakan.
Kan irin kudaden da kuke kashewa a kullun kan yuyuwan wanan abin gashi kunyi nasaran abin ya yuyu saidai zama gidan kuma ya gagareku zama yanzu.
Kun taba jin anyi wani na banza a duniya ai in kaji wani ba banza ba zai zauna hakane bai shirya kansa ba yana gwagwalmaya a cikin duniya da mutane kala daban daban.
Hjy sabuwa taja wani irin tsuki tana fadin yanzu wanan magansn me ya kawo shi idan ba zaka taimaka ba ka saka muna ido kawai nida yar ta dama zan sama muna mafita.
Tana fadin haka ta muguda baki kamar karamar yarinya tana juyawa baya.

 Na shigo gidan a gajiya don ranan dana kwaso a falo na samu Nafisa zaune na samu har yaran sun dawo gida lokacin.

Suka shiga yi min sannu da zuwa ina amsawa a lokacin da nake kokarin zama ina tambayan yarona don in bashi nonona da sukai min nauyi a lokacin .
Kallon Nafisa nayi wacce tunda na shigo bata dago kai ta kalleni ba har lokacin nasan tsiya take ji ranan don haka na shashantar da ita ina fadin hjy Nafisa ke nan kina jin dadin ki.
Sai lokacin ta juyo tana fadin naga kin dawo iyalin ki sun baibaiyi ki da sannu ne ai.
Dan dariya nayi ina fadin shine farincikin mace Nafisa ta wayi gari ta ganta takiyan iyalin ta a cikin farin ciki da kwanciyan hankali irin hakan.
Ubangiji ya nuna muna kuma kun tara naku iyalin irin haka na gyara zancen don kada in bada kafan da zamu samu wani matsala da ita a wurin don nasan gatse tayi min na mayar mata da amsa na.
Zatayi magana taji a karshe na mata addu,a tace Amin Fatima kun huta ku da daddy yai maku auren ku a cikin gata.
Yau gaki abinki zaune a dakin ki hankali kwance idan na kalli yaranan na tuna wai duk nakine Fatima sai inga kamar mu ba,ayi muna adalci ba wallahi.
Da sauri nace haba dai Nafisa kada ki manta komai mu kaddarine ga bawa tun ran gini ranan zane.
Tace hakane ni yanzu ba Mansur ba wallahi duk wanda ya fito idan dai yana da hali kwarai zam bashi bakine fatima.
Nace hakan yana da kyau don kinga bawai lalaine ka samu abinda kake so ko wanda kakeso ya soka ba .
Tace shina zauna nayi tunane sosai wallahi wai yau ki duba sati uku ke nan idan na kira Mansur bai daga waya karshe ma sai ya jefani block ko mai yake nufi da hakan oho ?
Kema kiyi kokari ki nuna mashi baya gaban ki yanzu don Allah nafisa ki nafisa ki natsu yanzu ki samu ubangiji ya turo maki miji na gari daidai ke.
Ki daina bin irin yar karyan nan da ba aure ne a zuciyar su ba sai holewa da jin dadi suna zubar wa mata da mutunci a banza.
Tace nagode da wanan shawaran da kika bani Fatima dama saida Anty salma ta fada min ke din mutumiyar kirkice ban yarda ba a lokaci.
Gashi yanzu ina ganin gaskiyan maganan ta idan da wata ce nasan tun zuwa na ba zamu kwasa da dadi dake ba a gidan nan.
Wallahi fatima ku godewa Allah ke da mahaifiyar ki don nasan shawara da tarbiyan mahaifiyar kine yake amfani a gare ki.
Da ace kowa haka yake samun mahaifiya irin naki da duk wani matsala mutum bai ganshi ba a rayuwa.
Yanzu ki duba Fatima mu din da kullun ake nunawa mune diya mune kuma da gida muna iya taka kowa yadda mukaga dama mu zauna lafiya.
Ke kanki kin sani izgilanci babu wanda ban iya iyiwa mutum shi ba saboda ina da daurin gindi a gurin hjyn mu nake hakan.
Mun dauki kishiyoyin hjy tankar makiyan mu ko kuma sa,oin mu don saboda tsanar su da hjy ta dasa a ranmu.
Murmushi nayi jin abinda take fadi tace Allah fatima ke ma kin san hakan ai ?
Tace ni yanzu abinda ya ban tsoro Fatima shine duk irin kudi da kaddaran da hjy suka kashe wurin auren samira da yaya wai ace wanan abin baiyi tasiri ba don ance har yau yaya baisan samira na gidan shi ba.
Nace ke da kike nan yaya akayi kika san wanan labarin tace wallahi labarin ne ai ba dadi Fatima .
Allah ya kyauta nace ina mikewa don zuwa dakina don ban son hiran yaci gaba daga nan.
Na shiga daki cike da tunanen abinda Nafisa ta fada duk da nasan kadan ne daga cikin halin yaya don nima na fuskanci wanan a wurin shi ai .
Sai dai ko na fada ba yarda zasuyi ba don ba kowane zai iya hakkurin da halaiyan yaya din ba don shi a baude yake sai idan ka san halin shi zaku zauna daidai.
Dole nakara sakawa kaina tanatsu na kara sauke komai daga kaina don dai banda matsala a yanzu dashi wanda hakkurina ne takaini ga hakan yanzu.
Munyi maganan da kamar kwana hudu kwatsan sai gashi ya sauka a garin daga sama kamar wanda aka jefo muna shi.
Nuna mai babu komai a raina nayi wanda Allah yaiwa fada haka mai zan tsaya yiwa fitina kuma don ko yanzu Allah ya gwada masu iyakarsu ai a kaina idan ma ni akewa don in koma baya.
Har dare yana tare da yaran shi sai faman bashi labarai sukeyi yana biye masu Nafisa sai kallon su takeyi kawai.
Nice na fara barin falin don ina da test ranan monday wanka nayi kafin in kwanta ina dan karatu.
Ban dade da fara karatun ba ya shigo dakin ya zauna a kusa dani injin zaman shi na sauke takardan da nake karatu a fuskana ina kallon shi.
Ya gida yace min ina kara sauke takardan nace lafiya ya mutanen gida suna lafiya koda yake ban samu sallama dasu ba na wuto daddy kawai na fadawa tafiya ta ya bani amsa.
Nace har hjy da amaryan ka balle Amman mu tsohuwa ko ita baka sallama ba ke nan ashe yaya ?
Yace bata ko ganni yakai sau uku ba wansn karon don ban samu zama sosai ba aiki yai min yawa.
Akwai aiki kan na bashi amsa nace tundai ga mai sabuwar amarya dal iri ka ina zata ganka ?
Yau kuma sheri zaki mun zahra ke da kanki ai na dauka kinfi kowa sanin halina yanzu idan ma sheda ce na dauka kece zaki bada a kaina.
Wurin kokarin nuna adalci a tsakanin iyalina duk da kalubalin da nake samu daga ko wace ku na zaman tare don kowa gani take nafi maida hankali a wurin yar uwanta.
Sai dai ni hakan bai hanani tsaya inyi adalci yadda ya kamata ba in tauye wata daga cikin ku ba ko wacece..
Sai dai ita bakuwar a cikin mu nake ganin kamar hadin mama ba zabina bane don ba zan yarda in dauko wanda baida tarbiya yanzu in jefa a cikin iyalina .
Yana fadin haka ya mike tsaye yayin da nabishi da kallo ina son jin kanun labarin da ya dauko bani a lokacin kuma ya katse.
Binshi da kallo nayi har ya fita daga dakin ba tare da ya kara furta min komai ba gashi ina son gulma don samun makami don ko wata kishiya tana son jin dan wani zance game da kishiyar ta don shine makamin bakin mu kamar yadda itama dole tana da dan wani labari data rike game dake.
Fauziya ne ta shigo dakin dauke da Abbati a hannun ta karban yaron nayi na bashi nono sai barci zama nayi na shirya yaron tare da aje mai abinci koda zai falka da dare.
Na kara shiryawa na nufi dakin nasa a zaune na same shi yasa wasu takardu a gaba yana duba jin shigowa na dakin ya dawo da hankalin shi gareni.
Aje abinda na shigo dashi daki nayi na zauna kusa dashi a hankali sannu da aiki yaya nace mai ya aje yana fadin ina yaron yake kuma ?
Yana gurin mamanshi na bashi amsa fauziya ke nan ko don nasan wanan sakaran bata iya komai ba sai gulma da cewan nafisa .
Nafiss kan ai kasan bata saba da rainon yara ba haka ai zata saba idan tayi nata ai ni wanan yarinyar mama ta bari ta lalace da yawa.
Gashi bata son a fadi gaskiya a kanta ko kadan nasan kunsha fama da ita nan a bayana .
Da sauri nace lafiya lau muke wallahi ba matsalan komai tun da na san halin ta tun farko yasa mukaci maganin zama da ita ko yanzu don bamu shiga harkan ta.
Sai dai hakan ya bani amsa yana kai bayan shi saman gado ina so ta koma satin nan mai zuwa daddy yayi maganan Fauziya sai dai na bashi hakkuri don nasan yana da wuya ki barta ta koma yadda kikaji dadin zama da ita nan.
Nace wallahi kuwa yaya ka kyauta daka rokan min kawu ita don yanzu nasan dadin zama da yarinyar sosai nama rasa irin godiyan da zanma wallahi.
Ji nayi ya da mirginoni zuwa jiki shi ya rungume ni yana fadin ba godiyan da zaki min banda in ta ganinki ke da yaran a ciki farin ciki ko yaushe kamar yadda na dawo yanzu na same ku a gidan kunayi.
Bana jin dadi idan naga kin sa damu kan wani abinda bashi ba can ki saka kan ki a damuwa ga banza.
Nace ba hakana bane ai yaya na fadi ina gyara kaina saman kirjin shi nace kasan ni mace ce dole inji haushin kasancewan ka tare da wata can daban.
Magana ya dan bashi dariya don sauti murmushin danaji ya sauke lokacin.
Sai naji yace yanzun dana je can na dawo gareki kin ga abinda na canza ne daga jikina ko wani halaiya nawa gare ku ?
Zahra ki saki ranki don Allah ki kara fitar da wani kishin dake makale a zuciyar ki kin fi kowa sanin har abada ina bayan ki.
Nace in sha Allah yaya nakuma gode dani da yaran da irin kulawan da kake bamu ko yaushe nima nasan banyi daidai ba a baya kayi hakkuri da abubuwan danai maka da farko.
Yace ni komai ya wuce a wurina muddin zan samu farin ciki a gurin ku ai kun gama min komai zahra.
Jin ya fara taba min jikina yasa nace dashi kasan fa haihuwa nayi ko suna har yanzu ba aiwa yarona ba ka tafi gashi kuma da sunan ubana.
Nasan dama za a biyoni bashin hakan ai sai dai yanzu ina rokon don Allah ki tsaya ki tayani kwana a nan don nayi kewan wanan laulausan jikin naki da ban gajiya da tabawa.
Na danyi murmushi tare da fadin dole ai mu saba da rashin juna yanzu fiye da yadda muka saba don yanzu mu ukune a wuri ka.
Ji nayi ya rufe min baki ya fara aika min da sakonni a jikins a hankali a ranshi yans fadin baki san komai ba ke nan yarinya da baki fadi hakan ba ke ma.
Haka dai yaita lalabani har ya samu ya samu abinda yake so a gareni ban fito dakin ba sai goshi asuba ko shi saida ya tayar dani don yaji wayana na kuka ya duba yaga fauziya ce a layin haka yasa ya gane yaron ne ya tashi take kirana a waya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button