NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:21 – ????????????: Kudi masu yawa yaban don tsaraban Nafisa tare muka fita zuwa sayayya da ita inda na bata zabin abinda ranta ke so tunda kudin ta ne.
Sai dai a lokacin ban yarda na nuna mata komai ba dangane da kudin tana ganin kamar kudin banza nake kashe mata tunda ina dashi.
Komai take so mun saya an kumayi mata packed din shi yadda za a iya tafiya dasu har Nigeria.
Ana gobe zata wuce muna falo zaune salma ta kirata a waya tun suna magana a gaban mu har yakai ta mike ta shiga dakin kwanan su ta dade a ciki suna waya.
Bayan sun kammala wayan tafito tun lokacin naga sauyi a gareta sosai ta koma shiru kamar wani abu yana damun ta.
Washe gari take ce min ita fa tana jin kamar ta fasa tafiyan nan har zuwa nan gaba .
Nace idan baki tashi ba ai sai kiyi zaman ki nafisa nan ai gidane gare zaki iya zama abinki har lokacin da kike son tafiya.
Saidai yaya yana dawowa nakw fada mai abinda tace yace sam ta koma gida don mahaifiyar su zata bukace su a yanzu ita da salma fiye da zaman ta a nan.
Nafisa bata so tafiya ba dole haka ta shirya muka rakata airport sai gida Nigeria ita da tsaraban ta na London.
Ba yaran ba har maria da fauziya murnan tafiyan Nafisa suke a ranan har yaya ya tsurasu suna zancen yi yayi kamar bai fahince su ba.
Sai bayan kwana biyu yake tambayana irin zaman da mukayi da Nafisa da farko ban so fada mai ba saida yayi min jan ido nake fada mashi komai da tayi muna a gidan sai dai ban fada duka ba.
Nasan ba zaiyi wani magana ba kyalewa yayi koda zai dauki mataki nasan sai gaba .
Karatuna na mayar da hankali sosai gare shi don ina son in fito a matakin na biyu ga likitanci yanzu don haka na mayar da hankalina sosai ga abinda nake koyo.
Mamu sun kawo muna ziyar bayan tafiyan Nafisa da sati daya najo dadin hakan sosai saida bata zo da yaran ba daga ita sai mahaifiyar ta da kanneta biyu babban yana makaranta a lokacin basu zo dashi ba.
Naso su sauka a wurin mu sai dai ban samu hakan ba ina dai girka abinci in kai masu a masaukin su can.
Satin su daya suka juya take fada min data koma zata koma gida insha Allahu don kawu har ya fara fushi da dadewan ta a sudan datayi.
Sun tafi sun barmu da cike da kewan su don mun dinga jin kamar kada su koma don kewan juna da muke ji.
Banga yaya yana zancen matar shi sabuwa ba nima bandamu da in san komai game da hakan ba.
Bansan zamu saudayi ba sai da tafiya yanzo gab yaya yake sanar dani hakan inda nayi murna kwarai da jin hakan.
Gaba dayan mu har yaran da maria don kula dasu muka nufi kasan saudiya inda na kara tabbatar da yaya ba karamin mutum bane a lokacin.
Komai namu special akeyin sa a can tun saukan mu madina har shigan mu birnin maka komai a tsare yake gare mu kamar wasu manyan mutane sai faman kafa kafa yake da yaran shi dani don tawaga na musan man muke daga kasan London.
Mun sauke faralin mu lafiya mun dawo gida a satin da muka dawo ne Allah ya karbi ran mahaifin merry kuma wanda yayi dan karamin jinya ya mutu.
Muna gida zaune da yamma yaya ya fita da yaran shi zuwa cikin gari sai gashi sun dawo muna da wanan labarin.
Lokacin daya shigo yanayin sa kawai na duba nasan yana cikin tashin hankali a lokacin baiyi magana ba saida ya zauna na dawo kusa dashi na zauna.
Yaya lafiya nagan ka a haka bayan ba haka ka fita gidan nan ba nake tambayan shi cike da kulawa a gare shi.
Ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin zahra mahaifin merry ne ya mutu dazun ta bugo min waya da kukanta lokacin daya mutum tana sheda min.
Cikin kidimay wa nake fadin innalillahi sai naga ya dago ido ya kalleni da sauri na tuna da katobaran da nake shirin yi a lokacin.
Nace oo mutumin nan ya mutu yau Allah ya kara nauyin kasa a gare shi baida amsa min da komai ba naji yayi shiru .
Mun dade zaune a hakan ba wanda yai magana a cikin mu kafin ince yanzu zaka tafi ke nan don ka samu a kawar dashi a gaban ka ko ?
Dan tsuki yaja yana bata fuska tare da fadin an fada maki irin kawar da gawan mu sukeyi da sauri su sai nan da dan wani lokaci mai zuwa idan sun shirya hakan.
Sai dai ban jin zasu dauki lokaci mai tsawo don shi member ne na church din su a can suna da shirin hakan gare su ko yaushe sai dai duk da hakan za,a dauki lokaci kafin su kawar dashi din.
Zan dai shiga na jajanta masu mutuwan inji shirin da sukeyi kan bizzine shi din Allah ya kyauta na iya fada mai kawai.
A wanan ranan na karbi layin merry wurin shi don banda layin ta akan zan kirata in mata gaisuwan rashin da sukayi din .
Ba nuna min zaiyi yaji dadin hakan da zanyi ba sai dai wanda ya fahince shine zai gane hakan kawai.
Washe gari ya dauki hanyar zuwa wurin merry sai lokacin nima na samu kiranta na kira kira farko bata daga wayan ba .
Ba zance taki dagawa bane don tasan layina don bamu taba waya da ita ba duk dadewan nan sai wanan ranan da dole yasa zan kirata din.
Karo na biyu yakai ringing uku ta dauka cikin muryan ta da ya dakushe tana fadin hello a sanyaye.
Nace anty merry its me Fatima from London na kiraki ne don in maku gaisuwan kan rashin papa da mukayi.
May his soul rest in piece ina fadin haka na kashe wayan yayin da merry ta dade tana kallon wayan dake hannun ta tana tunane.
Sauke ajiyan zuciya tayi tana kallon uwarta data tsura mata ido tana son taji wanda ya kirata a lokacin.
Omar wife ta bata amsa don tasan abinda take son sani a lokacin don irin kallon da take mata.
Omar wife uwar ta tambaya cikin mamaki sai kuma ta mede baki tana fadin is her business don,t mind her.
Mama stop sayin dis at dis moment please all what we need is to pray now to papa I fucking care who she is now if she can pray to my father.
Amma kin san haka suke da yaudara musanman ma matar musulman mu na Africa akwaisu da kissa sosai .
Ban damu ba da komai tunda har ta iya kirana kan rashin papa koda tana da wani abu a ranta ita ta sani don ban damu da ita ba.
Abinda na damu dashi shine mijina kawai ya dawo gareni da yata basu bane a gabana.
Duk da abinda yai maki merry kike mafalkin dawowan shi gareki baki sake kada ki manta da diya hudu ya haifa da ita yanzu fa a cikin dan wanan shekarun kan kani.
Mama stop all this rubish now let,s face our problems mun tsaya muna magana kan wanan yarinyar haka.
Kamar yadda ya zaci zaikai gurin su da dan safe haka ya isa don tashi asuba yayi zuwa can din.
Merry taji dadin hakan daya nuna masu don yakan nuna kulawan shi kan abinda ya shafe ta sosai.
Bayan ya jajanta masu ne suna ta faman koke koke ya katse su da tambaya ya suka shirya bizzene mamacin yanzu.
Uwar tace bamu da abin fadi sai yadda pastor ya tsara muna ina ganin hakan zai dauki tsawon wata daya kafin a rufe shi.
Ya zauna wurin su har sati yana basu kulawan daya dace kafin ya juyo zuwa London ya same mu a kullun muna waya dashi yakan bamu Queen mu gaisa wani lokaci har da yan uwanta.
Ban taba nunawa yaya kyamar iyalin shi ba duk da inajin dacin hakan a raina saidai mai kaya ya daure sai mai cirane zaiyi raki.
Haka yasa nake danne abin a raina saidai mai karatu kin san hakan yana da zafi sosai ace ana taraiya dakai da wanda bai sallah .
Dolena zama tare ya hada tawa kaddaran haka yazo min da hada alaka dasu ba yadda na iya da hakan.

Nafisa tana kwance daki lokacin barcine ya fara daukan ta can a cikin barcin nata take jin murya sama sama kamar fada a gidan .
Hakan yasa ta bude ido da sauri tana sauren abinda ke faruwa muryan hjy sabuwa ne ya karde gidan tana fada da karfin harshen ta.
Wanan ba zai yuyu ba jummai din bake yata ke aure ba wata da watanni ya wuce ya barta a gida tana masa gadin gida.
Kin san baki isa ba da danki kika yi min dadin baki akan kin isa dashi wanan abin kunyan dame yai kama hakane wai ?
Gaki ba kunya gototo dake kin tare masu a gida wai ke a dole gidan danki yau idan dai kece kika haifi umar ina son ki nunawa duniya kin isa dashi mu gani.
Zubur Nafisa ta mike a lokacin daga kwancen da take tana kokarin saukowa daga gadon hjy sabuwa na fadin jummai kin ban kunya kin kuma ba duniya.
Ace ka haifi da ka kasa juya shi yadda ranka ke so akan wasu iyalin shi can marasa asali da tushen banza.
Arniyar ce ko ita wanan yar filon bauchin mai kama da yanyawa zata fi karfin ki banyi mamaki ba don ko uwarta ta gagare ki kawarwa balle yarta da take juya ahalin ki yanzu.
Hjy idan ta gagari mama ai ke bata gagare ki ba sai ki dauki mataki akan yarki idan kina ganin itace matsalan ku.
Yarinya tana can bata masan kunayi ba nan don bata ko ta zancen yarki tunda aka aure ta ban taba jin tayi wanan zancen ba har na baro kasan.
Yanzu kinzo ki kara zuga mama kan ta tayar da kwanciyar hankalin danta saboda yarki tayi farin ciki mu mu rasa namu farin cikin uwar mu.
Hjy jummai ne cikin wani murya take fadin Nafisa kina da hankali kuwa hjyn kike fadawa magana haka kai tsaye babu kunya a idon ki ?
Barta ta fada min don ta isa take gani tunda tasan har abinda bamu sani ba mu gun maza idan batayi hakan ba ai bata cika yar bariki take ba yanzu.
Allah sarki dadin abin dai ba a kaina aka fara zama yar barikin ba don da yarki aka fara kwatancen hakan a gari anci legas an dawo cin kano don an rasa masunsuni a can saboda, , , ,
Marin da taji daga bayan ta ne ya hanata karasa abinda tayi niyar fada a lokacin don sai da ta dafe fuskan ta.
Juyowa tayi da mamakin ganin wanda ya mareta din lokacin Samira ce tsaye tana nuna tace ke har kin isa mara kunya da zaki tsaya kina fito na fito da uwata.
Sai in nuna maki karyan bariki yanzu in fasa maki kai a gidan nan ba,a komai dani.
Nunawa yar banza kinci legas da tushe ba a nan kika koya ba Nafisa ta daga hannun ta rama marin ta nan fada ya kaure a tsakanin su lokaci guda.
Hjy jummai dake kokarin rabasu batai aune ba taga hjy sabuwa da yarta sun taru a kan Nafisa suna duka da zagi .
Amma dai hjy sabuwa ke mutumiyar banzace ashe ban sani ba fadan yara kika shiga haka anayi dake.
Samira ta juyo tana fadin a cikin fada kada wanda ya sake zagin uwata wallahi don ban ragawa kowa akan uwata ehhe.
Hakan yaba Nafisa samun daman kaiwa samira kwalban data rarama na flawer vese saman table duka dashi ta samu gefen goshin ta.
Sai jini samira ta yanka ihu tana fadin kasheni zakiyi yar iska da karfin Allah suka kara taran wa nafisa har yar aikin su wanan karon sukai mata lis a gaban hjy sai fita hjy tayi tana kiran mazan dake aiki a gidan azo a cece yar ta lokacin.
Da gudu suka shigo sai dai kowa ya shigo sai ya koma baya saboda yanayin da suke a ciki babu dadin gani ga kuma nafisa kwance a kasa shame shame kamar ta mutu a lokacin.
Da sauri dayan mutumin ya nufi get ya rufe don tsaro kuma kada abuncin su ya kare saboda yana gudun karsu hjy sabuwa suzo su gudu su barsu cikin wahala.
Mai wanki ne yayi kundun balam shiga yana dago Nafisa data some a lokacin jinta koma sharkaf yace hjy shike nan kun kashe yar mutane har gidan su.
Ai hjy jummai tana jin hakan tayi kukan kura ta shake hjy sabuwa da karfin da bata san tana dashi ba a lokacin.
Sai fadi take ba zata tafi ita kadai ba sai da dayan ku wallahi gaba daya ta fita cikin hayacin ta sai sambatu takeyi .
Samira da tasan ba karfin uwarta daya da hjy bane don hjy sabuwa irin yan firit din mutanen nan ne sai masifan tsiya.
Tazo da gudu iya karfin ta ta ture hjy ta baya ta fadi saida kwatolon ta ya amsa hannun ta data tare don kada taje kasa ya amsa yaba da wani irin kara a lokaci guda.
Wani kara ta sake mai firgitarwa lokaci daya duk gidan dai da ya amsa ranan yan aikin gidan sunga tashin hankali.
Dabara kiran yan sanda driver yayi ba,a jima ba sai ga yan sanda har biyar a gidan maza da mata don shiga gidan.
Ya kira Alh yana sheda mai abinda ke faruwa da iyalin nasa jin bai samu wani amsa bane a gurin shi mai dadi yasa ya kira Aliyu wanda yasan shine kan gaban komai na ogan nasu.
Aliyu yace a tsare su har yazo kowa yazo kada a bada belin su harsai yazo da kanshi dan sanda yace angama don yaji za a turo mai kudi.
Sun kwashe su zuwa asibiti yayin da aka wuce dasu hjy jummai asibiti cikin ambulance din asibitin.
Kafin wani lokaci dangi kaf sun ji labatin abinda ke faruwa a gidan umar din sun cika asibitin lokacin da ake neman rayuwan Nafisa din ta dawo.
Nan zumunci yaso rabuwa a tsakanin su don ko wani bangare suna goyon bayan dan uwan su a cikin dangi nan wani tonon asiri ya taso a tsakanin su ana fadin kan zumutar su ai ba wani mai karfi bane.
Kawu ne ya raba gardama don yace a sake Samira ta koma dakin ta kawai bayan ya kira Aliyu da ya hauda fada akan me zai sa a tsare mata da auren su.
Nan kowa ya cika da mamakin adalci irin na Alh aka shiga tsuguri tsoma a kan maganan kowa da abinda yake fada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button