SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Taka a hankali mama zaki iya insha Allahu Aliyu ne ke wanan maganan yana rike da hannun mama dake kokarin tashi tsaye daga saman gado.
Sai dai duk kokarin ta takasa tashi yadda suke so matsalan daga mahadan kashin joint dinta na kafan tane ya gwauce.
Komawa tayi ta zauna tana runtse idanuwan ta saboda zafi da radadin da take ji har cikin rayuwan ta a duk lokacin datayi yunkurin tashi tsaye kamar yadda ake son ta mike .
Ido a rufe tana sauke ajiyan zuciya tare da tunanen sanadin hakan a gareta ga yarta Nafira da itama tana fama da jikin ta duk sanadin su sabuwa da yarta.
Mutanen da ta dauko ta saka a cikin ahalin ta don kawai suma a ci arzikin danta dasu saboda zumunci.
Ido ta kara rufewa lokaci guda tana mai kara jin zafin su a ranta gashi Aliyu yazo mata da labarin Samira tana nan gidan dan nata zaune.
Hankali kwance har da kokarin kafa dokan ba zata sake zama da hjyn ba a part din ta saidai a bude mata dayan part din ta zauna har in tana son zama a gidan.
Kuma daddyn yara ya yarda da hakan da suka bukata a cikin sharadin su tun a wurin yan sanda kafin a sallame su.
Jin wanan labarin da dan nata yazo mata dashi ya matukar bakanta ran hjy take jin kamar ta tashi ta samesu a gidan ayi duk abinda za, a yi sai dai ba halin hakan gareta yanzu.
Don ko tsaye bata iya mikewa dole sai likita yazo an kara duba lafiyan ta ansan inda matsalan yake a jikinta.
Ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki har tsawon sati yasa Aliyu ya kira yan uwanshi ya fada masu halin da mahaifiyar tasu take a ciki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:21 – ????????????: Mun dawo a gajiye ana labta ruwan sama muka shigo gida a gajiye maria ta gama tanadar muna abinda zamuci a gidan idan mun dawo kafin mu tafi don haka warming din shi kawai tayi taba yaran da su suka zauna ci.
Yayinda ni nake dakina ina ramuwar sallah dake kaina wayana da na bari a falone yake ta tsuwa Fauziya ta kawo min dakin.
Mamuce a lokacin na dauka muna gaisawa nake fada mata zancen tafiyan mu tace duk da dai hakan yana da kyau saidai makomar shi ga addini ne ban sani ba.
Mamu yaya zanyi tunda rayuwana yana surke da nasu yanzu koda banje don wanan ba zan tafi kan wani dalili na daban watan watarana ai.
Tace Allah ya sauwaka dama dalilin kiraki shine ki sheda wa mijinki cewa mahaifiyar shi fa tana jin jikin ta dan haka yayi gagawan zuwa dubata don Allah.
Yau munje dubata dan da kyat Alh ya barmu muka tafi duk da na fahinci hjy maryam kamar ta riga da ta tafi da farko.
Mun samu hjyn tana mai jin jikin ta sosai wallahi don ko matsawa bata iyawa don jikin yayi tsami sosai gaskiya abin gwanin ban tausayi.
Ga Alh yayi fushi sosai da wanan lamarin ya hana kowa zuwa dubanta daga bangaren shi haka itama nafisa kan ta ya bugu sosai ya hau yana bata matsala.
Innalillahi nace tare da fadin ke nan ba,a dauki wani mataki a kansu bane mamu ?
Ban san me suke ciki da zancen su ba don na dawo na samu wansn matsalan daya rigada ya farune nace yayan yana can mun barshi wurin merry nida yara da maria kawai muka dawo.
Mun dan jima da mamu muna zancen fadan su hjy din karshe dai mukayi sallama a lokacin ne na fito falo wurin yarana.
Har lokacin suna cin abinci basu kare ba zama nayi na dan taba kafin na karasa yaya ya kira layina yaji saukan mu.
Bayan mun gaisa dashi ne nake fada mai sakon mamu yace Aliyu ya kirani ya sheda min halin da ake ciki gobe zan dawo nan zuwa dare sai in tafi.
Allah ya basu lafiya nace ya amsa da amin cikin yanayin rashin jin dadi a ranshi a lokacin.
Sai bayan na gama waya nake ba su fauziya da maria labarin abindake faruwa a gida da hjyn na su.
Yaya ya dawo ya dauki wasu takardu ya tafi da yamma zuwa duba mahaifiyar shi inda yaje ya samu abin babu dadi a gare su don hjy tana jin jiki sosai a lokacin.
Yana zuwa dole yasa aka sauya mata asibiti don halin daya sameta a ciki na jin jiki sosai.
Alhamdulllahi don kudi yasha kashi sosai a gurin aka samu gano inda matsalan yake sosai don haka sai a hankali sauki zai dinga shiga.
A gidan shi kuma tunda ya iso samira ta fara farga ban abinda zai faru tsakanin shi don bata san irin matakin da zai dauka ba a kan hakan daya faru tsakanin ta sa mahaifiyar shi har sister din shi Nafisa.
Uwar ta kira tana sheda mata zuwan nashi a cikin tashin hankali da damuwa don ita dai tasan korarta zaiyi kawai a gidan.
Uwar taja wani dogon tsuki tana fadin wanan shashancin fa haka da kike yi ya kore ki mana idan kora banza ne ai yadda kikaga ubansa yayi shima hakan zaiyi don ba zan kashe kudin banza a nan.
Kedai abinda nake so dake yanzu shine ki maida hinma wurin ganin yaci yasha a bubuwan da muka karba da sunan shi.
Ta karba da tau umma don samun karfin gwiwan da tayi gun mahaifiyar nata taji wani dakewa yazo mata a lokaci guda.
Sai dai duk yadda tayi kokatin ganin yaci ko yasha daga gareta bata samu hakan ba don ko ganin shi ma yai mata wuya a gidan.
Don haka ta dauko dabaran barin abincin ga yan aikin shi ita ala dole sai yaci abinda suka hada da sunan shi din don su samu kanshi yadda suke so tunda mahaifiyar shi ta kasa juyashi yadda suka zata
Jin shiru yasa ta dauka yaci bincin da take aje mai a lokacin don haka ba wani matsalan da zata samu daga gareshi kamar yadda daddy shi ma bai iya daukan mataki a kansu ba.
Umar suna zaune a gaban mahaifin su dukkan su suna tataunawa dangane da matsalan mahaifiyar tasu kan abinda ya faru .
Don rayukan su duk a bace take bisa ga halin da suka samu hjyn tasu a cikin na tsananin jin jiki a lokacin.
Sai dai kawu din ya nuna masu rashin yadda su dauki wani mataki a wanan lokacin don a cewan shi ba a daukan mataki irin haka a cikin bacin rai.
Sai yayin da mutum ya gama nazarin abinda yake son a dauki mataki a kan nasa din ko abokin gaban naka ya gama kwantar da hankalin shi da kai.
Wanan maganan na kawu ya dan saka zukatan su sanyi don su da farko sun dauka saboda abinda mama din tayiwa kawune yasa yace samira da uwarta a sake su a police station.
Sai yanzu suka gane sanyin raine kawai irin na mahaifin su yasa ya yanke wanan hukuncin gare su.
Kulawan da hjy ta samu a yanzu yasa saukin da take samu yana kara wanzuwa a jikin ta har ya kai yanzu tana iya dan mikewa da kanta ba tare da an rike ta ba kamar farko.
Duk da hjy na kwance hakan bai hanata aikata wasu daga cikin halaiyan ta ba munana don ranan da Amma ta dan samu karfin zuwa dubata a inda aka mayar da ita ta matsa sai a kaita ta ga hjyn.
Suna zuwa basu dawo a cikin dadin rai ba don can ta shiga sake masu habaici wai anso aga bayan ta Allah bai nufa ba gashi diyanta sun mata gata bata kai ga halaka ba.
Sai mama Hadiye ne duk da warning din da Amma ke mata da ido da kai ta bata amsa tana fadin banda abinki jummai wa zai tsaya daukan wa kanshi nauyi a kanki kowa tasa ta isheshi yanzu.
Faduwan ki ai da abinda ya faru tsakanin ku da sabuwa wanan matsalanki ce ke dasu don mu ba abinda ya shafemu a cikin zancen ku domin kunfi kusa ai keda su.
Matar da kika zabi ki farauta ranta dana yarta kika iya barin dakin auren ki da yaran ki don ta don ta baki wanan goron har zamu tsaya bakin ciki kan hakan aimu bamu ga abinda tai maki ba da zaisa muji dadi hakan.
Tukun na ai yanzu kuka fara nunawa duniya nau,in taku kallan soyayyawa juna don yanzu aka fara wasan a tsakanin ku.
Amma ta gardadi mama hadiye suka bar dakin hjy tana jidali wai dama ai tasan ba gaisuwan Allah da annabi ya kawo su ba gurin ta anzo ne a samu abin fada .
Tun wanan lokacin kawu ya hana kowa daga cikin iyalinshi zuwa a kara duba jikin ta sai hakan yai mata zafi kuma, .
Salma tazo gidan don ta gana da yan uwanta maza kan zancen komawan mahaifiyar su gida don a yadda suke so daga asibiti hjy ta koma dakin ta a gidan kawu.
Sai da ta gama maganan ta habbib yace salma ke nan ina ganin kece kika damu da hakan don ita mama wanan zaman da kuma abinda ya faru tsakanin ta da hjy sabuwa kamar bai dameta ba.
Din jiya jiya jiyan nan ta gama ciwa so Amma mutunci kan kawai sun tafi gaida ita asibiti yanzu kuma yau korafi take a kan matan mu babu ko daya dayazo gaida ita wai kamar bata da gata.
Duk zancen su umar bai saka baki a ciki ba sai can da yaji sunyi shiru yake fadin ban dauka har yanzu mama zata saduda da halayen ta ba gaskiya .
Yadda mama takewa Amma tasan cewa itace mahaifiyar daddy amma take rufe ido tana ci mata mutunci daddy da Amman suna hakkuri hakkuri da hakan.
Yau gashi Allah da ikon sa an fara samun wace zata rama hakan daga kuma zabin ta sai yanzu nake kara gane mai daddy ke nufi da rashin daukan mataki a kan wa yan nan mutane ashe.
Sanin halin mama ya saka daddy yin hakan da hanani ni kaina daukan wani mataki garesu duk da yasan girman abinda suka aikata a gareni, amma ya tilasta min barin su su zauna min a gida.
Aliyu ya karbe da fadin wanan matakin daka dauka yayi daidai a yanzu ba dai gidan bane sai su zauna idan gidan zasu aura.
Zasu dauki mataki nan gaba don ba kunyane garesu ba a lokacin ya kamata a basu amsa habbib ya fada .
Din haka ke salma ki koma ki kara hakkuri har lokacin da mama zata dawo gida nasan lokacin zasu so sanin matsayin yarsu a gidan nan.
Ni dai da nine yanzun da an gama tsakanina dasu koda daddy ya hani daukan mataki a yanzu ya zama dole gareni in dauka koda a boyene.
Murmushi umar yayi yana kwantar da kai ga kujera tare da lumshe idon shi yana jin zafin irin yadda yan uwan shi keji game da maganan.
Salma ce ta kawar da shirun falon da cewa sai maganan Nafisa don daddy yayi fushi da zaman ta nan gurin mama datayi tun dawowan ta kasan nan sosai.
Dole yai fushi don sam basuyi tunane ba daga ita har mama din data barta a nan tunda nura ma daddy bai barshi ya biyo mama nan din ba ai habbib ne ke magana.
Eh hakane gaskiya don lokacin dana zo munyi wanan magana da daddy kan zaman ta wurin mama ya nuna min bacin ran shi kan hakan sosai ranan.
Yanzu shi Nura a gurin wa yake zaune umar ya tambaya cikin kulawa tare da bude idanuwan shi ga yan uwan nasa a lokacin.
Yana gun maman twins tun data dawo da farko a gurin maman su ikilima yake sai fitina ya dinga aukuwa a tsakanin shi da yaran ta a cikin hakan ya koma gun Amma dawowan maman twin’s din yace a gurin ta yake yanzu.
Idon shi ya lumshe yayin da Aliyu ke fadin you see zaici gaba da magana takon takalman da sukaji shine ya dakatar da shi ga maganan da yai niyar yi a lokacin.
Gaba dayan su ido suka sakawa samira da ta shigo cikin wani tako tana rangwada har ta kawo garesu.
Kuna nan ashe sannun ku da zuwa sai Aliyu ne da salma suka amsa habbib kan waya ya dauka yana duba a lokacin kamar baisan tazo gurin ba.
Akawo maku abin tabawa ne tace tana kallon inda umar din yake zaune idan bako tazo gidan ka sai ka tambaye shi ka bashi ruwa habbib ya bata amsa a gwatsale.
Ba hakana bane kawai naga kamar har kunsha a nan ne yasa na tambaya ki barshi duk a koshe muke.
Ta dan taka zuwa gefen kujeran da umar din yake zaune da niyar zama a hannun kujeran da sauri ya daga yana fadin.
Zamu iya tafiya yanzu salma muje mu sauke ki asibiti daga can mu duba mama kan mu tafi yana fadi a daidai lokacin da samira ta iso gurin .
Tsayawa tayi sororo tana mai bin shi da kallo kowa na falon ya fahinci may yasa yai hakan a lokacin.
Wani kallon banza habbub ya bita dashi lokacin da yake kwasan wayan shi saman table din.
Har suka fice tana binsu da kallo ranta yai bala,in baci da disgatan dayayi a gaban yan uwan shi din.
Wayan ta dake hannun ta dauka tana duba lanban mahaifiyar ta takira take fada mata abinda ya faru.
Bata kai karshe ba uwar ta hauta da sababi tana fadin ke tafi can samira kina ban mamaki da har yanzu kika kasa juya wanan sokon mijin naki.
Har yaushe kamar umar zai tsaya yana wani baki baya kina faman binshi kamar wata sokowa ki saurareni da kyau kiji may zan fada maki yanzu.
Ina jin ki umma ke har yanzu laifina kike gani kan hakan umma kwata kwata fa baida lokaci na balle in samu daman juyashi yadda kike nufi din.
Rufa min baki ke ba mace kike ba da har namiji zai gagare ki juyawa samira ?
May kika rasa a jikin ki wanda maza keso da baki dashi a yadda ya baro wacan matan nashi yanzu ne ya kamata ki nuna mai ke din mace ce.
Nan dai ta shiga nuna mata hanyar da zatabi ta samu kanshi tunda asiri ya gagareta aiwatarwa a gareshi sai su juya hanyar kisa da kisisina irin namu na mata.
Samira tace na gane umma yau insha Allahu zanyi duk yadda kika fada idan ya shigo tace kada ki manta ki dakatar da duk wani dan aikin gidan daga yi masa komai ki daina wanan kwanciya a dakin har mu samu kanshi.
Umma komai fa kikace har girki da komai ke nan fa ta fada a shagwabe katseta uwar tayi ta hanyar kiran sunan ta a kausashe da Samira .
Zakiyi abinda nace ko sai kwabar mu yacin ma ruwa zaki gane kuren ki don ina gab da fita bayan ki muddin baki bi abinda nake fada maki ba.
Umma zanyi abinda kika fada min daga yau din nan zan fara koke fa uwar nata tace da ita tana kashe wayan bayan ta ce ina sauraren ki zuwa dare.