NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Barci nake da safe bayan na karya nasha magani na dan koma barci don har yanzu jikin nawa bai gama warwarewa ba a lokacin.
Karan wayana dake gefe ya tayar dani tun ban dauka ba na gane shine ke kirana a lokacin ko kuma mamu don sune masu yawan kirana ko wani lokaci .
Dan dama dama salma da Atika da yanzu zama ya dawo dasu kano ita da mijin ta dake aiki karkashin yaya a yanzu .
Dauka nayi da sallama ina gaidashi kamar kullun tambayana yayi karfin jikin mu nace mai da sauki dukkan mu Abdulsalma yana falo babana kuma Fauziya ta goyashi yayi barci.
Ok bakuje asibitin ba ke nan yau ya tambaya ?
Saida na dan marairaice muryana kafin ince naga munji sauki ne yaya look zahra idan yaran nan basuji sauki don Allah ki mayar dasu asibitin nan please.
Nace zan kaisu yaya idan naga hakan Allah ya sauwaka yace na amsa da amin sai kuma ya danyi shiru nidai ina sauraren shi sai naji yace dani.
Idan kun kara jin sauki zuwa next week zanso ku shigo Nigeria kodan sanyi da yai yawa a can don yaran nan .
Allah ya kaimu na iya bashi amsa dashi tare dayin shiru yace ko akwai wani abinda kuke bukatane ?
Babu komai na kara bashi amsa ku kula da kanku don Allah kada ki bar yaran nan su dinga fito ko kofan gidane.
Na kara amsa mai da toh yaya kawai alaman dai wani abu yana damuna a likacin shima haka ya kashe waya yana mamakina a ran shi.
Nima ta bangarena mamakin shine fal a raina yadda dan kanshi yanzu yayi shawaran zuwan mu gida.
Jin hakan danayi daga gare shi yasa na fara shirin duk wani abinda nake bukata tare damu na hada a shirina har ina mamakin kaina da kayan dana hada don tafiya.
Kamar yadda yace din hakane don munyi waya dashi da kwana biyu saiga abokin shi yazo ya amshi pasphots din mu don shirin tafiya.
Abinda ya dan kara kaimu wani lokaci shine babana da yanzu nake goyo saida akai mai nasa shirin shima ranan Friday da dare muka daga zuwa Nigeria nida yarana ina dokin zuwa gida inga yan uwa da abokan arzikina.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:22 – ????????????: Tsakanin merry da Samira sai harara yanzu don tun ranan basu kara haduwa ba irin hakan merry taso ta tayarwa yaya da hankali ya nuna mata ba shike gaban shi ba don shi yanzu yana fama da jikin mahaifiyar shi ce.
Don tun wana ranan yaya ya mayar da hankali sosai a gurin hjyn su komai zai shiga yai mata shi tun lokacin daya fahinci babu jittuwa a tsakanin ta da matar da suka aje mata mai kula da ita.
A bangare merry har lokacin zuciyar ta na cike da kuna zancen samira bayan wacan da take tausan zuciyar ta akanta yanzu kuma ya kara auro wata mara mutunci.
Ai gara da Fatema bata taba mata rashin mutunci ba duk haduwan su da sukeyi wanan haduwa daya tayi masu rashin mutunci daga ita har diyanta.
Gashi bai bata dama ba da zatai mashi magana don yace shi zancen mahaifiyar shine yanzu a zuciyar shi ba zancen banza.
Wanda tasan hakan don batayi zaton halin da hjyn tasu take ciki yakai haka tsanani ba saida sukazo taga halin da matar ke ciki yasa ta dan tausaya mata duk da har yanzu akwai kallon tsana da matar ke aika mata.
Suna a hakan kwatsam sai gamu mun sauka garin ba tare da sanin kowa akan zuwan namu ba lokacin.
Abin kallo muka koma garesu dan tana daki da yarta take jin hayaniyar shigowan mu gidan don yara harka dasu ba bace yake ba.
Saukan yamma mukayiwa kano shida mansur da yake jin dadin kasancewan su tare a yanzu don kwazon shi da nuna wayewan shi da shishigin shi ya shigewa umar din a jiki sosai.
Ko mamu ban fada mata shigowan mu ba sai dai ji kawai sukayi mun shigo garin ranan a bakin murja dana bugowa waya ta samu labari.
Don nakira murja ta hannun damana da nomban Nageria tana dauka tace wai kina inane haka naga nomban naija nace muna cikin ta ina son ki zo gidan kafin mu karaso ki mun gyara don Allah.
Ihun murna ta dan sake tare da fadin ashe muna da manyan baki kasan nan bari yanzu in shirya kafin ku iso.
Shine take fadawa Amma da mama hadiye har mamu taji take fadin ban fada mata zamu shigo ba sam bata sani ba ita.
Merry bata san da shigowan mu ba Queen ce dake jin motsin yara ta dan saci jiki tafito daga dakin nasu shine ta samu yaran tare da mahaifin su a falo ina daki tare da murja a lokacin.
Sam ban san merry na garin ba sai murja ke fada min taji ana fadin merry ma tana kasa nan tazo akace sai dai har yanzu bataje can gidan mu ba don naji Amma na fada kan hakan.
Tana kasan nan fa murja na tambaya cikin mamaki murja tace min wallahi nima haka naji ita da yarta akace.
Dan jim nayi ina tunane kafin ince bai fada min hakan ba kuwa kodai wani dalili yasa ya taramu a nan din wanan lokacin na tambayi kaina.
Saidai zan share hakan kamar yadda bai fada min ba nima ido zan saka masu a kasan zuciyana kuma ina tunanen irin zaman da zamuyi a wanan gidan mu uku din.
Tambayan ta nayi hjyn su fa tana inane tace min a gidan nan naji akace take mana don nima tun shigowana ban samu ganin ta ba nan na nufo kai tsaye.
Shine ya shigo dakin nawa yana dauke da babana sai Sultana dake makale da jikin shi ganin shi yasa murja zata bar dakin yace no ki zauna fita zanyi yana miko min yaron da har yanzu bai gama warwarewa daga ciwon da yayi ba.
Mama fa tana inane wai na tambaye shi tana dakin ta ai, a nan gidan take ne na kara tambayan shi yace tana wancan dakin na farkon shigowa inda Amma ta taba zama.
Mikewa nayi ina fadin ai ban sani ba har na shigo ban shiga na gaida ita ba cikin nuna kula nake maganan.
Wanda hakan yai mai dadi har cikin ranshi saidai bai nuna hakan a fili ba fita yayi daga sultana dakin.
Mun fito zuwa dakin nida murja saidai tun a kofa bashi da tsami ya tare mu dake fitowa daga dakin.
Haka muka daure muka shiga nan muka samu mai kula da ita tsaye akan hjy tana faman kawar dakai gefe da alama dagata take son yi a lokacin.
Jin sallaman mu yasa ta dakata da abinda takeyi din da sauri muka karasa bakin gadon muna gaida ita ta amsa da kyat badon ta shedamu ba a lokacin.
Dan shirune ya biyo a dakin sai can nacewa matar ya naga haka take fadin tayi najasa ne nake son in kaita bayi in gyara ta kuma na kasa dagata ni kadai.
Dan shiru nayi a wurin kafin ince ai ba sai kin kaita bayi ba a yadda take din nan .
Yaya za aiyi idan ba a kaita bayin ba matar ta fada tana bata fuska da gani ta gaji da wanan aikin don da wahala sosai gaskiya.
Nace leda za a samo yanzu bari kiga yadda zaki dinga yi leda murja tafi ta samo min da sauran abin bukata irun deltol da kamshi dasu handglove.
Muna dakin har ta dawo nasa matar ta debo ruwan dumi a bayi a lokacin na shiga gyarawa hjyn jiki dagani sai matar a daki.
Tana kallon yadda nake komai har zanin gadon dana gyara a cikin dubara duk da hjyn na sama kwance sai nayi dabara irin yadda asibiti suke gyara duk a kan idon matar nayi shi.
Ta sauke a jiyan zuciya tana fadin wanan ai hanyar sauki ne yafi wanan cicibar da muke mata zuwa bayi kullun.
Nace yafi sauki da za a samu allurai yanzu ai mata zai taimaka mata sosai yadda jikin nata zaidan yi karfi taji dadin sa.
Wanan sai idan Alh ya dawo matar tace noce No bari a rubuta kawai sai a sayo yanzu ai mata har na fita daga dakin hjy sai bina da idanu takeyi kawai bata iya magana.
Ban kuma sa wanan matar tasan ni ko wacece ba ga hjyn sai bina takeyi da kallon mamaki har na fita daga dakin.
Saida nayi wanka na dan ci wani abu na fito dauke da ledan magani a hannu na zuwa dakin hjy muka hade da yaya da dawowan shi gidan ke nan tun fitan shi.
Gaidashi nayi tare da dan tsayawa yake tambayana inda zani nace dakin hjy.
Na shiga dakin bayan ya wuce tana kwance a yadda na barta da farko saidai wanan karon barci na samu tanayi.
Tambayan matar nayi ko taci abinci bayan fitana tace kwana biyun nan tunda ta fama wajen ta rage walwala da komai.
Abu mai ruwa nace ta hado ko kunu ko tea a bata sai ta hado tea don dare yayi ba kunnu a lokacin.
A hankali na dinga daga ta har tayi daidai a yadda nake son taji dadin shan tea din sai likacin ta dan bude idanuwan ta gaida ita nayi da sannu mama ya jikin ?
Ta gyada min kai kawai na mika hannu na karbi shayin ina dan bata kadan kadan ga kyale a gefe ina goge mata baki dashi idan ya dan zubo kada ya bata mata jiki.
A daidai wanan lokacin ya shigo dakin dauke da babana sai queen da sultana dake tare dashi gefe da gefen shi sun saka shi tsakiya.
Yana tafe yana Kallon mu da mamaki karara a fuskanshi yadda nake rungume da ita ina bata shayi tana sha a hankali har ya karaso wurin.
Da sauri matar ta shiga gaidashi tana fadin yau wanan yar uwar takula da tazo ta taimaka muna sosai wallahi nan dai ta shiga lissafamai taimakon da nayi mata wurin gyara hjyn.
Dan murmushi yayi yana fadin wanan baki santa ba ko tace yawa ne daku har yanzu ban gama fahintar ku ba ai Alh.
Nice na katse zuban da take mai na fadin dama allura nake son yi mata wanda zai dan taimakawa karfin jikin nata.
Yace hakan yana da kyau dama ina tunanen ko mu mayar da ita asibitin ne saidai likita ya zo ya dubata yace ba abinda zasuyi mata yanzu kuma sai bayan wata uku suga aikin da sukai mata din.
Ba matsala idan zan gana da doctor din dake dubata don wata course mate dina ta fuskacin irin matsalan nan sai dai ita faduwa tayi a bayi .
A lokacin na samu experice akan irin matsalan don an dan bamu hit game da case din nan shiyasa na sayo wanan alura na gwada yi mata duk da baikai wancan din danake so karfi ba.
Yace a sanyayye is ok idan kinga ba matsala ga hakan ai zaki iya mata mu gani ba bata lokaci na fara hada alluran hjy na kwance sai kifta ido takeyi tana son magana ga ciwo na cinta kuma ko hannunta aka daga sai tayi kugi mai nauyi na ciwo.
Dan daga ta mukayi da taimakon shi na cilla mata alluran a jiki muka mayar da ita a hankali muna mata sannu sai gyada muna kai take iyawa.
Mun dan dade tsaye a gurin ta kafin mu fito daga dakin don barcin da mukaga ya fara daukanta a lokacin.
Tare muka fito dashi har yaran shi din muna fitowa merry ne a zaune saman kujera ido ta kura muna tana bin mu da kallo har muka karaso inda take.
Fuskanta yana a daure na sakar mata murmushi ina fadin maman Queen you are welcome na tare ta da fadi kafin ta kare min kallon tsanan da take jefo muna daga ni har shi.
Sai lokacin dataji gaisuwan da nai mata ta da ce dani yaushe muka shigo kasan ne nace yau din nan .
Faith ta fada min kune kuka zo dazun nace karya take ashe gaskiya ta fada .
Tambayan mahaifiyat ta da yan uwanta nayi tare da fadin ya karin hakkurin rashin mahaifinta tace sun gode sai ban tsaya falon ba na nufi hanyar dakina nan na barsu tare a falon ban shiga daki ba saida na leka dakin yarana na samu sunyi barci ko sai fauziya da maria ne zaune suna hira.
Fauziya kinsan hjy tana gidan nan kuwa nake fadawa yarinyar ta dago da sauri tana kallona da mamaki naci gaba da fadin .
Tana gidan nan bata da lafiya sosai don nima ban dauka ciwon har yakai haka ba gaskiya.
Da safe sai ku shiga ku gaida ita don yanzu tayi barci na fada ina fitowa har na kai kofa na juyo ina fadin.
Maria sai kin kula min da yaran nan sosai wanan karon don bamu kadai bane a gidan nan yanzu gaba dayan mu muna gidan nan ko yanzu na bar sultana da babana a falo tare da baban su duk da nasan zai shigo min dasu nan idan sun gama.
Tace insha Allahu zan kula kamar yadda kikace hjy banda matsala kan hakan don nasan maria tana aikin ta da kyau yadda ya dace tayi.
Saidai dole in kara fada mata don bamu taba haduwa haka ba gaba dayan mu lokaci guda don hakan ban san abinda zai iya biyowa baya ba nan gaba a gidan.
Duk da ganin hjy yasa zuciyana shiga cikin wani yanayi hakan bai hanani kuma tunanen ko me yasa yaya ya hadamu haka a guri daya ba wanan karon abinda bai taba yi ba tun bayan dana fara haihuwa dashi.
Kara tsabatace jikina nayi bayan na shiga daki don yanzu babu abinda nake ji sai barci don haka ina fitowa na fara shirin kwanciya kawai.
Lokacin ne yaya ya shigo dakin nawa da yaran sa har lokacin Queen tana biye dashi a baya kallo daya nai masa naga yanayin da fuskan shi ke ciki nasan ran shi a bace yake lokacin.
Karbi yaron nan barci yake ji yace min nasa hannu ina karban yaron yake kara fadin ina ga har yanzu jikin nasa bai sake shi bane ko ?
Kafin mu taso lafiyan shi kallau saidai idan zaman jirgine ya taba shi yanzu din muryan Queen ne ke fadin daddy a nan zai kwata da maman shi ya bata amsa da eh.
Sai yarinyar tace itama a gurin baby din zata kwana tare dashi tana fadi tana dan jawo kafan yaron dake jikina.
Naji yace No kije gun mamakin tana can tana jiranki ku kwanta ta tabure mai fuska tana fadin ita tare da baby zata tsaya nan.
Da kyar ya lalashe ta suka fita ban kwanta ba saida na koma dakin naga maria ta rufe masu kofa na dawo na kwanta zuciyana cike da tunane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button