SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Washegari ina sallame sallah na kira fauziya ta dawo dakina ta tsare min yarana na nufi dakin hjy in duba su.
Na shiga da sallama dakin aka karba min wanan matar ne tana zaune saman sallaya inda ta idar da sallah muka gaisa nake tambayan ta jikin hjyn tace jiya sun samu barci sosai kuwa.
Nace da son samu ne a yanzu mama sai muyi mata wanka a bata abinci zaifi tasha magani kafin a kara wani allura zuwa anjima.
Tana mikewa take fadin ai tunda gani hjy ba matsala dama takan min nauyi ne na kasa daga ta ni kadai yasa muke tsaikon komai.
Ban dakin zamu shigane nace yawan motsawan da takeyi shike kara fama wurun ciwon nata a yanzu ba irun nomal wankan mu ya dace da ita ba sai dai a dinga goge jikin yadda zata dinga jin dadin sa kamar yadda kikaga nayi mata jiyan.
Ganin zata bata lokaci na shiga bayin na hado ruwan dumi na dauko tawul na fito na samu tana kokatin cire rigan na taimaka mata muka gyara mata jikin na cire wanan zanin gadon na saka mata wani cikin dubura hjy sai bina da idanuwa takeyi kawai tana kallo na ga sannun maman da muke mata akai akai tana amsawa.
Kitchen na nufa don duba dan abinda zata iya ci mai sauki na samu babu kowa a kitchen din a lokacin.
Ruwa na dora a gas din sai bin kitchen din nakeyi da kallo har na dan dama mata kunun bature dana gani a kitchen din na fito.
A kofa muka hadu da yaya ya dawo daga masalaci yana saye da brown jallabiya mai sulbi a jikin shi sai tasbaha dake hannun shi yana ja.
Gaidashi nayi da kwana ya amsa min tare da fadin kun tashi lafiya ya gajiyan tafiya nace tafiya yabi lafiya ta falka ke nan ya tambaya da nufin hjyn tasu.
Nace eh har munyi wanka zata samu abunda tace tasha magani yanzu don haka ya dace ta samu ealy morning.
Tare muka shiga dakin dashi na samu matar ta gyara ko ina na dakin tana saka kamahi don haka na umurce ta tayi kafin in fita.
Aje abindana shigo dashi nayi na fita na barsu a dakin falo naje na duba table da karami sai na danyi mai dabara ya koma kamar na asibiti na dawo dauke dashi ina fadin ki kama min wancan gefen mu daga ta dakyau.
A cikin dabara muka dago ta ta dan kai zaune yana tsaye duk abunda mukeyi ya kura muna idanu kawai bace uffan ba har lokacin da muka fara bata abincin tana karba kamar ba hjy jummai ce ba a kwance haka mutumba a bakin komai yake ba a gurin Allah idan ya tashi ikon shi ga bawan sa.
Yau hjy ce haka a hannuna sai yadda mukayi da ita babu bakin magana din tunda nazo banji tayi magana da bakinta ba hakan yasa na dago ina tambayan shi wai tana magana kuwa yaya ?
Ajiyan zuciya ya sauke da alama yayi nisa a cikin tunane lokacin yace tun lokacin data fama ciwon nan jikin nata ya kara rikicewa haka ai.
Zata samu lafiya da yarda Allah na bashi amsa ina mayar da hankali a gurin ta magani na dauko muka bata tasha muka mayar da ita ta kwanta tana lumshe ido sai ga hawaye yana gangarowa a fuskanta a hankali.
Haba mama kada kuma ki saka damuwa a ranki wani ciwo yazo ya shige ki kuma.
Fita naga yayi a dakin saida naga ta dakatar da hawayen na bar daki ina fadawa matar su kwanta su dan huta zuwa goma zan shigo in mata allura .
Godiya matar ke mun tana saka min albarka nayi murmushi na fita daga dakin zuwa nawa part din.
Daki na koma wanka na shiga don na samu har lokacin yaran suna barcin su a dakin Fauziya ma tana kwance a inda tayi sallah.
Wanka nayi na shiya sai ga maria ta shigo dakin tana gaida ni zata dauki yaran tayi masu wanka kamar yadda ta sabayi masu a can.
Sultana ta fara dauka a lokacin fauziya ta falka itama hakan ya tayar da babana daga barci.
Kafin takwasa duk mun shirya mun hadu a dakina inda na kara jawa kowa kunne da zaman gidan da zamuyi tare da wasu duk da bamu saba da hakan ba tun farko.
Alhamdullahi duk sun gamsu da warning din da nayi masu maria na umurta data fita zuwa kitchen ta duba idan masu aiki basu fito ba ta hadawa yaran abin karyawa.
Bata jima ba ta dawo tana fadin sun fito na amsa mata fita tayi zuwa dakin su ta gyara masu zuwa tara da wani abune na fito tare da yaran har lokacin babu kowa a falon gidan.
Dakin kwanan shi muka nufa tare da yarana su duka hudun nayi sallama a kofa kafin ya karba mu gaidashi mukayi da kwana yana kallin yaran cikin kulawa daga inda yake zaune har lokacin da alama bai riga da yayi wanka ba don jallabiyan da nagani a jikin shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:22 – ????????????: Zaune muke gaba dayan mu a dining yaya umar ya fito daga dakin shin a cikin shitin shi yaran suka mike a inda suke suna gaida shi yana daga su daya bayan daya yana saukewa.
Baifi minti biyar da zama damu ba sai ga merry ta fito da yarta fuskanta babu yabo babu fallasa a tare da ita.
Yarta ne tazo wurin shi yana subantanta suka gaisa kamar yadda yarinyar tayi hakama uwar tayi don sai da suka danyi hugging din junan a gaban mu.
Zama sukayi suma don karyawa a lokacin nice na fara gaida ita ta amsa bawani sakin fuska har lokacin tana gaidashi.
Muka fara cin abincin gaba dayan mu sai maria ce bata cikin a lokacin don har fauziya tana gurin zaune.
Kamar yadda ta saba shigo masu da kasaita ko wanan karon haka ta shigo muna tana tako dadaya dole hankalin kowa ya koma ga kofan don ganin mai shigowa banda yaya dake dauke da abbana sai Queen dake gefen su tana saita dauki Abba din ta rike shi.
Farinta na maine na fara hangowa sai gashin dokin da tai kitso dashi ya sauko mata har a baya sai wani cin chewing gun take a bakinta irin na yan bariki sosai din nan.
Itama dai kamar yadda muke kallon ta gaba dayan mu har yaran hakane take kallon mu da mamaki itama.
Take iskancin data shigo dashi ya gushe lokaci guda yanayin ta gaba daya ya canza ta shiga dan kame kame kamar zatayo wurin mu ta fasa shiga dakin hjy a lokacin sai kuma ta juya ta shiga dakin da hjy din ke ciki.
Bani da nake ba hausa ba har merry dake kabila saida ta harbo jirgin ta na daburcewan da ta shiga a lokaci guda don ganin mu.
Tsaki merry taja tana fadin pulish lady tana tsamanin kowama kamar tane haka ?
Banyi magana ba saima Allah ya taimakeni a daidai lokacin wayana yayi kara hakan yasani tashi a lokacin na barsu a wurin zaune tare da yaran.
Murjace ta kirani a lokacin na shige daki ina karba wayan bansan me zata fada min ba na rigata fadin ke murja yanzu naga wanan matar da yaya ya aure wallahi.
Dariya murja ta kwashe dashi tana fadi wai dama ke baki santa bane ko a photo nace ina zan santa nida ba wani dadewa nayi a kano sosai ba.
Ai bama zaki santa ba din don ba,a kanon suke da zama ba dama suna lagos duk dadewan nan sai yanzu da mahaifisu yai ritayane suka dawo nan tunda komai ya kare masu.
Suna dawowa kuma tana ganin yaya ta leke mai saishi take so nace amma murja wanan tsohuwace fa sosai don dai jikintane baya nunawa kawai.
Tace tsohuwa ko ta gaske ma don bakiga kannen ta maza bane ai da kin gaskanta tsofan nata sosai.
Yanzu kuma haka yaya yake zama da ita murja bakina ya subbuce da fadin hakan a lokacin don mamakine fal a zuciyana sosai.
Dariya ta kara kwashewa dashi tana fadin haka ko yake zaune da abinsa ba gashi har ta buge mahaifiyar shi ba tana kwance ba,ai komai ba koda yake su basu son a fadi hakan ai.
Nan murja ta kara ban labarin fadan nasu tana kwashewa da dariya sosai nake fadin don Allah murja barni da abin haushi mana haka.
Shi yaya wani irin zuciyane dashi haka da har mace zata nakasama uwa kana zaune da ita baka dauki mataki ba uwa fa ba wasa bace murja.
Ke bafa laifin yaya din bane don kawune ya tauye shi kan daukan mataki kinsa aiko bai dauka ba yan uwan dasun dauka yanzu.
Laifin kawune da ya hana kowa magana ke abinda baki sani bafa shine a yadda naji Amma na fadi ranan .
Babu ruwan yaya da uta tunda ta shigo gidan shi suna nan sai bare baren kudi suke a kanshi don dai kawai a jawo hankalin shi gareta.
Zuwan merry ma kasan nan ba karamin fitina aka kwasa ba a tsakanin har hjyn ta fama ciwon ta take rabke haka.
Humm Allah ya kyauta nace mata tace amin dama na kirakine in fada maki su mama zasu shigo wurin ku tare da Amma yanzu.
Nace kai ai da su barni in je don yanzu idan sunje yaya ba zai bari in tafi gida ba kuma kin dai san halin shi murja.
Tace sunce zasu shigo su gaida yaran da akace basu da lafiya ina ganin yaya din ya fada masu hakana.
Shigowan Queen dauke da Abbana dakin sultana na bayan ta tana fadin ta basu babyn su ya katse min wayan da murja da mukeyi.
Zama yarinyar tayi a nan tare damu yaron yana shan nono sai faman jagulan shi take da gani tana sha,awan yara kanana sosai .
Tana nan tare damu har wani lokaci a dakin yayin da suke dan surutun su wani lokaci in basu amsa don gaba daya yanayi jinsa nake babu dadi a tare dani a lokacin.
Sallaman su yan gidan mune da fauziya ta sheko da gudu tana fada min shigowan su yasani fitowa daga dakin.
Bayan sun gama mamakin girman da Fauziya din ta kara tare da yarana suka shiga dakin hjy don su gaida ita da jiki.
Sun samu ranan ta dan samu sauki sosai tana kwance idon ta biyu ba barci takeyi ba suka fara gaida ita a daidai lokacin na fadon dakin da sallamana don murnan ganin su.
Amma da yanzu tsofa ya kara takureta sosai sai lalaba rayuwa da akeyi tana ganina ta washe baki tana murna sai fadi take masha Allahu A ruwa kece haka kin zama wata dirkekiya dake sam barka .
Nace Amma ke kuma ga tsufa yana batun rufe muna ke a yanzu da mukafi bukatan ki a tare damu .
Nan dai muka shiga gaisawa dasu a dakin kafin in koma wurin da hjy take kwance ina tambayan lafiyan jikin nata yayin da dakin gaba daya yai tsit ana sauraren mu.
Ina fadin ya kamata ta samu abinci taci yanzu don Allah ki daina barin ta sai lokacin da za a gama abinci ace a lokacin za,a bata abinda zataci.
Mamu da tun shigowan ta batai magana ba tace gaskiya kan yunwa ma ai kanta ciwone sai lokacin matar ke fadin ai na gode da zuwan yarnan taku sosai don ita ta taimakemu a daren jiya da zuwan su ta shiga dawainiya da hjy sai gashi yau ta tashi jikin da sauki sosai.
Da ai tun ranan data fadi din nan jikin nata har jiyan ba dadi sosai wallahi sai mama hadiye ke fadin hjy ki bar motss jikin tunda motsawan shike kawo matsala irin haka.
Shine ai wanan yar taku ta fada ko wanka a nan saman gadon tai mata sabanin da can da sai mun tafi bandaki da ita munyi ko hakan ai sai ya jawo fitina.
Aikin sune hakan ai dadin karatun ke nan wallahi kinga abin yazo da sauki bama sai likitan da ake daukowa yazo din ba tunda ga fatima Allah ya kawo kasan.
Wai dama ba a nan suke zaune bane ke nan matar mai suna Asabe ta tambaya tare da fadin gaskiya na gansu kamar kabila har yaran don basu jin hausa.
Wai baki santa bane matar mai gidan nan ne fa yar uwanshi da aka aura mashi a can suke zaune da yaran su duka kasan waje.
Ikon Allah kaga mace kan wallahi Allah ya inganta rayuwan ku dana auren ku gaskiya kan Alh yayi dacen mace mai mutunci da tarbiya bakuga yadda takeyi ba da boyar Allah nan tunda tazo.
Ai shine dama haka duniya ta gada ai shi da na kowane don baka san ta inda zai taimaka maka ba watarana Amma ta fada tana mikewa tare da fadin Ina yaron da aka haifa din bamu sanshi ba mun daiga yan biyu a waje.
Tare da Amma da mama muka fito daga dakin muka bar mamu da hjy maryam a gurin hjy suna kara mata sannu da jikin.
Sai lokacin naga Nura autan su yaya yana gaidani yana zaune tare da yaran da Fauziya suna turanci kai katako kamar yadda yanzu nake kiran shi tun bayan aurena da yaya yace har yanzu baki daina kirana da wanan sunan ba.
Ina zan daina tunda bana karfen kake ba na dan tsaya muka kara gaisawa da yaron a wurin kafin in juya na kaisu dakina .
Nan muka kara gaisawa sosai dasu muna yaushe rabo sai mama hadiye ne ke tambayan ace merry ma tana gidan ai.
Nace eh mama a nan muka sameta ban ma san da zuwan ta ba saida muka zo garin na sani murja ce ta fara fada min tana nan amma shi bai fada min ba.
Fita nayi zuwa kitchen na sa aka hado masu abin motsa baki kafin in koma dakin na nufi dakin merry a cikin karfin hali irin nawa na kwankwasa kofan nata.
Kusan sau uku kafin ta amsa da who is dat nace it,s me Fatima kamar ba zata bude ba sai can naji ta bude kafan nayi mata yaya lokaci ban jira amsawan ta ba nace.
Parents din mu ne suka shigo duba jikin hajiya naga ya dace su gaisa da ita shine na zo fada mata.
Sai ta danyin jimmm a wurin nace zaki iya masu biyayya koda bakiso saboda martaban yarki da take jinin su hakan zai sa su soku sosai a jiki.
Ina fadin haka na bar wurin ba tare da tsayawa in saurari amsan da zata ban ba don irin kallon da take min a lokacin gashi da gani tasha kuka don idanuwan ta da suka nuna alaman hakan.
Dakin na koma inda na samu su mamu sun shigo suna zaune saman kujera ga abinda aka kawo masu ba wanda ya taba a cikin su.
Sai fadi suke su zasu tafi nace haba maman ikilima tun yanzu zaku tafi tace yaya na iya da wanan mai alkunyan wai da ita ba zata shigo dakin ba tace.
Mumu na kalla ina fadin ba zaku bari har a dan jima ba hjy maryam da sai kallon manyar jakkunan dake zube daga can gefen gadona ta juyo tana fadin Alh ne kawai a gida sai murja da Nafisa suma yanzu da mun koma zasu fitone sukace.
Muryan merry ce dake shigowa ya hana kowa wani magana merry ta shigo tana saye da wani bakin dogon riga a jikin ta mara hannu rigan sai gurin hannun da akaiwa dan tattara kamar kwalliya.
Gaida su ta fara tana tsaye suna binta da kallo hjy maryam da mamu suna tambayanta ina Amina saini ce suna tambayan Queen ce don haka suke kiranta nan.
Ta ce tana waje da sauran yaran a falo tun dazun bata tsaya ba kawai ta juya ta fita daga dakin tana mai jin zafin su a ranta don gaba daya kowa a wurin ta mai laifi ne gare ta.
Don sune suka jawo mata bacin ran da take ciki a yanzu wanda auren mu da yaya yayi take ganin da hadin bakin duka yan uwan shine akayi shi.
Basu dade ba suka fito har mama hadiye sai Amma ce da zata tsaya damu har aya umar din ya dawo gida .
Sai da suka biya dakin hjy sukai mata sallama kafin mu rakasu har waje nida maria ina fadin sai mun shigo suka tafi.
Ban koma daki ba kitchen na hada ma hjy abinci mara nauyi nakai masu dakin nan muka tsaya muka bata tare da matan kafin in fito na bata magani tasha.
Dakina na koma na samu har Amma tayi barci yasani fitowa zuwa wurin maria a nan na dan zauna don kada mu tayar da Amma danaga ta samu barci sosai a lokacin.
Daga dakin na yara na tskayi sallaman su murja na fito da sauri na tare su muka dunguma zuwa dakin hjyn da a yanzu zaune muka sameta tana zufa nace su kunna Ac sanyi ya gauraye dakin tukunna zata fi jin dadi.