SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

A haka har muka share kwanaki a gidan ba ruwan wani da wani a cikin a na zamane kawai a tsakanin mu kowa yana jin kansa.
Kwatsan da wani safiya nake jin dan hayaniyar yaya da merry tun suna rigima a hankali har aka fara jin muryoyin su .
Nidai ina dakina ban fito ba sai wani tsawon lokaci da maria ta shigo take fada min wai taga merry ta fita tana ganin kamar tafiyan ke nan tayi don da kayan su suka tafi.
Sai zuwa yamma kuma muka ganta ta dawo a rikice wai bataga Queen ba inda sukaje shiga jirgi.
Gaba daya hankalin mu gidan ya tashi sosai da wanan labarin batan Queen daya riskemu a lokaci daya.
Duk abin nan da akeyi amaryan yaya tana part din ta ta kure shiyanta da sauti gamu sai faman buga waya akeyi ko ina tun munayi mu kadai har abu ya karde unguwa ga baki daya security suka zo sai lokacin ne baba balarabe ya shiga yai fada sosai kan abinda ta aikata din ya fito yana fada sosai har saida merry dake tsaye a gefena ta jingina da jikina don kukan dayaci karfin ta.
Babu mai iya kama wani a cikin mu a lokacin duk hankali tashe muke a gidan gaba dayan mu ga baki daya .
Naga karfin halin wanan samiran don har mukaci muka sude muka koma ciki wanan matar bata ko leko mu ba kowa na fita da ita a baki a gidan.
Sai can cikin dare muna zaune a falon mu zugun zugun merry duk ta fice a yanayi ta sai ga su yaya Aliyu sun dawo da yarinyar wai a nan cikin airport aka sunce ta ta samu wuri ta boye don bata son bin mahaifiyan ta zata zauna da yan uwanta a nan.
Shi umar ma a lokacin bai garin yayi tafiya kasan south Africa wani business shida Nasir sai ta waya muke communicating dashi kawai.
Merry data gigice lokacin da aka shigo da yarinyar sai zubewa tayi sumay a lokaci daya kafirci baiyi ba wallahi.
Ranan munga tabara a wurin merry irun na kafirai da basu san Allah ba mahaifiyar ta ko ta kira yafi a kirga a ranan.
Sai lokacin muka samu kwanciyar hankali kama yarinyar nayi naje nayi mata wanka na bata tea mai kauri tasha sai barci.
Wayewan gari tun karfe shidda gidan namu a cike yakw da mutane yan barka da arziki da Allah ya kiyayye wanda ya nuna hadun kai ga musulmai gare ta.
Har wani kungiya na kirstan aka turo muna gidan wai daga kungiyar su na kiristoci na kasa da kasa sukazo sun so tafiya da merry din da yarta kawu balarabe yayi tsaye ya hana hakan.
Kuma sai abin yaso ya koma wani rikici a lokacin don sunyi tsaye sai abasu su su wuce dasu kawu balarabe yai tsaye sai uban yarinya ya dawo ya yanke hukunci da kanshi.
Dole ba yarda zasuyi suka barta suka tafi don kawu balarabe fitananen mutum ne sosai kowa yasan shi da fitina.
A wanan lokacin ne na zama kamar nice yar uwan merry din ko da yaushe muna tare ina bata magana duk ta fita cikin hayacin ta saboda fargaban data shiga na yar nata.
Kwanan yaya biyu ya juyo ya dawo saboda halin da yarsata shiga na bata hankalin shi yayi kololuwan tashi a can duk da an fada mai anga yarinyar saidai bai yarda da hakan ba.
Dawowan shi yasa mutane suka fara tururuwan zuwa masa jajen abinda ya faru da yartasa daga ciki kuwa har samira da mahaifiyar ta dako leke basu leko yiwa kowa barka da arziki ba da farko.
Ance abin duniya baya boyuwa don dai basuyi sa, an zuwa gidan ba saboda sun samu Amma da mama hadiye da tun faruwan abin suna gidan basu koma gida ba don tare muke dasu a gidan.
Gaisuwa suka fara sai jajen batar yar da suka fara mai a lokacin mama hadiye tace wai mamaki hajiya sabuwa wai me yasa kuke daukan mutane wasu iri kamar kunfi kowa dabarane ?
Kallon mama kowa dake falon yayi har da bakin dake nan a lokacin hjy sabuwa daba kyale ba tace akan me zaki fada muna haka hadiye ?
Dole in fada maki do naga kuna son mayar da kowa wawa a gidan nan saboda kunyi na farko ga hjy kunji dadi.
Ina nan ake kururuwan batar yar nan a gidan nan har wanda bamu sani ba ya shigo gidan nan taya mu bakin cikin abinda ya faru damu.
Amma yarki tana gidan nan bata leko kowa ba a gidan nan karshe ma sai kidan farin ciki data saka muna a gida sai yaya balarabe ne ya shiga ya tsawata mata.
Hakan baisa ta tako zuwa wurin uwar yar nan ta nuna bakin cikin ta ba gare ta ai na dauka ko akuyan muce ta bata yanzu tunda samira tana karshin inuwar shi tare da ita za ai zaman bakin cikin nan.
Yanzu kuzo don ganin ido saboda kunga umar ya dawo wai kunzo taya mutane bakin cikin abinda ya faru ko kunya babu don kun mayar damu bamu san abinda mukeyi ba ko mai ?
Hadiye akwaiki da wani magana yarshi ce ta tabata don haka shi muka zo yiwa tanzanko ba wani ba .
Wurin wa kike son muzone da wurin kishiya ko wa zamu zo din bamu gaji dukawa kishiya ba kema kin sani balle yar cikina ta tabi kishiya don son suna.
A take falon ya dauki hayaniya a wurin inda yan uwan hjyn su yaya suka karbe zancen ya zama nasu sai hayaniya ya tashi a falon .
Mikewa yaya yayi dauke da Abbana dake jikin shi yana rike da hannun Queen da sauran yaran dake biye dashi bayan shi suka fice daga falon.
Hayaniyar da yai yawa a falon yasa merry ta juyo inda nake zaune a kusa da ita tana tambayana meke faruwa ne wai na fara mata bayani abinda kowa ya fada a gurin.
Tace thank you mama da cewa wa mama hadiye da tai magana sun dauka kowa baida hankali da wayau sai su, .
Sun dauka zasu iya dumping din kowa a yadda suke son yi kome wanan matar ita da yar is devils they are very weaked in action.
Ba a daiyi ta da dadi ba a ranan don rayuka sun baci sosai a gurin samira tana taya uwar ta fadawa yan uwan hjy dake falon magana mai zafi.
Ga merry ta matsa min da tambayan me ake fada dole na koma hankalina ya kasu gida biyu a lokacin.
Sai bayan sun fitane sun koma part din su hjy sabuwa kecewa samira bance ki dagawa duk dan iskan dayaso ya kawo maki gani gani a gidan nan ba kaf.
Don basu da yadda zasuyi dake sai gani sai hange gida daine baki barin sa koshi dan iskan mai akidan turawa zai dawo haya bada dadewa ba zamu kamashi a hannu dumu dumu ya gama duk kwanaye kwanaye shi muna nan zai sake ki zakice na fada maki wanan maganan ai.
Amma umma baki ganin hakan da mukeyi duk da bai magana zai iya zama muna matsala tunda ba duka muka gama rufe bakin su ba jifa yanzu wanan gwaggon nasa data kawo wanan maganan a gaban sa.
Kyale yar iska idan na koma gidan boka zan bada sunan ta tunda tana ganin ita takai a yanzu.
Gaba dayan su sai nagama dasu kaf wallahi dani suke wasa basu san sabuwa ba jina sukeyi kawai.
Umma ni abinda yafi damuna a yanzu shine wanan matar tashi Fatima don ko ita kafiran kamar wanan fatiman ta shige mata a gaba a gurin shi.
Nima nayi wanan tunanen a yadda na ganta ta kara zama wata hamshakiya shegiya sai wani kyau da haske take karawa kamar itace mai dukiyan.
Yo yar banza dole ta haska tun yanzu ta cika mai gida da yan yayaye haka masu zubin turawa ko larabawa dasu can jifa ko hausa yaran nake ganin basaji.
Itama dole a satin nan mu kaita a sakarwa yar iska warin jaba kyauta da suran da take takama dashi duk ya tashi a banza yaji ya tsaneta ga baki daya.
Wanan maganan yaiwa samira din dadi sosai tace mama ko nawa ne indai har hakan zai faru da ita zan bada don a shirye nake inyi komai kan wanan yar iskan yarinyar .
Tunda tazo garin nan nake a cikin fargaba da tsoro daduk nayi arba ds ita wallahi sai naji gabana ya fadi uku uku ban san meke sa ina jin hakan ba a kanta da duk naga wanan yarinyar.
Wata rana kece zata koma tsoro ai uwarta ba sheri ta iya ba jummai ta samu sakarai ta kasa natsuwa ta juya yan banza yadda takeso sai kishin hauka da girman kai irin nata.