NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:22 – ????????????: Yaya umar tun fitan shi gidan su ya nufa tare da yaran shi da suke tare a lokacin , part din kawu suka nufa don yanzu sai suke jin gidan babu dadi gare su idan sun shigo.
Tun bayan barin hjyn su gidan na yan wani watannin dasuka shude gaba dayan su, gidan babu dadin zuwa gare su hakan kesa da sun shigo sai su nufi part din Amma sai wani lokaci sukan dan leka su mamu a part dinsu su gaisa.
Tunda ya shigo ya zauna suka gaisa da kawu bai kara magana ba yana zaune yaran nata dan surutu a tsakanin su sai can kawu ya dago kai ya kalle shi tare da fadin lafiya kake na ganka haka yau.
Dan murmushin yake ya sakarwa kawu tare da fadin babu komai daddy yana kara lumshe idanuwan shi a hankali.
Ko har yanzu zancen bacewar yarinyar ne ka saka a ranka ko kana zaton wasune suka dauketa da niyyah yin hakan.
No ba abinda nake wa tunane ke nan ba Amma wanan fitinar dai da mama ta dauko min a gidanane ya fara damuna .
Fitinan me ke nan saudaki kake nufi ta jawo maka a gida kuma bayan wanan zancen batar yar taka ?
Ya gyara zama tare da hade hannayen shi ya dan furzo da iska daga bakin shi yana fadin wanan yarinyar da ke zama a gidana .
Yanzun haka na barsu ita da uwarta a gidan suna masifa dasu gwago hadiye tana kokatin tara min mutane a gida.
Dan murmushi manya kawu yayiwa dan nasa yana fadin umar ke nan ai dama duk wanda ya sai lariya yasan zatai yoyo .
Ka taba ganin inda irin wanan hadin na mata zallah yai albarka abin son raine fa aka hada ba don Allah akayi shi ba.
Amma yanzu duk me ya kawo wanan zancen har suke wanan fitinan suna kokarin tayar maka da hankali kaida gidan ka.
Nan dai ya koro mashi abinda ya faru har fitina ya kaure a tsakanin su kawu yace ban san har sai yaushe wa yan nan mutanen zasu gane talala na sakar masu a gidan ka.
Wanan iya shegen shi jummai take son in barta tanayi a gidan nan sun dauka hakan wani wayewa ne ko burgewa a idon jama, a.
Basu san hakan zubarwa mutum kima da ajinshi yake ga duk wanda yaga suna aikata irin wanan rayuwan .
Ina dadi wai ace mahaifiya taje gidan yarta tana wanan sayar da halin haka kamar ba wa yanda suka samu irin tarbiyan mu ba a nan.
Na dauka hakan daya faru a tsakanin su da ita jimmai zai sa nadama da natsuwa yazo masu a rayuwan su sai dai ashe su a wurin su ba haka abin yake ba.
Daddy wa yan nan mutanen babu nadama a tare dasu abinda sukaiwa hjy sam su ko a jikin su ma don ko gaida ita sai wanan taga dama take shigowa ta dubata .
Gaba daya iyalina babu wanda ta sanda yazo a gidan balle harta kalle su da idon mutunci sai fadan nan nasu dasu mama na gane komai da takeyi da sanin mahaifiyarta take yin sa.
Don kalaman ds mahaifiyar ta jefawa su mama cikin zancen nasu ya nuna itace ke dora yarinyar a hanya ma.
Gashi gurin raba su fada da marry har hjy ta fado ta fama ciwon jikin ta tun ranan bamu gane kanta ba na kira likita mu mayar da ita asibitin yace ko mun koma da ita can babu abinda zasu iya mata a yanzu.
Allah ya taimaka zuwan Zahran nan kasan tun ranan da ta sauka ta rubuta magani da allura tare da bata taimakon daya dace muka fara ganin sauki sosai a gare ta.
Kawu dake kasa zaune yana wasa da Abbana daya rarafa zuwa wirin shi da sauri ya dago kai yana fadin madallah.
Al,amarin Allah ke nan yau yarinyar nan fatima ce maiba jimmai taimako har ta yarda ta karba daga gareta din.
Yarinyar da jimmai ta tsana har bata iya boye hakan a gaban kowa lalai lamarin ubangiji baida kadan.
Ko yanzu bukatana ya biya don ubangiji ya wankeni ga abinda nake son jimmai ta gane akan rayuwa.
Shi da na kowane balle mutum baka san a inda Allah zai turo ya taimake ka ba kaga yanzu sam babu wanda ya taba kawo hakan mu saman ma ita jimmai din data dauki duniya da girma takw ganin kaskancin yarinyar akoda yaushe.
Gashi yau wa yanda take ganin su din ne wata tsiya a wurin ta sun kasa taimaka mata dako sannu balle kallon arziki.
Dama irin haka yakan kasance sai Allah ya jarabe ka ta yarda zai nunawa mutane irin hikiman shi a ko yaushe.
Sai yanzu umar da yai shiru yana sauraren zancen mahaifin nasa ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin .
Ni kaina daddy ranan na dade ina irin wanan tunanen wanda ita kanta hjy naga alaman nadama a fuskanta lokacin da zahra ke rungume da ita tana bata abincin.
Murmushi sosai kawu yayi a fuskan shi yana fadi kuma a fili Allah yasa hakan ne a zuciyar ta .
Yanzu ina son ka kara kwantar da hankalin ka kan zancen batar yarinyar nan kada ka zargi kowa a kan hakan don a bakin yarinyar cikin hikima zakaji komai da ya faru da ita ba sai an saka zargin kowa ba.
Sai zancen wa yan nan mutanen naga abin nasu ba zancen nadama a cikin shi don haka duk hukuncin da kaga ta dace zaka iya dauka a kansu sai dai ina mai kara baka shara ka kara hakuri har gaskiya ya gama baiyana kanshi kowa ya fahinci manufan mu kan hakan.
Insha Allahu ya furta a sanyayaye ba tare da ya dago kanshi ya kalli mahaifin nasa ba in a son ranshine yaso wanan karon ayita ta kare a tsakanin shi da wa yan nan mutanen.
Saidai a yanzu dole yabi ra, ayin mahaifen nasa kan hakan daya bukata a wurin shi yanzu.
Bai fita gidan ba bayan yabar wurin kawu din saida ya biya da yaran part din su mamu suka gaisa ya dan jima a wurin mamu suka dan taba hiran batan Queen da tayi.
Ya dawo gida babu kowa a falo ga yaran dake a takure don sun ki cin abincin da kawu yasa a kawo masu da suka zo wurin shi .
Na idar da sallah azahar ke nan na dan kwanta in huta don merry bata barni kwanakin nan na samu natsuwa ba da tabaran ta irin na kafirai idan masifa ys yasame su.
Yaron ya shigo ya shimfide a kusa dani yana fadin gashi yayi barci kuma akwai yunwa a cikin sa.
Yanzu jan sai ya falka kuma ai tunda naga barcin nasa yayi nisa sosai abawa sauran suci kada suma suyi barci a hakan.
Yana kai kofa ya juyo yana fadin merry dazun take fada min irin kokarin da kikai mata lokacin da wanan abin ya faru da Queen.
Kai haba ai dole mu rausaya mata son bata san kowa ba a nan bayan mu idan duk muka juya mata baya da wanne zataji a ranta.
Dan murmushi kamar yadda yake ga al,adan shi ya sake yana murda kofan dakin y fita nema sauke ajiyanzuciya nayi na sauko ina gyarawa yaron kwancia kafin in fito daga dalin .

Kula sosai nake ba hjy kuma alhamdullahi tana samun a banci a kai dakai sai hakan ya kara taimala mata wurin jin sauki .
Bayan kwana biyu ne merry ta kara zancen tafiyan ta sai dai yaya ya nuna mata bai yarda ta koma mai da yar shi ba wanan shine kuma sabuwar fitinan daya kara kunnu kai a gidan namu kuma.
Ashe tun wancan ranan da mukaji suna fitina akan hakan ne har yakai yar taji uban na fadin ba za, a tafi da ita ba ta bar mashi yarsa a nan.
Shine dalilin da har Queen din taga zasu bar kasan nan tare da mahaifiyar ta ta gudu ta boye a ban daki akai ta neman ta taki fitowa.
Sai gashi kuma a yanzu din kuma wanan irin rikicin ya kara aukuwa a tsakanin su haka yasa ya dauke Queen bada sanin kowa ba ya turata Abuja gidan habbib dan uwan shi.
Merry na falkawane bata ga yarta ba ta tayar damu da kururuwa da tashin hankali dole kowa na gidan ya fito don jin abinda ke faruwa.
Banda ya umar da bai leko falon ba inda merry ke birgima da ihu dauke mata ya da akayi wanda tasan aikin umar din ne hakan.
Nice dai na koma mai kaunar nata a yanzu don haka na shiga dakin yaya din don ganin halin da yake ciki bai fito ba.
Samun shi nayi yana shiryawa hankalin shi kwance yana kuma waya a lokacin.
Jin motsin shigowan mutum ya tsaya yana kallona bai kuma daina wayan nasa ba a lokacin.
Maganan da yayi ne yasa na fahinci yasan inda yarinyar take a lokacin wayan ya kashe ya juyo yana tambayana lafiya ?
Queen ce kuma wai ba, a gani ba yanzu ihun uwarta ya tayar damu daga barci nake fada mashi.
Tana gurin na kawai ya fada a takaice tsayawa nayi ina kallon shi da mamaki ganin babu fuska kan hakan na juya na fita daga dakin zuwa falo.
Nan na samu merry tana kira a waya haka ya bani daman nufar dakin hjy don in duba su da kwana.
A zaune na sake su dakin suna magana duk yanayin su baya a cikin dadi a lokacin kara sallama nayi na shiga dakin .
Mun gaisa nake mata ya karfin jikin nata ta amsa min a kasalance da sauki bari na dan dawo yanzu sai sha magani.
Wanan karon Asabe ce tayi magana tana fadin mun tashi da zancen shan maganin sai ga kururuwan wanan matar ya tayar muna da hankali.
Dan murmushi nayi ina fadin mama kin san tsakanin da da mahaifi dolene hankalin uwar ya tashi haka .
Wanan dalilin yasa bata son zuwa da yar kasan nan don kada ta san kowa daga bangaren mahaifinta take nisanta ta da kowa nasa.
Ashe kuma bata tsira da hakan ba don yar ta nace sai a kasan nan zata zauna yanzu tare da yan uwanta.
Ni wanan abinda mai ya kama fitinan matar nan tunda tazo ya isheni a gidan nan babu kwanciyan hankali sam ga zuwan nata.
Sai yanzu nake hango gaskiyan Alh daya nace kan sai umar yayi aure a gida a lokacin har ina ganin laifin shi kan hakan hjy ta fada a cikin takaicin abinda ke faruwa din
Kafira kafira wa yan nan mutane ai basu da dadi wallahi kansu kawai suka sani kan komai halin su yan akidan su don haka muka zauna dasu a kaduna.
Fita nayi daga dakin a daidai lokacin da merry ta rike yaya kan ya bata yarta don ashe tun cikin dare ya fada mata muddin tace sai ta tafi da yarinyar shiko zai dauke yarshi a wurin ta.
Ni dai hankalinane ya tashi kan fitinan danaga suna yi din gata, tana ta barazanan kai karan shi ga hukuma yana fadin sai ta dawo.
Kawu na kira nake sheda mai abinda ke faruwa a gidan yace zaiyi magana da yay din da ita merry.
Karan da naji tayi ya kara firgitani na fito da sauri ina ganin yadda yaya ya hankadeta yana fita daga gidan.
Nikan wanan abin ya isheni nayi dana sanin zuwa kasan na samu merry din a nan do hutun namu sam baiyi dadi ba ga laluran hjyn su ga fitinan matan yaya din ko yaushe sai na kwanmace ace ina can abina yafi mun wanan zuwan haka a gidan sarka.
Zuwa nayi wurin merry din ina bata hakkuru wani tsawa ta daka min tana dadin in barta duk abinda akai mata nima da sanina ai.
Mamakine ya kamani jin furcin merry din a gabana ban iya furta komai ba na juya na koma dakina na barta a wurin.
Tun wanan lokacin ban kara shiga tsabganta ba duk da ina jin yadda suke kwasa cikin kwana biyun nan.
Rikici sosai sukeyi don har kotu suke da merry din dukda tana gidan nasa zaune ga samira idan zamu hadu kiyayyanane karara a fuskan ta babu sassauci a gareta.
A karshe kotu tace zata ba yar tasu dama ta fadi inda take son zama a tsakanin su.
Wanan case din nasu ya kara kawo cecekuce ga mutane suke ganin illan auren matan da ba addinin su ba don gujewan irin wanan fitinan.
Karshe dai Queen ta zabi zama nan wurin mahaifin ta hakan yasa yan uwan merry shigowa har kasan nan kan case din nasu.
Sosai sukai rikici dashi kan ya basu yarsu ganin fitinan yaki karewane yasa suka dauki yar su suka tafi suka bar Queen tare da mahaifinta.
Ganun hjy ra samu sauki soai don har sun koma wurin likita ya dubata ya yaba da nasaran da aka samu sosai.
Ya kara diban masu lokacin da zasu dawo a kara dubata again maganin da zasu saya ya tsaya ya sawo a hanya suka nufo hanyan gida.
Saida ya shigo da mahaifiyar har dakin ta inda ya samu mun gyara dakin nida maria sai kamshi ke tashi a dakin.
Abinci maria ta shigo masu dashi bayan sun dan huta tana ajewa na shigo dakin dauke da abinsha ina gaidasu da dawowa.
Wanda yanzu idan na gaida hjyn tana karba min sai dai babu sakewa a tare damu dagani har ita ko wani lokacin don ba sabawa da hakan a tsakanin mu .
Nikan na gama na fito daga wurin su na koma dining muka zauna cin abinci da yarana har maria da yanzu na mayar da ita yar gida sosai tare damu don irin kokarin maria din da kula ga rikon amana.
Ban farga da shigowan Samira din falon ba don ranan bata saka takalmanta mai yawan sauti ba ta shigo.
Sai jin muryan ta mukayi a kanmu tana huci take fadin ke yar aiki da cewa maria .
Duk juyowa mukayi muna kallon ta ta nunani ta sake fadin nace kada ki kara shanya min kayan yaran ku a wurin dakina baki ji ba ko.
Wanan ne karo na farko da wani magana ya taba hadani da ita tun zuwa mu kasan da muka same ta a gidan.
Nace amma ke baki da wayau ko hankali ko yanzu akan shanyi kawai zaki shigo muna nan da kashedin bar maki shanyin tufafi a kusa da part din ki.
Ko part din kine ta tambaya a gwatsale a cikin izgili a, a gidan ubankine nan din aikun sani.
Gaba dayan mu muka juya don jin muryan Nafisa data shigo gidan bada sanin kowan mu ba duba jikin mahaifiyarta da aka kai asibiti.
Ke kuma asuwa a cikin wanan maganan ko yanzu kuma kin fara kamun kafa da itane an gama zagin ta koda yake banyi mamakin yin hakan daga gareki ba don har manyarki ma haka suke nunawa bayan an gama bata ta da farko.
Duk wanda zai batani wata kila nayi masa ba daidai bane har ya fusata dani kada kuma ki manta Nafisa yar uwan hauhuwa nane na jini.
Ba abin mamaki bane don ta shiga magana na a yanzu kinsan ba, a raba anta da jini ai nake fadi a cikin zafin rai.
Ta juyo tana kallona kafin tace wai mamaki ke yanzu kina ganin kin samu wuri da har kike ganin kina iya taka kowa tau ki sani kijawa yar aikin nan naki kunne kada in karas ganin kayan yaran nan a gefen part dina don ba za,a tare min iskaba don isa da mallaka da ake takama dashi.
Isa da mallaka kan ai dole tayi shi a gidan nan tunda gida gidan mijinntane gidan diyan ta kuma nafisa ta fada.
Wani mahaukacin dariyan yan iska ta kwashe dashi tana fadin ke yanzu bakiji kunya fadin wa yan nan maganganun ba haka Nafisa ?
May ye baku fada ba akan wanan da farko daga ke har kowa naki sai yanzu ne kuma take mutum a wurin ki.
Ikon Allah ke yanzu wanan haukan ne ya turoki nan ina dai ni ban ma san da zamaki gidan nan ba don dake da babu duk dayane a gare ni don haka dani da yarana mu fita a idon ki.
Gida dai na uban su ne don haka ke kinyi kadan kice mun ga abinda za,ayi a gidan nan sai dai bari maigidan ya dawo muji idan ya raba gidan yaba kowa nasa kason ne ban sani ba.
Muryan hjyce ke dan tashi tana kiran Nafisa daga dakin da take a cikin damuwa a daidai wanan lokacin ne samira din taja wani tsuku mai karfi tana fadin aikin banza yiwa kare wanka duk a tafin hannuna kuke gaba dayan ku gidan nan.
Ta juya ta fita nan ta barmu da mamakin ta ina girgiza kai dalili daya zuwa biyu ya hana na bata amsa daidai da abinda tazo dashi.
Kudun hjy ta sake shiga wani hali kamar wancen na baya sai kuma yaran dake wurin tun shigowan ta sun kura mata ido a tsorace don basu saba ganin hakan ba isan ba a kasan nan ba yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button