SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ta shirya tsab ta dauki yaran zuwa part din Amma don ba bazata tafi da yaro ko daya ba tunda ranan zasu dawo garin.
Bayan ta rufo kofan ta ne ta juya tare da yaran suka nufi can a daidai lokacin da maigidan su ya fito daga part din shi ya nufi part din hjy jummai don su gaisa.
Hjy maryam da ta fito gaida Amma ce suka hade tun daga nisa take kare mata kallo irin shigar da tayi alama ya nuna mata fita zatayi a lokacin.
Dan murmushi ta sake mata don samun fuska taji inda zata tafi suna hadewa hjy maimuna tace ina kwana anty maryam.
Lafiya kalau maman biyu yau sai ina haka kuma ta dan sake murmushi itama tare da fadin zamu shiga wurin gwago ne ta saka ta a kwana itama tace to a fito lafiya.
Alh na shiga part din jummai dake hake dashi kan kudin da yarta ta fada mata jiya taga yana ba hjy maimuna a kofan Amma.
Bayan sun gaisa sama sama da sune yake fadin zanyi tafiya yau tare da maimuna zamu tafi bauchi gurin yarta.
Kamar bata ji shi ba tace dama ina son ka shigo ka bada kudin yaran nan su samu su tafi duba takardun su.
Kallon mamaki yai mata tare da fadin shi duban takardun har sai da kudi akeyin shi yanzu kuma in kuma na trasport kike magana ina dai diver ne zai kaisu.
Amma kaima kasan dole sai sun rika wani abu dai ko don ba za a sake su haka su kama hanya ba wani abu a hannun su ba ?
Yace to ki basu yau dai kan ban yi niya ba ni tace eh ai ba abin mamaki bane don ka hana su kudi yanzu amma kana iya ba wa yanda ka mayar mutane a gidan dul sanda suka bukata su.
Wani kallon mamaki yayi mata tare da girgiza kan shi ya juya zai fita ta kara fadin duk dai abinda mutum keyi Allah na ganin sa ai.
Idan na cuce ki sai ki barni da Allah yana fadin haka ya sa kai ya fita ranshi bace da al,amarin ta yanzu ko wurin hjy maryam da ya shiga itama basu kwashe da dadi ba da ita.
Don duk wace yacewa da hjy maimuna zasuyi tafiya wurin yar ta sai ran maishi ya baci itama hjy maryam din korafin tayi mai wai kiri kiri ita ya hanata karbo maganin ta da takeyi amma gashi zai tafi da maimuna da kanshi wurin yar ta ai.
Cewa yayi mata da bake zuwa dake da farko amsan magani sani akayi ko wani ya gune maki a gidan nan koda maimuna muke zuwa na hana din in kin isa sai ki tafi mu gani.
Ita ko hjy maimuna bata fito ba sai da ta bisu daya bayan daya tayi masu sallama duk da ba wani Allah ya tsare janya mai kyau data samu a wurin illa sai kun dawo.
A haka suka kama hanya sai bauchin yakubu sammakon da sukayi ga kuma lafiyar yayyar mota suka isa da wuri.
Ta san gidan don haka ne basu wani sha wahala ba gurin neman gida sun iso da karfe daya saura garin misau din lokacin na gama kukan wahala ina barci jikina duk yayi min tsami sosai ga zazzabi na son kamani Allah ya taimaka baffa ya aiko min da magani in sha.
Mutanen gidan suna zaune suja dinga jin sallama daga kofa sai wani yarone ya fito daga falon su inda suke yawan zama babu komai a cikin falon sai kwamatsen su da kayan dauda da suke tarawa a ciki don dakuna sun masu kanana yan matan kuma a falon suma suke kwana amma hakan baisa sun gyarashi ba.
Yana amsa sallaman ya juta don fadawa iyayyen don bai san ta ba sai umma saude ta leko da farko bata gane ta ba sai da tace yaya baki gane ni bane maimuna ce fa daga kano.
Tace Lah maimuna kece hakan ban sheda ki ba sa;un ku da zuwa yanzun kuke tafe ne sai ta hau kamay kamy da sabarin baki.
Saude ke da wacece a gurin wai umma safiya ke tambaya tace wallahi yaya kinga maimuna ce uwar fatima a garin namu yau.
Wace fatiman kuma tana fitowa take tambaya ganin maimuna a tsaye cikin shiga ta alfarma babu inda zaka ganta ka kushe mata ta waye ta zama babban mace sosai kamanin ta na asali ya kara fitowa fili.
Turus tayi tana fadin maimunan Abubakar ce haka ta zama wata yar gayu da ita ikon Allah lalai duniya mai canza kama.
Iso sukai mata da ta shigo falon nasu mai kama da dakin mahaukaciya don ko tsohuwa ba zata bar guri ta haka ba.
Bayan sun gaisa da ita ne suna dan kamay kamay take fadin babba fa ko sun koma azare ne ?
Babba na nan suna shiyan su bara a kai ki saude tace tana mikewa bata zaci a gidan part din yake ba sai da taga an nufi dan dakin da take zaton ko akulkine da ita a ranta tace ikon Allah tare da rashin jin dadi cikin zuciyar ta.
Daga kofa suke sallama sau uki suna yi can manjo ta karba masu sallaman tare da fadin iso daga ciki suka daga labulen tsohon zanin manjo da muka sa a kofan suka shiga.
Babba maimuna ce a garin namu yau ta zo tace wace maimuna fake nan tana tambaya hjyn ta kutso kai cikin dakin.
Suna arba da manjo sai tsohuwar ta sa kuka dan gurin ta samu daga gefen da nake kwance ta kai zaune itama tana share nata hawayen .
Maimuna ashe kina tafe manjo tace bayan gama kukan ta datayi tana kara dan gyara mata wurin da take zaune sai saude ne tace wanan barci take ne ?
Yomar ai dole tayi barcin wahala tasha duka haka da sauri saude dake jin tsohuwar na shirin masu tonon sila ta juya tare da fadin bara na kawo maki ruwa dai .
Hjy ta kalli tsohuwar tace tare da maigida na muke yana waje ko za, a kai mai abin zama a wajen .
Sauden tace barin tura yaro yanzun ya kira shi a shago don kada a barshi shi kadai a waje nan ta bar hjy da manjo.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:39 – ????????????: ALHAMDULLAHI ALAH QULLI HALIM MUNA KARA GODIYA DA TAWASSALI GA ALLAH MAI KOMAI MAI KOWA FATAN CIKAWA DA IMANI GA DUKKAN MUSULUMI AMIN, , , , , , , , ,
Kallon inda nake tayi tana fadin wanan barci ne haka idon ta a kaina tana mamakin irin girman da nayi a cikin dan lokacin da ta dauka bata ganni ba.
Idanuwan ta still a kaina tana tausaya ma itin rayuwan da muke ciki a can kasan zuciyar ta tunanen mijin ta marigayi ya fado mata a rai irin daulan da ya dauko basu dasu da mahaifiyar shi da yan uwan shi saida kash Allah yayi ikon shi akan sa.
Da yana raye da yanzun yana cikin masu fada aji a wanan nahiyar don kwazon shi ga aiki gashi mutum ne shi mai kokarin yiwa zumunci hidama.
Manjo dake gefen ta zaune tana share kwalla itama irin abinda take rayawa a ranta ke nan a lokacin daidai ganuwan su na jin dadi rayuwa Allah ya yanke masu shi ta hanyan dauke wanda suke sa ran hakan a gare shi.
Murya a raunane tace yar nan kin gan mu nan yadda Allah yake nasa ikon a duk lokacin da yaso yau nice haka Allah ya dawo damu nan.
Ta kara share hawaye hjy maimuna da itama hawayen takeyi tace Allah shiya san dalilin dauke muna dear a cikin mu babba a daidai lokacin da duk kan mu muke buakatan shi gare mu.
Manjo tace ki duba wai yau safiya ce mai goranta wa yar nan mahaifin ta bai tsinanawa kowa komai ba a rayuwan shi kiji mi butulun mata har ta manta da lokacin da mijin ta ke dirka mata cikin yayan nan ya dauki nauyin komai a kansa duk wanan agare ta ashe ba taimako bane.
Yar wanan marainiyar Allah daya bari ya daya tillo a duniya itace kuma don rashin tausayi suka saka a gaba cikin gidan nan bayan sun gama kwashe ganiman komai da mahaifinta ya bar mata yanzu sun dawo suna goranta mata da duka.
Wani miyau mai daci hjy maimuna ta hade a makoshin ta tare da fadin babba ai wanan ba komai bane dukan dai shine mai munin ciki.
Manjo tace kwarai kuwa yar nan ina wanan yar ina kattin diyan su kowa ya tashi dan magana kadan ya kai mata hannu.
Yar ina cikin bakin ciki yau irin dukan da dan banzan dan nan yaiwa yarinyar nan a gidan nan kan wanke wanke kawai alhali baci ko loman abincin ba sun hana muna.
Wani irin sosai hjy maimuna taji a cikin ranta ta tuna lokacin da mijin ta ke raye takanas zai sawo zabbi ko kaji ko naman rago yace aiwa babba girki aikai mata don ta na sayo shi don taci taji dadi yau itace kuma sarakai ke wa rowan abinci.
Naji dadin zuwan nan naki ko yar nan ta zama abinda ubanta bai kai ga cinmawa a rayuwa ba da farko da Asiya tazon min da maganan naso naki ne amma da ta lurar dani alfanun hakan sai na yarda don zaman A ruwa anan ba zai amfane mu da komai ba nan gaba sai dinbin dana sani idan na hana ta tafiya dake a yanzu.
Nasan zan shiga wani hali kamar yadda yarinyar zata shiga sai dai na dan lokacine ni nawa mai saukine dama may yarage min a rayuwa.
Hjy maimuna tace babba kada kice hakan ai mairai baya debe tsamani ga rayuwa kin sani ko sai kinga jikokin yar a duniya.
Sai lokacin manjo ta dan sake murmushin takaici a fuskan ta tana fadin kaiyya abin da kamar wuya yar nan.
Ji magana sama sama a dakin yasa na motsa sai kuma idona yai min nauyi budawa a lokacin don yanayi jikin nawa sai dai kuma maganganu nasu ya hanani komawa barci na.
Gani ina motsi alama ba barci nakeyi ba manjo tace ki tace A ruwa ga mahaifiyar ki tazo gare mu yau.
Zubur na mike daga kwancen da nake ban gara ko second guda ba ina wiki wiki da idanuwana a kan hjy dake zaune a gefe na wace kamshin turaren ta ya cika mi hanci tun ina kwance.
Bazaki min sannu da zuwa ba tace a dan hasale kin wani zuba mi manyan idanuwan kin ga sai dana turo baki gaba nace to sannu da zuwa ya gida ?
Kai ta girgiza tare da hango tarin matsaloli da take hangonwa yarinyar tu ba a kai ko ina ba a rayuwa ta ga rashin tarbiya ta fara hango mata tun yanzu
Kokarin mikewa nakeyi a lokacin don in fita daga dakin a lokacin ba ko ina nake so zuwa sai gida su Atika don in shakawa mahaifiyar su zancen zuwa hjy gidan .
Ina kuma zaki manjo ta fada tana kallona lokacin dana kai kofa na daga labule nace bako ina zan dan kewaya ne kawai.
Sai dai ina fita ban tsaya ko ina ba na nufi hanyar waje ina mai sauri har ina hada kafa wurin sauri a lokacin.
Turus naja na tsaya do ganin dirkekiyar motar dake fake a kofan gidan mu na gane Alh sani amma sai nayi kamar ban sheda shi ba saboda miskilanci.
Zan dan gwauta shi i wuce yana tsaye yana waya a waje motar driver na cikin mota zaune naji yace wa nake gani kamar fatima a nan ?
Kamar ban ji shi ina tafiya na nufi hanyar zuwa gidan su Atika kai tsaye ya sake fadin ke A ruwa baki ga baffan ki bane ?
Daga inda nake na tsaya cak don jin suna na daya kira kai tsaye tare da in kiyar sunan gaba daya don shi wani lokaci yana kirana da sayadi.
A hankali nake takawa zuwa inda yake har na iso na kai kasa ina gaida shi baiyi fushi ba ka abinda nai masa din sai ma fara,an ganina da yake sakewa a fuskan shi a lokacin.
Baffa ina wuni nace ina tsungune a gaban shi ya kura min ido sai kallon shartin dukan dake fuskana gefen idanuna daya kumbura sosai da gefen baki na dukan da yaya hashimu yayi min yau da safe.
Ba tare da ya amsa min gaisuwn ba have Sayadi may nake gani haka kamar duka a fuskan ki sai kuma ya kasa magana sai furta innalillahi ashe maimuna tana da gaskiya da taki kwantar da hankalin ta a kan ki yan kwanakin nan.
Muryanane ina fadin baffa kunzo lafiya ya hanya dasu Amma sai daya nisa yace Alhamdullahi suna lafiya.
Ina zuwa haka har lokacin yanayin fuskanshi na tausayine a kaina yana dan girgiza kai cikin mamaki.
Wancan gidan zan shiga na bashi amsa a takaice ina kokarin dagowa daga duken da nake din.
Baice dani komai ba na wuce shi da zumudi na shiga gida su Atika din a waje na samay su har yayun ta da mahajfiyar su ina kokarin gaida mahaifiyar tasu ce yaya yusuf yace dani.
Ke fatima wasu bakine suka zo gidan ku da tsadaden mota haka ashe malam salle nada yan uwa masu kudi hakan nan.
A sanyaye kai duke na ce dasu mahaifiya ta ce da mijin ta suka zo umma shine nazo in fada maki hjy tazo yau.
Umma na fadi kai yasuf wanan wani iri tambayan kwakwaf ne haka basu da yan uwa masu kudi sai ku.
Sai taji ina fadin mahaifiyatace da maigidan ta ai sai ta zaro ido tace Allah fatima yau mahaifiyar ki ce a garin nan nace wallahi amma Atika tace shine kika fito kika barsu ?
Nace nazo fada ma ummane kuma ni fa kunyar tama nake ji sosai wallahi shiyasa na fito na zo nan na barsu da manjo a daki.
Amma anyi yar kawai wurin nan kunyar mahaifiyar take hala sarakuwa ki ce ita da shirmay nan naki na banza kullun.
Ina kokarin zama ne tace tashi zakiyi ki koma yanzu kuwa mata tazo ta gane ki sai ki wani gudo ki barta a can zaune yanzu bata fi bukatan ganin ki akan kowa a gidan ba.
Anty murjane ta gidan mu da kanta ta fado gidan tana fadin kin wani zo nan kin zauna ana can ana neman ki a gida.
To ki taso baffa na kiran ki yanzun nan umma dake rike da hijjab a hannu tace yanzun nan ai zan tasata gaba mu shiga tazo min albishir din zuwa mahaifiyar tace.
A can cikin gida kuwa da suka farga da fita nayi hjy dai batace komai ba sai fitowa da tayi don ganin halin da mijin ta yake a waje.
Alh sani yace yanzun nan na ga sayadi ashe ta girma ne sosai hakan sai dai kuma na fara fahintar dalilin ki na so ta dawo gare ki da zama tun yanzu.
Don yanayin da nagani a tare da ita gaskiya banji dadi gani hakan ba don alama ya nuna sayadi na zama hakkuri ne a wanan gidan .
Maimako tayi magana a lokacin sai cewa tayi kin ko iya shan ruwan da aka kawo muku din?
Yace bar zancen ruwan nan don Allah muyi abinda ya kawo mu nan daidai lokacin Baffa ya iso daga kiran gagawan da saude ta aika mai cewa yana da baki a gida.
Shima bai sheda su ba sai da Alh yayi mai bayanin bayan sun gaisa yake fadin maimuna ce tazo daga kano lokacin yace a a a maimuna hjy kune tafe ?
Sannun ku da zuwa yaya hanyar duk ya rude ya rasa ina zai saka su a wani gindin bishiya mai yawan innuwa baffa yasa akai masu shimfida suka zauna .
Sai sabon gaisuwa ya biyu baya lokacin Alh sani ya saka driver ya fitar da tsaraban akaiwa hjy maimuna a cikin gida turamay zannu da bandarin shaddo dana yadi sai kayan masarufi dai sauran abubuwa iri tsaraba ne shake a bayan jef din nasu.
Akai ta shiga dasu gida ana labtawa a kofan manjo don nan hjy maimuna din take zaune tare da manjo suna hiran yaushe rabo.
Mutan gidan Baffa sai leken kayan suke suna gulma abubuwan da suka ga ana shigowa dasu gidan wai duk tsaraba ne.
Daga can ciki umma safiya ta tabe baki tana fadin dama ashe duniya ta samu haka tayi watsi da yar gun wana tsohuwar.
Kai umma kin taba gani uwar da taki yar ta a duniya ko yaya yar take balle fatima ai babu uwar da ba zataki taja ta ajiki ba daurowa ne haka kawai inji yaya sadi dake zaune.
Yana gugan wandon da zai saka a jikin shi rana wani kallo ta watsa mai tare da fadin kai fa naga kwanan nan ko maganan Fatima ake sai kai wani tattare mata may kake nufin da hakan.
Sai murja dake zaune a gefe tace kila yar gida yaks son ayi dashi baki ga kwanan nan yana wani gayu ba.
Yace ashe kin gane yar gari gaskiya kinci dari a wurina yau tunda kikai saurin dago ni dariya suka saka a falon gaba dayan su banda mahaifiyar shi.
Maganan gaskiya ne don na samu sassauci a gurin shi sosai indai yana gida ba wanda ya isa ya harare ni ko maganan banza yanzu.
Sai dai ni ban gane manufan shi ba ko kadan don wayau na da kuma tunane basu kai can da zan gane wani soyayya ba ni.
Mun shigo da umman su Atika tana ta gaishe su amma suna hayaniya basu ji ba don haka muka wuto kai tsaye dakin manjo dukan mu ukku din Atika na Allah Allah taga mahaifiyata yau.
Mun shiga da sallama manjo tace dama nasan tana gidan ku ai tunda na nemay ta ban ganta ba gidan nan .
Umma ta amsa da tana can babba taje fada muna hjyn ta zo yau garin sukai ma hjy sannun da zuwa umma na fadin lallai kuwa ga kama nan na zahiri ba sai an tambayaba.
Hjy tayi saurin fadin a, a ke ko anty yar ba inda ta kwaso ai ita gidan su duk ta biyu banki ba dai kice ido da hanncin tane kawai nawa.
Sin gaisa cikin raha da jin dadin ganin juna inda manjo ke gabatar da umma akan wace ke min kokarin komai tun zuwan mu garin sanadiyar shakuwar da yarta danayi.
Hjy tayi mata godiya sosai tare da fadin sai dai fa yau zamuyi maku laifi anty don yar naki zata barku ke nan da mamaki umma tace.
Ai da ita zaku tafi ke nan in sha Allahu hjy tace sai manjo ta karbe da fadin ai gara su tafi yar nan gidan nan ba wurin zaman A ruwa bane.
Kina gani yau ba son Allah ya gyara ba da dan banzan dan nan hashimu ya illanta mun ita gara kawai ta dauki abinta Allah ya taya ta rikon amanan da akabar muna duniya tare.
Jin haka nace ni kan ba inda zan tafi in bar manjo nan dan na fara kananan maganganu ciki ciki Atika tana tsunkula wai in daina tare da rada min wai zanji dadi a can fa fiye da nan.
A cikin bude murya nace ba wani dadi ninafi jin dadi a wurin manjo na gaskiya ba inda zan tafi umma tace to ai tunda baki zuwa ai shike nan ba mai maki dole kinji yata.
Shigowan su baffa dakin ne yasa muka fito gidan su umma muka koma tace kin ga Fatima maza debi ruwa ki watsa ma jikin ke baki ganin iyayyen ki a garin kika zauna haka.
Ina fitowa wanka ta bani sabon kaya daga cikin kayan Atika masu kyau dasu tace in saka na fito fes dani gwanin ban sha,awa.
Sai bayan la,asar aka aiko kirana har lokacin ina gidan su Atika kuma ba a nemay ni ba badon komai nayi haka ba sai nauyin mutanen da kunyan su, da nake ji a raina.
Muna shiga na samu a rabon kayan da suka zo dashi ana fadin wai ga na baffa gana matan shi da yara sai nayi carf nace dama kada a basu wallahi dan dama aba yaya hashimu da saude kai ko sauden ma kada a bata.
Murmushi hju tayi tace ke banda abinki wake hana alheri balle wanda akayi don ki ai sinci albarkacin ki ke nan sun san uwarki bata watsar dake ba.
Nace to a basu din ina wani daure fuska baffane ya shigo yana fadin Alh yace ta fito ina ta murnan zasu wuce sai naga yan kayana da Manjo ta bata ta hada guri daya wanda takardu ne kawai sai abinda ba a rasa ba ta dauka nawa komai tace manjo ta bayar ga mai so a nan.
Hankalina bai tashi ba sai da naji manjo tace to yar nan Ubangiji yasa da rabon zamu gana a gaba ki kula da kanki a duk inda kike ki kwantarwa mahaifiyar ki da hankalin ta idan na samu lokaci zanzo nagane ki a nan kano din sai kuma ta kasa karasa maganan ta fashe da kuka.
Nima ban san lokacin da wani kuka yazo min ba nan na fara ihu ina turje turjen ba zan bi hjyn ba baffa ya shigo ya tsawa ta min amma banki barin kukan ba.
Sunyi sai da hjy tayi min jan ido na shiga mota ga yan gidan mu sun min rakiya gaba daya da makwabtan arziki sai fatan alheri kowa ke mun a zaman kano da zanyi.
Mutane da yaiwa namin sam barka da barin gidan Baffa danayi tun ban hinjire kamar sauran yaran gidan nasa ba nima.
A haka dai muka dauki hanya ina faman rusa kuka kowa na jina har mukai nisa da garin misau kuka nake bil,haki ba kakautawa.
Muryan Alh sani ne da jikin shi ya mutu akan yadda muka rabu da manjo dole mutun ya tausya muna yayi gyaran murya ya kirayi sunana a hankali yace Sayyadi .
Ban karba sai kuka da nake rusawa ya kara kiran sunana yace fatima dake nake fa ki saurare ni .
Hjy ta daka min wani irin tsawa a motan yace a a a barta tai kukan ta kin fi kowa sanin shakuwan dake tsakanin ta da kakarta a duniyan nan.
Fatima kina jina ina son ki kwantar da hankalin ki ki daurare ni ba wai mun raba ki da kakan ki bane har abada a a mun dauko kine don mu inganta maki rayuwan ki ta yadda zaki taimaka wa kakan ki nan gaba .
Ko baki son ki zama likita kizo ki dauketa daga gidan baffan ki ki taimaka mata da magani ita da amma nima nan ki taimaka min da ciwarwutan nan na zamani dake damuna har hjy gata idan kin zama likita zaki iya taimaka mata watarana ya kare da fadin ko baki son hakan gare ki.
A lokacin na dan tsagaita kukana ina sauraren shi ya sake fadin idan mun barki a gidan baffan ki kina ganin wahalan ku dake da kakan ki zai kare maku ne na girgiza mai kai a hankali.
Yace da kyau Sayyadi da kika fahince ni kin ga idan kin zauna gurin kakan ki wanan mafalkin naki ba zai taba faruwa ba gare ku.
Amma kinga kinzo kano kin mayar da hankali ga karatu kin natsu ki cin ma burin ki mahaifin ki dake kwance a cikin kasa yasan yabar ya tagari mai tausayi da taimakon yan uwan shi a duniya.
Ajiyan zuciya na sauke yadda dukkan su a motar zasu iya jina a lokacin yace da kyau yar kawu haka ake son da mai tarbiya ya saurari nasihan manya idan suna mai maza share hawayen ki kinga mun kusa kaiwa kano kada Amma ta ganki da hawayen nan ta dinga maki sheri akan sa.
Hannu nasa ina share fuskan nawa kamar yadda ya bukata sai lokacin hjy ta sauke ajiyan zuciya a fili ya juya gurinta yana fadin kin san yaro dan lalashi ne fada bai yiwa yaron yanzu don Allah ki kula Allah ya bamu rikon amanan nan da aka bamu baki daya .
A sanyaye tace Amin ni dama ai ba tsanani nayi mata ba kukan nan ne naga yayi yawa wallahi yarinya kamar zamu sayar da ita.
Bamu shiga kano ba don munayi muna tsayawa a hanya yana sanyen abubuwa don haka sai bayan magariba muka ga sanyin da akeyi garin yasa ba wasu mutane sosai a titin sai kwan fitulun da suka haska garin sukai mata kawa kamar taurari a sama.
A gidan ma kowa na part din shi don haka koda muka shigo muka nufi part din hjy kai tsaye driver yana kwaso tsaraban hanya yana shigowa dashi cikin part din ta.
Kallona inda bake tsaye daga kofa rakube tayi tace ki shiga mana ki tsaya a nan sai bin gidan da kallo nake yadda ya tsaru da komai.
Ko da nashiga na ma kallo na tsaya yi naji muryan ta tana fadin ai ba zama zamuyi ba don lokacin sallah ya shige tun dazun don haka zo muje na nuna maki daki ki ke da kannen ki a ban zaki zauna .
Har ta fara tafiya ta juyo tace ko kin fison ki zauna ke kadai da sauri na girgiza kai har muka kai kofan dakin ta bude tare da nuna komai yadda zanyi amfani dashi.
Bayan fitan ta daga dakin zama nayi ban shiga wankan ba ina karewa dakin kallo wanda gado ne a ciki sai mirrow gadon da wardrop babba a dakin sai tv dake a kashe a lokacin.
Ina karewa dakin kallo na sauke ajiyan zuciya a hankali sai kuma manjo ta fado min a raina na sake sabon kuka ni kadai a dakin ina fadin an rabani ds kakata mai sona mai kaunata da tausayina yanzu dz ban nan yaya manjo zatayi a gidan nan ina nan ma yaya ta kare balle bani.