NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:39 – ????????????: ALLAH ABIN GODIYA NE GASHI YA BANI IKON KARA MAKU WANI PAGES A YAU DON HAKA NAKE KARA GODEWA ALLAH YA KARE NI DAGA RUBUTA MA KU HARAMTACIYAR KAMAL DAGA ALKALAMI AMIN, , , , , , , , , , , ,

Har taje ta dawo dakin ina zaune a takure yadda ta barni kallo na tayi da mamaki tana fadin ashe ba zamu shirya dake ba ke nan idan baki daukan maganata da muhinmanci.
Oya maza taso mu koma dakina kiyi wankan a gaba mu gani dole na tashi ina jin haushinta har kasan zuciyata na rabamu da manjon da tayi .
Muna shiga dakin wani kamshi ne ya daki hanci na mai dadi dakin kamar shagone a saman mirrow don tab yake da kayan shafe shafe da turararruka masu kwalabe masu kyau da dauka ido saman mirrow din ina tsaka ga kallon naji muryan ta tana fadin ga bandaki nan maza ki shiga ki wanka ki fito.
Kallon ta nayi nasan ta gane may nake nufi ta miko min wani tawul hakan na nufi hnyar bandakin data nuna min.
Ina shiga na tsaya kallo nan ma ban yi wankan ba kamar yadda ta bukata da sauri sai dana kare kalle kalle na kwabe kayan jikina na fara wanka.
Da tunane fal a raina don ba gidan su dana sani bane wanan, ke nan sun canza gida yanzu kuma.
Ashe su umma safiya basuyi karya ba ina can ina bakar wahala da manjona tana nan a cikin daula ita ta manta dani cikin duniya iba shan bakar wahla ba karya sukayi da sukace ta watsar dani tana jin dadin ta tabarwa mutane taulalina.
Da na fito bata dakin sai ganin zani da hijab data aje min a bakin gado da alama ni ta ajewa su don haka ban tsaya yin shakku ba na dauka na daura a jikina na tayar da sallah.
Na jima a wurin zaune sai gata ta shigo ta kalleni tace har kin idar da sallah ke nan ki dinga kwantar da hankali kina sallah mai kyau fa bari ma dai zamu kai ga wanan nan gaba yanzu ki tashi ga abinci nan ki ci kafin ki kwanta.
Na koshi na bata amsa ciki ciki tace oya maza ki tashi kici abinci ni ba babba bace da zan maki magana ki musa min.
Ina hawaye na mike nazo gaban abincin na zuba mai ido duk da haduwan abincin a idona hakan baisa naji sha,awanci ba don damuwan da nake dashi lokacin.
Ina nan zaune naji ta daka min tsawa dole na kai hannu ga abincin na fara ci da dan sauri sai dai kuma bakina ba test da alaman zazzabin jikina bai gama fita mun ba ke nan har lokacin.
Ina hawaye ina cusa abincin a bakina har nayi loma kamar biyar na dago kai inda take tsaye ta tsatdare ni da ido nace cikin rawan murya na koshi hajiya.
Murmushi ta dan sake a fuskanta tare da fadin Sayyadi yau nice hjy kike kirana da bakin ki ke nan har yanzu baki dauke ni a mahaifiyar ki ba.
Kaina girgiza don tsoron ta da na fara yi tace ki dan kara barin dauko maki magani ki sha kada zazzabin ki ya dawo again.
Tana wuce take maganan lokaci ne wasu hawaye suka zo min kamar an bude famfo kuma idan akwa abinda naki jini shine fada shine asalin abinda ke hadani fada da mutanen gidan mu don ban son fada shiyasa nake shan gwauran banza a wurin su.
Ta dawo dauke da kayan barci na wasu yadi mai taushi a hannun ta tana fafin ungo wanan ki saka sai ki hau gadon nan ki kwanta a nan yau don sauran yaran suna sashen Amma.
Ina gama sakawa na kashe sai dai barci bai daukeni ba naji shigowan ta dakin sai da ta kewaya ta kare duk abinda take yi lokacin har barci ya fara zo min naga ta kashe wuta ta hau gadon da nake kwancen ta kwanta daura dani.
Dan shiru ya biyo baya a dakin na wani lokaci ashe addua take don naji tofawan ta tare da ajiyan zuciya a lokaci guda.
Juyawa nayi daga fuskantar junan da mukeyi haka yasa ta kara gaskanta ba barci yarinyar ke yi ba a lokacin.
Sayyadi nasan kin kullace ni a zuciyar ki ko shiyasa har yanzu kike wanan fushin dani haka ke a zaton ki akwai uwar da zata watsar da diyar ta kamar ki zuciyar ta ya zauna lafiya ?
Sayyadi mutuwa ce mai yake kauna tayi muna hijabi a tsakanin mu a daidai lokacin da ya kamata ace kin san dadin mu mun san naki.
Ina son ki sani a karkashin iko iyayyena nake dana mijin da nake aure a yanzu bawai zaman kaina nakeyi ba daidai da rana daya da ina da ikon kaina da ban barki kin ba koda na second guda a rayuwana.
Sai dai ba yadda zanyi da abinda yafi karfi sai addu,a a tsakanin da yake Allah maji rokon bawa ne sai gashi a cikin ruwan sanyi na nuna bukatan son dawowan ki a kusa dani ban samu wani matsala suka yarde mun da hakan.
Sai dai ina son ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada maki ka zaman gidan nan da zakiyi kada ki shiga harka kowa a gidan nan kamar yadda nasan suma ba zasu shiga harkan ki ba.
Haka kuma ki koyi kama bakin ki akan duk wani abinda bai shafeki ba ko ni ko yan uwan ki cikin gidan nan .
Ina son ki zamo yarinya ta gari da za, a dinga kwatance da ita ako wani irin magana ya taso kai ba gida ba har ma wajen gidan nan kaf garin nan.
Kin zo gidan da kowa kansa ya sani da nasa gidan da nuna bambamci a gare su basu dauke shi komai ba a wurin su.
Don haka ki koyi halin da kikaga ina yi a cikin gidan nan ke ma watau hakkuri kada ki damu da maganan kowa a kanki kiyi harkan dake gaban ki kawai a yanzu shine karatu kamar yadda kikai wa kawun ki alkawarin yi.
Don nasa Alh ba zai taba gazawa da karatun ki ba har sai in kece kika nuna masa da kin gaji din ina son ki rike shi tankar mahaifin ki da baya duniya ko banza shi din mai rikon kine ko bani gidan sa .
Ina fatan kin dan gamsu da maganata kaina gyada mata na manta da cewa a cikin duhu muke a lokacin sai da ta ce ko kinyi barci ne nace na gamsu.
Don har lokacin haushi nake balle da tace min nazo gidan danger to don may ta dauko ni zuwa gidan danja din tasan abinda ke ciki.
Kamar tasan tunanen da nake naji tace sayyadi ina kaunar ki ina son ki kamar yadda ko wata uwa take son diyan ta asalima yarana kaf nafi sa rai a gare ki ban sani ba ko don baki kusa danine hankalina yafi karkata a gare ki.
Ni dai da irin wanan maganganun har barci mai nauyi ya dauke ni ban sani ba sai can cikin dare na falka ina jin kamar ana magana a dakin tsoro ya kamani don na manta shaf a inda nake sai dana saurara da kyau na tuno kuma da inda nake nike jiyo abinda ake fadi a cikin kuka a kunne na.
Ya Allah nakai kuka na gare ka ka kare min zuri,ata daga fadawa halaka ya Allah yadda na dauko amanan wanan yarinyar ubangiji ka shige min gaba ka tayani diban yar matainiyar Allah ka tsare min su daga duk wani abinki.
Ya Allah ka inganta rayuwa yar mairainiyar Allah yadda kowa nata zai wadata a karshin innuwan ta tana kaiwa nan sai kuma ta fashe da kuka tana fadin Allah kai kasan dalilin daukan mahaifin ta a daidai lokacin da muke cikin bukatan ka gare mu.
Dagowa nayi daga inda nake kwance ban san cewa nima hawayen nakeyi ba a lokacin duk da taji na motsa bai sa ta daina abinda takeyi din ba sai data gama ta shafa ta juyo tare da fadin yaya .
Mai kike so ne kika tashi nace fitsari zanyi ta nuna min ban dakin da hannu na shiga na yi kwarari na fito ta wurin dana barta ni dai har na koma barci ban san lokacin da ta kwanta ba kuma.
Washe gari ban iya tashi ba duk da ina jin hayaniyar yan kanne a dakin tunda ta tayar dani nayi sallah asuba na koma na kwanta sai zazzabi mai karfi ne ya rufeni kuma.
Ina jin tana fadin kada ku tayar da anty ku mana sameer duk da hankan na kasa bude ido inga yan kannen nawa a duniya da nake dasu.
Alh ne ya shigo yana fadin ko asibiti za a kaini ne alokacin tace tana jiran in tashi ne in karya in kara shan magani ko jikin zai sake min a lokacin.
Naji yace kin san Allah ba karamin danne zuciyata nayi ba a garin nan jiya don ji nake kamar inyi kara mutanen nan ga hukuma.
Tausayi mahaifin nasu naji a lokacin dana ganshi ya hana in dauki mataki a kansu kamar wanan yarinyar zasu bari kato kaman wanan yana dukan ta.
Tun jiya sai gode ma Allah dake nakeyi a raina da kika matsa akan a dauko maki yarinyar nan ta dawo wurin ki aida bamu dauko ta ba muka barta a can Alhakin ta zai iya tauye mu bamu sani ba.
Yanzu ba don Allah ya kaimu a jiyan ba da haka zatai ta wahala jinya daga ita sai kakanta a daki su kadai ga kakan tana fama da kanta itama.
Dattajuwar ta bani tausayi matuka na rasa ta inda zan taimaka mata wallahi sai dai idan hankali ya kwanta sai a dauko ta nan ta kwana biyu wurin amma daga nan sai a kaita asibiti a dubata sin bar mata tana wahala haka a daki ba wani kulawan da take samu.
Hjy maimuna tace nima abinda na kwana tunane ke nan gashi mai taimaka mata din mun dauko ta ga shi yayan ba wani zarahi ke gare shi ba manejin rayuwane kawai yake yi.
Dama marigayi din ne mai dan hali a cikin su Allah kuma ya karbi abinshi abindai gashi nan wallahi sai godiya ga Allah.
Alh yace zan zauna da hajiya muyi maganan akai sai ayi yadda ya dace ni zan fita idan ta falka ki fada mata na shigo tana barci.
Har yakai kofa yace a raba wanan kayan abawa kowa nasa don Allah ta amsa da to dama na tsaya sallaman yan makarantan nan ne yanzu zan raba ai.
Ya fice naji wani irin dadi a raina don maganan Manjo da naji sunyi a lokacin tunda ya furta yana da niyar taimakawa ke nan .
Sannu a hankali na sauko saman gadon na taka zuwa falon ds nake jin muryoyin su a ciki inda na samu hjy tana faman raba tsaraban da suka sayo na bauchi a hanya.
Inda naga ta kasa gida hudu daidai daidai tana ganina tace a, a kin falka ke nan yanzu ko Alh ya fita yazo duba jikin ki ta kara da tambaya yaya zazzabin yanzu ya sauka ko yana nan ?
Na dan ya mutsa fuskana tare da fadin naji sauki ina kokarin samun wuri in zauna tace kada ki zauna ki tashi ki wanke bakin ki wanka kizo ki karya kisha magani.
Na amsa da to tace kije dakin ki kiyi wanka idan kin fito kaya na nan cikin wardrobe dana dan fara tanadar maki kafin kizo inga tsayin ki dama.
Da to na amsa na fice a falon zuwa dayan dakin da ta kira da nawa ban shiga wanka ba sai dana bude wardrobe din sai naja nayi turus don kayan da nagani a ciki a jere.
Kaya nabi da kallo ina tunanen yaushe har taimi kaya iri haka ne da yawa tun banzo ina yan matan gidan mu masu dinka roba suna mi yanga dashi yau suzo suga inda kaya ke karya.
Ina dakin sai dana gama shirina wasu material da suka dauke min hankali na jawo naga ashe dogon riga akayi dashi .
A raina nace wanan kaya mai kyau aka bata a dogon riga kuma hakana dai na saka don kayan sun shiga raina sosai.
Ban tsaya yin makeup ba a lokacin don ban ma iya ba na fito falon inda take tana zaune da kayan data raba tana waya.
Ban kai ga zama ba sai ga wata tayi sallama ta shigo da kaso daga cikin kayan tana fadin wai hjy tace a maida maki sun gode.
Tace to ikon Allah a je a nan ki tafi sai da ta dan kalle ni kafin ta fita a dakin ashe lami mai aikin hjy ce don yanzu ita kadai takewa aiki a gidan tun lokacin da aka raba girki kowa ya dauki nasa.
Tana fita tace kin soma ganin matsalan gidan mu ke nan wanan ai ba komai bane daga cikin halin hjyn gidan nam.
Bance komai ba don ban fahinci maganan ta ba don haka ban wani kula da abinda take fadi din ba a lokacin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button