NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

LAMI tana komawa take fada ma hjy cewa hjy naga wata yar matashiyar yarinya mai kamada hjy maimuna sak a sashen ta.

Hajiya tace yarinya kuma wace yarinya ce wanan a ina ta kwaso ta kuma ko yar aiki ta dauko ba sani ba don shegen kishi ne da ita.
Kinga lami ki saka mi ido kiji daga ina yarinyar ta fito kuma ni ba zance yar uwan ta bace tunda nasa yan uwan ta kaf sai dai ida daga gutin mahaifiyar ta tafito amma kuma ina zata gansu matar da bama a kasan nan suke ba.
Au hjy ashe wanan batai kama da yar aiki ba fa wa itane fa yarjnyar sak sai dai idan yar wani nata ne tazo.
Da wanan maganan suka tsaya kan Lami zata gano mata ko wacece tazo dakin maimuna din don bata kawo cewa nice nazo ba don irin yadda suka nuna min zuwa na na farko ina karama a gidan.
Hjy maryam ta karbi kayan da aka kai mata sai dai bata wani yaba don ko godiya balle kin dawo lafiya.
Bayan ta kammala abinda take ina zaune na kurawa tv dake aiki ido tafito daga daki tana fadin taso in kaiki wurin gwago.
Don tun safe take mintan baki tashi ba har yanzu ta ganki don haka taso muje tunda jikin naki ya yi sauki.
A hanyar na zuwa ne muka hade da hjy maryam take fadin sai ga sako mun gani tace eh wallahi.
Har zata wuce tace wanan fa sai hjy maimuna ta danyi murmushi tace Sayyadi ce fa a, a tare kuka zo ne ta tambaya cikin mamaki.
Muka wuce ta tana tsaye tana mamaki mu har muka shige shiyan Amma tsuhuwar gidan mai sona kamar manjona .
Muna sallama a falon tana zaune da ledan goro a hannun ta tana dagowa taga tare mu da hjyn tace a a a wane kagani haka kamar kawallina yau a garin inji maki bako ?
Ina dan fara,a a fuskana nace ina wuni hjy tace har an wuni ne kwana dai ko na gyara tare da fadin ina kwana Amma tace kinga barni da ita fatan wunin take muna ai .
La le lale lale marhabin yar nan ashe kina nan na da bauchi kun shige kunyi shiru haka ?
Ta miko hannu alaman inzo gurin ta na dago daga inda nake zuwa wurin tsohuwar dake mika min hannun.
Ta rungumay ni zuwa jikin ta tana fadin A ruwa kece kikai girma haka ikon Allah kamar jiya ne fa rabon mu dake.
Na dade tare da tsohuwar don hjy fita tayi ta barni a dakin muna dan taba hira da Amma wanda hiran namu duk kan kakatace sai zaman misau da mukeyi.
Nakai wani lokaci a dakin nata don gidan ya koma tsit yara suna makaranta a lokaci sai gidan ya koma ba wani hayaniya a lokaci haka ya bani daman yin barcin gajiya sosai sai da lokaci ban falka sai da akai kiran sallah na tashi nayi sallah tare da Amma a wurin ta.
Yaro aka aiko wai inzo inji mamu yaro ya fada ashe yana nufin hjyn mu don ni yanzu har na manta da ana kiranta da mamu don hju ya karbe sunan a gurin tun lokacin da mukaji taje makka.
Amma tace muna shiri cin abinci ne bata dade da tashi daga barci ba har na mike a lokacin don zuwa amsa kiran mahaifiyata.
Inawa Amma din sai anjima tace bazaki dawo ba ke nan nace zan dawo idan nagama da haka na fice a part din zuwa sashen hjy na.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:42 – ????????????: ALHAMDULLAHI ALLAH KA SADA MU DA ALHERORIN DA KE CIKIN WANAN RANAN NA LAHADI ALLAH KA KARE MU DAGA SHERIN DUK WANI SHEDANIN ABU MUTUM KO ALJAN KO DABBA KO KWARO DA DUK WANI NAU,IN MASHERANCIN ABU, , , , , , , , ,

A ranan dai na san yan kanne na wanda muka fito ciki daya uba kowa da nasa ni dasu inda yaran ke daridari dani sun ki sake jikin su dani kamar yadda ni ma basu gabana a lokacin.
Don tunanen manjo dake addaban zuciyata har wanan lokacin ba,a taba raba mu haka ba ina da wayau na sai wanan karon.
Abincin da mamu kamar yadda naji yaran na kiranta dashi ta aje min haka nasaka shi a gaba ina kallo ko tabawa banyi ba balle in san dandanon shi.
Sai tv dake aiki a falon nakan dan kalla jefi jefi bawai don nasan may suke yi ba a lokacin.
Fitowan mamu daga dakin ta taja tayi turs tana kallona don ganin ban taba abincin ba ko kadan.
Takowa tayi zuwa inda nake ta samu wuri ta zauna hakan yasa na mayar da hankalina a kanta kai ta dangirgiza tare da fadin .
Watau sayadi ba zaki kwantar da hankalinki ki kama jiki har burin kakan ki damu ya cika akanki a hakan har zaki cin ma manufan iyayyen naki ?
Kin saka damuwa da tunane a gaba kinayi ko abincin da na kawo maki baki kalla ba wanan ai sai ki sa mutanen gidan nan suyi min dariya tunda dama ba son zaman ki a nan sukeyi ba din.
Idona ne ya kawo ruwa bulbul tace indai haka zakiyi na tabbatar da ba zaku shirya da Alh na gashi ya dauki son duniya ya dora a kanki tun baki zo ba .
Kinzo din kuma kina son watsa nai kasa a idanu ga idon jamma,a inda kin kwatar da hankalin ki gidan nan ina mai tabbatar maki duk wani dake gidan sai kin fishi jin dadi .
Amma fa sai ki kwantar da hankalin ki hakan zai faru, idan kuma kin ce ba zaki kwantar da hankalin ki ba haka zaki ci gaba dayi to ki sani ke keda wahala kuma ba komawa zaki ba don ki sani.
Jin da nayi tace komai zanyi ba zan koma wurin manjo ba yasa ni fashewa da wani kuka mai karfi tace ikon Allah ai sai kiyi tayi yarinya tunda baki san lalashi ba.
Yan kanne da suka ga ina wanan kukan sai tsoro ya kama su ina kallo suna shigewa jikin mamu suna lafewa inda ta koma kansu ta fita batu na sai haushi ya kara kamani lokaci.
Ina jin suna fadin mamu kuka takeyi ita macen ke tambayan ta tace she is not well.
Sai naga yarinyar ta bata fuska suna
Zaune sunyi sai ni suke kallo yadda nake kukan yarinyar ta mike ta fita daga falon can sai gata da goran ruwa ta kawo min tana bani tare da fadin sorry anty ki sha ruwa.
Ban karbi ruwan ba na mike zuwa dakin da ta nuna min a matsayin nawa na fada saman gado naci gaba da kukan ni kadai a dakin.

 Sallama tayi ta shigo falon  kamar yadda tayi tsamani haka din ne ya faru don hjy Jummai na zaune suna cin abinci da yaran da dawowan su ke nan daga school.
Salma ce sai kannen ta biyu mace da namiji ta saba da irin karba sallaman su wanan kuma yanzu ya bar damun ta ko kadan.
 Yaran ta fara magana don tasan shi kawai zatayi ta samu kafan yin abinda ya shigo da ita shiyan tace a, a yan makaranta sai yanzu kuke cin abinci ne.
Hjy jummai ta dan ya mutsa tace kin san su da shiriri ta ai ko cin ma ai sai na matsa masu suke zama har da wanan babban banzan.
Babu wanda ya dago kai daga cikin yaran ya kalle ta tace hjy ashe kuma mun samu bakuwa ne a gidan jiya ?

Bakuwa daga ina kuma ina take a, a yarinyar nan mana wa take da suna yar wurin maimuna da ta haifa can bauchi mana ashe jiya tare da ita suka zo.
Wani irin kibiya ya soki zuciyar hju jummai ta dago da mamaki tana fadin ke nan an kawo muna agola a cikin gidan nan ke nan ?
Masuyi iya magana sukace wai sani in fika ba wai agola da rabon gida lallai kan tana nan tazo kin ga yadda yarinyar ta girma kuwa ?
Ba zaki ce , , , , , don Alh hjy maryam rabani da wanan zancen kazantan wai may ke damuwan Alh ne haka yanzu ?
Lalai kan a bincike shi don abin ba lafiya ba wanan ma na gidan ya muka kare dasu balle an dauko agola an jefa a cikin namu kuma .
Hmmm, cabdijam ashe ko akwaita a gidan nan ke nan don ba zata sabu ba bindiga a ruwa samun wurin na maimuna har yakai ta dauko yar ta ta kado muna ita gidan nan .
Hjy maryam tace sai dai inda sunan hutu tazo nan amma kuma ai yanzu karatu akeyi ko ina shi yasa abin ya bani mamaki .
Ke yaba mamaki ko ni maryam zamu gani idan zai fada muna ko zaiyi shiru inko har yai gigin fada min zai ko ji amsa a wurina wallahi.
Hjy maryam da ta samu abinda take so ta hau zuga hjyn har da fadin wana karon akan maganan yar nan ba kyale shi zamiyu ba bore zamuyi masa wallahi.
Ko bakiyi ba aini zanyi don ni ake cutata fiye da kowa ni mai yaya da yawa a gidan nan abin bai tsaya ga wa yan nan shegun data tara muna ba har ya kai a dauko wata a dada muna kuma.
Duk da kalamin ya bata wa hjy maryam rai sai ta shaye da yake munafunci ne tace.
Duk fa abinda akeyi da sanin wanan tsohuwar mai glass tana zaune take bada umurni komai nina dade dagano su ai hjy maryam ke fadin haka.
Ta san komai mana, idan ma ance maki da shirin ta ne wanan ba za a yj musu ba don kuma kawai ta kuntata muna tayi haka amma maimuna bata farawa tace yar ta tazo ta zauna damu wane ita.
Wai a gidan an ake nufin yarinyar ta zauna sallama da tun shigowan hjy maryam ta hade rai sai yanzu tayi magana .
Maryam tace niyar su ke nan Allah, salma kun samu karuwa don wallahi yar ta kusa kama kafan ki wurin tsayi da komai nagani.
Kai haba maryam ko da na haifi salma ai fatima bata koyi aure ba sannan kuma da tai auren ta dade Allah bai bata yar ba sosai.
Hjy maryam ta nisa tana mikewa tare da fadin tana nan naganta dazun zasu sashen hajiya da cewa Amma tace munafuka ke nan inji hjy jummai.
Haba mama stop saying that to her ko banza she is Dad mum kinga bai dace and beside idan maganan ya fita ace kece mara kunya kina zaginta.
Hjy maryam ta gane nufin yarinyar saboda shayin uwar yar da takeyi ya hana tayi mata magana a lokacin.
Batai wani dadewa ba ta fito daga part din da zuman itama idan Alh ya dawo zasuyi mai maganan basu yarda da zaman yarinyar a gidan ba dukkan su.
Tana fita salma taja tsuki tare da fadin amaybo olo popo ita wanan aikin ta ke nan ta gani ta kwaso ta fada Allah mama yaci ki gane wanan matar haka.
Laifi tayi don taga abinda bai dace a gidan ba ta fada min idan an kyale wataran sai abin yafi haka girma take bani yanzun da take ban girman watau baki sun hakan kuma ?
Tabe baki tayi salis ya shigo yana fadin mama dad ya kara sayen motane naga mota har biyu sabbi a waje .
Da sauri tace wajen gidan nan ko ko dai kafin yaron ya bata amsa wayan ta yai kara ta dauka habbib ne a layin da sauri ta daga wayan ta kara a kunnen ta tare da yin sallama.
Sama sama suka gaisa da dan nata yace mama kin san da zancen motar da Dad yasa ya umar ya sayawa matan shi kuwa.
Cikin wani murya tace what tare da dagowa daga kujeran tana fadin umar ko na da hankali yaya akayi hakan ya faru ?
Ta mikw tana fadin hold on barin leka inga abinda ke gudana yace ai har motocin sun karaso gidan ko yanzu umar din ya kirani yake fada min wai ai ma Ahmed magana ya yi masu takardu.
Kai habbib yaushe umar ya canza hakane yace wallahi bai camza ba mama yana nan dai umar din da ko koka san shi miskili sai ma abinda ya karu.
Wai kana nufin matan nan za a ba motar yace kwarai kuwa nima yanzu yake fada min ashe tun lokacin da aka saya maki naki Dad yai mashi maganan nasu.
Ashe akwai bura uba a gidan nan don ba zai yuyu ba lokacin da nayj wahala daku su ina da yanzu zasu ce komai alai min sai an masu shi a gidan nan.
Mama wani abin ba amma ina zasu hada kanki dasu da dai kin kyale kowa ai don ki akayi hakan sun ci albarkacin ki.
Kin san shi bros wani bahagon mutum ne shiyasa ban masa magana a kan hakan ba sai ya nuna min nafishi sanin abinda zaiyi ne.
Kwai dai ki saka masu ido nasan ai Dad din zai maki bayanin ko ma may nene so ki basar kawai mama.
Ai bai fufe baki ba ta kashe wayan tare da mikewa zuwa hanyar wajen gidan inda ake aje motocin gida wuri ne mai girman gaske ko wacen su zata aje nata dana mai gidan guda biyu.
Turus taja ta tsaya tana karewa motocin kallo duk da nata ya na gaba sosai ga wa yan nan amma sai kyashi ya tartsu a zuciyar ta a lokaci daya take ganin nasu ya cunawa nata.
Ranan ina wuta ta jefa kanta idan da tasan ba zai kone ta ba ranta yayi bala,in baci da wani zataji a gidan da zancen dauko masu agola a gida ko kuwa zancen motocin da aka tillastawa dan ta ya saya wa kishiyoyin ta
Salma ne da kanwar ta suke tausan uwar tabi a hankali har ta gane komai don kila Alhajin ne ya bada kudi a saya mashi aiko a hasale ta juyo gare su tana fadin idan ya bada kudi sai akace an fitar dani a ciki ko ?
Ranan sai dare Alh sani ya dawo gida don haka bata samu zaunawa dashi ba don ko dan kewaya sun da yakeyi ranan bai samu yayi masu ba.
Sai washe gari suka samu ganawa da maidan wanda ta samu yana shirin shi na fita kasuwa a lokacin .
Tana shigowa dakin tace fita zakayi ne yace yau har na makara don jiya na gaji da yawa sai ta samu wuri ta zauna a bakin gado tare da fadin.
Dama nazo magana akan motocin da aka shigo dasu jiya ne gidan nan don banji kayi bayanin komai ba akansu.
Wani irin mamakin ta ne ya kama shi lokaci daya tare da takaicin ta ba ko gaisuwa zata fito mai da wanan zancen gatsau.
Sai kuma tace gaba da fadin bayan nan sai zancen yar wirin maimuna da hjy maryam tace min ta gani a gidan nan jiya da safe wani abin tazo yi garin nan halan ?
Lalai yau yasan Jummai sakariyace girman kawai Allah ya bata a gidan mutum mai yara irin jummai zai zauna yana kishin ba gaira ba dalili haka.
Jin yayi shiru yaci gaba da saka tufafin shi ta sake fadin Alh bayani fa nazo kai min kana jina kuma kayi shiru.
Wani irin kallo ya watsa mata daga inda yake kafin ya hade abinda ya taso mai azuciyar shi yace.
Jummai nike auren ki ko ke ke aure na dani dake wa ya,aje wani a gidan nan ne, jummai wai wanan wani irin rayuwa kike neman jefa kanki a cikine wai ?
Kada fa ki manta a karshina kike gidan nan dake da duk wani wanda ke zaune a gidan nan kada fa ki mata kamar yadda na auro ki haka na auro kowace ku a gidan nan.
Ina son ki sani na auro kune a gidan nan baki dayan ku kamar yadda kowan ku keda hakkoki a kaina.
Amma ke kin kasa tuna wanan hakin da nauyin da ya rataya a kanki kina kokarin shigo min da wanj akida na daban a gidana.
Aje ni kikayi da zaki zo min da wanan maganan ba ko gaisuwa ko wani da, a gaba daya kina kokarin cusa min wani ra,ayi naki a cikin gidana.
Kafin ki zo nan duk yan uwan ki sun shigo mun gaisa dasu da kwana amma banji wata wace ta tambayeni komai ba.
Amma ke kin taso zakal zakal don kin raina ni zaki sani a gaba kina tambayana kamar kin aje ni.
Zancen yarinya ai uwarta na gidan sai ki tura wace tace ta ganta taje ta tambayo maki abinda tazo yi maku gida.
Mota kuma ki manta ki tambayi wanda ya kawo su ya aje kafin ya tafi yai maki bayani kada fa ki manta ke matar aure ce kamar kowa a gidan nan.
Abinda ya kamata ace kin tsaya kin yi kin koyar bashine a gaban ki ba sai shirmay banza kin watsar da cina da sha na balle gyaran muhalina uwa uba hakkina don wani dalili naki na banza.
Yarana da iyalina a kullun sai kokarin watsa min tarbiyan su kikeyi don baki da tunane da lissafi zaki taso ki sani a gaba kina tambayana yar wurin maimuna
Shin kin mata da nima ya tace tana da daman zuwa gidan nan duk lokacin da taso koda kuwa ba maimuna a gidan nan..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button