SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:43 – ????????????: SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI, SUBBAHANALLAHI AZEEMUN, , , , , , ,
Mamu tayi murnan ganin har islamiya akai mun register da kuma yabona da yayi kan an gwadani na samu nasaran wucewa gaba.
Tayi farin ciki sosai da har ta kasa boye mai hakan a fili sai godiya take zuba mai tare da fatan alheri gare shi.
Bai jima ba yana gama mata bayani tare da kara ja min kunne ya bar gidan namu a daidai lokacin da nake kokarin shigewa dakin mu don rage kayan dake jikina don ban saba da hakan ba sosai mamu kanta duke tana karanta takardan da aka ban admision a makarantar .
Nakai kofa naji muryan ta tana fadin ashe makaranta daya kuke da sauran yaran gidan nan har kananin duk a can suke karatun su ai .
Banji komai ba ga zancen ta illa faman tunanen yadda zan saka dan kayan da naga yan makarantar dashi a jikin su wanda dan buje ne sai guntun hijjabin da baikai ko ina ba a kawunan su.
Har takalma da sock duk an bani a scchool din da littatafai masu yawa na karatu dans rubutu school bag kawai za a saya min a gida.
Ina tsaka da cire tufafi jikina Mamu ta shigo dakin tana fadin idan kin gama sai ki fito na kwance maki wanan kan a gyara su nan kin san duk sati ake kitso a school din su.
Wani iri naji gabana ya bada ace duk sati yanzu sai an taba lafiyan kaina ashe ko da magana ke nan a gurina don ba zan yarda ko wani sati ina cikin sance kaina ba aiko zaman kitson da sancewar aiki ne babba gaskiya nace a raina.
Ita da kanta rana ta sance min kai ta wanke min shi da kayan kamshi na gyaran kai sai faman fada takeyi dani yadda akayi na bar kaina a hakan dankare ina mace dani.
Shiru nayi ban bata amsa ba sai faman noke kai da nakeyi kawai a lokacin ranan dai na kara zama bakauya don abubuwan da take wa kan nawa.
Sai ya kasance a karshe banjin zafin dana nake ji sosai bata barni ba sai da tayi min kitso shuku manya a kaina sai ga fuskana ya fito wani fau dashi ni kaina sai da naji sha,awan kaina a lokacin don kyauna da ya fara fitowa duk yinin ranan ban leka wurin Amma ba ina sashen mu a zaune.
Da wuri na kwanta ina idar da sallah don dokin ganin gari ya waye na saka uniform din da aka ban a jikina.
Ranan tare mukayi aikin break fast da Mamu sabanin da kwana hudun da nayi a gidan idan tana aikin ina dakin kwance abini ina kallon komai da take hadawa a lokacin.
Sai da muka hada komai tace in je inyi wanka dana fito na zauna shiri ta leko tana fadin kiyi sauri don kada yan rigiman gidan nan su rigaki fitowa sina iya sa driver ya wuce ya barku ba karamin aikin su bane hakan.
Jin abinda ta fada yasa na kara sauri kagin wani lokaci na shirya inda tasa mu a gaba mu hudu muka fito tana gaba muna biye da ita har wani part da ban san ko na waye ba a gidan ashe part din mijin sune takaimu mu gaisa dashi.
A falon shi muka zauna inda na zube a kasa kafin ta fito daga dakin da ta shiga gurin shi can sai gasu sun fito a tare da maigidan ganina a kasa yace a, a Sayadi maynene haka zaki bata uniform din naki tun baki isa school ba ?
Ina kwana nayi mai daidai lokacin da yake magana inda kuma maganan nashi baisa na tashi daga inda nake zaune din ba har lokacin.
Yace kinga halin da baku koyawa yaran ku ba a gidan nan babba na saman kujera suma suna zaune a saman daidai lokacin da tagwayen suka ga na zube a kasa suma sukayi kamar yadda nayi iyayyen na masu dariya.
A daidai wanan lokacin hjy maryam ta shigo da nata yaran duka hudu a falon ko ba a fada ba nasan zasu girmay mun ga shekaru.
Mamakin yadda naga suna gaida mahaifin nasu nayi a tsaye ba tare da girmamawa ba a lokacin kuma mamu ke fadin ku tashi muje ko na yunkura da sauri bayan na gaida hjy maryam din da kwana tun shigowan ta yayin da sauran yan matan basuyi min magana ba sai kallo suke kare min tun shigowan su falon.
Muryan Alh ne ke fadin ina kuma zata ban gama magana da ita ba koda yake ku tafi idan Allah ya kaimu anji mayi maganan a tsanake.
Hakan yasa muka juya muka fara tafiya don barin shi da sauran iyalin nasa da suka shigo.
Lokacin naji dayan yarinyar na fadin Daddy who is she ?
Na ganta tare da mamu a gidan nan take ne kafin su bata amsa har mun fice daga falon bamu ji amsan da aka basu ga tambayan nasu ba .
Part din Mamu ta nufa damu inda a gurguje muka gaida su tare da fitowa da yan matan shiyan duk da ba wani maganan kirki mukayi dasu ba bayan gausuwa sama sama.
Wurin wata doguwar mota muka nufa data nuna muna shi da hannu tace muje ga motar kai yara makaranta can.
Sai dai suna tsaye waje basu riga da sun shiga motar ba ina tafe tare da yan kanne na har muja kawo gurin motan.
Kokarin tura kanne na nake a motar ba tare da nayiwa kowan su magana ba sai kokarin nemawa yaran inda zasu zauna nakeyi.
Suna kallo na suna magana kasa kasa suna dariya bakun ta nake masu a lokacin don haka ban kula da abinda sukeyi ba a lokacin.
Sai bayan mun zauna ne na hango wasu kuma tafe mutum uku suna tafiyan takama lokacin da suka kawo wurin motar naji babban nasu tace wace yar isan ce ta shiga motar ta zauna.
Watace muma dai bamu san da ita ba gata nan dai a ciki daya daga cikin yaran hjy maryam ke fadi don su ganin su dazun da mahaifiyar su danayi yasa na sheda su.
A cikin wani murya mai kama da tsawa tace min ke ki fito dan Allah kin zo kin wani shege mota kamar dashi kikazo daga gidan ku.
Kamar ban san dani takeyi ba lokacin na basar da ita ta kara fadi da karfi sai naji yar wurin mama hadiye tace ki bita sannu mana kin san ita bakuwa ce a gidan nan bata san yadda tsarin yake ba.
Bakuwa wurin mu tazo dallah malama fito kasa manya su fara zama koda yake ba saban ba na kauye yaga mota sai duk na kasan suka kwashe da dariya.
Yar wurin mamu ce fa ita kuma ma ai bauchi ta fito zakuce ta kauye ce inji yar wurin mama hadiye dai ta kara fadin tare kara wai may yasa kuke haka wa bako ne don Allah.
Mamu ko mamu tazo nan ai dole ta fito matan nan tunda ba don ta dady ya sai motar ba ehhe, sai yar wurin mama hadiye din ta leko cikin motan tana fadin ummm wanan fito daga ciki har su shiga sai su nuna maki inda zaki zauna ko ?
Nace ok ina kokarin dagawa daga inda nake zaune naji karamar ta kara fadin su ok manya wanan kowa ya sanshi harda yan kauye.
Ni dai bance dasu komai ba na fito daga motar lokacin naga tana jera yan gidan kaf din su yayan Alh daya haifa mu muna kasa zube da yaran mama hadiye.
Sai can ta nuna muna bayan motar ta hanyar dan kallona a kyamace tace ke shiga can baya karshe sai ku, ku zauna daga bakin nan ta farko wani kallo na watsa mata bayan na daure na fito daga motar.
Sai da kowa ya shiga tace oyo ki shiga cikin daurewa hakan na shiga sai dai a hanya a wani school muka sauke yaran mama hadiye.
Dama ina mamakin kayan mu ba iri daya bane don su nasu wando ne da riga da hijabin su fari .
Har muka kai school din raina yana bace da abinda tayi min ina jin suna shakiyancin su a mota ban kula su ba don rashin ambatan sunana da basuyi ba kuma mamu taja min kunne dama tun a gida.
Wurin pc din na koma kamar yadda yace idan nazo inzo wurin shi ina zuwa ya kira wata malama ya gabatar dani a matsayin sabuwar daliban ajin ta ss1A.
Ban samu matsala ba don bakowa na sani ba yasa na mayar da hankali gin darasin da ake koya muna.
Kamar yadda mukaje haka muka dawo ban ma kowa magana a cikin su ina zaune a bayan motan a inda ta aje ni din da safe cewa shine kujerana can bayan kuma karshe.
Mun dawo gida da murna da farin ciki a fuskan mahaifiyar mu tana tambayana ko na gane karatun da akeyi nace ina ganewa sosai don ni banga banga bambancin shi da namu ba ai .
Dan dariya tayi tana fadin ki dai mai da hankali nace zan mayar insha Allahu mamu abinci mukaci kafin muyi sallah tace in shirya don karfe uku zamu tafi islamiyan yau don haka time table din ya nuna.
Tace amma inje in gaida mamu da wuni na kwashi kanne na muka je part din tsohuwar mun samu su Aisha da bilkisu sun labartawa Amma abinda ya faru a wurin shiga motan.
Dan murmushi nayi da Amma ke fada tana fadin duk bakin halin uwarta yar nan ta kwaso shi har salma ne zata zauna tana bada doka haka a gidan nan.
A raina naji kwaein gwiwan yin abinda na shirya masu a gidan don na biyo uwata dake auren mahaifin su ai bace nazo bauta bane ?
Mikewa nayi ina fadin zamu tafi islamiya sai mun dawo tace masha Allah hakan na da kyau wallahi kinfi wa yan nan da jahilci yaiwa yawa a rai.
Tana magana tare da nuna su Aisha dake kwance mike saman dogon kujera bilkisu na dayan two seater.
Nidai na fice na barsu suna badakala a dakin da Amma irin na jika da kaka sai suka tuna min da manjo na wace nake kwana da ita ina tashi a raina da duk motsina.
Kamar yadda yace yazo ya bugo wa Mamu waya yana tambayanta idan na mun shirya don tun jiya tace tana son a hada da sauran yaran a tafi.
Muka fito lokacin babu kowa a wajea mota muka samay shi zaune yana jiran fitowan mu gaida shi na fara bai karba yace sallama ya kamata ki fara yi mun.
Sai kunya ya kamani nace na manta ne to sallamu alaikun na fada a kunyace ya amsa fuskan shi a washe.
Ya bude muna motan muka shiga baya dukan mu motar yai shiru duk yaran suma sun natsu a motan.
Sai ya kama dan jan twis da hira har suka dan sake jiki dashi duk da rashin sabon da diyan gidan basu dashi ga mutane duk zuwa gidan da yake yin bai sa yaran sun saba dashi ba.
Sai da aka gwada ni sosai Allah ya taimakeni dan karatun dana fara a azare da kuma muka dawo misau ina dan bin Atika jefi jefi ashe karatun yana mu amfani ba sani ba.
Naji dadin kasancewa na busy don yana debe min damuwan dake tare dani sosai dan kwana biyun dana fara karatu sai gashi ina warwarewa a hankali.
Zan zauna a part din mu muyi hira da kanne na ko in koya masu assigment din da aka basu hakan yasa ba ma yawan fita idan ma mun fito bai wuce mamu bace ta matsa muna muje gurin Amma.
Lokacin da sauran mutanen gidan su ka farga da ina canzawa a yan kwanamin da nayi a gidan wanda a lokacin kirana na asali dake samun gyara yanzu akai akai yana dada fitowa fili ga abincin lafiyayye har ina zaben abinda zanci a yanzu.
Yasa aka fara gulma wai dama wahala da yunwa nazo dashi ashe hallitana na asali yake boye.
Abinku da mata sai ga hassada da kyashi ya fara shiga fiye da da a tsakani da yayan Alh na cikin sa sosai duk da babu wani maganan atziki dake hadamu a ko inane.
Lokacin da Alh sani ya samu labarin muna zuwa islamiya mu kaidai ranan yayiwa yaran shi fada sosai akan haka nan ya tillasta masu zuwa suma dole.
Haka yasa sukai ta jinini akan wai iya yina yasa Abba ya tillasta masu sai sunje islamiya ai da a gida ake nemo malamin da zai koya masu.
Amma yanzu nazo da iya yina na saka an tillasata masu zuwa cikin yara dole ban damu da zancen su ba idan sunayi don kallon mai saman ruwa nake masu.
Satina biyu a gidan har lokacin ba wani abin arzikin dake hadani da kowa a gidan wanda hakan yasa na lura da hakan ma mahaifiyata take zaune dasu a gidan.
Yau kamar kullun mun shirya zuwa school ranan kuma Alh zai fita da wuri mun riga kowa fitowa kamar kullun muna tsaye muna jiran su fito mu tafi don dokan Salma ne ba wanda zai shiga mota idan bata fito ba.
Sai Alh yace ku shiga mana ku zauna kafin su fito akwai sanyi a waje don jan magana sai na kamay a wurin zaman salma din.
Can sai gasu sun fito tana ganina ta daure fuska lokacin uban yana waya tana karasowa gurin tace ke fito daga nan waya baki izinin ki zauna a nan yau.
Na nuna mata mahaifin nata nace gashi a tsaye sai ta dan juya don ganin wa nake nufi gaba dayan su suka juya sai mahaifin su suka gani a tsaye wurin da na nuna din.
Waro ido tayi tace wai Daddy kike nufi nace shi mana ko kina da magana ne shiko Alh ganin yaran cirko cirko a tsaye basu da niyar shiga ga lokaci na wucewa yace.
Cikin tsawa ba zaku shiga ku tafi bane may kuke a tsaye suka ce wanan yarinyar ce ta zauna ma anty salma wuri .
Yace motar ba daya bace maza ku shiga ku tafi don Allah kafin in saba ma wanan zancen banzan naku.
Dole ba yadda suka iya suka shige motar da sauri kowa ya zauna wurin zaman shi sai gurin da tace shine mazaunina dole ta zaunaTaTana cika tana batsewa muna barin wanjen suka taru a kaina da farko na kyale su amma da naga zagin yana son kaiwa ga mahaifiyata na saka masj waigi ta hanyar fadin kai fa malamai ku sani shiru shiru ba tsoro bane.
Duk wace tace zata fadi magana mara dadi ga uwata yanzun zan nuna mata koni wacece don kar nake kallon ku, idan yarinya ta isa kuma ta kara:.
Nafisa ce a kusa dani yar gurin hjy Jummi maibiwa sallama ra buds bKk zatayi magan ke nan sai ji tayi na kaiwa bakin ta naushi kut .
Ta yanka wani irin ihu nace kadan ke nan kika gani wallahi idan kin ce mamu zaki zaga a gaba baki ba dai idan ban gurin.