SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ni dai ina ganin yan part din hjy jummai sai shirye shirye sukeyi gashi an bude dayan bangaren da babu kowa a cikin sa sai dai lokaci lokaci akan bude wurin a gyara shi.
Ko idan anyi baki a sauke su a gurin sai naga duk wanan kwanakin ana ta yan gyare gyare a wurin hakan dana gani baisa na mayar da hankalina in san abinda akeyi ba a gidan harkan gabana kawai nakeyi.
Mun dawo daga islamiya ban shiga part din mu ba na bi ta baya don in kwashe shanyin uniform din mu danayi a baya sai nake jin murysn hjy jummai a wanan part din.
Nayi abinda zanyi har na bar gurin bata fito ba bayan na shigo ne na samu mamu a zaune tana waya don haka na shige ba tare da na gaishe ta ba bayan sallama.
Ina kokarin shiga bayi don in dauro alwalan magariba idan nayi sallah in zaman gugan kayan makarantar namu naji mamu ta kwala min kira.
Da sauri na fito daga dakina ina amsawa na fito falon na samay ta har lokacin tana rike da waya a hannun ta.
Nuna min wurin da yaran da suka dawo suka bata tayi da hannu nasan bata son kazanta don haka na gane may take nufi na juya zuwa dauko tsintsiya da packer don in dan tattara wurin.
A lokacin naji abinda take fadi a wayan tana fadin ko sun dawo gidan nan ina ruwa na dasu hajara ?
Idan mutum yace yanayi dani in yi idan kuma naga su maza sun dauki akidar uwarsu sai in share su tunda ba zaman su nake a gidan ba.
Banji may na cikin wayan ke fadi ba sai naji tace gobe fa gobe goben nan idan dai ba sun fasa bane baki ga yadda mahaifan ke ta rawan kafa ba mu dai iyakan mu ido ai.
Suwa zasu zo gobe naji mamu na magana na rambayi kaina da kaina da yake ba abinda ya shafeni bane na kwashe na fita daga falon.
Ina zaune ima zaune ina guga bayan magariba mamu ta fito daga daki na san ta sallamay sallah ne a lokacin don tana saye da hijjab din sallah ta har lokacin tace.
Sayadi kije part din gwagona ki karbo min kankara idan suna dashi nace to ina kokarin dagawa daga wurin gugan take fadin don Allah kada ki tsays hira dasu Aisha ki barni ina jiran ki.
Nace ba ma zan tsaya ba mamu fon ban gama gugana ba gashi dare yayi na fito ne naga ana shiga da wasu kaya part din har Alh kanshi yana gurin a lokacin .
Ko da na dawo still suna cikin part din fon daga can part din mu mutum zai iys hango abinda akeyi na raya a raina idan na shiga zan tambayi mamu .
Sai dai ina shiga na samu ta kara tayar da sallah haka yasa ban samu tambayan ta ba komai.
Washegari Jumma a ce tunda muka dawo nake kwance ina barci don ranan ba islamiya ga gajiya na kwaso yass na kwanta in huta.
Can cikin barcina naji gida ya rude da hayaniya sosai sama sama nake tsinkayo muryoyin mutanen gidan har da Amma.
Gyara kwanciya na nayi don nasan bai wuce wani fitina suka samu a gidan don su basu raina abin fitina gidan nan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:48 – ????????????: YA, HAYYU YA , KAIYYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS, , , , , , , , ,
Daga manyan gidan har zuwa yaran gidan gaba dayan su murnan zuwan bakin su sukeyi har Amma kanta saida ta fito lokacin da ake fadin gasu nan sun iso gasu nan.
Wanan hayaniyar ya hanani komawa barci na mike na fito falon mu babu kowa a cikin sa na nufi hanyar fita waje.
A daidai lokacin da Amma ke fadin banga angona a cikin ku ba don shi na fito taro saboda shine yasan da zama na yakan kirani jefi jefi mu gaisa dashi.
Kallo juna sukayi sai habbib ya daure fuska shi kuma dayan yace kai wanan tsohuwar da rigima kike dama muma ai bake muka zo gani ba dama.
Ta dan tabe baki tana fadin daga fadin gaskiya sai bakar magana ka dawo ke nan baka ko huta ba ka shiga halin naka.
Yace ai amsa na baki don ba wanda ya gyato ki nan maman mu da daddy muka zo gani sai yan kannen mu gasu nan sun tare mu.
Aikin banza tace tana tabe baki ta juya wurin habbib tana fadin kai kuma abinda ka kara koyowa ke nan a kasan rashin fara, a, ?
Ya dan gyara tsayi tare da fadin ohh wanan tsohuwar halin ki dai yana nan ashe ?
Dan murmushi ta sake tare da fadin kai da alaman zamu shirya wanan karon don da gani kafi wanan mai askin arnan da shiryuwa.
Kai Amma ki bar wurin nan ki bari mu gaisa da iyayyen mu don Allah tace ai yanzu ko ba sai ka kore ni ba marata ido.
Ba dai naga saukan ku lafiya ba yace wanda dai kika zo taro bai zo ba sai ki shirya ki samay shi can idan kin so ganin sa.
Hjy jummai dake ta bata fuska kan ba,an da suka tsaya yi da tsohuwan ta mayar da kallon ta gun habbib cikin nuna kulawa tare da fadin .
Ku shiga daga ciki ku zauna kafin ku isa sassanku sai lokacin su mamu suka shiga gaida su da zuwa wanda sun sha jinin su tun kalamin Aliyu din dayace mahaifan su suka zo gani ba wani va sai yan uwansu.
Ke nan su basu damu da tsayin su a gurin ba ke nan sai iyayyen su duk da haka abinka ga kawaici sai basu nuna jin zafin hakan ba a fuskan su.
Sai lokaci su mamu suka samu gaisawa dasu inda suka amsa ba yabo ba fallasa a fuskan su ko wani kula da su, su nuna su din matan mahaifinsu ne kuma uwayen kannen su basuyi ba.
Ni dai ganin Amma ta juya zata wuce nayi sauri kafin ta ganni ta sa inyi gaisuwan dole na bar wurin inda na samu kanne na a falon mu.
Hjy jummai ta kalli yayan nata cikin so da kauna ta nuna ma su mamu kuma itafa ce da gida tace ai sai ku shige daga ciki ku huta.
Daga baya ku gaisa da daddy da kyau ba mussu yaran suka fara shiga part din ta a can ta fara gabatar masu da lafiyayyen abincin dana sha wanda ba karamin kudi ta karba a wurin Alh ba don shirya ma zuwan yayan nata.
Abinci da abin sha har sun rasa wanda zasu fara dashi a falon suka dan tsukura ana fira sama sama dasu da mahaifiyar su.
Can tace watau dai ya tabbata shi babawo ba zai zo gida ba ke nan zaman can ya fiye mashi dawowa gida cikin yan uwan shi.
Aliyu dake goge bakin shi da tisue yace ba wai hakana bane mama kin san yanayin aikin sa baima da lokacin kansa balle na tafiya .
Ko yaushe shi a cikin aiki yake shiyasa ma ba,a faye samun sa sosai ba ai daiyi hakkuri don muyi waya dashi kafin mu taso na samu layin shi yace zai shigo da yardan Allah.
Sai lokacin habbib da yake shiru shiru yace mama sai kun yi hakkuri da yanayin bros don wallahi aiki yayi mass yawa sosai kin san in mutum ya zama haziki haka kowa ke son aiki dashi.
To amma habbib ace mutum ya shige cikin duniya haka ya manta da kowa nasa kamar bamu a raye ashe idan bamu raye ma shike nan sai ya manta da gida a rayuwan sa tunda shine agogo sarkin aiki.
Yanzu fa akalla babawo yakai shekara goma sha da zuwa kasan nan shike nan shi bama zancen aure yakeyi ba a rayuwan sa sai neman duniya.
Aliyu yace mama ke nan yanzu bros in dai duniya yake nema ai ya samu don ya wuce yadda kuke tsammanin sa gaskiya.
Yanayin sa ne haka tun farko kun sani ko anan din da yake ai kin san irin halin sa na kin shiga jamma,a sosai.
Amma ai zai zo fon ya tabbatar min da zuwan nasa tace yama zauna can idan mun mutu sai yazo gaisuwa .
Haba mama hakkuri dai za a yi yana tafe in sha Allahu don su kawar da zancen dan uwan nasu saboda sunga ran mahaifiyar su ya baci yasa habbib din mikewa yana fadin zai shiga ya dan watsa ruwa ya mike don akwai gajiya a tare da shi.
Nikan ina shiga wurin mu na gyara ko ina na saka kamshi na dawo falo muna kallon catton da kanne na muna dan hira a haka mamu ta shigo ta samay mu.
Bin yanayin fallon tayi da kallo tana zama take fadin yau baki ne a gidan namu yan wirin hjy suka dawo daga kasan waje.
Nace ai ihun murnan zuwan su ya tayar dani daga barci sai mamu duka maman su anty salma ce ta haife su ?
Ashe kin gansu ke nan ta tambaya tana kallona nasan abinda take nufi bangaida su ba nace ni mamu yadda naga suna sakin magana wa Amma ne bai mun dadi ba kamar ba jikokin ta na jini bane su.
Jikokinta ne kuwa don dukkan su uku hjy ta haife su babban nasu ina ganin bai samu zuwa bane kuma shi tun ina gidan mahaifin ki ya tafi.
Da yana dan shigowa lokaci lokaci daga bayane kuma ya daina zuwa don ance yanzu aiki yake ma kasan england da wasu kasashe.
Amma da ganin su zaman turai ya canza su ji don Allah yadda suke rungumar su salma da girman su tace ke dai don baki da yaya na miji ne kike ganin haka.
Ni kan har kwanan su uku da dawowa ban saka ko dayan su a idona ba na shiga part din Amma karban abu na samu suna maganan akan tsaraba da aka raba a gidan wanda suka zo dashi.
Sai nake jin Aisha na fadin kilama ko Fatima itama bata samu komai ba a cikin rabon nan hankalin su ya dawo kaina suna son ji ko an bani wani abu a cikin tsaraban nace .
Ban ma san da su ba balle tsaraban su don ni bada abin wani na dogara ba Amma ina kayan abinci in dauka mamu tace in karbo mata.
Tace shiga ciki yar nan ki duba kitchen sunanan a wanke na shiga kitchen din na fito Amma na fadin halin wanan matar sai ita duk irin kayan da yaran nan suka jibgo abawa yan uwa ta rike sai ita da yayanta ke shiga da fice a ciki.
Ni ban tsaya jin abin haushi ba ba wuce tunda ba magana na bane muna raba abunci da mamu nake fadin yanzu su Amma ke tambayana wai an ban tsaraba bakin gidan nan ?
Wani tsaraba kuma kai gwago ma dai da wani magana take komu da yaya aka bamu wanan tsaraban nasu ina sai da Alh yayi magana a kai ta dan yafuto muna Allah dai ya ba kowa nasa.
Ni kinga irin abubuwan nan ba damuna suke yi ba a rayuwa idan ta bayar ya kare idan bata bayar ba wataran ma ya kare don haka ba wani abin damuwa bane hakan.
Balle ma may ye a cikin tsaraban da suke magana wasu riguna ne sai atamfar holand guda daya yana nan saman gado na aje.
Don basu wani gamshe ni ba dama ake na ajewa su idan kina so a dinka maki su nace da sauri a,a mamu ki dinka abinki kayan da kikai min sun wadatar dani nikan.
Da dare ina zaune naga mamu ta kwashi kayan zuwa part din su amma ta dade a can sai gata ta dawo da su hade da wasu kayan ta zube saman kujera.
Ta fita da abincin maigidan dana gama blending bada dadewa ba ganin bata dawo ba yasa na dauki yan kanne na da sukai barci nakaisu dakin barcin mu.
Na dawo na kwashe kayan na shiga mata dashi ciki na jawo kofan mu na haye dogon kujera na kwanta a falon .
Har barci ya dauke ni sai gata ta shigo na bude idona inga ko waye ya shigo falon tace dama nasan kunyi barci ina can na samay shi da yaran shi suna hirane kin san halin sa yace in zauna in jira fitan su.
Jin banyi magana ba tace ina kayan dana aje wurin nan nace suna ciki na kwase dazu tace dama gwago ce tace akawo maki naki tsaraban kuma in tabbatar da kin dinka su kin saka.
Nace ni ba zan saka ba tunda bani aka bawa ba mamu tace na fada mata tace ai tunda bata baki ba sai ta ganki dashi a jikin ki .
Kai ita Amma akwai son rigima wani lokaci da kawai ta kyaleta tunda ba a tsirara nake tafiya ba.
Wai yar nan ashe da gaskiya akace tashin kaka manyan magana ke ga bakin su ke wai har kin san wanan zancen da kike fada.
Dan dariya nayi nace mamu wallahi har kin sa naji kewan manjo na ko a wani hali take yanzu bari dai in duba lamban Atika ko zanga inda na taba rubutawa a littafina da dadewa.
Ba wanan ba don babba lafiya kalau take don munyi waya da Addah ki kwanan baya take fada min hakan.
Sai dai abinda nake so dake yanzu a gidan nan ki kara kama kanki da zuwan yayan hjy gidan nan don ba mutunci ne dasu ba ko ni da nake mahaifiyar ki.
Ban ishe su kallon arziki ba a yanzu bayan a baya can tare muka taso dasu cikin wanan family din ko don yanzu suna ganin su din wata tsiyace ko kuma zugan uwar sune a kaina ban sani ba.
Nace mamu may zai hadani dasu niko a gidan nan yaushe ma na zauna a gidan ina gurin neman abinda zan zama in tallafawa manjona.
Kallon tausayi tayi min don dama tasan jajircewa a kan karatu da karfin gwiwan maganan manjo datayi min nake yin sa.
Sai dai a fili tace min nasan ki da tsiwa da rashin kunyawa na gaba wanan halin bai min dadi a raina ko yaya ne idan mutum ya girmay ka ya girmay kane.
Ban san irin tsonewa mutane ido da kikeyi ba sayadi duk da nasan kin rage wanan tsiwan naki amma kullun laifin gidan nan bai wuce kanki saboda haka ki natsu sosai da komai da kowa.
Wanan maganan da mamu tayi duk da bata fito fili ta gaya min dalilin ta ba na fagince ta a raina.
Watau tunda gida mahaifin su nazo inbi a hankali saboda a zauna lafiya don ita ba mai son hayaniya bace a rayuwan ta ko kuma tsoron su take ban sani ba.
Don haka naji a raina na tsani hjy jummai da dukka yaranta a raina matar da bata kaunan ganin kwanciyan hankalin mahaifiyata a rayuwan ta akan may zaga mutuncin ta nikuma.
Kamar yadda mamu taja min kunne haka ma Amma da yaya Ahmed don shi cewa yayi bai yarda kwata kwata da tarbiyan su ba .
Kamar sati daya da dawowan su garin ranan ina duke ina shara Aisha tazo shiyan mu tana daga kofa muna magana sai naji tana fadin ina wuni yaya Aliyu.
Ya karba mata a takaice da lafiya yana fadin wanan na ciki wai cewa da mamu yake nufi naso in share shi sai dai na dago ina fadin ina wuni kamar yadda ya amsa mata nima hakan ya karba min don jin zazzakan muryan da nake gaishe shi dashi.
Da sauri ya ware ido ya sake kallo na daga dauke kanshi da yayi da farko da kyar ya kara buda baki yace mai shiyan tana ciki ne ?
Na daure a yatsune nace tafita kawai ba tare da na sake dagowa na kalli inda yake tsaye ba naci gaba da aikina.
Ganin bai tafi ba ya tsaya yana danne dannen wayan hannun shi yasa na aje tsintiyar hannuna na shige part din mu.
Ya bi bayana da kallo har zan shige naji yana fadin idan ta dawo ku fada mata na shigo ban samay ta ba Aisha ce ta karba mai da to yaya Aliyu nan nasan shine Aliyun gidan.
Alhamdullahi ko ina a fadin duniya an dauki azumin watan ramadana har ya fara nisa ana neman rufe goman farko ba wasa a wanan lokacin .
Da safe haka zamu tafi tafsiri da Mamu da yan kanne na idan mun dawo ba wani hutu zan dan gyara gida inyi duk wasu aiyukan daya dace .
Don lokacin muna hutu dana gama zan tafi daukan karatu islamiya don ba kowane ke zuwa a wanan lokacin ba sai yan tsiraru daga cikin mu.
Idan na dawo da nayi sallah azahar zan fara aikin abinda zamu ci a part din mu sai part din su Amma da muke sakawa abinci koba watan azumi bane wannan ka,ida ne sai mun saka masu nasu daga tukunyar mamu.
Sai zamana a gurin mamu ya zamay mara alheri yanzu don dan lokacin ta samu saukin abubuwa a gidan sosai don yanzu na gwane sosai ga komai ba sai ta shiga kitchen ba idan ina gida.
Ga wani girma dana kara makerin yan matanci na ya zauna ya kerani gwanin ban sha,awa duk wani sura da akeso ga ya mace ya fito min fili.
Wanda hakan yake kara mun bakin jini gurin yan matan gidan don sai mutane su dauka nice ma yar gidan basu ba haka ke basu haushi har basu son abinda zai fitar damu tare dasu.