NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ENGLAND
Damuwa ne karara a fuskan ta ba sai an fada ma mutum tana cikin tanayin bacin rai da damuwa ba a lokacin.
Merry ce tana zaune ta hade kai da kujera tana faman tunanen tafiyan mijin nata wanda zuwa lokacin ya gama duk wani shirin da yake son yi don tafiya gida gurin iyayyen shi ko.
A hankali ya tako zuwa inda take zaune har ya zauna bata iya dago kai ta kalle shi ba sai daya dan dafa mata kafada ta dago jajayen idanuwanta ta sauke mashi.
Merry wanan abin da kikeyi na fada maki ba shine mafita a gare mu ba ina tafiyan nan da yardan ki na shirya yin sa.
Instead ki bani kwarin gwiwan yin sa don mu samawa kanmu da yayan mu mafita yanzu kuma zaki sare min gwiwa da wanan yanayin naki.
Ajiyan zuciya ta sauke tare da dora kanta saman kafadan shi tana fadin Omar jikina yana bani idan ka tafi gurin iyayyen ka ba zasu barka ka dawo gare mu ba.
Nasan irin rikicin dake a kanmu yanzu wanda dama na dade ina fargaban zuwan wanan lokacin a tsakanin mu nasan halin mutanen mu akan akidar su ta addini.
Abune mai wuya gare mu su yarda ka dawo gare mu idan ka tafi ka barni yaya zanyi da baby mu da sonka dake cikin jinina a yanzu.
Wani irin tausayin ta yaji a ranshi yasan maganan ta gaskiya ne abune mawuyaci mahaifanshi su yarda da zancen auren su kai tsaye.
Sai dai gaskiya ba zai iya barin merry da dancikin ta ko may kuwa zai faru dashi a gidan idan ya tafi wanan ya bashi karfin gwiwan karfafawa merry din zuciya akan zai dawo gareta ba dadewa ba don su tari abinda zasu haifa a tare .
Dadadan kalaman dayayi ta jera mata yasa ta kara yarda da mijin nata dari bisa dari har taji tafiyan nashi yana da muhinmanci sosai a gare su baki daya don ko ba komai yanzu lokaci yayi da zasu daina boye boye wa ahalin shi a san da ita da abinda zata haifa a zurian shi nan gaba.
Tun da safe ita da kanta ta kashi airport inda zai shiga jirgi zuwa gida na Nigeria tare da tarin abin arzikin daya kullo daga can wa iyayyeb shi da yan uwa da abokan arziki na kusa dashi.
Haka suka rabu cikin so da kaunan da suke wa junan su bayan sun dade manne da juna har sai da sukaji ana sanar da pasingers da su hallara a kofan shiga screning.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:48 – ????????????: WALLAHU GALIBUN ALAH AM,RIHIMM, , , , , , ,

Bakin Nigeria, jirgin su ya sauka a lagos sannu a hankali yake saukowa daga matakalan jirgin da zai sada shi da kasa.
Yanayi yana kokarin gyara nicktie din dake wuyan shi yana mai sauka a hankali iskan canjin yanayi ne ya ke barazanan tunkarar sa.
A hankali ya lumshe idon shi yana mai sauke numfashin shi saboda shakan iskan yanayin gida da ya dade bai ji shi ba.
Ko kadan bazai taba mance wanan yanayin ba kasan shi na haihuwa ba da ya jima baya cikin sa ya samu kamar yadda ya gama tsara komai akan zuwan nasa komai ya kammalu masa.
Motocin da ke dakon zuwan shi sun iso ko ba bata lokaci suka bar filin jirgin don yana son sai ya huta a lagos zai shiga jahar su.
Duk da yana son hutu a lokacin sai dai hakan bai samu gare shiba don masu dakon zuwan shi kasan nan Allah yai yawa dasu lokacin kowa yana kokarin yin bucking dinsa ne ta hanyar PA din shi na nan kasan.
Hakan yasa kwana biyun da yayi a lagos bai samu wani hutu sosai ba don haka yayi haraman tafiya gida don ganin iyayyen shi sai dai bazata yake son yiwa iyayyen nasa da zuwan sa.
Gida kano kasancewa azumi ne sai ya kasance ba kowa ne ke fita da safe ba sai idan rana ya dan buda mutane sun gama barcin safen su zakaga an fara zirga zirga a garin.
Tun daga layin namu har titi mutane jefi jefi zaka gani a waje da sanyin safiyan daidai wanan lokacin na gama shirina don ranan ba zuwa tafsiri makarantar safe zan shi don in tula karatuna wanda bamu samun yin shi sosai yanzu a cikin waran azumin.
Sun dade tsaye a kofan gidan dake rufe suna jiran fitowan wani su aika ayi masu iso ciki don ko ya kira waya a wanan lokacin yasan ba dauka zasuyi ba don basu da sabon layi shi na Nigeria.
Karan bude get din gidan ya nuna masu alaman wani zai fito daga cikin gidan a lokacin haka yasa suka mayar da hankalin su sosai a kofan.
Ina fitowa wasu irin bakaken motocin manya nagani guda uku tsaye a kofan sun faka tsoro naji da farko kamar in juya in koma ciki lokacin ganin yadda layin namu yayi wani tsit kamar abin hadin baki ga mutanen unguwar ranan.
Sai da na dan tsaya tsaye rike da kofan get din gidan naga na cikin motar yana kokarin bude motar yafio na juya da sauri zan koma ciki.
Wata murya naji tana fadin don Allah tsaya ki muna iso wurin mutanen gidan na dan juyo da mamaki ina kallon mai shi din .
Ya na gyara tsayuwa yake fadin nasan baki sanni ba ko ?
Kai kawai na iya daga mai lokacin alaman ehh, .
Ya sake fadin a gidan kike ko kin zo ne nace kaga malam ba shi na fito yi ba balle ka tsare ni da tambaya idan ma aikin jarida ka fito yi sai ka bari har diyan gidan su fito ka binciki sirin su a wajen su ni kaga tafiya ta.
Ido kawai ya tsura min da mamakin irin karfin halina yar ficiciya dani nake wanan zancen ga fuskana a boye da duk wani surana a cikin hijjabi.
Haka a raina kuma ina tasbihi akan irin baiwan da Allah yayiwa wanan mutumin dake tsaye a gabana.
Tsayi, hasken fata kamar balarabe dashi kyau fuska, ga uwa uba wayewa da na hango karara a fuskan mutumin.
Don Allah ki taimaka ki shiga ki fadawa hjy jummai cewa Umar ne danta a waje yake masu sallama ya fadi a takaice yana gyaran tsayuwan shi.
A hankali na maimaita sunan nace Umar Umar din da nake jin Amma na yawan maganan sa ko da yaushe ?
A she Umar din bature ne ma sai na dan ja tsuki ina fadin ni yanzu makaranta zan tafi dadai zaka samu wani ka aika da zaifi don ina ganin ma ba wanda ya tashi a gidan yanzu.
Ko ni don zan tafi islamiya ne yau muna da tulawa yasa ka ganni nan yanzu, ido kawai ya tsura min yadda nake zuba ba gajiya da magana.
Ki taimaka don Allah ki sanar masu nace wai kai ba kace gidan ku bane to ka shiga mana ni ban san abinda zai hada ni da part din nan na su a raina ma mutum wayau da safen nan.
Ganin kamar ma baiji abinda nake fadi ya mayar da hankalin shi ga wayan shi yasa na juya ina gunguni zuwa cikin gidan har kofan hjy jummai na je sai da na tsaya nayi shawara na fara nokin din kofan da karfi don nasan ko na tsaya bugawa a hankali ba bude kofan zasuyi ba shiyasa nayi masu na mahaukata .
Da zagi a bakin Nafisa ta fito tana fadin wani dan rainin wayau ne haka ke dukan kofa kamar gari zai tashi da safen nan ?
Arba mukayi ta galla min harara nima na mayar mata take fadin ke lafiya kika zo muna haka da sassafen nan kina dukan muna kofa.
Idan kin gama ki fadawa maman ku wani yana mata sallama a waje yace wai ace Umar ne danta yazo ina fadin haka na juya don in wuce.
Ta riko hannu na tana fadin ke hjy sa,ar kice da zaki mata wanan wasan da sassafe haka nace akan may zan mata wasa haka ?
Nace na saba wasa da kene abinda yace in fada ke nan na fada maki tare da galla mata harara ina fadin, ni sakeni in tafi don Allah .
Idan baki fada ki bari sai bayan na fisge hannu na daga rikon da tayi min na fara tafiya naji ta sake wani ihu.
Karan Ihun da ta sake ne ya sa na dan juyo ina kallon ta na tabe baki na bar gurin da sauri ina fadin kamar wani basarake yazo gidan.
Tun ban karasa fita ba naji gida ya rude ihun yan part din hjy jummai suka nufo waje da gudun su hjy jummai jikin ta har rawa yake don daukin ganin dan nata.
Yana ganin na fito yana tsaye kamar yadda na barshi saidai wanan karon ya dan jingina da motar daya fito daga ciki.
Na kalle shi sau daya na dauke kaina ba tare da fadi komai ba na nufi hanyar islamiyan mu da kafa sai dai ban yi nisa ba yaya Ahmed ya tsaya a gabana da mota.
Yace ba nace ki daina fitowa ke kadai da wanan safiya haka ba baki tsoron a sace ki wani kallo nayi mai daga cikin nikaf dina a raina ina fadin kamata za a sace ?
Ya bude min motar na shiga ya tayar muka dauki hanya sai lokacin nake gaida shi da kwana ya amsa min tare da fadin ina sauran suke nace suna gida sai dai ban sa zasu samu zuwa ba yau dan sunyi bako a gidan wani ne wai Umar yazo yanzu.
Cikin dan zaro ido yace Umar kika ce nace haka yace sunan shi daya turani in masu sallama.
Umar dai dan Alh yazo garin nan bayan su habbib da suka zo nace eh haka yace sai dai ina ganin kamar wanan din ko bature ne ko balarabe.
Yace kiji nace dan hajiyane da Alhaji zaki wani ce bature ne shi ki dai iya kanki dasu don ba mutunci ne da su ba koga kannen su.
Sai dai muna zuwa na samu ana dawowa daga islamiyan wai malam ba zai samu fitowa ranan ba haka yasa muka juya muka nufo gida.
Basu shiga ciki ba har lokacin da Ahmed din ya sauke ni suna farfajiyan gidan ana murnan zuwan bakon su .
Ahmed din bai tafi ba shima daya sauke ni ya shigo su gaisa dashi nikan nazo na raba su har su Amma da mamu da Alh kai kowa na gidan yana waje a lokacin har bakin da suka zo din.
Shiko bakon sai dadi yake ji na ganin sa a cikin dangin shi suna nuna mai so da kaunan juna a lokacin.
Haka nayi kokarin raba su zan wuce sai muryan Amma naji tana kwala min kira A ruwa ke Aruwa na juyo inda nake jin muryan nata.
Da hannu tayi min dakuwa tana fadin kinci gidan ku baki ganmu bane ga yayan ku daya dade da bata yau ya gane hanyar gida yazo.
Kai na daga na kalli bakon sau daya nace Amma nafa riga kowa ganin sa gidan nan don nice ma ya aika in fadi zuwan shi.
Na juya da tafiyana da suke kira na yauki da yanga zan wuce abina da mamaki gaba daya suka bini da kallo.
Don kin masa iso sai ba zaki gaida shi da zuwa ba kamar yadda kowa ya fito taron sa a gidan .
Naji kamar in fasa ihu don tsohuwar na son ta takura min kan gaida shi nace kai Amma duk wanan taron da kukayi a kansa bai isa ba sai na cika zai sani ?
Ke kan anyi yarinyar kawai a nan gaisuwan zai rage kiko kara ki idan kinyi yarinya sai gardama kamar arnan farko .
Muryan Alh ne yake fadin Hajiya kyale ta ko banza kada ya shamce ta kisa ta gaida tobashin ta akan dole balle tace sun gaisa da yazo.
Bai kai ga rufe baki ba muryan hjy jummai ya tare shi tana fadin hajiya data gaida shi da karta yi ai duka daya ne.
Ki duba nan duk yan uwa ne suka baibaye shi ta ko ina kika diba a gidan nan don haka barta kawai ta rike gaisuwan ta.
A daidai lokacin da takuran Amma yayi min yawa har na isa dan kusa dashi inda suke saye da yan uwan shi da suka baibaye shi.
Fari sol dashi sai yanzu zaka gane hakan da yake a tsakiyan kannen shi duk da suma di farare ne sol dasu.
Yana cikin suith bakake masu taushi da tsada agogon hannun shi baki sai sheki yakeyi a tsintsiyar hannun shi daya dan fito waje daga saman kot din jikin shi.
Ga bakin gashin kansa dana dan sajen daya bari a fuskan shi ya kwanta lub a jikin shi yana sheki daganin sa ba sai an fada ma ba duniya tana yayin sa a lokaci .
Duk da fuskokin su yana dauke da fara,a banda nasa dake a daure wanda babu alaman sauki a cikin sa ba sai an fada ba kansan irin mutanen ne da babu wasa ga al,amarin su dagani dai zaiyi wuyan sha,ani duk wanda yasan jan aji da isa yasan ya zauna ga wannan bakon dan Alhajin da yazo .
Sai na kasa bambamta shi da kanin nasa habibbi wayafi wani jin kai a cikin su don dan dama dama shi wanan Aliyu kamar ya fisu saukin kai a cikin su.
Ina mamaki yadda yan uwa zasu baibaye mutum ya kasa fara,a gare su haka zai kai shekara talatin ga haihuwa ko kasa da hakan .
Yana da tsayi sosai don zan iya cewa mahaifiyar su ya kwaso wurin tsawo sai ya zarta ta yana da dan lange langen jiki ba sosai ba wanda ke nuna ya jiku da ilimi ya goge sosai da duniya.
Cikin yar murya da sai ka saurara zaka jini nace sannu da zuwa ya hanya ?
Na fadi ina kallon amma cikin jin haushin takura min da tayi din a lokacin na wuce abina fuuu cikin gida ba tare da na tsaya bin ta kowa ba a lokacin don haka banji amsan shi ba ga gaisuwan da nayi mai din.
Ina jin Aliyu na fadin big bros haka unexpected ka diro muna kasan nan dai na shige su na nufi hanyar part din mu ba tare da naji sauran maganan su ba.
Su salma dake gefe suka tabe baki tare da fadin wanan da itace yar gidan nan bamu san inda tsiyanta zai tsaya ba .
Uwar ta amsa da fadin tsiyar abin tsiwanta ya tsaya ga agolacin gidan ku don dole ko tabi mutane.
Ni yanzu banda takaici a rayuwana, dama ita din ba mace bace ta dubi rufin asirin da Allah yai min naku don duk cikin ku babu na yardawa.
Ga ilimi da rufin asiri Allah ya bani ta ko ina haukan yar ficiciyar yarinya da uwarta ke ingizo ta tai muna rashin kunya ba zai taba damuna ba.
A cikin wani kasalalen murya yake fadin mu shiga daga ciki ko ku huta nima da gajiya a jikina yanzu haka.
Sai lokacin ya tuna da drivovin daya bari a kofan gida inda yace wa Aliyu yasa a sauke mai kayan shi akai sashen Amma don shi bakon Amma ne a gidan.
Ran hjy jummai baiso haka ba ga kuma kowa a wurin haka ya sakata dariyan wayayya aka wasance da fadin aiko ka kyauta babawo don ka wankewa hajiya laifinta wurin Aliyu ke nan don dafa isowan shi garin nan suka fara fada kanka inji mama hadiye dake fadi cikin dariyan fara,a.
Yace ai gwago ni na hannun daman Amma ce tun asali bana iya mantawa da Amma cikin rayuwana har abada don ta ban gatan da ban iya mantawa da ita.
Nan dai aka wasance hjy na ganin irin ganimar da danta ya shigo dashi akan idon kowa kattan mutanen nan sukai ta jida suna kaiwa part din Amma.
Sai wasu ne yake cewa a wuce dasu part din mahaifiyar tasu ba yadda ta iya dole ta sa ido tana kawaici ba don ranta ya so hakan ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button