NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ni dai har na kwanta in dan huta can naji muryan mamu na fadin ina anty ku take suka ce ina ciki na kwanta sai gata dakin ta shigo.
Sayadi barci kike ko may a lokacin na dago ina fadin na kwanta ne in huta mamu munje islamiya ance malam tafiya ya kamashi yau ba karatu.
Tace Allah ya dawo dashi lafiya sai dai sayadi duk wanan nasihan da nake maki kamar baya aiki a kunnen ki.
Yanzu ace kin shigo gidan nan kin gama a cikin yanayin farin ciki ki iya kada kanki zaki tafi ba tare da tsayawa ba badon gwago tayi maki magana ki gaida yayan ku ba ashe ba zaki gaisheshi ke nan ba.
Nace mamu sai da na gaishe shi fa nice ma ya fara gani daya iso a kofan gida na fadawa su part din su gashi a waje.
Mamu ta daga min hannu tana fadin idan zaki gyara wanan halin naki ki gyara don ni kike jawa zagi a gidan nan.
Ace kaida dan uwanka ba zaka gaisa dashi ba sai an tilasta maka gaisuwa da yake da lada a wurin Allah.
Amma ke ko yaushe sai abinda za a zageni akanki kikeyi gaskiya bazan kyaleki a kan wullakaci ba ta juya ta fita daga dakin ranta a bace.
Muryan Alh naji a falon mu lokacin yana tambayan ta dawa take fada haka take hasala tace ni da yarinyar nan ne sayadi wallahi wanan halin nata na nakasa ban son shi Yaya.
Yace haba may ye a ciki ina ko kannen nasa kinga ai basu san shi ba balle ita da tazo gidan nan kamar yau.
Zata daina idan ta saba dasu wanan ai na bakinci take masu don bata saba dasu ba hakan ma nada kyau ai ki godewa Allah da halin ta yake haka kinga baki da fargaban komai da ita.
Ina jin shi bai fita ba sai da yaga ya kwantar mata da hankali a kaina ta sauko har suna yan dararakun su na ma,aurata yabar part din.
Niko ina daki raina a bace da haushin Amma ranan don itace taja min wanan fadan da batayi magana ba da kowa bai farga dani a wurin ba.
Ko banza yaya nake a cikin gidan wurin bangaren tsana da tsangwama da nake fuskanta a wurin mutanen gidan
Sai mama hadiye da yaran su da Amma nake dan raba inji sauki sai ko bangaren mahaifiyata da kowa ke ji dani.
A ranan dai murna wurin hjy jummai ba a magana sai dai a wani bangare tana cike da jin haushin yadda yasa akai masa tarkacen shi dakin Amma.
Bayan sun gama hiran su na yaushe rabo da mahaifiyar shi da kannen shi ya nufi wurin mahaifin shi tare da yan uwan nasa.
Daga can suka nufi part din su da aka gyara masu a gidan inda ya tarar da wurin kamar yadda yake bukatan shi haka yasa bai nuna masu komai ba a lokacin.
Don komai na bangaren a gyare ya samay shi tsaba sai kamshi ke tashi a ciki haka yasa ya kwanta ya huta don dama da gajiya a jikin shi sosai.
Tun shigan shi ya sauya kayan jikin shi zuwa kananan kaya ya bi lafiyan gadon dake dakin don samun natsuwa ga azumin dake a bakin shi.
Sai bayan la, asar ya tashi yayi alwala ya nufi masalcin unguwar don yin sallah bai shigo ba sai gab da shan ruwa ya shigo gidan.
Kai tsaye part din Amma yace kanin shi Aliyu ya rakashi su sha ruwa a can inda suka samu Amma a zaune tana jiran lokaci.
Yace tsohuwa mai ran karfe gani nazo musha ruwa yau a tare dake ta kalleshi cikin fara, a da jin dadi tace.
Wanan aiki sai Umar sanda mazan fama wanan hatsabibin tun da yazo sau daya ya shigo dakin nan nawa balle ace maka wanan miskilin kanin naka guda shi ko sau daya ma bai lekoni ba.
Don haka ne nima bai a cikin lissafi na Aliyu yace ga dai miskilin zaune a gaban ki ai don kin samu kuna dasawa ne dashi bai samu zagin ba da tafi kowa zaguwa a gare ki gidan nan.
Lumshe idanuwan shi yayi a hankali tare da fadin ka san ita Amma ta daban ce a wurina don har yau banji akwai mai fadana a gurin ta ba.
Dan karamin kanin su dake tare dasu a lokacin yayi caraf yace akwai yaya don wanan A ruwa din kamar ta fika fada yanzu a gidan nan don ko kuda ya taba A ruwa zakaji Amma na fadin marainiya ce ai.
Amma tace ja,iri so kake ka hadamu fada yo in ban tausayawa yar marainiyar dake cikin mu ba ai da abin baiyi dadi ba gare ku.
Don gidan nan kaf kan ku kuka sani baku son bare a cikin ku don haka ne nake tausayin yarinyar da zaman kaddara ya kawo ta cikin ku.
Daga Aliyu har umar din ba wanda yai magana sai data kare Aliyu ke fadin Amma haka mukaji abubuwa suna faruwa a gidan nan kan zaman yarinyar nan cikin ku.
Amma tace kasan ance idan baka mutu ba ba,a kare hallitan ka ba rabon dai yayan nan ne a cikin ku da maimuna ta haifa da mahaifin ku ya kashe ma yar nan nata uban.
Sai dai kishi ya haba iyayyen ku mata su gane hakan a zauna lafiya sun dauki tsanan duniya sun dora kan maimuna da yarta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:48 – ????????????: YA HAYYU YA KAIYYUMU ALLAH KA KAWO MUNA DAUKI BA DON HALIN MU BA SAI DON DIBA GA MUMUNEI A CIKIN MU.
ALLAH KA GANI KA SANI DUNIYA TANA CIKIN WANI HALI NA NEMAN AGAJI A GARE KA YA ALLAH Jack TAUSAYA MUNA KA YAFE MUNA KURAKUREN MU, , , , , , ,

Shakuwa da so da kauna irin na tsakanin jika da kaka ne a tsakanin Amma da wanan bakon gidan daya zo daga baya.
Anan zai ci abincin sa ya zauna yana faman latse latsen wayan shi ko ya juya harshe da turancin yana hiran sa da matar shi a waya.
Don bai faye zama a wurin mahaifiyar tasa ba sai gurin tsohuwar kakan nasa dake nuna mai so da kauna fiye da kowa a cikin ahalin ta.
Nima tun ranan nake fushi da Amma don bata kara sakani a idon ta ba har yau ko mamu ta ban abinci in kai mata sai in kira kanne na muje tare zan labe daga kofa su mika mata mu dawo oart din mu.
Yau ma suna gama sallah isha,i ya shigo gidan don cin abincin buda bakin a wurin ysohuwar nan ya rutsani labe ina jiran fitowan kanwata dana ba abinci ta kaiwa Amman nina labe daga kofa.
Girshi na ganshi a gaba lokacin kaina yana duke a kasa don haka banga zuwan shi ba sai ganin sa danayi a kusa dani.
Bai mun magana ba ya shige abinshi kawai falon haka yasa na sauke ajiyan zuciya a hankali ina mai bin bayan sa da kallo.
Kamshin turaren sa da ya bari a gurin yasa na dan lumshe idanuwana a hankali ina kara shakan kamahin a hanci na.
A raina nace sai gyara kamar wata karuwa komai nasan tsab yake kai dukan su ma dai hakan suke da shegen tsabatan tsiya wai su sun waye.
Ina jin muryan Amma tana taron shi daga ciki a cikin fara a tana fadin dan halas, yanzu nake zancen ka a raina don naga ka dade baka shigo ba.
Yace da nai may Amma yana zama yake tambayan ta tayi yar dariya tana fadin ai baka laifin dan gidan Amma zance dai nake na dabi,un ka dabai canza ba a rayuwan ka.
Gaka kana ibandan ka yadda ya dace ko wani dan musulmi yayi dama shine fargaban mu akan dadewan nan dakayi a cikin masu jajjayen kunuwan nan.
Ya dora hannun shi saman cinyar ta yana zama a kasa kusa da ita yana fadin haba Amma idan nayi haka ai ba kaina kawai na cuta ba har daku da kuka bani tarbiya a baya.
Ganin Fauziya a tsaye tsakan falon yace wanan fa kafin Amma tayi magana yana tambayan fauziya da bai sani ba a gidan.
Amma tace kanwar kace yar gidan maimuna da suka fara samu da mahaifin ka a gidan nan yace ikon Allah har ta girma haka ?
Ai auren nasu ya dade kai ko don dai baka gidane kake ganin saurin sa kasan yar tata babba tana nan gidan nasa an dauko ta don barin marainiya haka yanzu abin tsorone tunda ita kadai ta samu a can.
Ko ita ce na gani labe a kofa yanzu da zan shigo tace ja,ira wai fushi take dani bata shigowa inda nake tunda nayi mata fadan bata gaida kai ba.
Fauziya ta karbi kulan abincin asuba a hannun Aisha da ta juye ta fice tana fadin Amma zan wuce sai Amma tace yar nan yanzu banda abin baki sai idan kin dawo anjima don ta saba da bamu dan wani abu idan mun kai mata abinci.
Tana fitowa nayi saurin jan hannun ta muka wuce a hanya muka hade da mutum biyu din suma zasu shiga part din Amma din wanda nasan zuwan dan uwan nasu nan ne ke sa suna shiga.
Suna shigowa daidai lokacin da Amma ke miko ma Umar fura mai sanyi da take saka mai a fridge, Aliyu yayi saurin mika hannun shi ya amshe furan tayi saurin fadin kada ka karasa gawan da ba naka ba dan nan.
Ya kwashe da yar dariya mara sauti yace Amma ai idan naga mai karasa ki sai inda karfina ya kare gara muna ganin kin nan muna wanan fadan dake da murasaki a yanzu sai kin goya yayan mu a bayan nan naki.
Yana fadin haka ya zauna gap da ita yana sake mata nautin shi tace kaga ja,iri kai da ka zama wani jibgegen kato dakai dibeka don Allah kana sakar min nauyin ka.
Duk suka kwashe da dariya habbib da sai lokacin yagama miskilancin shi yai magana yace ni fa na dauka wanan tsohuwar ta daya tun tuni ai.
Hararan shi Umar yayi yana fadin idan ta daya aiko kai ba zakaji dadi ba ina yanzu wanan ya gama fadin sai taga yayan mu ta goya su.
Harara Amma ta aika mai tana fadin kaji min dan banza zaka fadi haka mana tunda ni ba uwarka bace da kace uwayen ka na Dalla su mutu.
Suka fashe da dariya jin abinda ta fada habbib ya sake fadin kaji tsiyan tsofin nan da anyi maganan mutuwa sai su kama zage zage.
Yo ai ko na mutu yanzu na ci gari don na mutu nabar baya a duniya da za, a gani a tuna dani kai ko fa insha Allahu yanzu akwai sa,annin ka dake da diya biyar hudu a duniya.
Da sauri umar yace kai ban fura na in sha kunzo kun cika mutane da surutu muna shirin buda bakin mu mai dadi.
Dama shi ya shigo dasu zancen mutuwa suka kara fashewa da dariya gaba dayan su tace barin karo ma wa yan nan yan kwara kan sun bar abincin suna turawa can sashen uwar su sunzo nan zasu sauke muna rani.
Da sauri habbib yace bar abinki indai nine furan nan bai damay ni ba sai Aliyu yace shikan zai sha ta shekaran jiya tayi mai dadi sosai daya sha.
Tace dama ban taya maka ba miskilin banza kawai idan anyi magana kace an matsaka wallahi kuyi wa kanku fada kuyi aure haka na idan ba kuna son mutuwa a haka bane.
Bata rai sukayi suna fadin da anyi dan magana ku matsawa mutane suyi har nawa muke yanzu da zaku dinga muna zancen aure.
Ido Amma ta ware waje tana fadin kai dan nan kace nawa kuke idan da a kasan nan kake da yanzu bamu dade da shan bukin ku ba har ma matayen ku sun haihu kila.
A hankali yake shan furan shi bai kula da zancen su ba kamar ma bai wurin a lokacin sai da tace har kai nawa gaskiya ina dokin ganin auren ka a rayuwana.
Dan murmushi ya sake a gefen fuskan shi kafin yace Amma kwantar da hankalin ki kamar kinga aurena ne ai do yanzu ni kusan magidanci nake a idon ki.
Tace da kyau dan albarka shiyasa nake kara son ka a raina ba kamar wa yan nan ja,irai kake ba yanzu gashi naji magana mai dadi a gurin ka.
Ya kamata ace kun mayar da hankali rayuwan nan yanzu tsada take da shi sai kaga an dauki yaro karami an bar mu mu tsofi.
Amma bari dai in huta akwai maganan mai muhinmancin da nake so muyi dake a natse idan na samu lokaci.
Shigowan mamu falon gaida Amma da shan ruwa yasa sukai shiru gaba dayan su don tun zuwan su ba wani gaisuwan kirki a tsakanin su ko yanzu da tasan sunan ba zata shigo ba.
Ta shigo da sallama ta kai kasa tana gaida gwagon nata kafin ta juyo wurin su tace barkan ku da shan ruwa ya gajiyan tafiya ?
Suka amsa ba yabo ba fallasa a fuskokin su Amma da taga yanayin su tace haka ikon Allah yake yau ga maimuna ta zama cikin iyalin mahaifin ku.
Abin Allah bai karewa a duniya wanan rubutace ne daga Allah akwai rabo a tsakanin su idan rabo ya rantse sai mai shi.
Zanso kada ku biyewa iyayyen ku ku maza ne kunsan abinda Allah ya halasta kanku ko ku din nan haka yana iya faruwa a kanku don ba wanda ya wuce kaddaran sa cikin ku.
To baki kike muna muma muyi auren cin amana nan gaba habbib yayi gatsal ya fadi yana kallon Amma da ta tsaya tana kallon shi sarara.
Umar yace what noses talk kakeyi waye a ciki dan cin amanan mahaifinka ko ita da take zaman kanwar mahaifin namu kuma macen aure a wurin shi yanzu.
Ban son kuna saka kanku ciki shimay gin don ku maza ne ba mafa ba ya juya gurin mamu yana fadin maimuna kiyi hakkuri da abubuwan da suke faruwa a gidan nan.
Sai dai ba za mu so jin kuna yawan tashin hankali da mahaifiyar mu ba don kwanciyar hankalin ta yanzu shine namu.
Sai da ta murmusa tace ,
Haba Umar ko wanda zai tayar wa hajiya hankali na gani kasan ni mai tarewa ce ko banza don kishi ya hada mu yanzu kuma sai idona ya rufe .
Sauran dai tunda wan yayi magana su basuga abin magana ba don da ta nasu cema da bai tankawa maimuna din ba yadda suke jin zafin ta a ransu, kan ta hana uwar su shakat a gidan ta.
Salama tayi masu ta fita daga shiyan don ba zata iya zama ba suna gurin har takai kofa amma tace watau mutumiya ta fushi take dani dai kan nayi mata fadan gyara kayan ka sai kuma ta dauki fushi dani.
Gwago ba tazo ko dazun kawo maku abinci ba tace bata shigo ba yar nan karama taba ta shigo min dashi.
Kyale ta kurciyane wataran zata gane gaskiya na fada mata ai mamu tace haba gwago a kyaleta kamar ya karama da ita tasan fushi da babba haka.
Tace na dai ce ki kyale ta sanda zamu shirya kina ina ai fushin mu bai kai ko ina da ita ina zaune zata samay ni nan nasan ko yanzu ta gaji katfin hali dai ne irin nata.
Bayan wuce wanan mamu part din nasiha ta kara masu wanda yasa suka dan rage jin zafinta a ransu kan auren mahaifin su da tayi tana zaman kishi da uwar su inda Amma ta lurar dasu fa,idan abin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button