NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Amma na zaune a inda ta idar da sallah a falon ta tana jan tasbaha ya shigo falon yayi sa, a babu kowa a falon ita kadai ce zaune.
Ta dago kai fuskanta cike da farin cikin ganin shi a lokacin ya tako ya zauna gab da ita yana tankwashe kafa tayi sauri ta shafa adduan da take ta dube shi tace.
Dan nan ina kake shiga kwanan nan baka zama ga azumi ga zafin rana kana cikin sa ya dan canza yanayin fuskan shi zuwa na damuwa yace.
Wallahi Amma wasu aiyuka masu muhinmanci nake yi suka dauke min hankali sai dai yanzu na gama kammala su sai dai damuwa ta daya ce.
Tace Saudaki maye damuwan ka kuma bayan gamu a raye muna gaban ka har wani abu zai damay ka.
Yayi wata sanyayar ajiyan zuciya tare da tsure ta da idon shi yace Amma ai barin ki da Allah yayi har wanan lokacin ina ganin kamar don nine gaskiya.
Gabadaya hankalinta ta mayar gare shi tana mai kallon a cikin rashin fahintar inda maganan shi ya dosa sai da ya gama tace kai ko may ke damun ka dakake tunane haka ?
Yayi shiru sai wani gumi ke feso mai a goshi ya kasa magana Amma ko sai tsura mai ido tayi a cikin gigita hankalin ta ya tashi ganin dan lelen nata a cikin tashin hankali.
Can tace sadauki kayi magana karka daga min hankali nima kan abinda ban sani ba tukun ka tayar min da hankali sosai.
Wani ajiyan zuciya ya kara saukewa yace Amma nasan ke kadai ce mutum na farko da zata fara fahintana a gidan nan.
Amma nasan duk irin abinda na dauko ba zaki taba guje min ba idan ma kowa yaki abin nasan kina tare dani domin fahintar ki.
Kayi maganan ka kai tsaye Umaru don in fahinci inda ka dosa ka tsaya kana min kwanaye kwanaye.
Yace cikin dukar da kanshi kasa Amma ina da aure har da rabo sai dai matar tawa a yanzu bata haihu ba shiyasa, , , ,
Sadauki, Umaru kace kana da aure harda rabo yace kwarai Amma sai tayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi ta dukar da kai kasa tana tunane.
Can ta dago tana fadin sadauki haka kai muna ina daukan ka mai hankali ashe abin ba haka yake ba ?
Umar ya sunkuyar da kanshi ya kasa dago kai ya kalle sai ya ji wani nauyi da kunyar kakar tashi a karo na farko a rayuwan shi.
Cikin dakewa yace wallahi Amma kin san mai rai bai wuce kaddaran shi a zane yake nifa damuwa ta daya ne yanzu yadda su baba su amice mata a gidan nan.
Don ita din ba musulma bace ina dai kokarin ganun na musultar da ita ta zama musulma din nan gaba.
Jikin Amma ne ya fara bari tana tafa hannu alaman mamakin jikan nata da take gani mai hankali a cikin su tace ni Amamata na shiga uku yau ni jinina ya daukowa kafira a gidana.
Allah mayyasa ka barni inga wanan bakin ranan a gareni baka daukeni daidai lokacin da ka dauki mijina Attahiru ba a duniya.
Nan hankalin umar ya kara tashi kololuwa yake ji kamar ya hadiye ranshi a lokacin don zafin kalamin tsohuwar shi bai ga laifin a cikin auren da yayi ba da ake wanan tayar da jijiyoyin wuyar haka ?
Haka Amma ta barshi a zaune ba magana kamar bata san dashi a wurin ba lokacin sai faman salalami takeyi.
Can yaji muryan ta a cikin wani yanayi tana fadin idan ka gama zaman naka zaka iya tafiya tunda ka isar ma kanka ai.
Dan murmushi ya sakar a fuskanshi na karfin hali tare da fadin haba Amma a gurin ki nake kyautata zaton samun sauki a kan komai dana aikata ba tare da sanin ku ba don ke din ba jahila bace kinsan kaddaran rayuwan bawa.
Sai kuma yanzu na fahinci kuskuren tunanen hakan a yadda kika sanni kika san tarbiyar da kuka bani bai kamata ki mani fahintar da bashi ba Amma.
Umar ta ambaci sunan shi yace yau ta baci mai sau biyu ke nan Amma tana ambatar sunan shi da bata kira don yana sunan surikin ta.
Tace bawai ban fahince ka bane na yarda da nasan kaddara sai dai abinda baka gane ba shine niba auren ka na jahilta ba auren kafira arniya na jahilta a zuria ta.
Idon shi ya runtse lokaci guda yana jin zafin zagin da Amma ke surfawa matar shi merry har cikin ranshi.
Amma tace shike nan abinda mahaifin ku ke nunar da Jummai ya tabbata a kanka umar mahaifin ku a kullun fargaban shi ke nan da tsoron kada haka ya faru da dayan ku tun lokacin da ta sa fitinan sai kuje kasan waje karatu ita duk diyan kawayen ta suna waje .
Amma, Amma kin san ba laifi bane hakan ga addini ina sane da abinda nayi ita kanta yarinyar mace ce ta samu irin wanan kalubalin a gurin iyayyenta amma ta nace sai ni .
Ta bar komai nata da kowa nata tazo ta aure ni Amma don may nina miji ba zan iya hakkuri in rungumi kaddara ba tunda Allah bai hanani ba.
Wani irin nisawa Amma tayi tare da fadin Uhhmmm zamani yau Allah ya kawo ni kallon zamanin Annabi shaho da rayuwa a cikin zuria ta.
To ai sai ka je ka fadawa iyayyen naka abinda ka aikato masu can da bakinka ka fada masu tsaraban da kazo masu dashi.
Haba Amma ban taba tsamanin haka daga bangaren ki ba a duk iyaa tunane na dauka wallahi ke mai fahintar rayuwata ce ai.
Ki yarda dani Amma ba zan taba barin addini na ba don wata ko don wani abu ince na fita ga musilunci na sai ma abinda ya karu min a zuciyata.
Ai naga alama dan zamani tunda har kake iya kallon idona kana wanan maganan haka kan kafira data lasa ma zumar ta kaji dadi.
Dan murmshi ya sake tare da mika hannun shi ga nata ya dafa yake fadin Amma a gafarce ni nasan nayi kuskure amma a yafe mun.
Nan tayi saurin son jaye hannun ta yana fafin don Allah Amma ki gafarce ni kuskure na riga da na tafkashi idan kikayi fushi dani yau ban san inda zan jefa rayuwa ta ba a garin nan.
Saukowan ki shine kwanciyar hankalina Amma ki yafe min Umar din ki ya tafka kuskure mai girma a wurin ki amma don Allah kada kice kema zakiyi fushi dani a gidan nan ya kare yana hada hannayen shi guri daya.
Wani iri Amma taji a ranta yadda ta hango tashin hankali a tare da yaron lokaci guda sai tausayin shi ya kamata sosai sai dai a fili tace dashi.
Sai ka sanarwa iyayyen naka ai don ni wanan zancen yafi karfin fada a bakina gidan nan kasan komai kayi sai suce nice mai goya ma baya.
Ya kara fadin don yaga saukowa gareta ko yanzu kece dai mai sanar masu da halin da ake ciki don jiya Daddy ya fara min maganan aure.
Ai dole yai maka don hankalin mu ba akwance yake ba kunkai munzalin aje iyali ace baka motsa ba balle kannen ka su motsa.
Ashe mu bamu sani ba kai da iyalin ka a hannu mune ka mayar wasu bi nan can kana kallon mu wawaye.
Da sauri yace nina isa haba Amma kuna iyayyena zan ayyana haka gare ku lalacewan nawa bai kai can ba ai ya kare magana a cikin ladabi da kulawa a gareta.
Haka ya kara sa jikin Amma sanyi jikan nata ya bata tausayin kaddaran data samay shi gaskiya ya fada don kaddara na kan kowa amma dole ta nuna mai bacin ransu a fili don gaba.
Zaka iya tafiya ta bashi amsa sai yai shiru ta sake fadin bakaji bane ya dago a sanyayaye yace Amma fushi kike dani ke nan ?
Tace Umar ka barni in huta saboda Allah kasan a rike muke muna cikin lokaci ya fahinci mai take nufi ya mike a sanyaye ya bar falon nata zuciyar shi ba dadi a lokacin.
Bin shi tayi da kallo a ranta take fadin ban so haka gare kaba dan nan kaddara ta riga fata kai daya dace ace ka samu mace natsatsiya kamila mai rikon addini a cikin dangi kai ka aikata haka a kan ka.
Tirr da wani wayewan idan yai yawa bai haifar da alheri ta yaya yaro karami kamar sadauki zai yankewa kanahi hukunci a rayuwan shi.
Shiko umar yana fita ya sauke ajiyan zuciya tare da fadi a ranshi ashe akwai aiki Amma ke nan da yake gani da saukin samu tayi mashi haka ina ga iyayyen shi kuma ?
Tafiya yake kamar wanda kwai ya fashewa a ciki jiki ba kuzari can ya hango Ahmed da mamu sun shigo da kayan da suka dawo dashi daga asibiti kallo daya yai masu ya kawar da kanshi gare su.
Idan da sabo ta saba da halin yaran mijin nata wurin nuna ita ba kowa bane gare su don haka ne abin bai damuwan ta gashi dai tana son mai godiya sai dai ba fuskan hakan a wurin shi tun a dakin Amma dataji shiyasa a dauko manjo tana son mashi godiya ya daga mata hannu alaman bai son hakan gare ta ta kyaleshi.
Hakama Ahmed da shima yake nuna bai damu dasu ba don akwai tsana karara a idanuwan su indan sun hade dashi saidai da yake maza ne basa fitarwa fili.
Mamu ta shigo da sallama tana aje flask din data dauko a gefen kujera ina daga kitchen naji muryan ta, na fito ina mata sannu da dawowa.
Bayan ta amsa take tambayana ya aiki nace na kammala gyara wurin nakeyi naji muryan ki tace sannu da aiki sai dai da zan samu a dan sa min ruwan zafi kadan tuwo nake son tukawa yanzu .
Nace tuwo kuma mamu may zakiyi da tuwo na tsare ta da ido ina tambaya tace asibiti zan tafi dashi nace asibiti kuma wa naki ke asibiti ?
Sai da ta mike tsaye take fadin wasu ne baki san su ba amma dai da sauki jikin maishi yanzu.
Mamu da gaskiyane Manjo ke asibiti garin nan kika boye min na karasa fadi kamar zanyi kuka.
Ta kalleni da mamaki tace a ina kikaji haka itace a asibiti ?
Ammace tayi subul da baka ta fada dazun tunda naji ko ta fada tunda tana boyewa nasan da gaske ne don zuciyana taki natsuwa da maganan.
Ta mike tsaye tana fadin eh itace don baki da natsuwa komai kuka yasa na boye maki don kada ki tayar muna da hankali.
Sai na dora hannu a kai na fashe da kuka ta daka min wani tsawa da sauri na shaye kukan dana fara tace wawiyar banza ai kinga irin haukan naki ba.
Ke yanzu dadin kine a yadda akazo da babba garin nan wani ya sani a samu abin goranta maki nan gaba kul naji zancen nan ya fita sai na saba maki a gidan nan wallahi.
Da sauri na ja bakina na rufi na bita da kallo har ta shige dakin ta na sudada na koma kicin ina aiki ina kuka a raina ina fadin kila ma mutuwa manjo xatayi yasa basu fada min ba tunane kala kala nayi shi a gurin ni kadai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button