SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:35 – ????????????: SARKA MAI, , , , , , , , ,
3️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
GODIYA YA TABBATA GA ALLAH SARKIN KOMAI DA KOWA DA YA NUNA MUNA WANAN RANAN TA JUMMA,A UBANGIJI KA TAIMAKI MUSULUNCIN AKAN KAFIRCI KAYI MUNA DA YAN UWAN MU MUSULMI DAUKI A KO INIA MUSULMI YAKE A DUNIYAN NAN .
JUMMA, AT MUBARAK YAN UWA UBANGIJI YA BAMU ALBARKAN DAKE CIKIN WANAN RANAN MAI ALBARKA AMIN.
WANAN LITTAFIN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A NATSE YAR UWA BATARE DA SHIGA HAKKIN KOWA BA NAGODE, , , , ,
DOMIN SAMUN WANAN NOVEL ZAKI IYA KIRAN WANAN LAYIN 08036959257 KO KI TURA KATIN DARI UKU TA WANAN LAYIN 225428015 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN DARI UKU KACAL NA GODE, , , ,
Da sauri take tafiya don zuwa kai gulma wurin uwar gijiyan nata da ke dan mata ihisani kan orin wanan halin ko da yake sabone kawai don kowan su na mata abin arziki daga cikin su.
Da sallama ta isa dakin hjy jummai wace ke zaune tana kwasan girkin abin karyawan safen da aka kawo mata wanda sai da aka yaye mata wurin abin miyan kafin a zubawa sauran busashe akai masu.
Ganin yadda ta shigo yasa hjy Jummai sanin da magana a bakin ta ta shigo dakin nata a lokacin haka yasa ta mayar da hankalinta gurin lami din.
Cikin irin yanayin munafukai lami ke magana hjy ashe abinci kike ci barin bari ki gama saina dawo in fada maki abinda ke nan.
Haba yi magana ki mana Lami tunda kin zo ai ba zai hanani cin abincina hjy Jummai dake zaune take fadin hakan.
Hjy dama ba wani abu bane sai zancen wanan amaryan taku ne yanzun naje nakai mata abincin safen ta na samu ta hada nata suna karyawa da yaranta.
Hjy da kanta yake duke ta dago da sauri tana tambayan may kika samu ta dafa a can din, hjy ta tambaye ta da sauri ?
Lami ta gyara zama tana fadin ruwan shayi ne mai kauri sai kwai suke ci a plate .
Da sauri hjy tace Lami kardai ince kwan da aka ajewa Alh na amfanin shi ne ta diba ta dafa da yaranta ?
Lami tace ai shine nazo na fada maki kar aga ya kare a tuhumay mu muda ke aiki ko yaushe a cikin kitchen din .
Kwarai kuwa don kune a kitchen din ko yaushe dama nasan a rina wanan shiga kitchen din din da takeyi ba banza bane a gidan da akwai zanban da take shukawa.
To yau ya kare don asirin ta ya tono a gidan nan gaskiya idan ankai mata abincin suke kin tabawa sai dai ta dawo muna dashi kitchen.
Abincin da hjy Jummai bata karasa ci ba ke nan dama tana da takaicin hjy maimunan a ranta yanzun kuma an kara dada mata wani sai taji duk abincin ya fita ranta ga baki daya.
Da kyat ta yaki zuciyar ta har maigidan ya dawo ansan wace ake don ba zai yuyu maimuna ta dinga nuna masu tsageranci hakaba a ckin gidan.
Ita wacece da bazata ci wanda aka girka wa kowa ba sai tayi nasu ita da yaranta akoda yaushe lami tana ganin ta hada wanan ta mike zuwa aikin ta don tasan yau ko ba komai ta gyarawa uwar dagin nata rai da wanan maganan.
A bangaren hjy jummai kuma bayan sun gama karyawa ne ta tasa yaranta gaba don suje su gaida kakar su Amma tare da daukan kulan data sakawa hadiye dan abinda ta soya din.
Da sallama suka shiga dakin Amma inda ta samu hadiye a dakin suna hira da mahaifiyar ta da murna Amma ta tari yan jikokin nata inda hjy maimuna ke fadin.
Ashema kina nan tana fadin haka ne lokacin da take mika mara kulan data riko masu din.
Hadiye sai cewa tayi mai muka samu kuma a nan tana kaiwa zaune take fadin dan sauran kwanda yaya mustapha ya bamu ne ranan na gidan gonar shi na soya.
Kin san yaran kin ga har yau basu iya cin wanan abincin safen da ake girkawa a gidan nan yau ai kinga basu zo shan kunun gwago ba.
Cikin tabe baki Amma tace na rasa may ake da wanan uban kayan girkin da ake shigowa dashi gidan nan sai ga an shigo da kayan girki mai yawa.
Amma karshe haka za a kawo abincin nan ko almajiri kaba almajiran nan na yanzu ba zasu karba ba.
Hjy ke nan ana ko amfani dashi sosai don da yanzu zaki sashen yar mulkin gidan kiga abincin ta ita da yaranta sai kice ba guri daya aka girka da wanan din da ake kawo muna ba.
Hadiye ce ke fadin wanan magana ta karasa da fadin ni yanzun haka ko budeshi yaran nan basuyi ba don ba zasu iyaci ba ma ko sun bude din.
Nina rasa wanan akidar ace gida kamar wanan wai sai gaba daya za ai girkin da za a ci ranan dana shiga na samay ta tana ci nayi mata magana sai cewa tayi babban goro ai sai budin karfe dole itace za a fara zubawa don hakane na ga nata a hakan.
Tsuki Amma taje tana fadin wanan yarinyar tana daukarwa kanta nauyi da yawa ina zata da wanan alhakin haka a kanta.
Nina rasa hali irin na jummai a ce mutum baida abinyi a rayuwa sai kokarin danne hakkin wasu abin nan ana bayarwa ba ba a kawowa bane amma don kawai ta cutawa yan uwan zama ta kawo wanan akidar banzan haka.
Hjy ni indai zata barmu mu zauna lafiya duk wani akidar ta baya damuna kamar rashin kwanciyar hankalin nan da babu a gidan nan a kullun.
Hjy maimuna ce take wanan maganar cikin nuna damuwan ta da yanayin gidan nasu.
Kasancewar bata da girki yasa takai har sha biyu da wani abu tare da hadiye suna hira kafin ta koma part din ta da yaranta.
Wanda hakan ba karamin bata ran saura natan gidan yakeyi ba don a zaton su zaman zagin su akeyi gurin hadiye din.
Basu san abin ba haka bane kokarin kulla alakan business suke a tsakanin su shine yawan zuwa part din juna da sukeyi.
Bata fito ba tunda ta shige tana cikin sashe nata wanda haka ne komai a ciki duke da yaranta idan ba maigida ya dawo ya nemi yara a gurin shi ba sam bata yarda su fita daga sashen nasu.
Don da farko tana bari har i yaran suki fita ta tillasata masu wai don su saba da yan uwan nasu take yarda su fita da farko.
Sai daga baya ta gane fitan nasu cuta masu akeyi idan sun fita cikin tan uwan nasu don duk sun fisu girma a gidan da yawa kuma.
Shine dalilin da bata yarda su fita ko ina hakan kuma yana ma yaran dadi sosai na rashin fita inda za,a duke su da zagi iri iri.
Karfe biyar duk wani wanda ke gidan yasan lokacin dawowan maigidan gidane hakan ke sa kowa na gidan yake natsuwa.
Matan gidan kuma kowa takan dauki kwalliya don burge mai gida sukan shiga daya bayan daya wani lokaci ida yana da magana zai tsayar dasu yayi masi shi a cikin jam,i.
Idan ko ba wani magana sai a bar wace ke girki ita kadai tare da maigidan ta dauke mai sauran dawainiya kafin ya fita sallah mafariba.
Irin bada abinci miko min yi min wancan sai idan yana da baki suka dan samu su sarara.
Inda shi kuma yakan zauna da yara shi kanana suna hira kafin su fice masallaci dashi da yaran nasa.
Yauma irin hakan ya kasance a wurin hjy maimuna din inda take saye cikin atamfar code, voi,re dinkin zanin da riga half gun sai yaran da ke saye da yar katin su uku ta tasa su a gaba.
Ta makara zuwa gaida maigidan nasu a yadda ta saba zuwa idan ya dawo hakan ya samu dalili ne na tsayar da ita da yan biyun ta sukayi na yin kashi bayan ta shirya su kinsan abu ga mai kananan yara.
Da sallama ta shigo fallon kallon yanauin su kawai tayi tasan da akwai matsala don haka tana gaida shi da ta juya zata bar fallon.
Muryan mijin nasu taji yana fadin dakata maimu samu wuri ki zauna inda ya kalli yaran mm nata yace kuje ku jira maman ku ta dawo ko .
Yaran suka juya don bin umurnin mahaifin nasu yayi da yar mulkin ke zaune a gefen shi tana harare hararen yaran da suka saba da irin kallon da take masu a gidan.
Dan shiru ya biyo a falon sai can Alh ya kira sunan ta inda ta karba da fadin na,am yaya don haushi hjy jummai ta wani kawar da fuska tana mayde bakin ta.
Maimuna wani magana nale jin yanzu wanda banji dadin jin shi daga gare ki in ma har haka kike so ai sai ki gabatar da zancen a gabana in san abinyi ko ?
Hjy jummai bata so haka ba sai haushi ya kamata sosai na yadda yake mata magana a cikin tsigar lalashi itako a cikin sanyin murya tace wani abin akace nayi kuma tunda ba, a raina abin laifi a gidan nan.
Alh baikai ga magana ba yar mulkin ta karbe da fadin kina nufin kake akai maki ko may wa kikafi a gidan nan da bazaki ci abincin da kowa yaci ba sai kin fake ga satan kayan gida kin shige daki kin dafa da yaran ki kuci.
Salati hjy maimu ta saka tare da fadin yau kuma sherin yakai a laka min satan abinci a gidan nan ?
Ji munafuka waisheri cikin tsawa da daga hannu Alh ya dakatar da ita da fadin ke Jummai banson irin haka don Allah ki bari muji dalilin ta na yin hakan saboda Allah.
Falon ya danyi shiru kafin ya nisa yace hajiya babba da hakuri fa aka sanshi kila tana da wani hujjan yin hakan kamar yadda na fada da farko.
Hjy ta sake fadi may ye kuwa hujjanta illar son nuna gadara da isa ita a dole fata matar gida a yanzu za ta iyayin komai a gaba gadi.
Yace wai ba zaki shiru muji ta bakin ta bane ko may ko ke zaki daukarwa kanki mataki in kyale ku da ita.
Ai idan ya kama sai mu dauka don batafi karfin kowa a gidan nan ba ke nan ita gata yar gida muko bare ke ba zakici abinda aka girka kowa yaci ba ke nan sai ki fito da naki fi, ilin.
Don kina takama da hjy na cikin gidan da zance ya tashi abi bayan ki to ko hjy ba zata yarda da wanan halin da kika dauko yiba.
Irin maganganun da take fadi dole suka saka mata ido har ta kai aya don bata jin taro a lokacin kishin ya motsa sosai kan dan abinda baikai ya kawo ba.
Sai fadi take ai ba akanki na fara zama da kishiya ba a gidan nan balle kizo ki min aikin gaba gadi ke gaki yar gatan dangi .
To ki sani nan din dai gidana do a ciki kika samay ni balle kice zaki zo ki kafa min wani iyayi can a gida .
Wallahi tunda na gane abin naki tsiyane yanzu zamu saka kafa wando daya dake a gidan nan gobe ko ance ki raina ma wani hankali ba zaki sake ba.
Abinci ne yadda na tsara ayi dole haka zakici dake da yara ki don ba fin mu kukayi ba a gidan don shi ko wan mu ke ci har yaran mu.
A fusace hjy maimuna da ta gaji daji abinda hjy jummai ke fada mata kamar ita ta ajeta a gidan yayi yawa bata san lokacin da ta bude baki ta fara bata amsa ba.
Ke hjy jummai zancen ya isa hakan koda nayi balle van san da nayi wani abu a gidan nan makamancin hakan ba don ni kinfi kowa sani kayan gidan nan basu taba tsone min ido ba ko kadan.
Kuma ki sani idan kin bada doka a dafa muna abunda kike so ai ba zaki shiga dakin Alh ki bashi dokan ga yadda zaiyi dani a gado ba ko ?
Yau wanan bakin halin naki na gadara da nuna isa yasa dan sauran mutuncin ki da nake gani a gidan nan ya zube wallahi.
Shi yaya din kika raina da ita wanan ta nuna hjy maryam dake zaune tana kada kafa wai itama ta hasala da zancen ke nan.
Dokan ki na banza tunda ba dokar Allah da annabi bane ra,ayine hakan idan mutum ya ga zai iya yabi do a zauna lafiya idan ba ka iyawa ba dole bane tunda takardana ba a hannun ki yake ba.
A fusace hjy Jummai tace haka kika ce zan ko nuna maki wata abu nake a gidan nan don kina ji kina gani sai zaman gidan nan ya gagare ki zama da duk wani wanda ya daure maki gindi, a gidan nan.
Ta Allah ba taki ba idan kin saba batar da mutane ni maimuna nafi karfin ki wallahi zaman gidan nan gare ni mutu ka raba tunda nariga da na shigo.
Da dai ace ban shigo bane sai barazanan ki ya dan tsoratani sakariyan banza kawai wace bata amfani da ahekaruta uwargidancin naki na zalunci har kike gadara dashi.
Ba hjy jummai ba har hjy maryam da Alh ranan sunyi mamakin hjy maimu din yadda ta tsaya tana fadin magana ga yadda kowa ya santa mace mai hakkuri da kawar da kai ga komai na gidan.
Tashin muryan su ya dawo da hankalin mutanen gidan gare su cikin sauri Hadiye da Amma suke rige rigen zuwa inda suke a garden suke maganan.
Tu daga nisa Amma ke tambayan abunda ke faruwa a tsakani shi da kyar aka samu sukai shiru Alh sani ya fara bayani abinda hjy jummai ta samay shi dashi daga dawowan shi.
Salati hadiye ta saka tare da fadin hakika Allah yayi gaskiya da ya ce zato zunubi ne koda yazama gaskiya.
Kwanan da muka samo gidan yaya mustapha da muka samu an debo a gonan shi shine ya dibarwa su yan biyu mai yawa muna zuwa gida ta raba ta aikawa kowa da nasa sauran da take dafawa yaran ne yau ta soya masu shine kuka gani kuke wanan magana.
Hadiye dakin kyalesu ai har ina naga kwan gidan da zan diba bayan makuli store din yana gurin ta ko gishiri kake so sai da umurnin ta za a baka.
Alh sani yace to ke kinji da kike ta wanan irin tayar da jijiyoyin wuyan akan abinda baikai ya kawo ba tun dazun na fada maki abi maganan nan sannu don a gane gaskiyar maganar kin kiya.
Yanzu ga gaskiyar maganan ya fito may gari ya waya da hakan da kukayi shiyasa ake son bincike kafin yanke hukunci.
Amma da dakyar ta kawo kanta ta samu wuri ta zauna tana fadin to ai yanzu shike nan gara da Allah yasa haka ya faru yau din nan.
Abinda nake so dakai daga yau aiwa kowa cefanen ta a bata ita da yaranta mace ta dafa abinda ranta dana yaranta ke so suci.
Wanan bakar akidar ba dai don baka dashi bane ake hakan don shiga hakkin wasu ne kawai wanan maganan kuma umurni na baka ba son jin ra,ayin ka nake nema ba kan magana ta.
Gaba dayan su sunyi mamakin jin fyrucin tsohuwar da bata faye sa baki a cikin zancen da ke wakana a gidan dan nata ba don kawaici.
Sai gashi yau da rana tsaka tana bada umurnin kawar da dokan da hjy jummai ta kafa take ganin ba mai iya ta da wanan dokan a gidan.
Tsohuwar ta kawar akan dalilin fadan ta da yar ta kuma amaryam su sai take gani anyi hakane don dama a kuntata mata a gidan.
Har taso tayiwa tsohuwar rashin kunya nan Alh sani ya falfalle ta a gaban kowa abinda take ganin gazawa ne hakan da yai mata din.
Tun daga wanan ranan suka kulla da hjy maimu a gidan wanda zaman lafiya ya kara kawuwa a tsakanin su.
Ta dauki kiyayyan duniya ta dora akan hjy maimuna da yaranta bata kaunar abinda ya shafesu ko kadan