SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:55 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM RABBANA ATINA FIDDINIYE HASSANATA WA, KINNA AZBAN NAR, , , , , ,
Ko da na koma part din mu mamu tana kitchen tana hada breakfast don fita nayi zuwa wurin Aisha sai muka tsaya shiririta a can har kaddara rabon mari ya hau kaina.
Jin motsina da tayi ta leko daga kitchen tana fadin kina can kin samu gwago kin shagala da zancen abinci ko ?
A sanyaye a cikin murya na daya dan danlashe don kukan da nayi nace Amma ce ta tsayar dani can.
Tsaye take a gurin frige tana daukan abu jin muryana da tayi hakana yasa ta saurin juyowa tana kallona ganin ta zuba min ido kamar tana nazarina yasa nayi saurin dukar da kaina kasa.
Kallon shatin yatsun habbib da ya kwanta a kunci na da suka feto ras a binka da farar fata sai wajen yayi jajir dashi alaman taruwan kwancin jini da shafin hannun shi a kumatun nawa.
Sayadi waye mare ki haka har wuri ya nuna tana tambayana fuskanta karara da mamaki ?
Na sunkuyar da kaina hawaye na gangarowa a fuskana ban iya buda baki na bata amsa ba haka yasa ta aje kwalban data dauko a fridge a hankali ta tako zuwa wurina.
Ta sake tambayana a hasale nace wayayi maki wanan mari haka da sanyin safiyan nan kin kyale ni ?
Mamu wanan dayan yayan su salman ne ya mare ni na fada ina karashewa da kuka sosai tace da kikai masa may ya mare ki haka sayadi ?
Nayi shiru ina sheshekan kuka a cikin bacin rai ta fara magana wanan wani irin cin fuska ne haka wani irin laifi kika aikata masu mai zafi haka akai maki wanan marin haka har shedan yatsu ya tsaya a fuskanki ?
Wallahi wanan karon ba zan yarda ba abinda ma ba zai yuyu ke nan ba ban taba dan kowa a gidan ko harara ba ba zan zauna ana saka min diya a gaba ba.
Ta kara tambayana nace may ya hadaki dasu a cikin kuka nake fadin ban san suna tafe ba naci karo da babban su shine gudan ya mareni.
Hannuna taja fuuu muka fito daga part din hanyar part din Amma muka nufa sai ga kawu ya fito ranshi a bace daga part din.
Yana hango mu yayi saurin karasowa gare mu yana fadin ina zaki da ita ku koma a gabanta ai nayi magana ko baki fada mata bane ya juya saitina yana tambayana niko sai kuka nakeyi sharba.
Yanzu Yaya ya dace hakan da sukai mata diba fa shafin hannun shi a jikin ta yadda ya kwanta a fuskanta tana nuna mai don idon ta ya rufe bai taba gani ta haka ba akan diyan ta.
Ya dai samu ya lalasheta ta koma dani a ciki tana cika do yasan idan ya barta ba zai ai mai dadi ba ranan.
Waye a cikin su ya mareki haka ta tambaye ni nace wanan dayan ne wanda baya dariya a cikin su tace habbib ke nan ko shine mai bakin ran tsiya.
Gaskiya ba zan laminci hakan ba dole na kwata don wahalan dana kwana biyu ban shiga ba.
Wanan abin yaiwa mamu zafi sosai sai da ta samu Amma sukai magana ta kara bata hakkuri.
A kasuwa Alh ke fadawa Ahmed abinda habbib yayi min tare da abinda umar ya aikato a can ya jajanta wa Alh kan hakan.
Sai dai hankalin shi yana gun maganan marin da akai min din wanda yake jin zafi a ranshi haka ya samu daman sulalowa daga kasuwa zuwa gidan kawun nawa.
Ya iso gidan namu direct part din mu ya nufo ya tsaya daga kofa yana sallama kani yazo yana dubawa sai ya dane mai jiki.
Tura yaron yayi, yayi mai iso gurin mamu yaron ya juya da gudu sai a wurin Ahmed kawai suke jin dan sanyi a gidan idan ya shigo.
Mamu tace dashi ya shigo falon lokacin tana kokarin saka hijjab din ta a jikin ta ya karaso yana zama yake gaida ita ta amsa har lokacin yanayin ta ba dadi kallo daya zakai mata kagane hakan.
Bayan sun gama gaisawa yake fadin hajiya ashe abinda ya faru ke nan dazun Alh ke fada min a kasuwa maynene ya hadasu haka dasu har ya iya marin ta ?
Malam Ahmed ke nan a gidan nan ai ba sai munyi wani abuba zasuyi iya muna haka tunda so suke su rabamu da gidan ko ta halin kaka.
Idan ba haka ba daga bangaza kawai sai wanan irin marin Ahmed yace shike ban mamaki ai
Don ran Alh ya baci sosai yau shike fada min abin ya taba mai zuciya sosai wallahi.
A to ni dai na fada mai abin ya isheni wallahi dan magana kadan sai a kama min yara da duka sai sun kwata ciwo don ha,inci.
Yace ina fatiman take ne ta nuna da hannu tana fadin tana nan daki tun da ta shiga ta kwanta kila barci takeyi.
Kai shima dai yasan bai kyauta ba tunda yarinyar nan dai batayi mai komai ba idan dai ba dama suna hake da ita bace din don hjy bata da dama yanzu haka wani abin ta fada masu wanda zai sa suki yarinyar nan a ransu don halinta ne na sani.
Mamu tace idan ma ta fada masu ai kansu zai kare sheri dai kare ne maishi yaka bi tsakanina da kowa a gidan nan sai fatan alheri.
Gidan dai take son mu bar mata kota halin kaka shine take kokarin daga min hankali dana yayana.
Dan dariya mara sauti yayi yace yanzu kan ai sai dai ita tabar gidan idan batayi hankali ba don kiris ya rage tsakaninta da Alh yanzu.
Itako abinda Umar ya aikata bai isheta tunane ba gaba dayan su basu da tunane nake gani mamu tace abinda nake son ka gane ke nan.
Ace kishi har da yara a ciki yaran ma maza da suka san ciwon kansu haka ai ko kaga akwai aiki a gaba ke nan.
Ta kalli fauziya tana fadin jeki kira masa anty ku kice ga yayan ku nan Ahmed ya zo dubata.
Fauziya ta mike da sauri zuwa dakin mu ta samu ina barci ta shiga tayar dani daga barcin na bude ido take fada min anty yaya Ahmed yazo gaida ke wai inji mamu.
Sai da nan danyi mintu a kwance na dago da kyat daga saman gadon na sauko kasa na dauki dan gyalena dake gefe na yafa a kaina.
Na fito falon yana zaune yana fuskantar dakin dana ke fitowa daga ciki a ranshi ya ke fadin tsarki ya tabbata ga mahaliccin mu Allah daya halita wanan yarinyar.
Yaga na kara cika nayi mai kyau a fuskan shi na kara cika nayi bul bul dani fatan jikina ya goge yanzu yayi kyau sosai ba kamar yadda nazo gatin ba.
Na koma kamar a tabani jini ya fito saboda gogewan da fatana yayi ga zanen lalen da akai min na sallah wanda ya kara kawata kafana da hannuwa ya fito radau dashi.
Ina dago kai muka hada ido dashi nayi saurin kwantar da kaina kasa na karaso kujeran da mamu ke zaune na tsaya daga bayan ta ina gaida shi.
Gaba daya yaga na sauya mai a yadda ya sanni dana zo tunanen shi yana neman kwancewa a cikin dan kankanin lokaci.
Da kyat ya iya saita kanshi ya karba min gaisuwan da nake mashi yace Fatima yanzu Alh ke fada min kasuwa abinda ya faru dazun.
Ba ina fada maku tunda suka zo gatin nan kuyi taka tsamtsan dasu ba na dan bata fuskana nace ban san suna tafe bani Aisha ce ta biyo ni da gudu sai naci karo dashi.
Yace barsu da Allah ai suma suna da kanne mata ko ina dai bai maki ciwo yanzu ko nace kaina dai ke ciwo sai fuskata dayayi min nauyi dazun yanzun kuma naji ya rage dana tashi.
Duk abinda muke mamu tana zaune tana jin mu sai can tace banace kisha magani ba kafin ki kwanta.
Na sha na bata amsa a takaice a daidai lokacin da Ahmed ke dagawa yana fadin zan koma hjy Allah ya tsare gaba adaiyi hakkuri don Allah watarana sai labari insha Allahu.
Tace nagode Ahmed sannu da kokari yace haba ba komai wallahi danaji ne nace ai barin zo in duba ta idan ba matsala.
Yana fadin haka ya fita har yakai kofa ya kira fauziya yana fadin kuzo in baku goron sallah ku ko ban samu shigowa na baku ba yaran suka bishi sai gasu sun dawo da kudi zaikai dubu goma a hannun su suna murna ya bamu don yace su raba har dani.