SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:57 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA HAIYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS ALLAH ????
Kawu ya maida duban shi ga baban nasa yace shike nan baba na yafe masa tunda kazo da kanka sai dai nima ina da uzurina akan hakan daya aikata bada sanina ba.
Gaba daya kowa ya kallo kawu da kyau a falon ana sauraren irin hukuncin da zai yankewa umar din.
Malam Nuhu yace kana da daman yin ko maynene a kansa matukar dai zaka yafe masa har cikin ranka idan kuma naka uxurin bai sabawa shari,a ba.
Kawu ya dan girgiza kai yace har yanzu akan koyi da addinin da kuka tarbiyarta dani nake baba.
Sai tsohon ya kada kai alaman gamsuwa da maganan dan nasa yace kai muke saurare dana.
Kawu yace ina son duk wanda ke falon nan ya sheda kai balarabe da sulaiman ku sani ko bayan raina idan na, idan ba ayi abinda na bada umurni ba ban yafe maku ba.
Gaba daya sukace subbahanallahi har abin yakai can yaya wanan wani irin hukunci ne mai tsauri kake shirin yankewa akan yaron nan ?
Kawu ya dan yi murmushi yace bashi kadai ba baba dukkan su ne abin ya shafa tunda haka suke so gareni.
Hakan kuma naga yafi dacewa ga wanda bai dauki iyayyen shi da zumunci da muhinmanci ba a rayuwan shi.
Jin yace dukkan su yasa gaba dayan su har mahaifiyar su suka kara mayar da hankalinsu wurin shi sosai.
Yace ke kuma jummai kafin in fadi hukuncin nawa ina son kowa nan ya sheda cewa duk kika kawo min wani izgili a cikin magana ta zai iya kaimu ga sakin auren ki wallahi.
Gaba daya zufa ya gama jikasu a inda suke zaune don fargaba da rikicin da suke fuskanta daga mahaifin nasu ga tsatsauran kalamin dayayi akan mahaifiyar su kuma.
Bai damuba da abinda sauran yan uwan shi ke fadi sai takardan da ya ciro daga Aljihun shi yayi rubuto a cikin sa kamar haka.
Rukkaiya, Aisha, fatima a ruwa. Ya dun kule su wuri daya ya watsa a tsakiyan falon tare da duban yayan nada yace kowan ku ya zabi daya duk wanda mutum ya dauka shine zabinsa a gurin Allah .
Allah kuma ya albarkaci auren har zurian mutum yasa masa albarka da gamawa da duniya lafiya ga baki dayan ku yana fadin haka ya juya yana gyara zaman shi a hankali.
Duk falon akai tsit ba wanda ya iya motsawa a cikin su sai gumin dake fetso masu a lokacin duk sun fita a cikin hayacin su ga baki dayan su.
Kallon kallo aka fara a tsakanin su kowa nawa dan uwa alaman ya fara dauka sai dai dukan su sun kasa.
Hjy jummai da ta kusa fashewa a zaune tace baba nima ina da magana don bashi kadai ke da hakki akan yara nan ba nima ina da hakkina don lokacin da nayi goyon abina nashi damu idone kawai.
Subbahanallahi jummai wanan wani irin magana ne kike sakewa haka da girman ki da shekarun ki kawu dai murmushi yayi yana kallon ta.
Tace dole inyi magana don nima ina da hakki sosai a kansu ya manta lokacin da nake wahala da abina lokacin da kowa ya saka min ido dasu sai yanzu ne zai kawo min wanan sharadin nasa.
Mama please umar yace yana hade hannuwan sa alaman yana rokonta tayi shiru don Allah sai kawu yace nina gama yanke hukunci na akan su don yayana ne idan kuma suna da wani uban bani ba yau ta fada min.
Ku bar wanan zancen don Allah ayi abinda ke gaban mu mama hadiye dake gefe ta fadi cikin damuwa da abinda ke wakana a falon.
Habbib ne ne cikin zafin rai ya mika hannu ya dauki takardan daya ya rike a hannun shi ganin haka shima Aliyu ya dauki nasa ya rike a hannun shi shima sai Umar din daya dauki na karshe a kasalance shima ya jinke yana runtse idanuwan shi a hankali.
Baba Nuhu yace bissimillan ku ku bude mana muji abinda kowa ya dauka a cikin ku wanan hukuncin na mahaifin ku yana da kyau matuka don nasa Sani bai aikata abinda bashi ba.
A sanyaye kowan su ya fara bude takardan a hankali suna dago kai ga abinda idanuwan su ya gane masu cikin takardan lokaci daya.
Banda umar da tunda ya duka bai dago ido ya kalli kowa ba bai ma san a inda yake zaune ba alokacin.
Amma dai tayi mutuwar zaune a inda take bata sanda wanan irin hukuncin da dan nata zai dauka ga diyan shi ba da ta dauki mataki tun farko kada ya soma sai dai yanzu bakin alkalami ya bushe ko don ya zantar da abinda yake gani shine mafita a gare shi.
Da kyar Amma ta iya budan baki tace sai ku fada muna abinda ke ciki don mu bamu sanda wanan hukuncin nasa ba don baiyi shawara da kowa ba kafin ya yanke.
Kawu yace hajiya ki gafarce ni don suma ba shawara suke damu ba idan zasu aikata abinda sukai niyar yi.
Tace baka ganin su akwai kurciya a tare dasune yace shiyasa nayi aikin basira a kan su hajiyan mu nima.
Kallon umar da kansa ke sunkuye tayi don shine damuwanta tace sadauki may ke a cikin takardan naka kai ?
Maimakon ya bata amsa sai ya kara dunkule takardan a hannun shi yana kakaro murmushin dole a fuskanshi kawai.
Habbibulah fada muna naka don kai naga namijin gaske ne dama soja kaje da wanan zuciyar taka mara imani kawai.
Ya harare ta kawai yana sauke ajiyan zuciya da karfi baba bala yace may ke a takardan naka dana ?
Yace wai Rukkaiya balarabe aka rubuta kawai a cikin karfin hali da dakewa yake maganan shi yana kallon kawu bala kai tsaye .
Kawu bala ya juya gurin sauran Aliyu shima cikin karfin hali a kasalance yace Aishan hadiye na gani rubuce.
Kai fa baba na malam Nuhu ya tambaye shi kai ya dago a hankali ya kalli tsohon tare da nuna mai takardan hannun shi ba tare daya furta komai ba.
Sai Aliyu dake kusa dashi ne ya yi saurin karba yana fadin Fatima A ruwa.
Ba umar ba duk wanda ke falon Amma a lokacin sai da ya kalli inda kawu yake zaune da sauri yayin da hjy jummai ta mike tana fadin wallahi ban yarda da wanan hadin in har zan yarda dana kowa banda wanan hadin.
Ina sam wallahi ba acikin jini ba wallahi kowa ido ya zuba mata da gani kasan bata a cikin hayacin ta sai malam Nuhu ne ke kokarin fadin haba hjy ki kwantar da hankalin ki kina sane da irin hukucin da Sani ya dora maki a wanan maganan .
Da sauri Umar yace mama please ki bar zancen nan a haka Allah yasa haka yafi muna alheri nasan nayi kuskure ina mai kara rokon ku ku yafe min don Allah don ni na jawo maku wanan rigima don Allah ku yafe mun.
Yana fadin haka ya mike zai fita malam Nuhu yace dashi dawo ka zauna babana bamu gama da ku ba ai don bai gama bayanin shi akan takardun da kuka dauka.
A sanyaye ya dawo ya zauna inda ya tashi da farko ya dukar da kanshi kasa bai san inda yake ba a lokacin sai tunanen da yake a cikin ranshi.
Yana raya waye fatima a ruwa waye ita da har daddy ya yanke wanan hukuncin da ita gashi yaji mama na fadin ko ta yarda da na kowa bata yarda da nasa hadin ba.
Aruwa ya maimaita sunan a zuciyar shi da sauri ya dago kai yana dan duban kowa a falon don tuna mai sunan da yayi cikin gidan.
Babana yaya naga kamar kuma kana da magana a bakin ka da sauri ya dan dukar da kanshi kasa tare da fadin ba komai.
Alh sani malam Nuhu ya dan kalla yace da sauran bayani ke nan ko ka gama hukuncin naka ?
Kawu ya dan duka a cikin ladabi ga tsohon yace baba sauran bayani shine sai mun zauna da yan uwana mun tsayar da magana yaushe ya kamata a daura auren ?
A lokacin kuma na samu iyayyen ita fatima nayi masu magana zuwa lokacin da yaran zasu kare karatun su sai ai bukin gaba daya.
Idan kuma ta Allah ta kasance a gare ni ga yan uwana nan su sheda ko bayan raina idan ba , ayi abinda nabar wasiya ba ban yafe ma duk wanda ya daga zance na ba ni shine bayani na yanzu.
Malam Nuhu yace alhamdullahi duk kowa nan yaji bayanin dan uwan ku akan yayan ku sai dai kafin in tashi zanso nima inji yaran daga inda suke.
Kawu yace ba wasu yara bane na waje dukkan su yaran gidane babu bare a cikin su fadin haka da kawu yayi yasa hjy da yaran ta kallo shi a lokaci daya.
Yace ta wajen shi habbib yar wurin balarabe ne gashi nan sai yar gurin hadiya gata da Aliyu ya dauka dayan kuma wanan yarinyar ne da nake riko yar wurin Maimuna yar mutanen bauchi dake nan gidan.
Kai daga malam Nuhu har kawu balarabe suka girgiza don jin irin danyen hukuncin da ya yake ga kuma sharadin daya kidanya masu akai.
Amma dake zaune wani irin farin ciki take jin ya lulube gaba daya don wanan abin yai mata dadi sosai a ranta.
Malam Nuhu yace Alhamdullahi yanzun abinda ya rage ina son tsakanin ku da maidakin ka ku sulhunta junan ku ku yafe ma juna a zauna lafiya a tsakanin ku.
Don kwanciyan hankalin ku a yanzu shine fatin cikin yayan ku da gaba daya family mu.
Kawu Sani yace ni ban rike ta ba muddin ana son a zauna lafiya kada wanda ya sabawa maganata don haka a kiyayye gaba.
Zuciyar hjy jummai data kawo iya wuya tace baba ni sam ban yarda da zancen hada zuria da maimuna ba da Alh yayi mun .
Yarinyat nan fa yar agolan gidan nan ce marasa asali da rashin tarbiyan tazo muna sai lokacin Amma ta kara magana a wurin tace.
Haba Jummai idan hakali ya bace hankali ke nemo shi don haka kada kiwa yar nan sheri ki masu fatan alheri ga abin nan da aka hada.
Ta kai iya kololowa wurin sukuwa nan ta botse tana fadin ita saman kawu bai mata adaLci a nan.
Taro dai ya watse da addua bayan sun samu sun lalabata tabar gurin hankali a tashe kowa ya kama gaban shi bayan fitan yaran suka kara tautaunawa akan matsalan za a bar zancen iyasu yasu yasun su har lokaci yakai na buki.