SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Daga uwar har yaran nata da suka biyo ta daki banda umar da kai tsaye fita yayi daga gidan baki daya don yana son ya kadaice a lokacin.
Suna shiga haka suka koma kamar mahaukata shi habbib nashi ya kaiwa kujaran da yake tsaye a gaban shi.
Aliyu ko tunda ya zauna ya dafe kai bai dago ba har tsawon wani lokaci hjy tun da take daga ita har su basu taba shiga irin wanan halin ba.
Kuma hakan ya faru ne sakamakon irin hukuncin da kawu din ya yankewa yaran nashi suna ganin ha,incin akai masu.
Ganin habbib zaiwa kansa illa tace ya zauna su neme mafita su dan bata time tasan abinda zatayi nan gaba kan maganan.
Hanyar fita daga falon habbib ya nufa uwar ta kalloshi da sauri tana fadin ina zaka kuma ka zauna mana muyi magana ina shi yayan naku ya tafi ?
Hannu habbib ya iya daga mata kawai ya fice ta bishi da kallon tausayi tana kada kai cikin takaici.
Tasan lalai yau ran yan mazan nata ya baci ga ba dayan su su uku ta rasa wanda zata fara dashi don ita duk zabin da akai masu din bai gamshe ta ba ga baki dayan su.
Can suna zaune shiru ta sake dago kai ta dan kalli Aliyu tana fadin ina yayan ku ya tafi ?
Kasa bata amsa yayi da magana sai inkiyan da yai mata da hannun shi na yana waje.
Can shima ya mike yana fadin wallahi mama imposible ina imposible yana mai girgiza kanshi hadi da fara tafiya zai bar falon shi ma.
Ganin yaran zasu salwance mata yasa ta daga waya ta kira sisters din ta da suke uwa daya uba daya su biyu tana fadin suzo gidan ta akwai matsala babba dasu.
Tana zaune zurun ita daya a shiyanta don su salma sun fita zuwa islamiya tun four na yamma.
Shigowan yan uwan nata a gigice yasa ta dan jin sanyi dukkan su suna a rude suke tambayan may ke faruwa ne wai ta kirasu haka don har magariba yayi a lokacin.
Dama na fada maku akwai asiri yanzu tsakanina da Alh har diyana asiri ya shafe su a gidan nan.
Wai yaran nan Alh zai yankewa tukwaici don kawai laifin babawo gare shi har ya yanke hukuncin hada su auren gida gaba dayan su.
Da sauri cikin mamaki suke hada baki auren gida dawa yau akewa da namiji wani auren hadi yanzu ?
Dama abinda nakewa gudu ke nan da dawowan yaran nan kasan nan ke nan yanzun an sihirce shi kan mu gaba daya.
Wai kamar yaran nan Alh zai dauko diyan yan uwan shi yace a dole su zasu aura wai dan rainin wayau da son kai irin nasu har da yar agolan nan yar wurin maimuna yasaka.
Gaba daya sukace ina wanan tsarin ya fitowa Alh haka kuma yanzu wa ya saura yin wanan akidan hadin irin aure gida din nan ?
Wanan abin baiyi ba gaskiya da sake a cikin maganan nan dole a zauna a duba wai ma yaya hakan har ya faru ne wai ?
Hjy tayi dan murmushin takaici ta girgiza kanta tare da fadin don kawai wanan auren da yaron nan yayi a can bada sanin mu ba duk ya kawo hakan.
Yaran da suka waye idan su ya bude yan mata tsalatsala kyawawa son kowa kin wanda ya rasa suke rubibin su wai zai dauko wasu kwailan diyan su ya hada su dasu.
Yanzun Anty ba wanan ba kamata yayi ace an samu mafita tun wuri kafin wana magana yai nisa ya lalace a dauki matakin hana wanan abu faruwa.
Tace waini abin haushi a gare ni idan ma aure yake son suyi a nan ya basu dama da zasu diba yan mata da kansu da suke ke suka waye na gwadawa duniya mana.
Kallon ta juna sukayi a fakaice don a zaton su zatace a cikin yayan su don ko wacen su tana da yan mata tsala tsala dasu ke son yan uwan nasu tun dawowan su kasan da suka gansu suke damun iyayyen su da zancen su.
Sun kai wani lokaci suna kulawa suna kwancewa a tsakanin har karshe suka aje maganan zasu zauna da kawu akan maganan wanan hadin a canza lale.
Dukkan su ranan basu kwana a gidan mahaifin nasu ba kowa hotel ya kama ya kwana a can don shi umar yana barin gidan kai tsaye motar shi daya ke amfani da ita a kano da tunkan yazo yasa a bokin shi ya saya mai mota uku daya a kano daya lagos da Abuja don yayi zirga zirga dasu idan ya zo.
Ya koma hotel din daya kama na kwanaki ya shige dakin shi ya kulle kanshi don ya kawar da tunane wayan merry ya kira yaji lafiyan ta dana baby su.
Tana dauka ta fara mai kuka ita ba zata iya jure rashin su a kusa dasu ba don haka zata shigo Nigeria ne idan ma yana tunanen komawa can ne da zama ta yarda su zauna nan tare yanzu a inda take ganin sa kulun.
Ciki tsigan lalashi ya samu ya lalashe ta akan ta saurara masa karshen wata yana tafe insha Allahu da haka ya samu ya rarashe ta bar kukan da take mai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:57 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA YAHHYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS, , , , , ,
Kasance yau zamu koma makaranta ranan farko na wanan time din yasa bamuyi wani sakkon fitowa da safe ba kwarai sai dai duk da hakan sai da muka tsaya jiran su salma da kannin ta a bakin motar.
Don yau driver zai sauke mu gaba dayan mu don mun dade bamu je makaranta tare dasu ba mamu ce ke kaimu ganin haka sai hjy maryam itama take kai yaran ta hakan ya rage muna fitina a tsakanin mu yanzu.
Sai dai ko mun hadu ba wani shiri ake ko gaisawa ba sai dai kowa ya wuce ba tare da ya kula dan uwan shi ba.
Yau ma tana ganin mu ta wani bata rai sosai sai da kowa ya shiga ta zauna taja tsuki tare da fadin in dai da kwadai da wullakanci ai .
Nafisa ta karbe da fadin rashin zuciya ko kare bai jan mai shi haka kawai don anga haske a cusa kai a inda ba kwar jini.
Salma tace komai matar mutum kwalelen shi dai don bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane.
Wai ke salma wa kike jefawa wanan arashin haka ke baki so dai a zauna lafiya yanzu kuma may akai maku don Allah kuke sake wanan maganan haka ?
Dallah malama rufe mun baki da wanda ya tsargu dashi mukeyi idan kin tsargu dake muke Aisha .
Aisha tace wani aiko kunyi wa banza indai nice don ban san kunayi ba ni indan da sabo na saba da wanan halin naki ai.
Kamar ban cikin motar don yanzu ni abinsu ma dariya da haushi yake ban ko kallo basu isheni ba idan suna haukan su rabona da tanka su tun ranan da sukai min gori da agola gaban yannen su da sallah wani abu bai kara shiga tsakanina dasu ba.
Yau ma na sha alwashin har mu dawo ba zan kula su ba saboda hudubar da mamu take min ko yaushe a gidan a kansu.
Har muka sauke su Aisha da zata fita tace Allah ya hadaki da daidai dake ta fita suka bita da zagi da kushewa hallitanta sai dai ni banga wani abin kushewa ba a gurin ta da suke zagi.
Nasan don in tankane Nafisa tace mu za a gwadawa fari mutum kamar zabaya fari ma ai idan yayi yawa cutane ake wani zuzuta mutum har ana wani hadawa da kalar dangi.
Mota na tsayawa taki fitowa sai data batawa mutane lokaci ta sauka muka samu muka fito mu dake baya.
A nan na barsu suna yan dararakun su naja hannun kanne na muka nufi hanyar ajin su.
Tun ranan da akai case din nan kowan su ke yar boya tsakanin su da kawu su a dole suna fushi da kawu din don yai masu ba daidai ba don da kyat mahaifiyar su da yan uwanta suka shawo kan su don sunce su zasu koma ne abinsu inda suka fito.
Shikan umar ma tun ranan baizo gidan ba sai yau yake niyar zuwa gidan don mahaifiyar su dake nacin kiranshi a waya.
Bakin wandon jeas ne a jikin shi sai wata bakar riga mai guntun hannu da anineiya har kasan riga rigan ba wani sauka sosai tayi masa ba a jikin shi.
Ya fito fes dashi a cikin kayan kana ganin sa kaga wayayyen namiji tashin turai wanda boko ya gama ratsa ko ina nasa sosai.
A waje ya parker motar shi sai dai kafin ya fito sai daga motar ya kara gwada layin merry wace tun safe yake neman layin ta bai samu ba zai iya cewa rabon shi da suyi magana kwana uku zuwa hudu ke nan lokacin.
A kan idon shi motar kawu ta dawo ta shiga gidan yana mamakin mai ya dawo da kawu gida wanan lokacin haka.
Ganin layin nata yaki shiga ya fito daga motar ya tunkari cikin gidan nasu inda ya samu kawu a tsaye bakin mota shida Ahmed yana duba wani takarda.
Sai da yazo dab da mahaifin nasa ya tsuguna yana gaida shi a cikin ladabi kawu ya dan dago kai ya amsa ba yabo ba fallasa ya mayar da hankalin shi ga abinda yakeyi.
Sun gaisa da Ahmed sama sama kamar yadda suka saba gaisu ba wani sabo saidai sanayya kawai daga haka ya shige part din mahaifiyar shi direct inda ya samu su habbib a zaune.
Fuskan shi babu annuri ko kadan a cikin sa ya samu wuri ya zauna yan uwan na gaida shi sama sama don damuwan da suke ciki.
Ya juya wurin mahaifiyar su yana gaida ita da wuni saboda lokacin anyi azahar ko ta amsa tana kallon shi tace babawo fushi kake da kowa ke nan a gidan nan daki shigowa tun ranan da akai zaman nan da mahaifin ku.
Don may zaka daura muna laifin da muma ya shafemu yanzu duk a dalilin ka.
Ya dafe kai yana sauraren ta ya kulu matuka ji yake kamar ya hadiye ranshi don kawai ya yi aure zaisa daddy ya yanke masu wanan iron hukuncin.
Ai koma auren ne sai a barsu su zaba a nan gida tunda akwai yan mata da zasu dace dasu amma sai kawai daddy ya yanke hukuncin da shi yake gani daidai ne a gurin.
Da kyat ya iya buda baki bayan ya hadiye wani miyau mai daci daya tsaya mai a bako yace .
Mama ya dace ace daddy yayi shawara damu ko ke kafin ya yankr muna wanan hukunci.
Habbib yace ni tuni dana bar kasan nan ko badon mama da suka tsayar dani ba kamata za ayiwa auren hadi na gida why daddy zai muna haka kamar bai san darajan mu ba.
Duk naku bai ban haushi ba kamar na babawo don may zai hada zuria ta dana wanan makiran yarinyar da bata kaunan cigabana a gidan nan ko kadan.
Tana bakin ciki da hassada da komai nawa kuma yau yarta ce Alh ke kokarin jefawa a cikin zuriata a gidan nan duk yakan kauna ai bayan wanan hadin dayayi ne.
Mama ki daina fada haka akan maimuna mu fuskaci matsalan dake gaban mu yanzu don ni a iya nazarina banga wani rashin da a da take maku a gidan nan ba.
Ni matsalata yar maimuna za ace waini na aura yau dan dama dama ace Aliyu ne ko shi habbib din daya daga cikin sune ya zabi yarinyar mama ina zanje da yar cikina sai dai idan rainon ta zanyi .
Babawo ka ban mamaki da wanan maganar taka yanzu kai baka damu da koma bayan da yarinyar nan take jawo muna ba a gidan nan kilama fa da hadin bakin ta a ka kitsa
komai da Alh ya zartan don kawai taga ta kuntatamin.
Yasa tace ya jefa yarta a gunka dama da gaiya ya aikata hakan yana sane ya jefa ma takardan wurin ka don ka dauka.
Mama ba hakana nake nufi ba ke yadda kike nufin mu dauki wani mataki a kanta maimuna mu bata nuna muna wani hali na rashin dacewa a gare mu ko a gareki.
Gaskiya ya fada mama inji Aliyu dake kallon su ni yanzu sam ban ganin laifin ta kamar wana hjy maryam din dake da fuska biyu wa mutane.
Yanzun mama ina kuka aje magana da daddy don naji shi bros har yana wani magana wai dama mune da nasa zaben, ma,ana ya yarda shi da hukuncin daddy din akan mu.
Habbib kasan abinda rashin biyayan mu ga daddy zai haifar akan mahaifiyar mu kana dai jin abinda daddy ya fada ranan kan mama.
So kaga maganan wai bama so ma bai taso ba agaremu ya zama dole muyi biyayya a furin daddy tunda mahaifin mu ne shi yana da ikon komai a kan mu.
Kai ka rufe mun baki kai ya zama na dole kai masa biyayya ba dai ni ba akan maganan da wata mace tasashi ya aikata har kake tunkaho akan hakan.
Bari kaji muddin ina raye wanan auren naka da yarinyar nan ba zai taba yuyuwa ba a tsakanin ku.
Mama kibar fadin haka kinji irin abinda daddy ya fada a kanki gaskiyar bros ne zamuyi biyayya ga daddy kodo farin cikin ki a gidan nan Aliyu ke magana.
Kai rufe mun baki ku may kuka sani a zaman kishi idan doni zayi wanan auren ban yarde masa yayi shi ba.
Idan kuma har Alh yaci galaba a kaina ya matsa akai wanan hadin a tsakanin ku ban yafe ka kula wanan yar mara asalin kwarai ba.
May akayi akai maimuna mutumiyar banza munafuka mara asali da ita may ke ga maimuna balle yarta a duniya irin tsiya da minafunci.
Kiyi hakkuri mama ya zama dole muyi biyayya a gare ku batace masa komai ba tabarshi yana a tsaka mai wuya a lokacin.
Wayan shi dake hannun sa tayi kara ya dauka yana duba bamuwar nomba layin mtn na Nigeria yaga bakuwar nomba yana mamaki har wayan ya katse bai dauka ba.
Ba a jima ba aka sake kiran shi ya daga da tsuki yana who is on the line ?
Omar i am in Nigeria right now in kano inside your family compound where are you ?
What ya fada a razane yana dagawa har saida kowa ya zabura a falon a tare suke hada baki may ke faruwa bros hankalinsu a gare shi.
Akasale ya kalle su ya fara tafiya yana fadin wai merry ce tazo.
Gaba daya suka mike tsaye suna mara mai baya zuwa waje inda tace take sai dai ganin Alh sani tare da Ahmed tsaye a waje ya dakatar dasu daga saurin da sukeyi su fito din.
Kawu da Ahmed kewa bayanin sakon daya tura mai na kudi sukayi aune da wasu mata biyu suna shigowa gidan.
Ko wace tana saye da dan karamin buje iya cinya ganin yanayin su kawai basai ka tambaya daga wani akida suke ba.
Don kamannin su ya gama nuna daga inda suka fito saidai yanayin jikin su ya nuna jindadi da kulawa a gare su sosai.
Dayance tace wa kawu hyy a cikin dan dags hannu kawu dake masu kallon mamakin abinda ya kawo su gidan shi don shi baida wani alaka da irun su ya kasa amsa mata don bai iya kallon su kamar a tsirara suke yake ganin su.
Ahmed ne ya karba yace are you looking for someone here ?
Yeah we looking for Omar dis his wife merry tana nuna mai merry din dake tsaye tana dan murmushin tana kokarin gaida kawu din.
Umar da yan uwanshi suka karaso wurin da sauri yana fadin merry how dear you come here ?
What bout you here ?
Suna ganin shi dayan ta miko mai hannu tana fadin O Omar so you are around nice to meet you ta miko mai hannu ya rike suka dan rugumay juna ya dan bubuga mata baya kadan ya sake ta ya juya wurin merry din ya rike mata hannu sukai kamar yadda sukayi dana farkon sai dai ita bata sakeshi ba sai ta makale a jikin shi.
Kawu dake tsaye ya daskare a wuri daya ga wani irin malolon bakin ciki yana taso mashi.
Sai can umar din ya tuna da daddy su na gurin ya saketa bayan sun gama tabaran su ya gama shafan cikin jiki ta a gaban daddy ya juyo yana fadin.
Kawu wanan ce matana da na aura a can merry ya juya wurin ta yana fadin merry meet my Dad dan my brothers.
Tace wanderfull daddy nice to meet you tana dan rusunawa kadan da sauri kawu ya kawar da kanshi gare su ba tare da ya amsa ba
Hjy ta fito ya nuna ma merry mahaifiyar shi a cikin yanayin rashin jin dadin abinda dady yayiwa merry din na nuna mata kyama a gaban ta.
Hjy kan ta dan washe karan kada ham tana karewa merry din kallon mamakin abinda yaja danta a ga wanan bakar arniyar dake gaban su yanzu.
Ganin su a tsaye waje yasa hjy cewa ku shigo daga ciki da sauri kawu ya juyo yana fadin kada ki soma ki shiga min gida.
Ya fadi a tsawace gaba dayan su dake wurin sai da suka razana don irin tsawan daya daka a lokacin.
Ran hjy jummai ya baci itama tace don may zaka hana ta shiga gidan bayan kasan bamuwar danka ce gata dauke da jinin ka a jiki.
Wanan hayaniyae da suke yi ya jawo hankalin sauran mutanen gidan gare su suka fito waje da gudu.
Jini na fa kikace jummai a ina badai a jikin wanan kafirar data shigo min gida haka tsiraci waje ba tir da wanan rayuwan da danki ya zabawa kanshi.
Yaya gaskiya hjy ta fada idan baka raga mata don komai ba zaka raga mata ko don cikin jinin mu dake kike jikin ta ai balle ba a kore bako don da dalili tazo nan din da bata da dalili saita wuce ko kallon gidan nan ba zatayi ba ai.
Ke ke maimuna ni kike son koyawa ilimi ko may a gidan nan har ke kin isa in kafa doka kice zaki min nasiha.