NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:35 – ????????????: SARKA MAI , , , , , , , , ,

4️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

SAKON GAISUWA DA FATAN ALHERI HAR KULLUN GARE KU MASOYANA DA BAKU LISSAFUWA A GARENI DA MA WA YANDA BAN SAN DA SU BA NAGODE NAGODE UBANGIJI I A SADAMU DA RAHAMOMIN SA AMIN ALLAH YA BIYA MUNA BUKATUN MU NA ALHERI.

MASU FADON ZAINAB NADA NAKASA DA GIRMAN KAI RASHIN SANI NE YASA KUKE DAUKANA HAKAN AMMA INA MAI BAKU HAKKURI GA DAUKAN DA KUKAI MIN DIN.
YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A NATSE BA TARE DA DAUKAN NAUYI A KANKI BA MALAMAI SIN SUN CE NAUYIN AMMA KADAN SAI YA HANAWA MUTUM NASARAN SHI ALLAH YASA MU DACE.
DARI UKU NE KACAL KATI KO TA BANK ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 2254380105 ALLAH YA BADA IKON BIYA AMIN

Idan nace maku masu jin dadin wanan tsari da tsohuwar gidan ta kafa yau sunfi wacce akai case din domi ta sun fi yawa a gidan don hjy maryam tafi kowa farin ciki da wanan tsarin da akayi masu.
Hjy maimuna bata so wanan hukuncin ya fado a sanadin ta ba don sanin halin waye hjy jummai da riko a ranta sai dai batai wani damuwa ba iya kokarin watsar da zancen da tayi a ranta taci gaba da harkokinta.
Bayan kwana biyu da yin wanan maganan mota dake kawo masu kayan masarufi ya tsaya a kofan gidan tare da yaron shagon Alh sani babban yaron shi dake kula da al,amuran komai na Alhajin daya shafi shago da gida da duk wani al,amuran daya shafi rayuwan Alh din.
Ahmed yaro ne mai rikon ammana da sanin ya kamata sosai shi din ba wani hadi tsakanin shi da Alh sani haduwa ce ta irin gamon jinin nan ya hadasu tun yana yaro yana yawon almajiranci suka hade da Alhaji a kofan gidan shi.
Yayo bara bai samu ba ya dawo kofan gidan Alh sani ya kwanta ga hadari ya gama gari a lokacin ruwa na barazanar saukowa a ko wani lokaci a garin .
Hakan yai daidai da dawowan Alh sani daga kasuwa don ganin hadarin da yayi suka rufe shago don sun san idan ruwa ya gwauce wanan hadarin sai yadda hali yayi a lokacin .
Yana sauri zai shiga gidane ya ankara da yaron a waje kamar ya shige ya kyale shi sai kuma yanayin yaron ya bashi tausayi sosai ya dawo baya yana tambayan shi komay yake a nan ?
A ciki yanayi damuwa yaron ke fada mai yayi bara bai samu bane ga hadari ya dawo nan ya fake tausayi shi ya kara shiga ran Alh sani kaaancewan shi mutum mai tausayawa na kasa dashi.
Sai yaji ba zai iya barin yaron a yanayin wanan hadarin da ya gama hade gari bai dace ya bar wanan yaron a waje haka ba sai ya umurce shi da ya biyo bayan shi zuwa ciki.
Hjy jummai na ganin shi shigowa da yaro a bayan shi ga yaron bagidaje dashi kana ganin shi kasan almajirine don yana dauke da dan kwanon baran shi.
Nan ta hau fada don ko tariyan arziki ranan Alh bai samu ba a gurin ta sai fadan ina ya kwaso wanan yaron dake binshi a baya haka.
Dan murmushi Alh sani ya sauke a fuskan shi tare da fadin yanzun dai bashi abinci kafin ki fara tambayana zan shiga in fito sai in fada maki komai akan yaron.
Yana fadin haka ya shige ya barta da yaron a wurin tana binshi da harara mai nuna kiyayya a gare shi inda yaron ya sha jinin jikin shi da kallon da take aika mai din.
Cikin tsawa ta dubi yaron tare da fadin bace min da gani ni banda wani abincin baka daga ganin ka irin almajiran nan ne munafukai ka fake ka marairaicr mai kamar na kwarai ashe mayau dari.
Da wanan kazantar naka zai wani kwaso min kai har cikin falona haka kana wani irin bashi da tsami kazo ka kakkaba min keyan kuna almajirai iyayyen ku ma sin gaji daku a can suke turo ku cikin duniya da sunan almajiran ci.
Haba jummai wai mai yasa ke baki da tunane ne wai idan idon ki ya rufe ai ba yaron zakiwa fada ba nida na kwaso shi ya kamata kima fada yanzu.
Alh sani ne daya fito daga daki yake wanan maganan rai bace inda bai tsaya jin amsata ba ya tambayi abincin sa ta mike tana cika tana batsewa ta tafi dauko mai abincin nasa.
Zo nan yace wa yaron tare da tambyan sunan shi yaron ce dashi Amadu yace kace Ahmed kake mai babban suna samu wuri ka zauna kaci abinci idan ruwa ya tsaya sai ka wuce makaranta kaji.
Nan yaron ya samu wuri daga nesa ya dan tsugun na yana ma Alh sani godiya irin wanda almajirai kewa wanda ya kyautata masu sukaji dadi.
Lokacin ta fito dauke da tire din abincin data shiryawa maigidan ta nufo inda yake sai dai ganin shi tare da yaron yasa ta bata ranta sosai.
Sai da ta aje abincin ta samu wuri ta zauna tana kallon ikon Allah a cikin plate din da ta dora mai saman kayan don cin abincin shi ya fara zubawa da yawa ga mamakin hjy sai taga ya mikawa yaron abincin a cikin plate din.
Haba kaiko a cikin plate dinka ma zaka bashi gaskiya ya kawo kwanon shi a zuba mai kuma da ka kwashe abincin ka zuba mai kai wani zakaci yace .
Jummai ke na ai cin wanan yaro yafiye ma cin dani zanyi albarka baki sa wanda ya taimaki iri yara nan ba ga Allah shike da lada ciyarwa
Ko banza fa yaro na kowa ne don baka san abinda Allah zai mai dashi watarana ba kaima har ka more shi.
Yana ci yana mashi tambayoyi akan garin su yaron yana fada mai komai nasa har izon da yake sai da Alh sani ya tambayi yaro a karshe dai ya juya wuri hjy jummai yana mata nasiha aka taimako,
Bayan a gama ruwa ne yaro yace zai tafi sai godiya yake zabga masu akan taimako shi da sukayi din Alh sani bai barshi haka ba yasa hannun a aljihun shi ya ciro sabuwar naira dari yabawa yaron yare da fadi ya dinga zuwa kullun ana bashi abinci ba sai yaje bara ba.
Ran hjy jummai ya kara baci sosai da wanan sabon yaye yayen da miji ta ke kokarin mata don ita a rayuwanta bata iya daukan dawainiyar dan kowa.
Ai da iyayyen shi na son sa da ba zasu sako shi cikin duniya da niyar yin bara ba tunda akwai tsangaya a kowani gari ana karatu kuma.
Taso ta musa ya murtuke fuska tare da fadin umurni na baki na yin hakan har yaron ya gwauta ya sake kiran shi tare da fadin da karfe biyar nake dawowa gida.
Kullun zaka zo da safe kafin karfe tara ka karbi abin karyawan ka a nan gidan kaji Allah ya tsara muna ku a duk inda kuke ya karasa fadawa yaron.
Na gode Alh Allah ya biyaka da gidan Aljanna sarki da akaiwa ya sani Allah ya daukaka a cikin duniya dakai da zuri,an ka baki daya Allah ya kara maku soyayya dakai da matar ka.
Inda hjy Jummai take tsaye Alh sani ya kalla tare da fadj kinji cikin dan sake rai da adduan da yaro yayi masu tace ai yawan adduan kai yaiwa bani ba.
Alh sani yace in banda abinki idan addunan ta kamani aikema ya shafe ki don Allah jummai ina rokon ki arziki ki dinga sawa yaron nan abinci fisabillilah.
Sai da ta nisa tace naji amma kuma nima ya zama dole in har zan bashi abinci gidan nan sai yai min dan aiki shima a gidan nan.
Jummai wani irin aiki kuma wanan dan yaron zai iya maki kamar wanan in ba hali na wasu iyayye ba ai baici ace an barshi ya shigo duniya ba haka.
Don Allah ki jaye wanan zancen aikin ki bashi abinci saboda Allah kamar yadda na bukata kiyi din ba don ni ba sai saboda Allah.
Tace naji cikin wani irin murya dake nuna rashin jin dadi ta ga maganan mijin nata idan ba do son da takewa mijin nata ba da babu abinda zai sa ta dinga wahala da dan wata can.
Sai dai maganan bai wani shigeta ba don sai da ta dinga ba yaron aiki irin wanke wanke da shara tun yanayi tana maida shi ya sake har yazo ya gwane da aikin sosai daga nan kuma ta buge da bashi aikin wankin kayan ta da na yaran ta.
Amadu dan dogon yarone siriri dashi baki baida kauri sosai kana ganin shi kai kasan daga kauye ya fito sosai yazo kano almajiranci.
Don hakane aiki da hjy Jummai ke bashi a lokacin bai taba bata ran yaron tunda ya saba da aikin wahala tun a gida kuma shi yana samun abincin da zaici koda yaushe haka yasa ya fara murjewa jikin sa na kyau ya fara wayewa.
Tun bai san hanyar kasuwa shagon Alh sani ba har ya sani da ya fara wayo hjy tana aiken shi gurin Alh karbo wani abin indan tana bukata.
A ciki yan shekaru Amadu ya murje yayi gwanin ba sha,awa dashi saboda kula da yake samu a gidan Alh sani din.
Duk da yawan aikin da hajiya jummai ke bashi bai hana jikin shi ya nuna samun hutu a gare shi ba ga gorin da take mai wai yana da bakin cin tsiya ko yaya ta cika mai kwano da abinci zai cinyeshi tas idan an bashi sudi kuma jikina rawa yake karba.
Mahakurci mawadaci don hakkurin Ahmed bai baci ga banza ba lokacin da ya sauka iyayyen shi suka zo daukan shi ya gabatar dasu ga uwayen gidan nasa da yayi a nan kano.
Inda Alh sani yai murnan haduwa dasu har ya bukaci da su bar mai yaron a hannun shi yana son ya sakashi makarantar boko don ya samu karatun zamani.
Ganin yadda yaro nasu ke samun kulane a gidan yasa suka yarda da bukatan Alhaji sani di amma da sharadin zasu kaishi gida yaga iyayye shi mata daga baya zasu dawo dashi.
Har Alh sani ya debe rai ga dawowan Ahmed gare shi rana kwatsam sai gasu dashi da mahaifin shi da zasu zo har da dan tsaraban su na kauye suka zo mashi dasu.
Inda mahaifin nasa ya danka amanan dan nasa a hannun Alhaji sani din suka tafi bai barshi a gidan shi ba can gidan hjy Amma ya aje yaron don sanin halin maidakin nasa.
Inda Amma ta rike shi tsakani da Allah har yake jin sune yan uwansa na jini a jikin shi ya samu karatu gwargwado sannu a hankali ya fara harkan kasuwanci da Alhjin shi inda ya fara zama dan hannu ya murje yai kyau dashi ya zama dan gari.
Sai dai suna shan artabu da hjy jummai don ya kasance shi din mai hakkuri ne kamar uban gidan nasa yasa har ya cin ma bukatar shi a duniya.
Lokacin da ta farga da sanin Alh sani ya dora shi ga harkan kasuwancin sa ta nuna rashin yardanta ga hakan sosai sai dai ba yadda zatayine dole ta kawo ido tasa amma duk da hakan takan so bashi umurni wani lokaci yabi wani sa,in ya nuna mata hakan ba mai yuyuwa bane a gare shi.
Wanan ne dalilin da yasa har gobe take tsanan yaron da take ganin baida galihin da za a kaishi ga matayin da aka kaishi a yanzun a gidan yasa suke yar tsama dashi akoda yaushe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button