NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:03 – ????????????: ASSALAMU ALAIKUM JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH SADAMU DA ALHERUN SA AMIN ????

Hjy jummai dake zaune har lokacin tana fada dakin ta yaran ta kowa na harkan gaban shi don dun gaji da bata hakkuri taki yin shiru suka fita batun ta.
Kawu da shigowan shi daga masalaci ke nan ya na dan zagawa dakunan matan nasa ya fara da sashenta don itace babba a gidan idan ya gama sai yaje gun Amma itace karshe su dan taba hira ya dawo part din shi mai girki ta samay shi a can wanan zagayawan da yake a lokacin yakan ji korafin diyan shi da damuwan su.
Tun da ya tunkaro sashen yake jin muryan hjy tana masifa ya karasa shiga da sauri don ganewa idon shi da wanda take fadan.
Sai dai ga mamakin shi babu kowa a cikin yaran ta da alama ya nuna dashi take fada a lokacin wurin da take zaune ya diba yana fadin ke dawa ke fada haka muryan ki har waje ?
Yi tayi kamar bata ganshi ba a wurin taci gaba da fadan ta saida ya tambaye ta a tsawace tace.
Alh ina son ka tsawatawa maimuna ta fita harkata don ban shiga nata ba da zatai min kakagida don neman waje da sarakuwa na ta jira zuwan nata sarakan nan gaba.
Ya gyara tsayuwa yana fadin haba jummai wai ke may yasa baki hankaline klun yanzu may ya kawo wanan irin maganan don Allah ?
Yanzu ace wanan yarinyar sam bata son ma shigowa wurina sai dai taje gurin maimuna inba tasan abinda tayi ta rabani da ita bane.
A kan wanan kike wanan fadan haka don kawai an maki kara an karama sarakuwar ki sarakuwa ma kafira har kike wanan jidalin haka ba kunya a idon ki ?
Eh banyi mamaki don ka fadi hakan dama kai ba zaka taba hango illar hakan ai do ko mai maimuna tayi daidaine a gidan nan.
Ya girgiza kai yana fadin kaji matsalan ki ai indon wanan ne zanwa maimuna magana tafita harkan kafiran sararkuwar ki ina shike nan.
Duk da tasan ya gasa mata magana hakan bai hanata cewa daya fi ba haka kawai don munafunci ki shishigewa yarinya ke kinga wurin ci.
Fitowa Nafisa tana fadin daddy sannu da dawowa ya hana shi yin wani magana a cikin sakin fuska yace Nafisa an wuni lafiya ya karatu ?
Salma ma da lastborn suka fito suka gaida shi ya amsa tare da danyi raha da yaran ya fita zuwa part din hjy maryam dake zaune suna cin abinci da yaranta ga waya a hannunta tanayi.
Sun gaisa nan ma yadanyi hira dasu ikilima yai masu saida safe har yakai kofa yaji muryan hjy jummai tana fadin nikan Alh wai maina kashewa Umar ne har yau fa bai shigo nan ba balle ya kawo min matar shi mu gaisa.
Amma zai iya kaita wurin maimuna ko ni da wata manufa yake daukana a gidan nan ne.
Yace don wanan maganan kika tsayar dani maryam ki tambaye sa mana idan ya shigo tunda kina son shigowan su nan din ne.
Yasa kai ya fita yana jin zafin maganganun su duk akan abu daya wanda ba komai bane sai zalla kishi akan yar uwan zaman su din.
Zaune muke a kasa saman carpet muna cin abinci sai fauziya dake gefe daya tana fitina kan dan uwanta wai ya sha mata ruwa.
Yin sallaman shi yasa duk muka shiga cikin natsuwan mu tunkan ya karasa shigowa muma shiga gaida shi yana amsa muna hankalin shi yana kan fauziya dake kuka.
Yace mai akai mata take wanan kuka haka fitina kawai take ji mamu ta bashi amsa yace mutum na fitina babu dalili ina dan dariya nace kawu da ita da samir ne ke fada wai ya sha mata ruwa sai ya debo mata wani ruwan.
Yace fauziya baki son kuyi zumunci da dan uwan ki ko baki son ki bashi abinki idan kin girma shima ya baki nasa.
Kada kiyi rowa fauziya ke ba antyn shi bane ki kara ruwan yadda kowa zaisha ki kwashe ladan aikin ki ko baki son ladane ?
Ya tambaye ta yana kallon fuskanta mamu tace fitina da gangan takeyin shi don kawai ta azawa mutane tashin hankali niko yanzu dan banzan duka zan mata idan bata rabamu ba da kukan banzan nan.
Kawu ya duka ya rike hannun ta yana fadin a, a akan may zaki doketa gadon uwar ta jummai tayi mai rikicin gangan don jummai sarkace ko ba dalili sai tayi fada.
Aiko tayo mugun gado inji mamu tana dan ya mutse fuska yanzu na samay ta tana jidali tun ina waje nake jin harshen ta na shiga ina tambaya wai dake take fada.
Mamu tace subbahanallahi dani kuma may nayi mata ni dake nan yau zan iya cewa tun safe ma bamu hadu ba a gida nan da ita.
Yanzu dai tace in maki magana ki fita harkan sarakuwanta ki jira taki sarakuwan in su hussaini sunyi aure.
Wani irin gulolon bakin ciki ne ya ziyarci zuciyata lokaci guda tare da yiwa mamu gwai a raina da taba kafira fuska ga goron data samu a baya.
Itako mamu cewa tayi ikon Allah ni na dauka hakan karane a gare ta amma ba matsala zan kiyaye in Allah ya yarda .
Dayafi maki alheri don jummai bata san ya kamata ba ita sai abinda zuciyar ta ya anyana mata.
Allah yasa mufi karfin zuciyar mu mamu ta fada yace Amin ya juya gurina yana fadin yau fatima may aka karanto a islamiyan ne kafin in bashi amsa mamu tace yau basu shiga ba wai malam suna wani taro.
Nace kawu kayan islamiyan mu sun dake muna ranan har an dukemu kan hakan wai hijjab dina baikai kasa ba sosai.
Yace shine baki fada min ba yana kallon mamu tace da rigima take banace zan yanko masu yadi a dinka wani ba mantawa nakeyi wallahi.
Yace gobe insha Allahu za a kawo maku idan na fita yai muna saida safe ya bar part din wurin Amma ya nufa.
Sun dan dade da Amma suna hira ya koma part din shi inda mamu ta samay shi bayan ta tabbatar da na rufe part din.

Ammace zaune a falon ta tana taunan goro daya zama mata jaraban rayuwa idan tana ita kadai ta kama tauna ke nan har sai ta samu abokin hira ta dan tsagaita.

Nayi sallama na shigo ta dago tana kallo na yanayin ta kawai na duba nasan tana cikin dan damuwa ina kawai kwance nace kedawa da safen nan haka kuma Amma ?
Ni da dan uwanki ne mana yaro ka shige cikin gari kayi shiru haka ni tun zuwan wanan matar tashi ban gane kanshi ba.
Wani kallo nayi mata daga inda nake kwance nace kai Amma dai Amma din nan mutum da matar shi ya manta dake ne mana tunda matar shi tazo.
A dan hasale tace au haka zakiyi idan kinyi aure ki rike min majin nawa kada yazo inda nake.
Nace nikan mijina ma a ina zaki ganshi Amma balle ki dinga damun shi da mita baizo inda kike ba nifa Amma kilama dake zan tafi don kallon danaga tayi min na gyara magana ta da sauri.
Kamar an jefoshi dakin ni kaina saida nayi mamakin ganin shi a wanan lokacin da safe haka .
Amma tace ikon Allah kai kuma daga ina haka da safen nan muna maganan ka sai gaka kamar an jefo ka daga sama.
Sai lokacin ya kalli inda nake da sauri nace banice ke magana ba itakeyi ita kadai wallahi na fada a dan tsorace.
Dama an ce dake ake yanzu dai nake fada maki damuwa na kan rashin ganin shi kwana biyu.
Yace wallahi abubuwa ne sukai min yawa Amma yanzu ma na sauke merry church ne daga can na biyo nan mu gaisa.
Na mike don in basu wuri Amma ta kalleni tana fadin ina kuma zaki keda kika shigo yanzu shi gudu zaiyi kinji yace daga coci yake .
Allah da ka taro min wanan dan wai jininane yau da zuwa coci ni Amamatan da kaina ta karasa fadi a cikin takaici ban fasa yunkurin fitan da nake son yi naji tace zo ki mika mai abin karyawa don nasan bai karya ba yanzu haka.
Yace wallahi kuwa Amma kamar kin sani sai dai taje gin maimuna ta tambayo ta idan akwai kunu merry ke son ta sha.
Yi nayi kamar ban ji shi ba don kiran maimuna da yayi gatsau ba sakayawa ko kadan Amma tace baki ji ba wai ki je gun uwar ki ki samo masu kunu kin san ya zama mijin tace yanzu.
Dan baki na turo tare da fafin ai bansan ita yake nufi ba don naji yace maimuna kaji min ya da fitina A ruwa haka kike fa kamar tsohuwar mace.
Shi dai yana dakilan wayar shi bai dago kai ya kallemu ba balle yace yasan abinda mukeyi a falon.
Ina fita tace dashi haka ba kyau ka duba yar nan tayi fushi ga yadda kuke kiran uwarta gatsau ba ko sayawa ga bakin ku kamar ba wayayyu ba daku.
May zan kirata ya dago kai yana kallon Amma din da mamaki ?
Ta dai ci daraja biyu a wurin ka ko uku na farko matar ubankane na biyu sarakuwan ka nan gaba sai na uku ko kunki ko kunso kaunar ubanka ne .
Kai Amma ke da wani magana kike wallahi ni wanan duk bai a gabana yanzu abinda ya damay ni ya damay ni.
May kuma ya damay ka kaiko yace merry ta matsa sai mu koma gashi ban gama abinda ya kawo ni nan kasar ba ni ban san ya zanyi da ita ba , , ,
Kai tafi can hular mata har yaushe mace zata saka abinda baka tashi yi ba tare kukazo da zata matsama ko zata hanaka ganawa da yan uwan kane ?.
Kai da zaka dinga bata umurni zaka zauna tana baka umurni ko may ka zama namiji a cikin iyalin ka shine cikar kamalan magidanci a idon jama,a ba ya zauna mace na dorashi a hanya ba wanan akidar nasarane.
Lalai zama da tsoho wani lokaci babban ilimi ne yanzun dan zaman da yayi Amma ta bashi haske biyu da bai daukeshi komai ba a da.
Gaskiyar daddy da yace yana son ya dinga shigowa akalla sau uku ko biyu a shekara don shi yanzu yadda yake jin dadin kasancewa a kasar shi yana ganin abubuwan da ya kamata ayi naci gaba da irin tsarin rayuwan su daya baro a baya.
Na shigo da sallama dauke da flask a hannu na na aje a gaban shi tare da fadin wai tace tana lafiya, ?
Yace kamar baison bada amsa lafiya take na juya abina nafita daga falon Amma din.
Amma tace maimuna ke nan jiyan nan uwarku ta kama hauka wai maimuna tana son raba tsakanin ta da sarakuwar ta don haka yaron nan yai mata iyaka da ku.
Yace subbahanallahi may yasa mama take hakane Amma ni abin yana damuna wallahi irin yadda mama bata daukan girman ta ko kadan.
Yanzu fa nasan ko na aika mata ba samun kunnun nan zamuyi ba gashi tunda maimunan ta koya mata shan kunun ta zage da sha yanzu haka wanan ya isheta sha har gobe.
To ita ai bata duban hakan don kanta kawai ta sani gani take kamar wani abin kukewa maimuna din na alheri.
Yace ni har kunyar matar nake wallahi har dinkuna tayi wa merry taki karban kudi amma ita sai da na bata kudi har yau ba a kawo din kunan ba datace.
Sai hakkuri uwarkace kadai kiyayye yanzu dama nacewa maimuna ta bari zan maka magana idan kazo ku dinga zama a wurin mahaifiyar taku tunda haka takeso.
Ran umar ya baci sosai da jin wanan maganan don baiga abin laifi a gurin tarbon da mamu tayi masu in banda abin mama matar dake kokari danaka ai mai son kane.
Ina fita komawa nayi part din mu na kwata cike da mamakin halin irin ya umar ba kunya yake fadin wai yakai matarsa coco a gaban Amma.
Har barci ya fara daukana naji murya shi kamar daga sama a part din mu ya shigo suka gaisa mamu ta tambaye shi merry yace ta tafi coci kai tsaye.
Tace Allah sarki Allah ya fitar da ita daga wanan akidan Allah yasa tana da rabon gane haske a rayuwan ta.
Yace a sayaye Amin nagode yanzu daga gurin Amma nake take fada min yadda kukayi da mama shine na shigo in baki hakkuri kan hakan.
Mamu tace babu komai don Allah nake komai gare ku ba kamar yadda hjy take tsamani ba duk wanda ya taimaki wani kanshi ya taimaka.
Gani nayi merry tana bukatan a jata a jiki don ta sake jiki damu yasa nake mata abinda zataji dadin zama damu.
Don merry bakuwa ce a cikin mu al,adan mu ba daya bane da nata sai ta samu wanda yake lurar da ita wasu abubuwan don tana da saukin kai sosai.
Yace nasan wanan maimuna kuma nasan manufarki akan ta sosai shine nake kara baki hakuri kar hakan yasa kice zako janye daga gareta don hakan nima ba zai min dadi ba.
Kamar daga sama sukaji muryan hjy a kofa tana fadin yau zanji zan gani wai an birne tsohuwa da ranta.
Mata kamar manya idan ba kina da wani manufa ba yanzu abin har yakai ki tura babawo a daki kina mashi hudubar tsiya da zai kini wai a haka ake son lalaka mashi jinin ki mu kaita ina tin yanzu kina kokarin raba shi damu ace ya shigo gidan nan bai zamay ko ina ba sai gurin ki.
Muryan hjy maryam ne ke fadin kokarin ta ke nan da manufarta wanan halin ai sai addua yanzu kan don ta rigada ta tura masu mugun akida ko.
Dama ita yasan ta ganshi da zai shigo yana rike da flask din kunun da mamu ta aika mai dashj suka hade gaisheta kawai yayi ya shige part din mamu shine taji haushin hakan taje ta tseguntawa mahaifiyar su.
Shiru mamu tayi don abin ya daure mata kai bata da abin cewa ga kuma umar a wurin bai dace tayi wani magana mai zafi ba gare su a lokacin don ana barin halas don kunya badon tsoro ba.
Umar ya fito ranshi bace yace haba mama wanan bai dace ba matar nan tana kokari duk saboda mu amma ke ban san abinda yasa baki ganin hakan ba.
Oh kai baka san halin mata ba ko to ina zaka sani kafan ka na rawa kana son a lakaka ma wanan yar mai zubin aljannu duk shine makircin da maimuna keyi ba komai ba.
Haba mama yanzu ma merry ce tace in karbo mata kunu a wurin ta shine nazo fa.
Eh lalai shike nan ni nawa ya samay ni abinda nakewa gudu ya soma faruwa babawo kazo gidan nan ko kallon shiyana bakayi ba kazo nan tun yanzu ke nan kafara hakan.
Ina ga ka auri yarta hajiya maryam tace lalai fada masa yaya domin wanan dai ba abin hadawa bane duk hakan takewa take take .
Jikin umar yayi sanyi sosai takaci ya ishe shi kamar ya buge hjy maryam yake ji a lokacin don itace taje ta hasalo mahaifiyar tasu da alama ma daga barcin safe take ta tayar da ita.
Jikin shi babu kuzari ya juya yana fadin mama Allah ya baki hakkuri nidai nasan maimuna taimakon mu take kan hakan amma tunda baki so ai shike nan .
Har ya juya muryan mamu data kasa hakkuri ne ta fito tana fadin kaji yaya da wani magana wace yar kike tunanen zan hada da umar wai Sayadi kike nufi ko wa ?
Kema yaya da rikici gangan kike kina bi ta wanan hadasanan tana saki abinda bai dace ba sayadi kan ai ba kayan umar bace har nawa sayadi take da aka fara mata wanan hasashen.
Umar ai kamar matsayin uba yake a gurin ta don ya wuce ace mashi wa a gurin wanan yar don Allah a dinga tauna magana kafin a furta koda rai ya baci.
Ni don zama tare da zumunci nake abinda nake ko kun mata da umar dan dan uwane wai don haka abinda duk ya shafi diyan ku ya shafeni.
Kaji munafuka karya kike munafuka ko kin dauka bamu san komai da kike shiryawa bane a gidan nan .
Bai tsaya jin karshen fadan su ya juya ya shaki wani iska takaici ya fesar ya fara takawa a fusace ya nufi hanyar fita yana zuwa ya tayar da motar shi ya bar unguwar rai bace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button