SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:04 – ????????????: ONCES MORE AGAIN ASSALAMU ALAIKUN YAN UWA MUSULMAI YAYA RUWA YA LOKACI ALLAH YASA MU FI KARFIN ZUKATAN MU AMIN, , , , ,
Na idar da sallah har isha,i na fito falon inda su mamu suke ta dago kai ta kalle ni tace koke fa gaki da gashi sai ki tsaya ana dunkula maki shi wani iri gashin ki na wullakancewa nan gaba idan ya zube ai kya nemay sa.
Nace mamu ni idan zai zube duka ma ina so in huta wanan wahalan kitson har shawan kai askake ne idan na gani.
Tace shike nan kin zama irin su meery yayan ku Faruq nace da sauri arniya fa ke nan mamu ?
Tace to ba haka kike so ai yana daga cikin bambamcin mu dasu don Allah ya halasta muna aje gashi mu gyara shi yana daga cikin bambamcin da maza sai kumshi a kafa gashi ke duk bakya son yi.
Nace mamu harda kushin tace kwarai musaman irin namu na asali yana bada sha,awa da lafiya da kariyan mace daga tarkon aljannu.
Koda a hannu ne ko yan tsun ki ya kasance kina saka lale dai nace tsiyan abin makaranta basa barin aiyi kumshi.
Tace ba jakkadun shedan bane su ta yaya zasu bari muyi abinda Annabin mu ya umurce mu muyi wayan ta ne yayi kara ta dauka sunan mijin su ta gani take fadin Alh ne ko lafiya yake kirana yanzu ?
Nace ina zama zan fara zuba shinkafa da salad din da suke ci mamu kin manta da yace bayan magariba yana neman ku falon shi ne ?
Ba ruwa na da rikicin yayan hjy sayadi wanan matar bata sona da alheri na gama karanta ta har wayan ya katse bata daga ba ina kallon ta can ya sake kira ta daga yace kin manta da ina neman ku ne a sashe na bayan sallah.
Tace naga maganan bata shafe ni ba Alh tunda tayi min iyaka da yayan ta don Allah ka fitar dani cikin wanan zancen ban iya jidali kullun kan dan kankanin abu a gaban diyan mu.
Yace haka kikace ya kashe wayan ko mai mamu ta gani ta tashi tana kunkumi ta fita daga dakin naci gaba da cin abincina muna kallo da kanne na kafin barci ya dauke su.
Daya bayan daya suke shigowa falon da sallaman su kowa nayi wa kansa wurin zama a gefe daya samu inda yaran suka ware kansu a gefe daya.
Kowa na maganan zuci a ransa banda hjy da ta tasha mur wa kowa har diyan nata abin alfaharin ta a duniya.
Har Amma yau a falon dan nata tazo don amsa kiran gagawan da yai masu a zauna da yaran shi ba wanda yasan manufan yin hakan.
Wai Alh zaman may muke a nan haka ina kowa ya halar ai a kan mutum guda zamu tsaya mu bata lokacin mu haka ?
Ido kawu ya zuba mata cikr da zafi da takaicin ta yace lalai jummai baki da ta ido mutum dayan ita bata da hakkin jin tsarin gidana ne kokuwa ?
Yadda kike da hakki da ke da diyan ki haka take da hakki da ita da diyanta a gidan nan don haka ki kama bakin ki sai ga mamu tayi sallama a falin cikin zubulelen hijab din ta wanda ya rufe mata ko ina sabanin sauran dake zaune kimkan a falon don dan gara jummai atamfane a jikin ta.
Bayan kowan su ya zaunane kawu ya bude masu da addua kamar kullun ya dan ja lokaci kafin yace yau ina kasuwa aka kirani hankali tashe a gidan nan.
Wanda banji dadin abin danazo na sama a gidan nan ba don hakan ya nuna munyi sakaci da tarbiyan yaran gidan tunda har yakai da yana iya fushi da iyayyen shi kadan karamin matsala yace zai shiga duniya.
Amma ta karbe da fadin hakan baiyi dadi ba sai dai kasan aikin kurciya yadda yake kuma fa Aliyu ne mazan fama.
Ya juya gurin yaran tare da fadin irin tarbiyan da muka baku ke nan ko irin tarbiyan da zaku ba diyan ku ke nan nan gaba ?
Kowa na shiru sai hjy jummai dake aikawa mamu harara tana dauka itace ta kira Alh ga waya don sheri.
Alh ya kula da hakan tun lokacin dayai magana sai taji yace yau idan badon hadiye data kirani ba da tafiya ke nan zakayi ko don ba wanda ya isa dakai.
Ran maza ne ya baci yau ai ban san wanan Aliyun nawa da zuciya ba Amma ke fadi tana dan kallon shi.
Fada sosai yayi wa yaran kafin yasa ya ba uwar tasu hakkuri ya juya gurin hjyn su yana fadin mamakiyi hakkuri a sanyaye.
Alh ya dubi hjy yace ke kuma ki yafe masa tace aini ban dauka da zafi ba dama fada ne dole in masa don bata zaci Alh zaiso jin fadan ba a lokacin.
Sai muryan shi taji yana fadin ai zanzo ga na dan zan so naji abinda ya kawo wanan fadan haka ?
Ya juya gurin Aliyu tare da kafe shi da ido yana fadin ubana may yayi zafi haka ka fada min gaskiya al, amarin.
Da sauri hjy tace ai ba dole bane duk abinda mukayi da yarana a daki sai anji shi a waje don kowa na siri da diyan shi a daki.
Bai kulata ba yace kai nake saurare don wanan yazama dole in ji shi don ba karamin magana bane a gurina ifan kina daukan shi da wasa ke ya fada tare da juyewa zuwa namijin zaki lokaci guda.
Ganin haka Aliyu ya fara fadin No daddy kawai dai don nace ta bar brother yayi gaban kanshi yanzu shi ba yaro bane don kawai tace bata son shi da hurda da maimuna shine nace bai dace tana samu a harkan su na mata ba shine tayi min wanan marin.
Ikon Allah kan dan wanan maganan don kawai ya fadi gaskiya jummai zaki hana Umar hurda da maimuna ne ko ta halin kaka.
Eh to ban dai sani ba ko a yanzu zaki iya kiyi nasara amma a lokacin da ya zama surikin ta na gaskiya nasan ba zaki iya ba sai wahal da zuciyar ki da zakiyi kawai.
A hasale tace dama burin ku kenan ku kwace min dana daga gare ni na gano shirin ku shiysa nake sin yiwa hakan ruwa tu yanzu.
Ke nan kina iya ja da ikon Allah na fada maki aure a tsakanin yarinyar nan Fatima da umar ba fashi haka tsakanin Aisha hadiye da Aliyu habbib da Rukkaiyan balarabe.
Ihun hjy jummai saida ya firgita kowa a falon tana fadin wallahi karya kasha Alh wanan ba zai taba yuyuwa ba sam.
Don an maishe ni mara iko zaka tsara son ranku don kawai an zuga ka kan hakan bazan taba yarda a hada jina dana maimuna ba kai duka ma ban yarda a aura masu matan da hankalina bai kwanta ba ai nima ina da yayan yan uwana da suka dace dasu.
Kawu yace kiyi duk abin da zakiyi wanan magana ba fashi a cikin sa muryan mamu ne take fadin haba yaya kadai gyara zancen ka kam badai sayadi zaka hada da wani a cikin yayan hjy ba.
Don wallahi wanan abin ba zai taba yuyuwa ba ni dai su basuyi min komai ba a rayuwana ita dai ce ba zan hada iri da ita ba don kowa nason ma dan shi kwanciyan hankaline.
Shima ai Alh da gangan yayi wanan hadin don yasan ba abinda zai yuyu bane ya hada inji hjy maryam mara zuciya.
Mama hadiye ta karbe ta da fadin don may ba zai yuyu ba kanwa ke aikin ki kenan maryam baki gyara sai bata zance to idan ya yuyu ki hana.
Maryam kyale hadiye duk munafukai ne don da ita akai wanan shirin don kawai su cusa diyan su ga yayana anga wurin ci watau ko za a zo aci banza.
Sauikin abin dai ba kanki aka fara diya da arxiki ba don in kinga nawani a garin nan baki ko motsi mama hadiye ke magana ta kare da fadin babu yar dake da mugun kama a cikin diyan mu.
Wata kilama idan yaya ya barsu baiyi wanan hadin ba su dauko muna wanda sai kinyi mamakin sa mu bamu tayar da umurnin dan uwan mu don musan muhinmancin da a gare mu.
Koma dai may nene ni ba a wanan hadin dani mamu tace don kowana ma dan shi fatan shiga gidan arzikine ba wurin tashin hankali ba .
Kai haba haba maimuna yaushe kika zama haka har kike fada akan yar ki yar farin ki ban so jin haka daga bakin ki ba Amma tace.
Gwaggo in dai in zauna wanan tana gasa min magana kullun ne abin ya fara isata nima banyi maraba da wanan hadin ba kije ki jika diyan naki kisha.
Kawu ya dubi Amma da zatai magana yace hjy ki kyale kowan su yayi haukan shi don ba sauraransu zanyi ba na gama maganata ya dubi diyan nasa maza yana fadin zaku iya tafiya abin ku a kara da hakkuri.
Kowan su ya mike jiki ba kwari suna fadin sun gode suka fice daga falon zuciyar su babu dadi ga uwayen nasu.
Amma tace dama idan tura yakai bango haka ke kasancewa don bai kyau wanan halin tun kuna yin shi a bayan idon yaran nan yau har gashi kunyi a gaban su.
Aure ne ba wani abin haramun ba zai hada kowan ku ke wanan bakin rantse rantsen haka hajiya aiki barsu in ga iyakar su akan zance watau ke maimuna kina son nuna min ban isa da yarki ba ke nan.
Don ita ta dade da nuna min ni ban isa da yayana ba a gidana yanzu gashi kema kin nuna min hakan a gabana maimakon mamu taci gaba da magana sai ta fashe masu da kuka tana fadin yaya ba ai mi adalci bane wanan yar itake nan ubanta ya bari a duniya.
Sai ace za a hadata da jinin hjy jummai don kawai a kuntatawa rayuwan mu ko may da sauri kawu ya kalle ta tace maimuna da bakinki kike fadar wanan maganan haka a kaina yau din kawai nayi bugun gaba da fatima ?
Tace ba haka bane yaya a cikin kuka ni kowa zaka bata ka bata amma dai ba cikin yayan jummai ba kan matar da ta fito fili ta nuna bata yarda da hakan ba zaka hada yar nan da diyan ta.
Ya gyada kai tare da kada kafan shi Amma ta kalli mamu tana fadin kin ga maimuna tashi ki bar falon nan tun ban kai ga saba maki ba mara kunya kawai.
Mamu ta tashi ta fice daga dakin tana kuka gwanin ban tausayi a yadda naga ta shigo dakin ina zaune ina karatu da kallo rabi da rabi na mike da sauri ina fadin mamu mutuwa akayi ne ?
Bata tankani ba sai rufo part din da tayi ta juyo gare ni tana fadin ki kashe kayan kallon nan kije ki kwata hakana.
Na mike nayi abinda ta ce min daga haka na kwanta zuciyana cike da tunane kala kala ina faman sake sake a raina.
Washe gari mun shirya tsab a cikin uniform muka nufi hanyar part din kawu don mu gaida shi don lokacin da muke tafiya school bai fito ba wani sa,in shiyasa muke samun sa a falon shi mu gaidashi da kwana.
Kawu yana zaune saman kafet din sallah dake falo daga shi sai babban riga a jiki sa yana duke yana karatun kur,ani kawu mutum ne dogo ba sosai ba mai dan jiki ya kwaso jikin su Amma da haske shima wanda wasu daga cikin yaran shi suka debo a guri shi.
Kawu mitum ne mai dattako da sanin ya kamata a zamana gidan sa ban taba ganin bambamci a fuskanshi ba gare ni.
Ga ilimin addini dana boko daya ratsa shi don ranan danaji yana turanci sai dana sake baki ina kallon sa haka idan yana larabci da malaman islamiyan mu sai kace a saudiya aka haife shi.
Sai da Kawu yakai ayyah ya juyo gare mu yana fadi a cikin fara, a kamar komai bai faru ba a daren jiya fatima har an shirya zuwa makarantar yana kallon agogon falon shi yake magana.
Nace kawu ina kwana don tun ranan da su salma sukai min gorin ba ubana bane shi Amma tace in ba ubanki bane ai kawun ki ne don haka kema yarsa ce ta cikin shi Allah dai ne bai nufa shi zai haufe ki ba tun ranan na fara kiran shi da kawu a bakina a gaban kowa kuma.
Fatima zaku fita ke nan uwar ku zata kaiku ko motan gida zaku bi nace motar gida zamubi yau tace bata jin dadin jikinta yau.
Yace to ku kula da kanku ki kula da kannen ki kiji Allah yayi maku albarka nace amin cikin dan siririyar murya ya daga gefen kapet din da yake zaune ya ciro sabbin yan dari biyu guda hudu ya miko min yace to ga kudin taran ku nan na yau.
Na karba ina godiya muna shirin dagawa yace banda fada dai a schoool din kunji ko nace insha Allahu kawu a daidai lokacin su Salma suka shigo falon suma Nafisa tace ashe har kun shirya.
Kuma kinga A ruwa na manta banyi assignment din maths dina ba fa nace ni tun a school nayi abina ranan.
Mun fice mun barsu da kawu suma yana gaisawa dasu muka fito daga falon muka barsu a ciki basu wani dade ba suka fito su ikilima suka shiga ba group din dake yarda su shiga da yan uwan su ganin haka nima na koya a gidan.
Mun dawo har lokacin mamu tana a yanayin da na barta a cikin hakan mun samu tayi muna abincin da zamuci idan mun dawo nina bawa yan kanne na don ita tana daki dunkule har lokacin.
Muna zaune muna cin abinci mama kubura tayi sallama a kofan falon mu muka tare ta da murna tace ke fatima idon ki ke ga ke baki zuwa wurin kowa garin nan sai idan anzo gidan nan ake ganin ki.
Nace mama ba inda muke zuwa ne sai makaranta tace harda in anyi hutu ba a zumunci ke nan ko nace islamiya muke zuwa mama.
Rufa min baki ai baki da laifi anty maimuna ce mai laifin tace ina antyn take ne da hannu na nuna mata kofan dakin mamu.
Mama kubura kanwar mamu ce da suka hada uba duk cikin yan uban su tafi shiri da mamu sosai mamu na zuwa itama tana zuwa gurin ta sosai akai akai basu yada zumuncin su ba don sauran ukun maza ne su.
Ta shiga sun dade banjin hanayin su sai can na kama jin kamar kuka a dakin haka yasa na kashe kunne na ina sauraren su.
Muryan mamu nake ji tana kuka abinda ya kara samin natsuwa da sauraren su ke nan a dakin daga falo inda nake.
Yaya yaya zai mun haka kuma gwaggo ta goyi bayan shi idan nayi magana ace banyi daidai ba ya rasa wanda zai hada da zuriata sai diyan hjy jummai ina ma laifin Ahmed da yake nuna mata so a fili haka kodai da bai baiyana ba.
Yafi mun don ya halin shi yafi kwanta min a rai sau dubu da wanan hadin da yayake son yi matar da ta nuna a fili ba a boye ba bata so bata kaunar mai kaunana a duniya.
Zan yarda a kaita akai mun ya inda za a salwantar mata da rayuwan ta ita kadai nake gani a duniya mu tuna da mahaifinta.
Mama kubura tace nima dai abin ne da daure kai wallahi wanan hadin fitina kawai za a yi a gidan nan karshe rayuka suzo su baci.
Yanzu dai dole samu gwaggo zamuyi ansan yadda aka gyaro zancen a samu a shawo kan yaya sani ya janye wanan maganan.
Jin zasu fito yasa na bar falon da sauri na shige daki na ba a dade ba naji muryan su suna zasu fita mamu na fadin ina nake daga dakin mu na amsa da gani nan ina shirin islamiya.
Tace kijirani mu dawo zamu shiga wurin gwaggon mu ne na amsa da to ina tunanen wai maganan wa akeyi haka don kurciya ya hani fahintar may suke magana a kai.
Sun samu Amma a falon ta aka gaisa ta dago sau daya ta kalli Mamu ta kawar da kai gare ta alaman fushi take da ita har lokacin ita ma.
Bayan dan shiru mama kubura tace gwaggo munzo wurin kine akan wanan maganan daya fito jiya daga bakin yaya na hada fatima aure da dan wurin hjy gidan nan.
Gwaggo sai nake ganin kamar in anyi hakan kamar anyi ganganci sanin halin jummai da kowa yayi a gidan don ba zata barsu su zauna lafiya ba karshe ma yarinyar ita zata sha wuya tunda itace mace.
Maimakon Amma tayi magana sai ma ballan goron ta da tayi tana tana kaiwa bakin ta.
Mamu tace ni abinda yafi kona min rai wai fa bako Aliyu ba sai umar dake da mata ga uwar shi azzababiya da wani yar nan zataji.
Sai lokacin Amma ta dago kai ta watsa masu wani irin azzababen kallon daya sa suka shiga hankalin su a lokaci daya kowa yaja bakin shi yai shiru.
Sai can tace yanzu dai tunda kunfi dan uwan naku sanin ya kamata sai kuje kuyi abinda yafi zama daidai ko baki haka ba ai kin nuna muna kekeda yar ki bamu ba don haka ku tashi ku ban wuri da maganan banza.
Ke maimuna in kina da kunya har zaki kalli idona ki fada min abinda dan uwan ki ya zartan akan yar ki yau bai maki dadi ba don tsaban raina mutane da kikayi .
Maimuna kin ban kunya wallahi yau idan wani ya fada mi zaki iya aikata haka zan ma maishi musune sai gashi a gabana kika nuna min mu ba kowa bane a gare ki.
Gaki ga yar taki sai ki zaba mata wanda kike gani daidai ne a gare ki ke da wata ce aiko yadda jumnai take haukan nan bazaki watsawa dan uwanki kasa a ido ba.
Ke kuma kubura dayake kema sha shace iri ta shine kika kasa lurar da ita wanan haukan da takeyi kika wanko kafa kikazo gani gwaggon banza anzo a sani abin da ban tashi ba.
Yau kun nuna min cewa akwai bambamci a tsakanun jinina dana musa ke nan don gashi kun nuna min karara babu sakaye.
Da sauri su mamu suka zube a gaba ta suna fadin gwaggo ba nufin mu ke nan ba mu saba maki baki dai fahinci manufar mu bane gwaggo.
Tace shi al,amari in yazo addua ake son bawa yayi idan mai yuyuwa ne ba hani sai anyi wanan aure haka idan babu alheri a cikin sa idan Allah yaga dama sai ya karba adduan bawan sa amma kunzo min na goyawa karya baya ko may ?
Haka dau suka samu suka fita daga part din bayan tai masu tas suna bata hakkuri.