NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:05 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM WA, WA DADAKA A, ILAN FAHADDE, , , , ,

Mamu na zaune tana waya yayin da mu muna zaune mun fara cinn dan waken fulawa da dan wake kadan a ciki da mamu ta shirya muna as a lunch.
Ko wanan mu na son wanan cimar haka yasa muka bazu a falon mu mun mai dashi abin marmari don haka wasu mu naci da tsinke wasu suna ci da fork.
Sai ganin merry mukayi ta fado falon ranta a bace tana fadin i told you I don’t want to go there that woman hate me at all she fight with out resing.
Mumu tai dan murmushi tace don’t mind her is her habit, she can’t talk polityly.
You have to bear it she is you mother inlaw so nerver mind with her habit.
Dan zaku dawo ku zama daya wata rana idan kun saba yanzu abin yana sabo ne a gare ki ta dan mede baki alaman abin ya ishe ta.
Dan wake mamu ta zuba mata a plate tana mika mata saida ta dan kalla ta girgiza kai don bata taba fani shi ba kuma bai burgeta ba.
Mamu tace test it will enjoy it , is made with bean and flower tadai karba a ya tsune tana dan kokarin dauka a kyamace daga inda nake zaune haushe da takaicin yadda mamu ke lalashin ta taci ya cika ni.
Yaji na dauko ina karawa nawa da mai ta bini da ido tana kallona sai gashi ta hade wanda ta saka a baki tana kara daukan wani takai baki.
Sai ga merry na batun tashi da plate din abincin gaba daya da aka zuba mata ko magana bata yi sai ruwa da mamu ta zuba mata mara sanyi don ta kula bata shan ruwa mai sanyi sosai.
Muna gab da gamawa ne ya fado falon da sallaman shi ya dan tsaya daga kofa yana fadin sorry nayi distubing din ku a yanzu.
Mamu tace ba komai dan wanke muke ci da mai da yaji dan murmushi ya kirkiro a fuskan shi yana fadin ta iyaci don an tsanmanin ta taba cin sa ba?
Aiko gashi sai ci take babu kakautawa mumu ta fada da dan murmushi ya danyi kamar zai zauna sai kuma ya ja ya tsaya yana fadin na gode kwarai maimuna da wanan karramawan sa kike mata sai dai ina ganin zuwa wani sati zamu koma don shirin haihuwan ta don ina ga ta kusa haihuwa yanzu ga lissafin mu.
Mamu tace da sauri haka zaku koma ai na dauka a nan zaku tsaya sai ta haihu kan ku tafi ?
Ya dan sosa kai yana fadin zanso hakan nima sai dai hakan ba mai yuyuwa bane don ba zata so hakan ba ita ga kuma wanan yawan fitinan datake fuskanta wanda ba sabawa da hakan tayi ba ita.
Kayi hakkuri umar wanan ba zai sa ku wuce a yanzu ba da zaku dan daure ku kara lokaci zaiyi kyau har ga iyayyen ku yanzu sai suga ai ba wani dadewa kukayi a kasan nan ba zaka koma kuma.
Kaga sai su dora laifin ga ita merry din datazo daga baya ya dan ja iska ya furzar tare da fadin nasan zasuyi wanan tunanen a ransu amma ba yadda zanyi ne don tun yanzu merry ta fara fuskantar matsala da hjy wanda ba zan so hakan ya faru ba gaskiya.
Hakkuri zakuyi don iyayye dama zama dasu sai hakkuri don kullun a yara suke kallon ku kadai ga yadda yake kasancewa ko ga mahaifan mu ai.
Dazun da ka ganni daga wurin baba nake yau min tas daga naje mai da shawara sai yake ganin na raina su.
Dan tsohon nan ai bashi da fada ko sosai sai dai yanzu da tsufa ya fara zomai dole ne ya fara fada kan dan magana kadan.
Muryan merry ne take fadin ta koshi da yawa bata dauka zataci sosai haka ba yace ta tashi su tafi wani kallo tayi mai tana fadin so soon ai na dauka kace sai dare zaka dawo ka dauke ni yace haka naso amma yanzu na fasa.
Tayi kokarin mikewa sai ta koma ta zauna dan murmushi yayi ya duka yana kokarin dagata da kanshi da sauri na kawar da kaina ina kokarin kara yaji sosai do ya dauke mi hankali daga kallon su.
Wai ke may ye haka kina ta zubuda yaji ga abincin ki tun dazu kina sane da bai baki lafiya kuma.
Mamu ina son sa da yaji ne na dan fada a shagwabe ina bata fuska lokacin har ya mikar da ita tsaye suka tsaya suna kallon plate din abincin nawa.
Prity ko zaki bimu zuwa masaukin mu yau ki debe muna kewa na dan lokaci kadan ina son zama dake mu danyi hiran yanayin ku na nan.
Merry ta fada tana kallo na da sauri na girgiza kai ina fadin No no no is time for my qur,anin school and want to miss it.
Ganin suna magana da mamu tana mata bayanin abinda nake nufin nayi saurin shigewa dakin mu na fara shirin barin gidan suna nan na fito a cikin zubulelen hijjab dina ina fadin fauziya ku dauko hijjab mu rafi kada mu makara.
Ranan da mamu ta karbi girki hakana ta daure zuciyar ta ba dadi har lokacin ta shirya zuwa sashen mai gidan don gabatar da hakkin shi daya rataya a kanta.
Kawu ya debe rai da zuwan mamu part din shi do har ya fara gabatarwa kanshi wasu al,amuran da sukeyi masa idan sun shigo.
Sai ga ta ta shigo fuskanta ya kalla wanda har lokacin ba walwala a tare da ita , sallaman da tayi ya karba ta aje abinda ta shigo dashi a hannun ta.
Sai da takai zaune ta fara gaida shi da dawowa shima ya karba kamar yadda ta gaida shi din a sanyaye,
Dan shiru ya biyo falon kafin kawu ya kawar da shirun da falon yayi da fadin kinki ki tuna min zancen kayan yaran nan don ni na manta da zancen shaf a raina..
Sai da na hadu da Fatima dazun suna dawowa na tuna dan kunya ne ya kama mamu tace abubuwan ne da yawa itama dai fitina ne da ita wallahi.
Yace kin san halin malaman da saka yara a gaba suna takura masu in bashi ba ai wanan da take amfani dashi ba laifi yana da tsawo nagani.
Ai ka santa da shegen son uztazanci dan maganan da akayi bai saukaba ya daga mata hankali.
Wanan ai yana da kyau yaran nan kaf din su ina hankalce ta fisu son addini shiyasa nake son zancen fatima akwaita da kokari wurin wurin riko da addini sosai.
Kai yaya sayadin da saida nayi da gaske take wanan halin yace to ai kinji tunda har zaki iya sakata abu tayi shi.
Jikin mamu ya kara sanyi tayi shiru sai can race shekaran jiya naje gida gun baba .
Ya katse ta da fadin kinje kai karan mu ni da hajiyan mu ko ba haka bane yaya ta fada a dan kunyace tare da fadin kun dai ki fahintana ne kan wanan zancen.
Amma ta yaya zanki umar da sayadi tunda ban san abinda kayi tunani kai wanan hadin ba ni abinda nake jawa yadda tun yanzu hjy ta nuna bata son hada komai dani a fili yasa nima na, , ,
Kema sai haukan kishin ya kwashe ki kuka kara bakanta min rai ko kawu ya karasa fadi kafin ta furta nata.
Kin ban mamaki maimuna da har kikayi zaton zan kai fatima gurin da zata sha wahala ko wani abu makamancin hakan nafasan abinda nake maimuna.
Yaya kayi hakkuri banayi hakan don in bata maka bane abinda nake hange cikin wanan auren duk kun kasa hangen shi ku a yanzu.
Matar da ta nuna wa bare ma halinta balle yar nan da tun yanzu ta nuna bata kaunan ta don may ni zan nuna ina kaunan wanan hadin kenan nida yar mun zama kwadayayo ke nan a wurin ta tana hattaran mu muna biye don kwadai wanan ba zaiyuyu ba.
A takaice dai baki yarda da hukunci na ba ke nan har yanzun ?
Tayi kasa da kai tana magana kasa kasa a cikin ladabi tace ni bance na ban yarda ba kai tsaye ai kadaiji hujjan da nake dashi.
Girki dai haka akayi shi ba wani dadin rai gare su dukkan su duk da mamu tayi kokarin danne zuciyar ta ga zancen kamar yadda shima kawu bai kara tayar da zancen ba a fili sai dai ba gudu ba ja da baya ga abinda ya zartan.
A cikin satin ne kuma kowa na gidan yasan da zancen gidan da umar ya gina dama wasu harkoki da yakeyi.
Hakan bai hana mumu wanke kafa taje har falin hjy jummai tai mata murna ba lokacin suna zaune da yaran ta ana hiran haduwan gidan daya gina din.
Tayi addua tare da fatan alheri daga haka ta juya ta fita ta barsu tana fita hjy jummai tace munafukan banza munafukan wofi.
Ta wanko kafa tazo don wani simi simi da ita tana fadin wai Allah sa kaza Allah sa kaza kamar yakai ciki munafuka watau a yarda da yar ta ko mai.
Mama ai tayi kokari don tazo habbib ya fada cikin rashin kulawa shiko Aliyu mikewa yayi yana fadin bros yanzun zaka fitane ?
Binsu tayi da kallo suna ficewa daga dakin Aliyu yace mama bata son zancen gaskiya may ye laifin matan nan datazo mata murna ko yan uwanta ai ta riga su zuwa.
Gidan umar sukaje sun samay shi a waje da wani abokin shi suna magana haka yasa basu tsaya ba suka shige ciki.
Merry dake kwance ta karde falon da kidan coci tana bi daga inda take kwance din ta dago ta kalle su ayatsune tana fadin wanan shigowa haka kamar wasu yan aike fa.
Sai da kowan su ya samu wuri ya zauna suke fadin gunki aka aiko mu inji Aliyu habbib ne ya kalle ta tace ba zaki bamu ko ruwa mu sha ba ai ki tare mu da wani zance.
Tace ruwa nine zan debo maka ruwa kasha ko wa tana fadi tana gyara kwanciyar ta amma kin san mu haka akidar mu yake maigida shi zai tari bako da abin sha ai .
Tace to hell with your culture at all no any respect in that culture baku san ku yadda ake girmama bakon ku ba ko kadan.
Sunyi galala suna kallon ta haka yasa habbib ya fara mikewa yana fadin kai mu tafi ta tabe baki tana kallon su a wullakace tace akan ku zan fara rama wullakancin da ake mun.
Umar dake shigowa falon yace har zaku tafi ke nan yanzu fa kuka zo bako zauna ba halan.
No bari mu tafi zamu dawo wani lokacin habbib yace yana tafiya Aliyu ya mara mashi baya.
Ciki ya shiga ya samu merry a yadda suka barta yace kinga su brothers sin shigo ko zama ina basuyi ba kuma sun wuce.
Tace eh da sanina suka wuce don raini suke son kawo min wai na basu ruwa su sha wani kallo yake mata kafin yace merry kin san mai kike fada ke kika kore su ke nan ko ?
Tace idan zasu zo su kawo min raini zan masu abinda yafi wanan ma a gidana don ba zasu zo suna takura mi ba.
Alamarin merry ya fara ba umar tsoro ga matsin da take mai kan tagaji da zaman Nigeria ita dai sai su koma taki yarda kuma ta koma ita kadai.
Ya dai samu ya dan rarashe ta kan ta yarda ya karasa abinda yasa a gaban shi ita babba damuwan merry shine ta samu ta raba umar da mahaifan shi da take ganin tsana daga idanuwan su.
Tunda ya samu ya rarashe ta tadan yarda zasu kara lokaci sai kuma dokokin data na ba zata sake zuwa guri mum din shi ba koda kuwa ta shiga gidan.
Gashi kuma zuwa lokacin ita hjy ta dan sauko ta fara nunawa merry ta fuska da baikai ciki ba tana son jan ta a jiki.
Hjy da kanta tayiwa merry korafin rashin zuwanta gidan su kwana biyu merry ta kama mata yawo da hankalin cewa ai suna tafe.
Sai dai har lokacin bata ga duriyan ta ba a gidan sai kuma ta fara zargin ko mamuce ta zuga merry din a kanta kada ta yarda da ita ko kuma ta zuwa gidan ita a boye.
Haka yasa hjy ta kasa hakkura ta tun kari dan da zancen a ciki waya yace yana lagos idan ya dawo zasu shigo ai .
Har kwana biyu bata ganshi ba ta kara kiranshi a waya yace insha Allahu yana tafe a gobe zasu dawo.
Washe gari da yamma sai gashi ya tun karo gidan lokacin baiko karasa gidan shi ba ya nufo gidan su don yawan kiran mahaifiyar tasu da take mai yake daukan wani abune ya faru.
Yayi sallama ya shigo gidan ranan saye yake da wando da rigan bakaken kayada farar riga a cikin kayan suit din.
Wuyan shi yana daure da nicktie sai kamshi turaren sa ke tashi mai dadi da kan gauraye wuri idan yana gurin.
Kayan suyi mashi matukar kyau a jikin shi kai kace don shi aka hada kayan ya karasa shigowa yana fadin mama na dawo don naga kamar kina bukatan gani na sosai.
Tace ai dole babawo kana kasan nan matar ka tana kokarin rabaka damu ina ga kun koma can yanzu dai maimuna takai ga bukatan ta fafir wanan yarinyar takini a kasan nan..
Haba mama merry har ta isa ta rabani daku kawai dai daurowane hakan tace wana dalili;yasa bana son ka auri wanan yarinyar yar gurin maimuna.
Kai mama har yanzu kina ga wanan zancen na dauka ai an bar wanan maganan tunda itama ta nuna bata son hadin .
Karya ne munafukane balle yanzu da take ganin ka samu ci gaba haka ai yanzu take da kwadan hakan sosai wai ranan don bata da kunya sai gata tazo min murna har nan part din.
Mama ni sam ban dauki wanan wani munafunci ba tunda kuna wuri daya tare haka kema watarana alheri zai samay ta kizo mata murna ina har hjy maryam duk sun zo.
Wani kallo tayi mai tace maryam ne zata zo min murna nan ta dai zo min gulman wai taji hajiya na fadin gidan ya tsaru ke nan suna zuwa gidan naku ke nan.
Kai mama ku dai baku rabuwa da wani zance zan karasa gida don ko gida ban samu zuwa ba na wuto nan mu gaisa do ki ganni.
Dadin haka hjy taji tamike ita ma tana fadin yaran nan sun min magana wai suna son su koma hakana sai dai nasan ba abune mai sauki ba Alh ya yarda da zancen komawan naku kuma.
Tsaye suke aharaban gida suke wanan maganan sankarewa yayi a tsaye tankar ruwa ya ci shi dama yasan wanan abin zai faru gun mahaifin nasu.
Motar da tashigo na mamu data kwaso su manjo da Adda daga tasha ne ya dauke mata hankali har bata san shock din da dan nata ya shiga ba a lokacin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button