NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ya shigo gidan ya nufi gurin hjyn su sun gaisa ba wani damuwa ya dan taba hira da ita take mai maganan bukin yar uwanta da take son su halarta ranan asabar yace mama ai tunda muna gari zamuje daurin auren insha Allahu.
Ya mike yana fadin zan leka wurin Amma kwana biyu bamu hadu ba sai hjy ta tabe baki tana fadin ai kunfi kusa da ita kadaiyi takan tsantsan don kasan kansu a hade yake da wanan.
Yi yayi kamar bai fahinci may take nufi ba yace babu komai mama insha Allahu ina kiyayewa ai taji dadin samun kansa yadda take so a ranta.
Ya shigo da sallaman shi tana zaune saman kujera three seater inda ta mayar kamar shine wurin zamanta.
Shidai da zai samu sai yace Amma ta koma gidan sa da zama har matar shi ta haihu sai dai yasan hakan ba zai samu ba.
A yadda yasan Amma tana taushe zuciyar tane kan shi da matar shi don kawai, kawai a gare shi don haka ne ya kasa fadar manufan shi ga hakan tunda yana ganin wata kila merry ta haihu a kasan nan kafin su koma.
Tunda aikin daya dauka wasa abin ya wuce nan saboda wasu abubuwan sai a waje ake sayosu can.
Wanan matsalan ya kawo mai cikas ga komawan nasa inda da kyat ya samu ya shawo kan merry ta yarda ta zauna na dan lokaci ga kuma can iyayyenta ba faman kiran waya ta dawo kada haihuwa ya rutsa da ita a nan din.
Zama yayi a gefen Amma saman kujeran da taks zaune a kai tace nikan ban gane wanan auren ba yanzu tun zuwan matar ka sai ka share fiye da sati baka shigo gidan nan ba.
Ya dan kalleta yana fadin dama nasan da haka ina zuwa sai dai a kuraren lokaci nakan shigo gaida mama wani lokaci ma ban samun dady a gida idan nazo.
Eh lalai kuwa yanzu na fahince ka watau har ka shigo gidan nan ka fice sadauki baka damu da ka leko nan inda nake ba ?
Yana dan dariya yace tuba nake tsohuwa mai ran karfe kaina a kasa kin san ni ban iya karya ba a rayuwana ko nayima kamani akeyi.
Turmin zanin da ke shan kallo a gurin Amma tu lokacin dana bata ya gani aje a gefe yace wai ke Amma har yanzy kina dinki da kanki ne haka ya mika hannu ya dauki turmin yana juyawa tare da fadin zanin nan ko yana da kyau sosai.
Amma ta dan kalle shi tana murmushi tare da fadib kaima dai ka fada din daga masu kaunana zani yafito yasa yake da kyau sosai haka kowa na fadin kyawon zanin ai.
Su waye masu kokarin kife min gwaunati a furin ki har kike murna haka Amma a sanina dai nine dan gaban goshi naki tace har gobe kuwa.
Don wanan zanin daka gani daga gurin ka ya fito ya fada hannuna saboda so da kauna.
Da sauri ya kalleta yace ni kuma Amma yaushe akai hakan tace gashi nan dai ka tuna idan zaka iya.
Ya dan girgiza kanshi yace ban tuna ba gaskiya tace to ba wani ya bani ba sai amaryan ka cikin wanda ka saya mata dama wamu ta zaboshi ko dakin uwar ta batakai ba ta kawo min nan.
Da sauri ya aje zanin saman kujera yana tsuke fuska Amma tace ni wanan hadin naku yafi min dadi dana sauran .
Ta dago kai tana kallon shi ganin yadda ya bata rai tace ya kuma naga kamar bakai murna ba da hakan ko ita kaso ta daura zanin kagani a jikinta ?
Kai Amma da wani zance kike ni ban ma san abinda ta dauka ba a shagon don hankalina baya gare su.
Dan murmushi Amma ta sauke a fuskan ta tare da fadin sadauki ina fatan ba uwarka taci galaba bane a kan ka yadda na dauko maganan yarinyar nan ka bata ranka haka.
Yace No ai idan nace zanyi abu zanyi ne tunda kikaji na amsa zanyi din ne da ba zanyi ba tun farko zan bijire maku kan zance sai dai ina son farin cikin daddy mu nima tunda hakane burin shi.
Shiru Amma tayi tana dan nazarin maganan shi a ranta kafin tace sadauki shin tsakani da Allah ko zaka auri yarinyar nan don kada azo ai abinda za a dawo daga baya ana da an sani a cikin sa.
Yace watau Amma har yanzun dai baki gama fahinta ta ba ke nan tace ina zan fahince ka dan nan da wanan maganan taka.
Yace ba wani abu bane Amma sai rawan kan yarinyar dayai yawa dole daddy ya bamu time har zuwa lokacin da zatayi wayau.
Ikon Allah A ruwa din ce yarinya dan nan yarinyar data dade da zama mace mu lokacin da akai muna aure aiko faduwa bamuyi don a dakin mijina na fara al,adata ganni nan ko har yanzu ba abinda ya samay ni.
Amma maganan da kikeyi ba na yanzu ba zanso ace anbar zancen nan har nan da shekaru masu zuwa nan gaba daidai lokacin ta kara karatu sosai tasan komay.
Kaima sadauki da wani zance kake ai indai ina raye yaran nan ba zasu kara shekara ba a gidan nan nan gaba.
Yace amma Amma tace hakan ne buri na gare ku sadauki kaji na fada maka.
Shiru yayi yana tunane a ranshi kafin ya mike ba tare daya kara furta komai ba yana fadin ni zan tafi Amma sai wani lokacin.
Tace ka gaida iyalin naka idan ka isa gida maganata dai babu fashi a cikin sa baice komai ba ya nufi hanyar fita tace wai ko kasan kakan yarinyar nan tazo tana garin nan kaje ku gaisa.
Ya kulu matuka ji yake a lokacin kamar ya hadiye ranshi don haushin maganan tsohuwar shi da yazo da niyar su danyi hira ta dauko mashi magansn wanan fitsarararan yarinyar kuma.
In ko banda biyayyan mahaifa kamar shi za ace wai za aiwa irin auren nan na hadi haka kai tsaye.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:07 – ????????????: YA ALLAHU YA RAHAMAN YA ZUL,JILLALI, WAL,IKIRAM ALLAH,

Kawu ya dawo a gajiye yau girkin hjy jummai ce yasan ba wani kulawan da ya dace zai samu a wuri ta ba.
Ga mamaki shi hajiya ce ta shigo dakin dauke da kayan abinci yau bata turo yar aiki ta kawo mai ba kafin ya dawo a jera mai sai dai ya dawo gidan ya samu an aje .
Zama tayi bayan ta aje abincin tana mashi sannu da zuwa ya amsa mata a cikin sakin fuska don yaga yau tazo gare shi da shiri.
Sai dai yasan ba zuwan Allah da Annabi bane dole akwai wani shiri da tayi a kasa da take son gabatar don ya gama sanin halinta kamar yunwar cikin shi.
Remote ta dauka tana rage karan tv don karan yai mata yawa shidai bai tanka ta ba yana kallon ta sai da ta rage take fadin .
Yau ka jima a waje mana tana kallon shi yace eh abubuwa ne suka tsayar dani don kayan da Ahmed yaje daukowa suna gap da shigowa kasan nan.
Sai ta dan nisa tare da yin shiru kafin tace amma ina ganin lokaci yayi da Ahmed zai daina wanan tafiyan a samu wani daga cikin naka su fara wanan hidiman da kan su.
Dan murmushi ya sauke irin na manyan a fuskan shi yace jummai ke nan a cikin yaran nan yanzu wa kike ganin zan dorawa wanan nauyin mai wahala a kansa ya iya dauka .
Ko kin dauka aikin wasa yake fita yi can din kawai tace koma may nene shi ya iya balle naka humm kawai yace ba tare da yai mata magana ba.
Sai can yace zuba min fruit din nan in sha kafin a fara labaran kasa ya fadi ba tare daya kalleta ba yake magana.
Ta mike da kyat tinkis tinkis zuwa wurin data aje ta fara zuba mai ta kawo mai gaban shi ta aje tana zama ne tace wai ni wasu irin bakine haka suka zo muna gidan nan.
Da sauri ya dago kai yana fadin baki a ina suke don shi ya manta shaf da su manjo na gidan lokacin .
Tace wa yan nan bakin mana da suke dakin maimuna kasan fa muna da yara kankanu a gidan nan irin tsofin nan data kwaso ba abin yarda bane a yanzu da duniya ta lalace din nan.
Sai da ya kurba fruit din yace ai kin gama maganan ki da kika ce duniya ta lalace ko ba baki sai a samu mugai a cikin gidan nan ba a bin mamaki bane.
Tace Alh ke nan ai na gida an saba da halin su wlh gaskiya nake fadi a magana ta kasan tun farko ni ba son wasu suzo su zauna muna haka a gida nake so ba don tsaron lafiyan mu.
Yanzun may kike nufi da wanan maganan naki bakin nan fa ba wasu baki bane can na waje kakan yarinyar nan ne fatima tazo checkup da yarta su kike kira da baki ?
Tace baki ne kan tunda ba zuriam kowan mu bane banga dalilin da dan wanan halakan zaisa suzo su zauna muna a gida haka ba.
Don ni ban yarda da zubin mutanen nan ba kamar wasu muna fukai dasu kullun a daki kumshe.
Kai jummai kin san abinda kike fada idan ma hankalin ki bai kawo ba ki tuna mutanen nan nan gaba halaka zamu hada su mai karfi a tsakanin mu ba gida na ba har gidan dan ki watarana zasu iya ziyarta.
Wani kallo tayi mashi kafin tace gidan dana fa kace Alh wani dan nawa kake tunanen zasu ziyarta a cikin yaran nan , ?
Yanzu dai na fahinci abinda ya kawo ki dakin nan kinzo ne kawai ki tayar min da hankali na dawo da gajiyan kasuwa a jikina haka ?
Wanan kuma sai in kaso fadin hakan ni dai akan wa yan nan mutanen yanzu nayi ma magana ba fitina nazo nema da kai ba.
Yace bakina ne tunda bakin matatace don haka ki barsu nan inda kika gansu tunda ba a kanki suke zaune ba.
Mutanen da ko waje ban tsanmani suna fitowa zaki zo da wanan maganan ke yanzu ba abin farin ciki bane a gare ki yau bakin sun sauka a gidan nan zamu samu ladan da Aah ya kwadaita muna ga wanda ya ciyar da bakon sa.
Hjy data gama hasala da zancen shi don ba haka taso ya dauki maganan ba tace dama nasan abinda zaka fada ke nan akan may maimuna zata gaiyato muna su a gida haka ?
Wai maiye matsalan ki da mutanen nan kilan ma tun da matan suka zo baki sauke hakkin ki kun gaisa dasu ba to don may zaki zo ki sakani a gaba da zancen su yanzu.
Gidan nan gidanane fa gidan mata hudu kuma saboda ke sai in tauyewa sauran iyalina hakkin su ko haka kikayi a baya kan yan uwan maryam dake zuwa gidan nan kai da kai sai da kika samu fitinan da kika dora mutanen nan suka dauke kafan su da gidan nan.
Ta kalle shi tana fadin sheri zakai mun kuma yanzu akan maryam yace meye abin sheri a ciki tunda anyi hakan nasani.
Daga haka ya mika hannu ya dauki remote din shi ya kara ya barta nan tana cicika do ba haka taso ya dauki maganan nata ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button