SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Sauri nake na fito daga part din mu zan shiga wurin Amma dake kirana hjy jummai ce tsaye da wasu hamshakan mata a waje.
Tunda na gansu nasha jinin jikina dasu hakan kuma bai hanani saurin da nakeyi din ba nazo daidai inda suke naji hjy tana fadin kungama ga yarinyar nan da Alh ke son lalakawa yaron nan.
Gaba dayan su suka jiyo suna kallo na a raina nace kiyi ki gama ni ba ruwana da lamarin ki iyaka dai ki nunani kice nice agolan gidan ku ga kowa don na dauka shi take fada masu din.
Dayar matar dake da haske a cikin su tace tuburkallah ai Alh baiyi hadin banza ba a nan kina ganin ta nan idan ta samu wuri bajewa zatayi sosai yanzu akwai sauran kurciya a tare da ita.
Dayan mai tsayi kamar hjy tace eh da alama kan zai more auren sa sai dai matsalan abin ne ai yar kishiyar tace fa aka fada maki shine babban matsalan ai.
Ni ai ban hango wanan hadin ba don zancen banza naji kunayi a nan kamar baku tayani bakin cikin wanan abin ma ?
Har nakai Part din ina mamakin maganan su don duk abinda suke fada a kunne na yake ina jin su.
Ina shiga nace Amma ji min wanan matan tace wacece kuma na kai zaune ina fadin hjyn su salma mana yanzu na wuce ta da kawayen ta a waje suna gulman wata har da fadin wai ita ba zata yarda dan ta ya auri yar kishiyar ta ba sai fa da ta ganni take wanan maganan Amma ?
Ko an fada mata diyan ta suna burgemu ne oho indama ba yaran nata arna suke auro mata ba a matsayin sarakai.
Ni kan indan na tashi don taji haushi uztazu zan dauko gidan nan yazo yai ta maku wa,azi taji haushi.
Amma tace kaiya yar nan ai kaddara ta riga fata koda yake mijin naki ba laifi a wani wajen yana da gwargodon ilimin shi sosai.
Ji Amma don Allah ke kin san wanda zan aura din ne da kike wanan magana keda kuun kina a falo zaune murmushi tayi tana kallo na tare da fadin idan na sakaki a lale zaki bayani.
Fauziya ce ke fadin wai inzo mamu na kirana dama guduwa nayi kawai in tsokali Amma zamu tafi islamiya ne lokacin.
Hakan yasa na mike da sauri ina fadin bari in mun dawo sai inzo ki fada min mijin da kike min hasashen.
Bayan fitar mu islamiya mamu na tuka tuwon dona dora kafin in fita hjy maryam ta yi sallama a falon part din mamu din.
Daga ciki mamu ta karba tana fitowa falon don ta sheda muryan nata ko ta fito tace a, a hjy kece ashe da dan murmushi a fuskanta.
Wlh nice nace bari idan leko in gaida baki ashe baki kikayi haka gurin hjy nake ji da take fada akai.
Mamu taja ta tsaya tana fadin ikon Allah fada akan may kuma ko wani abu ya faru ne tace kawai dai kin san halinta ita kanta kawai ta sani ai.
Ta fada maki zancen bukin da sukeyi ne sai mamu tace hjy ke nan ina zanji tana da buki Allah dai yasawa auren albarka.
Ta tabe baki ba tare da fadin amin ba take fadin ai ko yaya ne dai zaka sanarwa wayanda kuke tare dan uwan ka na buki ko addua aikayi masu.
Idan da sabo aini na saba da halinku a gidan nan tun ban iyaba har na iya yanzu Allah dai ya huci zuciyar ku ya bamu hakkurin zama da juna tunda zama ya hada.
Dan dariyan yake tayi tana fadin kai maimuna akwaki da wani zance aiko ni ba zaki fada min haka ba a kanki.
Ida ban damu dake ba ai ba zan shigo yanzu in kula da bakin ki ba dama dai ai itace mai nuna bata son mu,amulan kowa a hade.
Allah ya kyauta mamu ta kara fada tana kwantawa sama ha;u kujeran da take tsaye kusa dashi.
Tace zama tare ne ya kawo hakan sai hakkuri da junan mu sai hjy maryam itama ta dafa kijeran kamar yadda mamu diin tayi tana fadin aiko kan maganan hadin auren nan bakiji abinda take fadi ba.
Mamu tace komai zata fada nafita baki ciki da wanan hadin don ni diyata na sani kamar yadda tasan danta.
Itama ta kyamace mu balle mu da za a tauyewa yarinya yancin ta na budurci a hada da mutum kamar umar ni ainafita jin zafi da kyamatan hadin wake son hada zuri, a da ita idan ba dole ba.
Anty bari kiji nifa badon gwaggo da Alh da suka roke ni in yarda da hadin nan ba babu abinda zai sa in yarda da wanan bakin hadin.
Mumu tasan zancen ta a kunnen hajiya yake yasa take bada sako a kai mata don tasan da dawowan ta sakon ta zai isa gare ta ta tsaya ta fadi magana iya son ranta kafin hjy maryam din ta fita.
Muna islamiya fauziya tazo min da kuka dan wurin hjy maryam ya duketa don suna fada da kanin su karamin.
Ina zuwa ban tsaya tambaya na rama mata dukan naja hannun ta muka tafi har mu fara hanya ikilima ta samay tana fada wai don may zan doki kanin su.
Nace na doke shi ki tambaye shi shi may yayiwa fauziya na rama mata shike nan don wani yafi wani karfi sai ya duke shi daga dan magana kawai.
Kamar zatai magana sai kuma tayi shiru na juya na fara tafiya naji muryan ta tana fadin wai ita A ruwa din nan don kawai taji ance zata auri yaya umar ne takewa mutane wanan rawan kan dama ba cusa mashi ke akayi ya aura dole ba balle kiwa mutane sallo.
Na juyo da sauri ina fadin wani ya umar din tace ai duk kin sani bari kiji idan ma cusa mashi ke akayi ba ya aura bai so shida hjyn su.
Balle ki dinga yiwa mutane rawan kai a gida kina kutin ke zaki auri mai kudi har asirin da akayi don hakan ya faru muna da labarin komai.
Ikilima shirin naku na gado har ya kawo gare ni dama kulle kullen da kukeyi ke nan daku da uwar ku don kawai ku bata muna suna.
Yau Allah ya matsi bakin ki ki fada da kanki kowa yaji sai dai ki sani ni har yanzun ma ban gama sanin sunayen diyan hjy ba a kaina balle in san ko waye umar a cikin su.
Nace kukan kunyi hasaran rayuwa uwa gulma diya gulma sai ko ta kai min duka nan fada ya kaure a tsakanin mu Allah yaban sa an ta na kaita kasa na haye na murji bakin ta sosai ban daga ba sai da naga hancin ta da bakin ta yana fitar da jini su Aisha dasu salma suka banbareni a kanta.
Har muka kawo gida ana cacan bakin maganan ida nake ji kamar dukan danayi mata bai isa hakana ba.
Dan tsayawan da mukayi a hanya fada yasa muka bata lokacin mu sosai a hanyar dawowan mu gida.
Muna shiga gida wani sabon fadan ya kaure don ban kai ga shiga gida ba su ikilima suka rigamu shiga gidan har sun fadawa uwar su tana ganin jini ranta ya baci ta fito da jidali.
Sunana uku da ake kirana dashi ta kirani dasu a jere tana fadin an aiko kine ki masu wanan dukan haka don jin haushi da takaicin su da kike ji ko may ?
Saratu kanwan ikilima tace wai fa don kawai tace kanta yana rawa don taga za a aura mata yaya umar ta daketa.
Hjy maryam tace dama ba asirin da rokon shi akayi akan ya aure ki ba din ba har uwar ki na wani cika bakin banza ga mutane.
Munsan komai wa zaku dagawa hanci nan idan ba asiri bane mai zai kai Alh yin wanan hadin haka tunda kowa yasan ba ajin ki bane shi.
Uhumm dama abinda kakeyi shi kake dauka kowa shiya keyi ai hjy maryam ke kika san zuwa wurin boka da malam ni ban gaji wanan ba a rayuwana.
Auren Umar da ya tsone maku ido ki wanko yarki ko wata naki ki bashi ki gani in ya taba ran maimuna ko wani nawa.
Fada ne na yara amma ke babban kanki kin fito kina wanan baran bakin a gaban yara haka.
Allah waddan wanan halin naki maryam ke da diyan ki yanzu don baki da kunya ke, ke fadan haka a bainan jamma,a waye baisan har gatin nan kike bari zuwa bin bokayen ki ba.
Mama hadiye ke magana a fusace tana kallon hjy maryam din wanan maganan da aka barshi iya mu manya gidan nan muka san da zancen nan ashe har kin feasawa yaran ki shi.
Fada sosai da musayar harshe ne tsakanin mama hadiye da hjy maryam da har yakai su Alh dawo gida suka samu suna wanan rikicin tsakani su da fadan ya koma tsakanin ta da mama din.
Wai may ke faruwa ne haka tun bakin get nake jin muryoyin ku haka cirko cirko akayi a gurin gaba daya saida ya kara tambaya mama ta juyo tana fadin.
Zancen yaran na fa sun dawo islamiya ashe sunyi fada a can tau shine sai abindai ya zama musu rikici har yakai ita ikilima tayiwa Fatima gori wai sunbi boka da malam ita da uwar ta don a aura mata umar.
Wani kallo ya watsawa su hjy maryam har yaranta kafin yace ita ikilima a ina taji wanan zancen ?
Shiru ikilima tayi ya daka mata tsawa sai data kada tana rawan baki tace dama daddy na sani zaki fada min yau ko hukuncina ya hau kanki.
Kuka ta fara ya sake fadin wallahi ko ki fada ko yau gidan yayi maki tsami da sauri yaron da ya jawo maganan muke fada akan shi yace.
Daddy ranan da kukai maganan ne maman mu tace taje ta labe taji mai kuke ma taro har da baba na dawanau.
Innalillahi ya fara ambatawa a bakin shi yanawa hjy maryam kallon tsana a fili kafin yace maryam abin naki har yakai can don kawai zan gana da yan uwana har ki tura min yara suyi muna labe ke a dole sai kinji kinga komai a rayuwan ki ?
Tir da wanan rayuwan da kika koyawa yara nan ya juya gurin ikilima da idon shi yana cewa ke kuma nasan maganin ku kafin ku karasa gurbacewa a gurin uwar ku ai.
Kai ranan dai sarka tayi halinta a gidan kawu don gidan ya rikice a baki daya don sarka gidan ta fadi kasa kowa ranshi babu dadi a ranan.
Don hjy maryam ta fadi har maganan da sukayi da mamu ranan cikin fadanta haka yasa hjy jummai hawa sosai.
Sai fada take da mamu wanda mamu na tsaye tun amsan farko da ta bayar Amma ta kada mata kai tayi shiru taja bakin ta gum tana sauraron ta.
Ganin hakan tana cin mutunci a gaban kowa duk abinda yazo bakinta na aibanci gareni ko mamu fadi take ba jin nauyin kowa a wurin.
Kawu da har ya shiga part din shi ya fito yana fadin kowa ya koma gurin shi a barta taita haukan ta aure dai ne ba fashi har salma da ikilima in Allah ya yarda rana daya zan wanke su gaba dayan su gidan nan.
Dama shi mutum in yayi ilimin iya shege idan ya rika sai ya koma yiwa kansa ai gaskiyar maimuna da tace albarkacin mu danki ya samu a gurin ta ta yarda da auren don haka na gode tunda har naci albarka gurin ta nida mahaifiya don mun fada taji.
Sai ga hjy na kuka da hawayen ta abinda yasa jikin duk wanda ke gurin sanyi ke nan itama hjy maryam din kuka ta aza wai har ikilima nawa take da zaice zai aurar da ita.
A cikin part din mu tunda kawu yai furucin sa na tabbatar da gaskiyar maganan ashe ba kake ikilima tayi min ba haka zancen yake na yanka wani uba ihu a gurin mamu ta bugeni a baki na shige dakin da sauri ina mai ci gaba da kuka ni kadai.
Mamu na shigowa falon ina takure a kasa gefen kujera nace mamu wai da gaske kawu keyi zai mun aure da ya umar don su Aisha a hanyar dawowan mu sun fada min ko waye ya umar din cikin yaran hjy.
Mamu ki fadawa kawu ban son shi don Allah a mayar dani gidan baffa na misau da ai min wanan aure.
Wani irin tsawa ta daka min saida na firgita na manne da kujeran dake kusa dani tace ke har kinsan wani so can yanzu.
Halan shima an fada maki yana son nakine ba biyayya yakewa mahaifin shi ba dake zaki kasayin abinda yayi ko butulci zakiwa kawun naki ne yanzu bayan ya gama inganta maki rayuwan ki na baya har kike fadi yanzu da bakin ki wai a mayar dake misau gidan baffan ki.
Kaina dake dunkule na sake dagowa ina fadin don Allah mamu ki taimake ni ke kadai nake da a garin nan ki hana aimin wanan auren don Allah mamu na karasa cikin kuka mai ban tausayi da marairaice muryana.
Au sayadi har kawun ki zai saki abu ki iya watsa mai kasa a ido ke nan ban sani ba ashe shi yana ganin yayi bugun gaba dake ya nuna ma duniya shiya isa dake kike son bashi kunya to ki matsa har ya sani baki da biyayya kamar yadda ya zata zaki mai.
Tana fadin haka ta shige uwar dakin ta itama kukan take a daki data shiga abin duniya ya taru yai mata yawa dama tasan za a rina duk ranan dana tsunci zancen.
Jin shiru mamu bata fito ba naci kukana ya isheni a gurin sai yan kanne na da suka zagaye ni kowa yai tagumi saman kujera sun zuba min ido suna kallo na kawai.
Na mike da kyat na nufi part din Amma a cikin kuka da yai min yawa har ya fara sakar min da ciwon kai lokacin.
Ina shiga na samay ta saman sallaya tana sallah isha,i lokacin ban ma san lokaci yayi haka ba sai dana fito zan shiga wurin ta naga ko ina yayi duhun dare.
Ban damu da wai tana sallah ba haka na zube a gabanta ina kuka Allah yasa ashe tahiyan karshe takeyi zaune.
Cikin kuka ina fadin wayo Amma ki ceci rayuwana ki taimakeni su kawu da mamu zasu ci amanan yar marainiyar Allah da suka dauko.
Sun rabani da yan uwana da sunan karatu Amma sunzo nan zasu min auren dole kuma yanzu Amma an tsaneni gidan ga dama ba a sona ban dauka har da kawu da manu basu sona ba sai yanzu Amma.
Amma son Allah kisa a mayar dani gidan mu inda aka dauko ni kar ai min auren nan wayo ni amma na shiga uku na lalace agarin mutane.
Ban dauka takai adduan da takeyi ba ta shafa ta dago cikin damuwa da kulawa a gareni tana fadin haba A ruwa ba tsana bane wanan so ne kin taba ganin iyayyen da zasu haifi da su tsane shi.
Yanzun ke ba abin alfahari bane wanan hadin a gurin ki yaron da yafi kowa kwazo da sanin yakamata Allah ya zabar maki.
Kwazo Amma wanan mugun da bai sallah cikakke ne zanyi alfahari dashi Amma kin fa sani matarshi kafirane kuma wayo ni Amma su kawu sun tsane ni dana sani inbi su manjo mu koma tare jiya.
Tunda nan ba,a sona an kini har ana sadaka dani Amma sai na fashe da kuka sosai na kasa ci gaba da maganan sai kuka nake sosai.
Su Aisha da sukaji kukana wurin Amma daga dakin su suka fito suma kukan sukeyi daga inda suke tsaye sun kasa furta komai a wurin.
Naci gaba da fadin Amma kin san fa bai sallah ko shigar shi kika kala bana musulmai yakeyi ba bai mu,amula da kowa a cikin yan uwan shi sai kannen sa ranan fa har giya mukaga matar sa nasha a gidan sy kuma ya gani baiyi magana ba.
Amma wanan mugun ai ko kasheni zai iya yadda uwarsu bata son mamu damu din nan a fili suke nuna muna tsana fa.
Ran Amma ya dan tabu da aibanta mata jika da nakeyi da wasu maganganu da nake fadi ba a cikin hayacina ba.
Sai data daure tace yakashe ki hauka yakeyi komai lalacewan shi ai ba zai fara ya baki wani mugun abu ba a gidan sa.
Ke zama aure fa zaki dole sai kin sauke wanan tsiwa naki da kaifin bakin nan na tsiya idan ba haka ba ki sha bakar wahala inkinje masa da rashin kunya haka don kin san su umar bakar zuciya ne dasu shima wanan yana da zuciyan yasa kikaga bai faye mu,amula da mutane ba sosai.
Na kalli Amma da idanuwa da sukai ja don kuka nace Amma kema kin yarda da maganan kawu ke nan yanzu a aurani ga wanan mugun?
A ruwa zan hana abinda Allah yace ayi ne aurene fa sunnan ma,aiki don may ba zan zamo cikin masu so ba nikuwa.
Kaina jijiga nace yanzu na gane Amma yanzun na gane komai wallahina gane dalilin rabani da kakata mai sona da kaunana tsakani da Allah.
Wayo babana wayo daddy na ka dawo ina bukatan ka a yau kusa dani banda kowa sai Allah sai manjo na Addah kuma an rabani dasu anzo nan za a cuce ni.
Amma bata iya cewa komai ba gaba tasani tana kallona kamar yadda kowa yake kallona cikin mutuwan jiki suna sauraron kalamina.
Mamu ce ta shigo falon tana fadin ashe nan tayo wurin ki gwoggo da shirmay ta tazo zata daga maki hankali da daren nan ko ?
Kamar kada inga mamu na fara kuka da karfi ina fadin wayo daddy na ka dawo ka dauke ni mu tafi tare na kwanmace ma in mutu in bika da a zarga min wahala a kaina daddy basu sona basu kaunana sun rabani da manjo na sunzo nan zasu cuceni.
Kayau kayau mari har biyu mamu ta sauke min a fuska sai da nayi mutuwar wacin gadi lokaci guda kafin in tashi in ruga da gudu sai mukaci karo da kawu ya riko ni yana fadin yaya hakane may akai mata kuma ?
Ya sake tambaya a hasale yana fadin nace may akai matane haka fuskanta ya hau cikin takaici Amma tace dukan ta tayi wallahi a gabana .
Ya juya wurin mamu yana fadin wanan ai cin zalin ne maimakon abi yarinya da lalama sai kuma ki hada mata da duka haka.
Ko kene da girman naki za ai maki haka ai ba zaki ji dadi ba lokaci daya wanan wani irin haline haka maimuna ?
Mamu tace yaya don may yarinyar nan zata daga muna hankali haka tazo ta saka gwaggo a gaba tana fadin wai mahaifin ta ya dawo ya dauketa hannun makiyanta.
Kawu yaja tsuki yana fadin banji dadin haka ba wallahi ba abakin yara yan uwanta ya kamata yarinyar na taji magana nan ba taji kuma sai a hanata shiga wani hali.
Zaki samu yarinya da duka kamar jaka dawani kike son taji dukan ko wanan magana kawu yayi fada sosai kafin ja hannu zuwa wurin kujera ya zaunar dani a kusa dashi yana kiran sunana da Fatima.
Share hawayen ki kinji ki saurare ni mu nan da kike gani kaf ba makiyan ki bane mu illar masayon ki kina ganin ni zan cuce ki ko mahaifiyar ki koko hajiya zata hada baki damu ta cuce ki na girgiza kaina alaman a, a gare shi.
Fatima kin taba ganin inda uba yaki yarsa yayi abinda zai halakata ko baki dauke ni mahaifi bane a gare ki cikin kuka nace kawu na dauka Amma don Allah kada ka hadani aure da mijin arniyar nan koma waye ka bani ba wanan da bai sallah ba yana auren kafira.
Kawu yadan runtse ido yace naji to ki kwantar da hankalin ki yanzu zamu san abunyi amma fa sai kin kwantar da hankalin ki haka zai faru ko kina son gani bacin raina ne dana mahaifiyar ki.
Na girgiza mai kai ya kama min magana a cikin nasiha da lalashi har ya samu na rage kukan da nakeyi din sai kuma ya lura da rawan darin dana soma a lokaci guda haka yasa yakai hannu shi a goshina yaji jikina ya gashe gaba daya.
Da sauri ya mike yana fadin ina zuwa ya fita daga dakin sai can gashi ya dawo da goran ruwa da serchers din panadol a hannun shi ya bare ya bani biyu yace in sha.
Nasha yace in samu wuri in kwanta na mike ya tambaya ina zani nace part din mu yace dawo ki zauna nan guri hajiya ban yarda ki koma wurinta tunda bata san ta rarashe ki ba.
Ban zauna ba nace a wahalce sallah zanyi ya gyada min kai na shige dakin Amma na barsu a falon suna ma mamu fada a kaina.
Na dade a ban dakin ina kuka kafin mama hadiye ta kwala min kira na fitoda kumburarun idanuna ina neman hijab.
Aisha mama ta kwalawa kira tazo tace kawo ma Fatima hijab ta saka sallah zatayi ta koma da sauri ta shigo dakin Amma ta kawo min .
Rana dai a dakin Amma na kwana har dare barci yaki zuwa min sai tunanen banza nake barkatai a raina ina jin Amma ta tashi zata je alwala tana magana ita kadai.
Wanan rayuwan damay yai kama ace ta ko ina babu dadi duk jummai ta rikita min rayuwan gida wanda ma bakayi zaton zai iya abu ba halinta ya koya mashi.
Mata kamar ibilishiya kun hana min farin ciki a rayuwana dana iyalina baki daya wanan yaron dake kokarin ganin ya gyara tarbiyan gidan shine kuma yazamo makiyin su a yanzu.
Taja wani uba tsuki ta dan dade a ban dakin koda ta fito ta samay ni a zaune bakin gado ta kalleni tana fadin tashi kikayi nace banyi barci ba dama Amma.
Ido ta zaro waje tana kallona yar nan ai gara ki ba kanki lafiya ki runtsa shima wanda ake rikicin kanshi nacen bai san abinda akeyi ba yanzu.
Wuce ta nayi ba tare danayi magana ba na shige ban dakin nima alwala na dora na fito na tayar da sallah koda na sallamay na dade a gurin zaune na hade kaina da gwiwana ina hawaye.
Ban san lokacin da kukan nawa ya tsananta ba har ya fito fili daga inda Amma take tace Allah buwayi gagara musali yar nan har yanzu kukan nan bai kare ba.
Ina kunyi magana da kawun ki yace zai duba a kai kodai makiyin ki za a daura maki ai kyaba kanki hakkuri ko ?
Nace cikin kuka Amma ki taimakeni ki ceci rayuwa ta kada ki bari a aurani ga wanan mutumin don Allah wallahi Amma tsoron sa na nake ji wallahi.
Ki kwantar da hankalin ki yar nan ai tunda na fahinci bakya so ba maiyi maki dole idan kuma sun matsa sai anyi ni da kaina zan warware auren idan naga yana maki ba daidai ba.
Nace Amma baki faga iskancin da sukeyi da matar sa ba ko a gaban kowa ne baida kunyar rungumar ta Amma haka Allah yace ayi don Allah?
Tace ina fa yar nan nima yanzu ai na gano ki sosai ba so hadin nake son ayi ba amma fa kinga sai idan kin kwatar da hankalin ki.
Don kada su dauka kece baki da tarbiya tunda shi namiji yayi shiru ke mace mai zai hana kema kiyi kamar yadda yayi .
Kin san mutane a ruwa sai a dauka baki da kunya da har kika tsaya kina fito na fito da iyayyen ki a kan auren ki gashi kinji har kawun ki ya fara fadin ko baki daukeshi a matsayin mahaifi ba.
Wanda hakan nasan ranshi ya baci sosai ne ga irin abinda yaga kina nunawa akan dan cikin sa kamar kin nuna shi bai haifiki ba ke nan tunda shi yayi biyayya ga mahaifin shi bai musa masa ba tunda ya tunkare shi da zancen.
Jin haka da sauri nace Amma nima in sha Allahu zan dauki shawaran naki kamar yadda kikace.
Tace to kiyi shiru duk abinda sukace kice masu to kamar yadda suke so kinji ko nace to Amma na gode.
Tace nasan manufar mahaifin ku kan wanan hadin shine yaga rayuwan ki dama ya inganta ne kamar yadda yake tausayin ki ke kadaice gun mahaifin ki kuma gashi ba wani mai karfi a gidan ku .
Haka yasa yai wanan hikimar ki samu suma yan uwanki su samu ta karkashin ki suci arzikin da Allah yai maki.
Shiru nayi ina sauraron ta tace ai da farko itama uwar taki tayi wanan haukan sai dana zauna muka fahintar da ita manufan yin hakan ta kafin ta sauko ta yarda da auren .
Don ba wanda ya zaci haka daga gurin ki tunda ai kina da ilimin ki yanzu kin san abinda ya dace mai kyau da marakyau ashe abin ba haka yake ba ke a gurin ki.
Jikina ya fara sanyi don tulamin kasan da Amma keyi don dai kawai taga hankalina ya kwanta a lokacin.
Na nisa kafin ince Amma nifa duk wanda kawu zai ban ya bani amma dai ba wanan dan hjy ba tunda ta nuna bata so na shima nasan ba zaisoni ba Amma.
Tace kwantar dai da hankalin ki yanzu abinda nake so dake shine ki samu iyayyen ki da safe ki basu hakkuri akan abunda kikai masu su yafe maki.
Sanan da kike fadan wau ba zai soki ba ai halin su ba daya ba da mahaifiyar sa kuma ke mace ce A ruwa zaki iya jan hankalin duk wani da namiji komai shekarun shi ko mukamin sa balle umar da yake mai saukin kai wani lokaci.
A hannun mu fa yake har yanzu ko da kike wanan maganan da uwarsa zata iya raba sa da abinda yake so da nine mutum na farko da jummai zata rabashi dani a duniya.
Sai dai ba yadda zatayi jinina ne shi din ko taki ko taso dole ne diyan ta su bini don nice dai kakar tasu balle ke da zaki zama matar shi nan gaba tasan lokacin da zaki kama abinki ga hannu ne.
Kai na dago na kalli Amma don jin furicin ta na karshe a gare ni sai dai ban iya furta komai ba don yadda nake jin bakina yayi nauyi ga magana yanzu.