SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Wana ke nan yana tsaye aka sauke komai da yazo dashi gidan inda ya kasa komai hudu kamar yadda suka tsara da ubangidan nasa tun a kasuwa in yazo za a yi da kayan a gidan.
Bayan ya gama rabawa ne ya shiga ciki ya kira dukka matan gidan harda hadiye dake part din su ta fito kowa da mamaki akan may ake neman su a farfajiyan gidan.
Hjy Jummai bata taso ba sai da dole ya sheda mata abinci aka kawo gashi can a farfajiya ya zube.
Da sauri hjy ta taso jin abinda ya ce mata din sai dai tana tunkaro wurin ta hango yadda aka kasa kayan abincin sai ranta ya baci taja tayi turus ga kuma kowa na fitowa daga part din shi bayan kiran su suma da akayi.
Wanda da can baya idan an kawo kaya ita kadaice mai bayar da ikon yadda za a yi da kayan a gidan tana karasowa ciki fada tace kai Amadu ya naga haka kuma ?
Don har yanzu da Amadun shi, da yazo gidan take kiranshi ita da yaranta ba kamae yadda maigidan ya mayar dashi Ahmed kowa ke kiranshi dashi ba yanzu
Cikin wani murya tace kai Amadu ya nags haka kuma yace hjy may kika gani kuma abinci ne aka kawo Alh yace in mikawa kowa nata a hannu ta idan na kawo ba wani abu bane ai.
Kaba kowa nasa kamar yaya ta bukaci kari bayani daga guri Ahmed din daya mayar da hankalin shi wiri kayan.
Yace eh Alh ne yace indan nazo inyi hakan da kikaga nayi din shine dalilin kiran kowa don ta kwashe nata a idon ta.
Eh lalai wuyar ka ya isa yanka Amadu a gidan nan idan gaskiya ya shuka shi Alhjin yazo da kansa ya bamu din amma da yake yasan bai shuka gaskiya ba shine kai issashe ya turoka kai wana rabon.
To ka koma ka fada mai wana rabin baiyi ba a gurina babu wanda zai raba muna kan gida saboda a gyarawa wata rai taji dadi a cikin mu akai hakan ko ?
Don samu wuri to ba za a raba muna girki ba don kawai wata can a gidan nan sai ka hade shi kamar yadda ka kawo shi ka koma ka fada mai nace ba za, a raba ba.
A, a hajiya Jummai ke wa ga yadda mai gida yace ayi mai da abinsa zaki wani ce ba za ayi hakan ba to mukan namu kwasa zamuyi duk wanda zai tsaya bin dokan ki sai ya tsaya ya biki mukan mun bar bin dokan wata mace gidan nan kuma tunda ba ke kika ajemu ba.
Hadiye ce data iso gurin yanzu take wanan maganan ga hjy jumman ta kara da fadin Ahmed wanine namu daga ciki mu dauka.
Salati hjy jummai ta saka tare da fadin yau ni jummai naga abin al,ajabi abin mamaki ke Hadiya kin kasa zaman gidan mijin ki kinzo nan zaki bata muna namu zaman.
Duk da maganan ya batawa hadiye rai bai sa ta tsaya mayar da martani ba alokacin sai ma umurtan mazan dake tsaye a gurin da tayi akan su dauki buhuhunan su shiga muna dasu sassan mu takare da fadin idan baki da niyar daukan naki kya iya barin shi a gurin.
Tana tsaye tana kallo hadiye ta umurci kattan nan su saka muna kayan abinci a part din mu dole muka bar wurin ba shiri don mu nuna ma mazan wurin da zasu aje muna kayan abincin don akwai store da kitchen a part din kowa dama.
Fin karfi ne yasa dole ake girki gaba daya a gidan na kowa da kowa don ra,ayin uwargidan namu ran gida.
Sai da Ahmed ya tabbatar da an shigar wa kowa da nasa bayan ya mika masu kudin cefane yabar gidan zukatan kowa cike da farin cikin samun yancin kai a gidan ranan.
Ranan ba karamin jidali suka sake yi da Alh sani da hjy jummai ba don ta nuna bata yarda da wanan tsarin raba tukunya a gidan ba.
Inda shi kuma ya dage akan hakan za a yi tunda yana da halin yi kuma mahaifiyar shi ta umurta da ai hakan a gidan dole ne kuma kowa yabi dokanta har shi.
Ranan dai fadan hjy jummai bai tsaya ga mijin ta kadai ba har tsohuwar gidan ta hada ta fada mata abinda ke mata zafi gamay da ita akan zaman ta gisan dasu.
Har tayi ta gama babu wanda ya lekota daga sashen Amma don Amma din ta hana hadiye ta tanka mata tace a barta da zafi abinda ya samay ta ya fi komai ciwo a zuciyar ta.
Sai Alh sani ne da yaga abin nason ya wuce wuri akan mahaifiyar tashi ya fito da kanshi ya tsawata mata.
Ganin ba wasa ga maganan daya furta akan idan ta kara tankawa a gurin zai dauki mumunan mataki a kanta a lokacin.
Tuni ta bar wurin ta koma dakin ta tare da kamay bakinta tayi shiru don tasan zai iya yin abinda yace din wanda tasan akan mahaifiyar shi zai iya yin komai.
Yar ta ta uku ce ta fito daga daki a natse don tunda aka fara maganan tana ji bata fito ba sai da taji shigowar uwar tata ta leko falon nata ta samu guri ta zauna daga gefen uwar tare da kura mata ido.
Jin uwar taja tsuki yasa ta kara dago kai ta kalli uwar tasu kafin ta soma yi mata magana a cikin natsuwa tana fadin.
Mama maiye acikin yin hakan da har kike tayar da hankali ki kan dan wanan abi tunda baba ya zabi a raba ai shike nan ko shi yaga zai iya tunda ba kudi ki bane.
Ni ina ganin ai sai ki kya,, , , , , , , , tsawan da uwar ta daka matane yasa bata karasa abinda tai niyar fadi ba a lokacin inda mahaifiyar taci gaba da fadin wallahi salma ki fita idona a gidan nan.
Idan kema son samay ki kamar yadda suka samu ubanki suna juyawa ni ba su samay ni ba kuma ba zasu taba samuna ba.
Yarinya kamar ba nace ba baki san kishin uwarki ba ko kadan ki sa may yin haka ke nufi kuwa a gare ni a gidan nan hakan na nufin durkushewa na ne ga idon kowa yau ace har an samu macen da akanta za a rushe abinda na dade ina kafawa a cikin gidan don wata can mace yar uwata.
Mama ki kwantar da hankalin ki ba wai haka nake nufi ba nima kaina wanan matar sam batai min ba wallahi don bata kaunar ki nima ba zan taba kaunar ta ba a raina.
Kin san da hakan zakice in kyale saboda ita ai min yadda aka ga dama a gidan nan wallahi bai wanan matar ba a duniyan nan.
Mama ni naga idan kina irin haka sai su dauka abin yaci maki rai ne sosai har kike wanan magana tunda gaba na da yawa mamaki faketa har gaba ai zaku hadune da ita in tana ganin sunyi maki haka yanzu sunji dadi.
Nan gaba zaki kama su a hannun ki amma fa sai idan kin kwatar da hankalin ki har wanan munafukan maman su Rashida ni sam ban yarda da ita ba a gidan nan .
Don da tana bayan ki ai da zata baki hadin kai ku hada kai kar hakan ya faru amma sai kika jita shiru batai magana ba sai komai ya lafa zaki ganta nan tana maki dadin bakin data saba.
Sannu a hankali maganar yar tata ke shiganta wanda yasa a hankali ta fara saukowa daga zafin da zuciyar ta ke mata a lokacin.
Kafin suyi magana wayan uwar yai kara inda ta kasa duba mai kiranta a lokacin sai yar tata ne ta iya yunkurawa ta dauki wayan tare da fadin yaya Abbsa ne ke kiran ki mama.
Ki dauka uwar tace mata don yadda take ji ba zata iya daukan wayan kowa ba a lokacin salman ne ta dauki wayan yayan nata.
Bayan sun gaisa yake tambayan maman nasu tace gata zaune tare damu bata wayan man yace wa kanwar tasa bro ka kira anjima don yanzun bata iya daukan wayan kowa.
What yace cikin wani irin murya tare da fadin may ke faruwa da mahaifiyar tasu ce sai salman tace kawai dan matsala aka samu a gida yau da ita.
Kinga fito fili ki fada min abinda ke faruwa cikin tabe baki tace akan dai wanan matar ta baba ce wai Amma ta tsaya mata akan su raba girki a gidan kowa ya dinga yin nasa a part din shi.
And so what ya furta sai may idan anyi hakan ai an hutar da mamane da wani abu salma tace shi nake fada mata ai yanzun mamane bata ganewa.
Yace common bata wayan muyi magana ta karawa uwar wayan a kunne taji dan na fadin mama akan dan wanan maganan kike tayar da hankalin ki a gidan.
Bayan kin san kina damu gani ga yaya Habbib ga su salma da Abba karami akan may hankalinki zai tashi haka kin san dai zamu iya tsare maki komai a gidan yanzu.
Abbas ba zaku gane abinda ke tayar min da hankali bane ku yarane har yanzu No no no mama kibar fadi hakan don Allah.
Yanzun dai ki kwatar da hankalin ki don Allah wanan maganan kada ya tayar maki da hankali zanyi magana da yaya habbib asan abinda za a yi kan maganan .