NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:08 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , ,

Tun dasowan shi gida zuciyar shi take cike da tunanen wanan al,amarin bai taba gaskata yarintana a fili ba sai yau din da yai min kallon tsaba.
Tsuki yaja yana gyara kwanciyar shi tare da lumshe idanuwan shi ya rasa gane dalilin nacin daddy akan sai ya auri wanan yarinyar wanan ai wahala kawai daddy yake son dora min.
Yarinyar da ma kila yanzu take shirin fara period din ta ko ta fara ma ai wanan bada wani dadewa ba can.
Juyi ya kara yi sai jin hannun merry yayi a saman jikin shi tana sauke numfashi tare da fadin mey yasa bakai barci ba dear ?
A hankali ya sauke numfashi yana kai hannun shi saman cikin ta ya dan shafawa sake tambayan shi tayi may ke damun zuciyar ka haka ?
Yace nothing kai tsaye tare da dan sunsunan wuyar ta yana lumshe idanuwan shi a hankali.
Sai dai ba wanda yai magana itama merry kamar yadda ya makaleta haka ta manne a jikin shi a haka barci ya dauke su.
Washe gari ma akwai damuwa a tare dashi sai dai yayi kokarin boyewa merry din abinda ke damun shi a wanan dan takin yan cikin halin damu iri iri.
Ga na tafiyan merry da suka sashi gaba ita da mahaifanta ga hjy shi tace ba zancen tafiyan merry din a gurin ta da kuma umurnin bijirewa mahaifin shi data umurceshi yayi ga mahaifin su dake son yayi mai nasa biyayyan kuma.
Wanan abin ne ya taru yai masa yawa a zuciya ya kasa samun natsuwa a tare dashi a cikin dan yanayin da ake.
A gagauce yayi breakfast ya fito don merry na ciki kwance bata tashi ba tun barcin daren jiya din akidar tace bata tashi sai kusan sha biyu ko sha daya da wani abu na safe.
Duk da yasan ba wani itin hurdan nan a tsakanin shi da Nasir abokin shi amma sai yau yaji yana bukatan shawaran Nasir din don shi yafi kwanta mai a rai duk cikin wa yanda yake mu,amula dasu yanzu
Yana fita gidan ya kira layin Nasir sai da Nasir yayi mamakin ganin nomban Umar din dake kiran shi yau yasan tun suna yara suke tare dashi.
Zuwanshi kasan waje ne yayi sanadin raba karfin abotan su sosai suka dan rage yawan hurda da juna da farko Nasir kayi kokari ya neme shi a layin sai ya kasance ba kasafai yake daukan wayan shi ba.
Hakan ne yasa Nasir din ya fita batun shi shima ya hakkura da lamarin umar din a tafi a hakan ko wanan dawowan da Umar yayi kasan bai wuce sau biyu da suka hadu ba dashi.
Shi yasa yanzu da yaga kiran umar din yake mamakin kiran nasa a yanzu din don hakada mamaki ya dauki wayan nasa yana sallama gare shi.
Umar da zuciyar shi ke cike da kunci da takaici daya taro mashi a zuciya sai tunane barkatai a yanzun yana ganin ta hanyar Nasir kadai ya rage mai ya samu mafita da tashi shawaran don shi a bangaren shi abubuwa sun taru sun masa yawa.
Ta yadda ya kasa lalubo don bai son yai wa kowa daga cikin mutanen nan uku butulci a rayuwan shi.
Sallaman Nasir ne ya katse shi a lokacin yaji yana amsa wayan tasa daga bangaren shi amsa sallaman yayi tare da fadin Nasir kana ina ne ya bashi amsa da ina gidana umar lafiya ko ?
Yace kajirani ina hanya yanzu gani tafe gidan daga haka ya kashe wayan yana ci gaba da tukin motar.
Da lalube da tambaya ya samu ya isa gidan Nasir ya isa ya tsayar da motar a kofan gidan ya fito sai da ya dan tsaya yayi tunanen abinda zai fadawa Nasir din ya danna remote din motar tashi motar ta rufe.
Kallon gidan yayi gidsn na a rufe haka yasa ya dubi wayan shi na laluban layin Nasir din yana ganin kamar ya fita dayaga bai zo ba.
Nasir kana inane gani na iso kofan gidan naka a samu get a rufe .
Nasir ya bashi amsa da ina ciki ai tunda kace kana tafe ban fita ba ina jiran ka gani nan fitowa yanzu.
Cikin yan seconds sai yaji ana budan kofan gidan Nasir ne ya fito daga ciki yana washe baki da ganin umar din yana mamaki.
Umar din dake tsaye a cikin wata shada gizna mai kalar ruwan kasa dinkin rigan mai dan karamin hannu din kin bai sauka kasa sosai ba sai gaban rigan da akaiwa dan karamin ado da aninaya kalar shaddan.
Hulan dake kanshi kalan kayan ne yar karama da gani daga waje yazo dasu sai takalama bakake masu daukan ido ga kamshin turaren sa da yakeyi.
Ganin Nasir din da fara,a shima ya yana dan fara,a a fuskan shi wanda bai hana dinbin damuwan nasa ya boyo a fuskan shi ba.
Nasir ya kalle shi yana mika mai hannu tare da fadin abokina yanayin ka ya nuna min akwai damuwa a tare dakai mana yau.
Dan murmyshin da baikai ciki ba ya kara kakarowa a fuskan tashi yana rike da hannun Nasir din yake fadin gani dai Nasir yau garin babu dadi a gurina.
Nasir ya sake hannun nasa yana fadin subbahanallahi mu shiga daga ciki mana mu tsaya nan waje muna magana don naga maganan mai muhinmanci ne sosai ke rafe dakai.
Umar yace kasan yanzu kai magidanci ne ba zan so shiga gidan ka kai tsaye haka ba Nasir.
Nasir dai yayi murmushi yana fadin ka wuce hakan a wurina umar har abada ko da ka yar da Friendship din mu ni ban yar ba a guna don haka ka shigo kawai ciki malam nan kamar gidan ka ne ai in ga zumunci.
A tare suka shiga falon Nasir din wanda umar din kalamin Nasir yasa yaji ba dadi a ransa don gaskiya ya sake abokin shi na kwarai mai kaunar shi tun farko.
Suna shiga Umar ya fada a saman kujeran farko na shiga falon yana lumshe idanuwan shi a hankali kallo daya zakai mai kasan yana cikin tashin hankali.
Nasir ya tsura mai ido ya kasace masa komai har tsayin dan lokacin kafin ya dago ya dawo kujeran dake fuskantan na umar din.
Yau yanayin abokin nasa ya bashi tsoro don yasan halin sa idan abu ya damay shi sosai yake ganin sa hakan .
Da kyat nasir ya bude baki yace mai wai lafiya mayke faruwa ne haka abokina don yanayin naka ya fars rikitani gaskiya.
Maimakon Umar din ya bashi amsa sai ya koma kwantar da kanshi saman kujera ya daga kai sama tankar wanda ke tunane.
Naris daya kura mai ido yakai hannun shi saman kafadan shi yana fadin be a man abikina ka fada min abinda ya faru ko zamu samo mafita.
Saida umar ya sauke ajiyan zuciya ya dago kai yana kallin nasir din tare da fadin Nasir ina cikin tsaka mai wuya akan mutun uku daddy da mama da kuma matana dana fadama na aura tana nan ta biyo ni da tsohon ciki tun bayan tahowana.
Nan dai Umar din ya labarta mai komai dake faruwa dashi wanda ya rasa shawo kan matsalan da kan shi.
Nasir ya jinjina kanshi yana fadin lalai abokina kana cikin matsala sosai sai dai idan mun kwantar da hankali mukabi maganan a sannu ko wani zamu samu mafita akansa da yardan Allah.
Jin hakan ya sa umar din yadan fara samun natsuwa yace na rasa yadda zanyi ne Nasir don mama tana kan bakanta auren sauran yan uwana bai daga mata hankali ba kamar nawa.
Nasir ya murmusa yana fadin tana da nata dalilin in kayi la,akari da halin su na mata akan kishi don kaga ba wani shiri bane sosai a tsakanin diba ga yadda ita maimuna din ta auri daddy yanzu.
Umar wanan bai isa ya tayar ma da hannkaliba haka har yanayin ka ya nuna kamar wani abin tashin hankaline ya samu haka.
Umar yace maganan ka gadkiyace don yadda da farko mama ta matsa muna mu dawo kasan nan mu kwatar mata inci a gurin daddy da kishiyoyin kai har Amma abinda take fada muna a kanta muna can babu dadi in gajarce maka.
Sai bayan mun zo ne din muka samu abin ba haka yake ba don da farko har ina mamakin sauyawan ita maimuna din ga yadda mama ke fada muna maganan ta muna can.
Sai gashi mun samu maimunan tana binta sauda kafa saidai ita mamadin bata bukatan hakan don tana ganin wai don a kuntata mata ne maimunan ta shigo gidan.
Tsuki Nasir yaja yana fadin wanan ku maza ba damuwanku bane ai akan wanan bamu da matsala nake gani yiwa daddy biyayya gare ka ya zama dole amma fa sai ta hanyar yiwa mama hikima ka nuna mata kana bayan ta a yanzu dari bisa dari ka yarda da maganan ta .
Ta haka ne har a sannu ka cikawa daddy nasa burin a boye ta hanyar yiwa daddy bayanin gaskiya.
Sai maganan matar ka da zamu fahintar da mama kada wani matsala yazo ya faru da meery din a nan a kuka da ita har daddy kai masa wanan bayanin tunda ita mama ai dole ta yarda shawaran da daddy ya yanke a gidan sa.
Umar da yai kasake yana sauraren Nasir din ya nisa sannu a hankali tare da kada kanahi alaman gamsuwa da maganan Nasir din.
Sai da yaji Nasir yace ina dai fatan ba zaka ha,inci daddy ba ga wanan manufan nasa zaka rike mai amanan yarinyar kamar yadda yake rikonta shi a gidan sa?
Murmushin karfin hali Umar yayi a fuskanshi yana fadin don wanan kada ka damu nasan ta yadda zanyi in farautawa daddy din rai a kan ta idan na inganta rayuwanta kamar yadda nasan shi daddy ke hasashe a gare mu.
Ya marauraice murya yana fadin yarinyar fa karamace sosai Nasir ina zan kaita yanzu ina jiyewa kaina ranan da merry zata fahinci hakan Nasir a raina.
Nasir da yai shiru yana sauraron abokin nasa da yake fadin zaiyi auren yarinyar ne a bisa umurnin mahaifin shi shima kawai.
Can Nasir ya nisa yana fadin Nasir naji maganan ka a yanzu kan yarinyar sai dai ni shawaran da zan baka shine ka rike amana aure yafi gaban wasa wallahi.
Dole ka ba yarinyar nan hakkinta daya rataya a wuyanka koda kuwa ranka ba zai so hakan ba sai ka cire son zuviya a ranka komai zai zo maka daidai.
A fusace ya juyo yana fadin bani da ra,ayin yin mata biyu a raina nasir kafi kowa sanin wanan tsarin nawa tun muna yara banda ra,ayin yin hakan a rayuwata.
Nasir yayi murmushi yana fadin a dai bi wanan a sannu yanzu domi aure wani babban sha,ani ne sosai.
Waya Umar da yai kara ya hanashi magana da nasir din ya bi wayan dake aje a gefen shi da kallo yaga merry ce ke kiranshi lokacin ta tashi bata gamshi a gida ba.
Bai san lokacin da ya saki guntun tsuki ba ya bar wayan bai dauka ba har ya tsunke.
Nasir ya kalle shi yana fadin kayi hakkuri a bokina mu hwada wanan mu gani ko zai fishemu ga wanan maganan kaga daga baya sai mu san yadda za a bullowa sauran magana yanzu a samu ita merry din ta bar kasan nan tukun.
Saboda hakan ne ake son auren yar kasanka don wani tsari na al,adan mu nan kaga a wani fannin mama tana da gaskiyanta .
Don ka riga da kayi kuskure tun farko na auro bare baren kuma yar a halul kitabi da bata sallah kamar mu sai dai shi kaddaran mutum bai wuce shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button