SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Da safe aka sallamoni daga asibitin don sunga zazzabin ya sauka sosai yasa suka ban sallama muka dawo gida a daidai lokacin da mamu ke shirin zuwa dubani.
Sai gamu mun dawo gidan hakan shi ya hana mata fita a lokacin sashen Amma muka nufa har ni .
A can ma shigewa dakin Amma nayi na kwanta bayan nayi wanka sai wani barci mai nauyi ya kara daukana kuma.
Amma tajini shuru ta leko dakin ta samay ni ina barci itama wanka tayi ta wanke warin asibitin da take korafin ya bi mata jiki tun safe take maganan.
Har ta fito ta dawo falo tana mita a cikin ranta na rashin zuwan kowa na gidan kawu ya dubani ba tun tana mita har mamu da ta shigo kawo mata abincin rana ta samay ta a damuwa sai Amma ke fadin.
Ni wanan zama da jummai ta juye min gida dashi yana damuna yar nan a raina ace tunda yarinyar nan ta kwanta ciwo ko karen su bai leko mu ba.
Murmushi mai kama da dole mamu tayi tana fadin babu komai ai gwaggo wanan idan da sabo na saba a cikin sa ni wanan bai taba damuna ba don nasan manufar su dayin hakan.
To Amma a ce yar nan har da ciwo za a hada a kishi haka ?
Ina ciwo ya kauda komai a rayuwa sai yanzu nake tausayawa yar nan nima don irin rayuwan da zata tarba a gidan yaron nan don jummai ba zata bar yan nan su zauna lafiya ba.
Gwaggo duk abinda zatayi Allah yafita don shi yasan dalilin wanan hadin a da can kan na tayar da hankalina don haka.
Sai dai a yanzu banjin komai a cikin wanan barazanan nasu don kamar taki suke zubawa zuciyata nake ji hakan na kara sani fahintar wasu abubuwa da dama dasu.
Don haka gwaggo ki kwantar da hankalin ki kada wanan abin ya dami zuciyar ki ko kadan.
Amma ta nisa tana fadin ki kara hakkuri yar nan don wanan zama sai hakkuri da addua a cikin sa komai yai farko yana da karshe.
Ban falka ba sai wurare n karfe hudu da rabi sallah nayi na dawo falo gurin Amma na kwanta a saman doguwar kujeran falon na kwanta.
Abinci fa Aruwa ki bar cikin ki yana zama da tunwa haka ina yanzu an samu mafita ga wanan maganan taku tunda uban naku ya fahinci dai bakya son hadin.
Dago kai nayi ina fadi Amma da gaske kawu ya hakkura ba a cikin fushi ba tace to yaya zaiyi yar amanan sa tana ciwo haka kan.
Kaina na mayar na kwanta ba tare da nayi mata magana ba ina tunane a raina.
Nan su Aisha suka dawo suka samay ni kwance sukai min yaya jikin na amsa da kyat da sauki.
Basu jima a gurin ba suka shige ciki don cire tufafin su don daga islamiya suke mikewa nayi zan shiga ciki Amma tace ina zuwa nace ban daki.
Ban fito ba sai da alwala na fito na dan zauna bakin gadon dakin na Amma ina karewa dakin kallo yadda yake cike da kaya fam dakin ashe gaske idan daki ya faye tarkace ake cewa kamar dakin tsohuwa.
Murja ta shigo dakin da sallama sai dai da yake nayi zurfi a tunane banji ta ba.
Ta samu wuri ta zauna a kusa dani tana dafani tare da fadin A ruwa tunanen fa yai maki yawa baki ganin wanan hadin bake kadai akawa shi ba ki duba fa Aisha ita murna ma take da hadin nata tun jiya dataji.
A jiyan zuciya na sauke na dago kai ina kallon ta da idanuwa da suke shirin zubar da hawaye don banjin zan iya yin abinda tace Aisha nayi a nata hadin.
Ta kada kai tana fadin kai A ruwa kinfa san kawu ba zai maki abinda zai cice ki ba inkiyi duba ga wanan hadin kinfi kowa fa dace a cikin sa.
Kallon ta na sakeyi tare da fadin uhumm murja ke nan don bake bace a matsayin da nake yasa kike fadin wanan zancen haka.
Ni badon kawu da zai ga nayi masa rashin hankali ba babu abinda zai sa ban nunawa kowa koni wacece a gidan nan ba.
Dariya ta bushe dashi tana fadin yarinya kin maji dadi zaki fada cikin daula har kike yanga ?
Wani kallo nayi mata tare da fadin daula ko wahala murja gun hjyn tasu zaga daulan ko a gunshi.
Ki duba fa yana da mata fa kuma matar tasa ma kafira ce fa wace bata sallah murja kike fadin nafi kowa dace a cikin mu?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:08 – ????????????: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM YA JULLALI WAL, IKRAM, , , , , ,
Nace murja ki gyara kalamin ki kice nafi kowa fadawa halaka murja ku kiran da marigayi tun yanzu shiya fi sauki a gare ni.
Ke kanki kin sani babu wani karuwa ga auren ya umar a gareni murja mutanen da basu kaunar majaifiyata da yan uwana da suka fito tsatso daya.
Haba A ruwa kada kice hakan don Allah karki manta sanaditan fauziya ranan yaya ya kaimu shago ya saiwa kowa abinda ranshi ke so fa ya kuma nuna kulawan shi sosai ga yarinyar a gurin.
Dan dariyan yake nayi mata ina daukan hijjab don ana kiran sallah a lokacin na juyo nace murja son da ba,a iya nuna masu a fili ai raggage ne.
Ina gani da zanje gidan sa a matsayin makiyar su tunda shima dole akai mashi a kaina kamar yadda akai min dole yanzu.
Ina fadin haka na fara kokarin tayar da sallah bina tayi da kallo tana fadin Allah ya kyauta ki dai yi abinda ba za,aga laifin ki ba shine shawarana na kada kizo ki jawa kanki matsalan da bai gyaruwa nan gaba.
Mamu ta leko dakin tace mufito muyi sallah sai ta samu har na tayar da sallah don haka ta hau murja da fada ta fice dakin itama.
Ban fito ba sai kusan takwas bayan nayi sallah isha,i na fito daga dakin ina sayi da hijjab a jikina nan falon na zube Amma ta shafa tana juyowa gare ni tace ina zuwa kuma yanzu nace zanje gun mamu ne in gaida ita.
Tace zauna muci abinci itama yanzu ta kawo min abinci ta fita ba dama in musawa Amma saidai kuma na zauna din babu alaman cin abinci a gare ni.
Ina gurin kawu ya shigo wurin Amma gaishe ta da sauri ba mike daga inda bake don girmamaqa gare shi ina bashi guri tare da mashi barka da dawowa daga kasuwa.
Ya kalleni yana fadin Fatima ya jikin yazun na shiga wurun ku gaishe ki ashe kina nan wurin hajiya ?
Amma tace tunda muka dawo ai tana nan wurina jikin nake son yayi kwari kafin ta koma can din sai dai kagane ta bata son cin abinci ta yaya za a gane tayi lafiya yanzu tun abincin safe da kakai muna har yanzu bata ci komai ba.
Subbahanallahi yace ya juyo gareni yana fadin Fatima kina son ki kashe kanki ne ko yaya ?
Kafin in bashi amsa mamu tayi sallama falon ta kalli inda nake tsaye da sauri na kai rusunne tana fadin tayi halin rashin hankalin nata ko ?
Amma tace wani rashin hankali kuma yarinya bata da lafiya kuma zaki hauta da fada abincin da bata ci muke magana don ban tamtama tun abincin shekaran jiya ne a cikin yar nan sai ruwan shayin da take dan kurba.
To a barta mana cikin wanine ai nata ne idan tace tayrin kan tsiya ke gare ta shima namiji bai muna wanan boren ba sai ke har kin san wani abu auren dole ?
Kawun ki kike son ki watsawa kasa a ido a idon jamma kuma baki isa ba walla, , ,
Hannu kawu ya dagawa mamu yana fadin maimuna idan ba zaki bi yarinyar nan a sannu ba to ki fitar da bakin ki cikin maganan nan ya fada ranshi a bace.
Cikin kuka nace mamu bazan taba ba kawu kunya ba a rayuwa na don kawu mahaifina ne saboda ban taso nasan mahaifina ba sai kawu.
Duk abinda kawu yace inyi duniyan nan zanyi indai ina raye a duniyan nan koda kuwa abin nan mai cuta min ne a rayuwata.
Kaji diya da hikima da hangen nesa a rayuwa Amma ta fada tana washe bakin ta gare su kawu ko cewa yayi .
To Alhamdullahi ina godiya ga Allah daya bani diya masu albarka dama ni nasan Fatima ba zata taba watsa min kasa a ido ba yadda ake tsamani .
Yasa nayi wanan abun da nake ganin haske mai tarin yawa a cikin sa nan gaba ki kwantar da hankalin ki ki taimaki rayuwan dan uwan ki Fatima wanda yake gab da fadawa ga halaka .
Rokona Allah a kullun in ga rayuwan ya dauro a ta farkin addinin musulunci sai gashi umar yana gab da rushe min wanan mafalkin nawa a kanku.
Kada tsoro ko razanan matar shi ya kamaki a zuciyar ki zaki shiga da haske irin na salama ki shiga da akidarki da addinin ki ya koyar dake fatima.
Ina tsaye gare ki ga duk wani al,amuran rayuwan ki fatima dashima kanshi umar din duk cikin yayana umar yafi kowa zafi dakuma saukin kai wayewan shi bai kashi ga barin muna biyayya ba har gobe hakan yasa nake alfahari dashi a cikin yayana sai kuma ke yanzu dana buga gaba dake baki watsa min kasa a idanuna ba Fatima.
Ubangiji ya albakaci auren ku dashi abinda muke hasashe a kanku ya zamo mai albarka a garemu baki daya.
Ina son kada kiji komai akan mahaifiyar shi hjy duk wani barazana da zasu kawo maki ko mahaifiyar ki kada ki dauki wanan wani abu komai zaizo karshe da ikon Allah.
Kukana ya yawaita wanda hakan ya tunzura mamu tace shi kuma wanan kukan na maye kawu yace maimuna ki fita falon nan don Allah ta danyi murmushi tare da mikewa ta bar falon ba tare da fadin komai ba.
Kawu bai fita ba sai da yasa na zuba abinci naci yana ta kara kwantar min da hankali yayi da Amma kuma ke masa korafin gidan shi yace zai dayki mataki ga kowa yana sane da komai dake faruwa a gidan.
Sai da yaga na dan cinye shikafan dana zuba a plate yayi muna sai da safe ya fita daga part din.
Da safe ma da muka tashi nace zanje school Amma kin yarda tayi wai jikina bai gama warwarewa ba in bari wani sati in shiga kawai tunda gobe jumma,a dole na yarda da hakan ba don naso haka ba.
Hakana na wuni a kwamce lalace daga tunane sai barci har lokacin babu dan gidan dake shigowa wurin Amma kamar hadin baki har yar gaisuwan safen da suke mata ma ni banga sun shigo yi mata shi ba haka yasa na yarda hadin baki ne kuma sun hani diyan su da raban kakar tasu yanzu.
Washe gari safiya jumma,a kawu bai faye shiga kasuwa ba ranan jumma,a yana wuni ne tare da iyalin shi a gida sai dai idan wani abu maimuhinmaci ya fitar dashi lokacin zuwa kasuwa.
Wayan Ahmed da bai gani ba tun ranan da ya kaini asibiti ya kara kira yayi sa,a Ahamed din ya daga kira don kawu har gidan yake ya samu gidan nashi a rufe kuma wayan shi bata shiga hakan ne ya kara daga hankalin kawu.
Ahmed may ke faruwa da kaine kwana biyun nan kai baka zo ba naje gida a rufe kuma wayan ka baya shiga ?
Yace Alh na danzo gidane gani hanyar dawowa kano kana jin maganan sa kasan baida lafiya ko damuwa na damun sa sosai.
Amma da kasan zakai tafiya ai sai ka sanar dani ko ka barmu nan hankali a tashe yace Alh ayi hakkuri nima tafiya ya dauro min ne ba shiri.
Allah ya kawo ka lafiya kawu yace yana kashe wayan dake hannun shi din mamu sake gefeb shi tace ka samay shi ke nan yace eh wai garin su ya tafi tafiya ta kama shi can .
Allah ya sauwaka mamu tace tana tatara kayan abinci dake gefen shi na faten waken da yasha da don karyawa safe gare shi.
A daidai lokacin ne Umar yayi sallama ya shigo falon sai da suka gaisa da mamu tare da tambayan shi merry ta fita.
Gaisawa sukayi da mahaifi nasa da ya lura dan nasa ya fada sosai a idon shi ya kalle shi yana fadin dattijon gida may ke faruwa da kaine kwana biyu kai wanan fadawan haka ne ?
Umar ya dan shafi kanshi yana fadin daddy al,amurorin yau da kullun ne kawai sai kuma zancen merry da muke muhahawara da mama a kanta.
Hannu ya mika yana dauko tooth pick saman table din dake gaban shi yace wani abin kuma matar naka tayi mata kuma ?
Yace a a daddy akan dai maganan komawan merry din can gaban iyayyen ta ta haihu ne mama ta nuna bata yarda ba da hakan.
Kawu yace akan wani dalili nata zatace bata yarda ba tunda kai ka yarda da hakan ita ke auran maka itane ?
Idan ma ta rike ta a nan wani abin zatai mata yaushe jummai ta tsaya taba kanta kulawan daya dace balle ta ba wani can ?
In ma dai din zata bata zata iya da al,adan sune ko tasan yadda al,adun su yake ne a nan wanan maganan banza ne yaushe ne ka shirya tafiyan nata ne ?
Ya tambaye shi yana kallon shi a fuska yace daddy naso next week mu tafi ne sai daga baya idan ta haihu zan dawo in karasa aiyukana a nan din.
Ita matar taka na nan may kake nufi da ita idan ka tafi ya dago kai da mamaki yana kallon mahaifin nasa tare da saurin dukar da kai kasa yana fadin.
Daddy naga kamar ai karatu take yanzu tukun ko ?
Karatun a yanzu ba zai hanani fitar dasu gidan nan ba kamar yadda nayi niya a raina karshen shekaran nan nake son gaba dayan su a wanke su.
Idan kana da bukatan taci gaba zata karsa a gidan ka idan taje idan baka da ra,ayin hakan sai ka barta a gida kamar yadda uwayen ku suke suna bautan aure.
Sai dai saboda bambamcin zamani kaga ita zata iya karasa nata karatun har ma ta dora ga hakan idan da halin yin hakan a wurin ka.
Zama ya gyara zuba na karyo mai a goshi don baiyi tsamanin har wuri haka kawu yake nufin yin auren ba.
Kawu ya kalle shi yace ko kana da magana ne naga kayi shiru ?
Daddy banda magana sai dai ta fanin mama ne ban san yadda zan fahintar da ita ta gane ba har yanzu.
Indon wanan ka barni da ita zan mata magana sai dai abinda nake so dakai shine ka kula da addinin ka a duk inda kake umar don shine haske da jagoran ka gobe kiyama kada ka bari rudin shedan ya rude ka don Allah.
Daddy insha Allahu zan kula na gode Allah ya saka da alherin sa yace tare da yin shiru gaba daya ya dukar da kai.
Ya fito ya shiga part din mahaifiyar shi ya gaida ita ya dan dade a gurinta suna hiran zancen aikin da habbib zai fara nan kasan.
Kafin yai mata sallama yana fadin zai tafi ga mamakin shi har ya bar gurin ta bata tambaye shi merry wace ke dauke da cikin shi a jikin ta ba.
Yana tafiya part din Amma zuciyar shi fam da tunane irin halin hjyr su har ya fada tunanen kodai shine hjyn ta daina so kwata kwata tace bata son wanan choice din daddy haka kuma har yanzu ta kasa na,am da merry a matsayin sarakuwar ta.
To may hakan ke nufi a gare shi ne wai babu yadda zaiyi don mahaifiya ce sai ya basar da zancen kada ya fara zargin mahaifiyar cikin sa haka.
Ni da Amma ne a falon tana zaune nikuma ina kwace a falon ta fuskana yana kallon inda take zaune sai dai a zahiri ba ita din nake kallo ba.
Ya shigo da sallama ya tsaya daga gefen kujera haka kawai ganin sa ya sanya kirjina bugawa nayi kokarin mikewa yayin da Amma ke masa sannu da zuwa ya tsaya a mangali kujera yana amsawa ba tare da ya zauna ba.
Sai dana daga na juyo ina fadin ina wuni Amma tace ke kuma ina zaki muna hiran mu zaki gudu kuma ?
A takaice nace mata daki zan shiga.
Tace wanan ba mai zama bane ai tunda ya zama magidanci yake guduna yanzu.
Nidai ban tsaya ba ya dan kalli bayana ina tafiyan ya dan basar yana zama saman kujera Amma ke fadin.
Kai kuma gaka duk ka ramay mana may ke damuwan ka haka angon karni don nasan matar ka bata nisa da haihuwa yanzu.
Maimakon ya bata amsa sai cewa yayi ita wanan bataji sauki bane har yanzun komai Amma tace gata nan dai kasan yaran nan yan banzan yarane su suka tayar mata da hankalinta.
Yace wasu yara ke nan Amma tace kannen ka mana marasa ta ido da suka koyi mugun abu a gurin iyayyen su.
Kai Amma muke nan gaba daya fa kike nufi tunda kinyi jam,i haka ?
Kaji nace dakai tace tana tsure shi da idanuwan ta tare da fadin na tambaye ka kaki ban amsa ko har haihuwan boyansa kuke yi kamar na auren ?
Murmushi yayi yace ko auren ai ban boye maku ba Amma nisa ne kawai ya hana kuji ai.
Wani sati nike son mu koma insha Allahu don iyayyen ta sun matsa ta dawo hakana gaban su.
Allah dai ya raka taki gona umma ta gaida Assha duk sai yaji ba dadi irin yadda ahalinsa ke nunawa akan merry din yayi kasa da kansa kafin yace .
Nina dauka dake zamu tafi ki kwana biyu muna a can tace in ka ganni lahira maza suka kaini kaidai da ka saba dasu ka karata can.
Yace a a Amma kada muyi haka dake ina kullun addua kike Allah yasa ki goya yayana yau kuma zaki dare haka kiki zuwa don kinji maganan barin kasa zaki inda baki samun fura ko.
Tace ja,iri koma dai maynene ban zuwa idan ka gannin gidan ka naje reno sai in A ruwa ta haihu wanan kan komai nidan duniyan da kuke zan taka idan muna da rai da lafiya.
Ahogon dake daure a hannun shi ya kalla tukun ya mike tsaye yana fadin Amma ni zan tafi kin san yau jumma,a lokacin kurarene.
Zaka gudu ke nan don kaji na dauko ma zancen da baka so ko haba Amma may zaisa in gudu dama ba dadewa nazo inyi ba nazo ganin daddy ne don nasan yau yana gida bai fita.
To ka gada ita mai dakin naka a sauka lafiya sai ka sake shigo ya amsa da nagode Amma yana fita.
Ina jin su daga kuryan Amma inda nake kwance har ficewan shi wasu zafafan hawaye ne suka gangaro min a idanuwana ina tausayin kaina da kaina.