SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Hjy wace ta shigo falon don amsa kiran maigidan nasa bayan sun dan gaisa ne yake fadin wai umar ko yayi maki zancen komawan su can England ?
Tace komawa kuma kamar ya Alh shida yace zai iya kai wata shidda zuwa takwas a nan kawu yace da farko ke nan ko don yanzu dai kinsan matar sa ta biyo shi nan ai.
Gata da tsohon ciki kina nufin a nan zamu bar yar mutane ta haihu muna bayan mu bamu san irin al,adun su ba can.
Alh sai naga itama dai ai yar kasan nance gaba da bayanta har wani al,ada suke dashi daban da namu koma suna da wani yanzu tunda ta auri dan mu ai dole tabi al,adun mu kuma.
Ke jummai ki dinga cizawa kina hura abu kafin ki tauna ke baki gudun wani abu yazo ya samu yar mutane a nan wurin mu.
Da ganin yarinyar fa kasan irin sagartattun yaran nan ne da iyayye suka sagarta tun farko saboda haka ki barshi ya maida ita inda ya daukota shine umurnina .
Maganan daya dauko min na auren ta ya isheni a barni dashi kada ku dauko min wani ina zaune kalau.
Koko so kike su dira garin nan suzo su barmu da abin kunya nan gaba bayan wanan dayayi don haka su tattara su koma inda suka fito.
Tace to amma Alh naga, , ,
Hannu ya daga mata alaman shine umurnin shi hjy ta cika fam ta dade zaune batayi magana ba sai can ta mike zata fita tana fadin shike nan ita mace bata datace da danta sai abinda aka tsara mata.
Shidai baiyi magana ba ya basar da ita haka ta fita tana jinini da korafin tauyewa ne hakan a gare ta don ba karamin shiri taiwa kanta ba kan haihuwan.
Yanzu shike nan duk Alh ya rusa mata plan din ta kan wani dalili nasa can sai kuma ta koma zargin shi umar din ko shi yakai karanta wurin Alh.
Neman dan nata tayi tana fadin tana neman sa bayan ta fito wurin maigidan nasu rai bace.
Yadda yaji muryan ta ya fahinci tana cikin bacin rai sosai bai samu zuwa gidan ba sai da yamma ya shigo.
Tun shigowan shi ya farga da tana cikin fushi sosai har lokacin sai ya soma zargin kansa.
Tun bai zauna ba yake fadin mama lafiya ko naga kamar ranki a bace wani abin kuma ya faru ne ?
Hjy ta dago kai tana masa wani kallon daya kara shan jinin jikin shi sosai da ita.
Babawo yanzu har kakai in kiraka kaki zuwa a lokacin dana bukace kazo gurina da sauri yace haba mama nina isa koda kika kirani a lokacin ma muna jigawa nida Nasir.
Ta kara kallon shi a shesheke tace yanzu babawo karana kakai gun mahaifin ku na hanaka tafiya da matarka ?
Subbahanallahi mama shi daddy yace na kawo karanki akan may zanyi karan ki gun daddy kuma mama ?
Da kyat ta samu ta daidaita natsuwanta kafin tace nasan zaka iya tunda na hanaka tafiya da ita ?
Mama ina mun gama wanan magana dake ko akan may kuma zan tayar da maganan yanzu kuma ?
Kara kallo shi tayi irin duba na tuhuma duk sai yabi ya tsargu don bai san abinda zai biyo baya ba kuma yanzu yadda yaga ta hau din nan.
Tace bawai ya fada min kakai karana bane tuhumar hakan dai nakeyi dama babawo wai may yasa baku gudun bacin zuciyana ne ?
Yace mama idan ni na fadawa daddy ai zan fada maki gaskiya ko cewa nina fada mai din.
Tayi shiru bata tanka ba na dan wani lokaci kafin tace yanzu dai burin ka ya cika amma ka tabbatar da sanin duk wani abin al,ada da akeyi idan mace ta haihu zaka barmuna muma nan ayi kamar yadda al,ada yake.
Dago kai yayi ya dan kalle ta tace eh haka nace babawo don ba zaka maishe mu dakarkarun iyayye ba.
Naka tsarin kaje can ka kashewa kafiran banza kudade munan ko oho kenan mun haifar masu da daga sama.
Ayi hakkuri mama insha Allahu za ayi yadda kikace din sai a lissafo min duk wani abinda zaku bukata a nan din ayi yadda aka saba din.
Tace dama hakan za ayi don ba zan haifawa wata da ba saida lokacin cin moriyan ku yazo wata can daman ta amshe min ku.
Ga mata nan kasan yan asali amma duk basuyi maka ba saida ka tsalaka kaje inda zaka jawo min abin gori ga jamma,a.
Tana fadan haka ta mike zata shiga dakin ta ya bude baki da kyat yana fadin mama don Allah kiyi hakkuri idan ranki ya baci ne ?
Sai ta juyo jin yadda yai maganan kuma sai ya bata matukar tausayi sai dai babu yadda ta iya don hakan da takeyi tana son dasa masu tsorontane a zukatan su.
Ta maida kanta ta juya ta shige umar yaji kamar ya dora hannu akai ya kurma ihu dan tsaban takaici saidai koba komai daddy ya kwatoshi daga tafiyan tunda alama ya nuna ta yarda.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:08 – ????????????: BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHEEM
Ban shiga school ba sai ranan monday kamar yadda Amma tace mun kuma har lokacin a gurin ta nake kwana sai dai danaji sauki ina dan zuwa part din mu in kai wani lokaci a can.
Haka sai yasa Amma bata son inyi nisa da gurin ta ko kadan ko yaushe idan ina gida ina wurin ta zaune idan kuma nazo part din mu zakaji ta aiko wai in zo.
Koda nazo din kuma ba wai wani abin zan mata ba zakaji tace kin je can kin zauna ta dinga matsa maki kawai.
Kawu ko da ya dawo da dan tsaraban Amma kullun wanda muke taruwa dani dasu Aisha mu cinye abin mu sai yan kanne na dakan biyo ni nan part din ta din su zauna tare dani saboda sabon da mukayi.
Wanda hakan yana a kunnuwan mutanen gidan da suke ganin kamar an kaini can gun Amma ne don wani abinda muke kullawa tsakanin mu.
Salma ne ta shigo muna tare da Amma a falon wanda a yanzu zamana a cikin sa yana samun gyara sosai kai da kai ina tsabtace shi.
Wuri ta samu ta zauna ba tare da taiwa kowa magana ba sai Amma ta kalleta tana fadin gaki kamar a jefo ki kinzo kin zaunawa mutane kimkam a kai ?
Cikin wani murya na shagwaba tace yanzu Amma don na shigo gurin ki shine kuma zakiwani ce min na zauna maku kimkam a kai ?
Amma tace kinga sakona nane kizo naki dai ya kawo ki dama ta mike zuwa wurin fridge din Amma tana fadin akwai fura a fridge din ko baki dama ba ?
Aiko ina dashi bazan baki ba son ba don ki nake ajewa ba ta juyo tana fadin Amma ai kin ba A ruwa tasha ko ?
A ruwa ai bake bace don A ruwa ta fiku sanin zafi na da darajana a gidan nan yaushe rabon da na sakaki a idona gidan nan ?
Dama ai hakane sai bare ya zo ya fika daraja kai da gidan uban ka ko baki furta ba mu san da hakan a wuri ki Amma.
Amma tace A ruwa tafi karfin zama bakuwa a gidan nan ko bare don duk daya kuke a gurina tunda suka fara magana ban kulata ba tun shigowanta falon sai yanzu da tayi wanan maganan.
Dadin abindai da ubana ba shegiya aka haifeni ba gida kuma gidan kawuna nazo salma ko anty salman da tasa muke kiranta ban kira ba lokacin.
Tace dama wani yace baki da ubane ko kinji na fadi hakan sallon kuma ki koma kice ga abinda nai maki yanzu daddy ya samay ni da fada.
Allah sarki ai bagware ba bobawa bane kowa yayi jifa a kasuwa yasan wanda ya jefe balle ma kin fito fili kin kira sunana kai tsaye abinda kuke dauka ba shi nake a nan ba.
Kada ki soma ki fada min maganan banza a gidan nan don kina ganin wuyan ki ya isa yanka ke a gidan nan kowa zaki iya fadawa magana kai tsaye.
Cikin bacin rai Amma tace salma ki fice mun daga shiya tunda ba alheri ya kawo ki nan ba yarinyar nan ko lafiya bata da amma saboda bakin halin ku kuda iyayyen ku ba wanda ya iya budan baki ya tambayi jikin ta.
Yanzu kuma kinzo zaki tayar mata da hankali haka muna zaunen mu kalau a nan wanan wani bakin hali ne shin inda uban yar nan yaje ko yau ko gobe iyayyen ku kuma tafe suke sai ko idan zasu tsaya gadin duniya ne in sani.
Mutane a kullun baku da magana sai gori a kan mutuwa to iyayyen naku da suka dauki duniya da fadi su zauna jiran duniya.
Juyawa tayi tana fadin shigowa nan yasa har za a fada min magana kan iyayyena saboda wanan yae sadakan da ake neman likawa mutane.
Kikai kuwa nace mata dama a kwance nake ina magana na mike zaune ina fadin duk mune yan sadakan idan sadaka illace ashe .
Gara wake da kowan wake don a sarafa waken a nau,i nau,i wani ko a kowan yake tsayawa tace may kike nufi nace kije wanda ya turo ki yai maki bayani ni yar sadakace .
Daga hakan ta wuce fuuu ta bar falon nan tabar Amma na sababi da ita bayan fitan ta na dauka zasu dawo da hjyn ta sai naji shiru kuma.
Sai washe gari kawu ya shigo yana tambayan Amma abinda ya faru Amma ke fada mai yadda akayi ta kare da fadin wa yan nan mutane ba mutanen arziki bane.
Ni ba don ka rigada kayi wanan alkawarin ba da an fasa wanan hadin abu tun yanzu yakici yaki karewa haka tun ba,aje ko ina ba.
Hajiya dama ai shine bukatan jummai ta dagawa mutane hankali ba gaira ba dalili ni amsan da fatima ta ba salma yai min dadi.
Da yake basu da tsoron Allah ni ba haka uwarta ta mayar min ba don cewa tayi Fatima tana zaginta ta hanyar diyar tane.
Lalai wa yan nan mutane basu tsoron Allah a rayuwa su yar nan ta shigo muna kamar an jefo ta tazo muna da tashin hankali haka ?
Hajiya nasan halin kowa a gidan nan fa ba sai kin tsaya kina bata ranki ba a kansu ina daga ciki ina jin su ban fito falon ba tunda baji ya dauko zancen namu da salma.
Ya fice tare da yi mata sallama saida takai kofa yake tambayana tace ina ciki na kwanta ne tun dazun yai mata saida safe ya fice .
Umar da merry wace yanzu cikin ta yayi girma sosai suka shigo gidan don yin sallama da iyayyen nasa wanda daga sama sauran mutanen gidan sukaji tafiyan nasu.
Sun dan jima gurin kawu kafin su fito su shiga dakin mahaifiyar shi a nan ma sun jima a dakin merry data kagu su tafi tace zata fara shiga wurin mamu kagin ya iso ta mike da kyat zuwa gun mamun.
Zaki gane kuren ki idan kin san sheri da macuciyar suke kulla maki sai kare ya fiki daraja gidan nan ta fada kasa kasa ba tare da daga murya ba.
Sai kuma ta juya gurin dan nata tana fadin ka sai dai ban yarde maka zuwa gurin maimuna ba yace na sani mama.
Daga haka yai shiru yana latsa wayan shi dake hannun shi ba tare daya sake magana ba sai can dataji shirun nasa yai yawa tace ke nan goben zaku wuce kai sai yaushe zaka dawo idan kun tafi ?
Ina ganin sai ta haihu zan shigo kasan nan ya bata amsa tace aikin dakake a nan fa tunda kace baka kare ba.
Na barshi a hannun wa yanda ke aikin ya bata amsa mata a yanayin rashin son magana don yadda yake ji din a lokacin.
Kasan zaka bar komai da za ayi a nan kamar yadda na fadama ina son ayi ta sake fadi ya dago kai yace amma mama cewa kikayi ai sai idan ta haihu zan turo maku ko ?
Ban yarda da hakan ba yanzu na canza shara kabar komai daya dace a gurina yadda zai ishe mu yace ba matsala mama.
Yana mikewa tace zaka tafi ke nan tunda matar ka ta kasa zama nan din ko ?
Yace gurin Amma zan shiga muyi sallama da ita yana kallon fuskanta yaji may zatace mai sai tayi wani iri da fuska kawai ba tare da tayi magana ba.
Yana ganin haka ya fita kiran layin merry yayi don baida halin shiga part din mamu a yanzu saboda bin umurnin uwarshi.
Merry ta fito suka shiga gurin Amma don yi mata sallama sun dan zauna bayan gaisawa yace Amma mun zo mu sallame kine gobe zamu koma England insha Allahu.
Ta kalle shi tana fadin goben nan dan nan ni na dauka wasa kake min ai da ka fada min ranan hankalin shi yana ga wayan hannun shi da yake tura sako yace.
Ina fatan kin shirya tafiyan ta dan tabe baki tana fadin rabani da shirmay yanzu in ka tafi sai yaushe zaka dawo ke nan ?
Yace gaskiya Amma ba maza ba don zan dan dauki lokaci a can sosai kafin inzo kasan nan.
Amma tace idan ka tafi zancen yarinyar nan fa da sauri ya dago kai yana fadin wace yarinya ke nan Amma ?
A ruwa nake nufi don naji mahaifin ku na fadin karshen shekaran nan zai aurar dasu duka.
Ya dauri fuska kafin yace Amma yaran nan kanana ne fa may daddy kewa sauri ga auren su haka yanzu da wuri ?
Ka tambayi uban nakama shida yake son hakan yarinya ko kallon arziki bata samu gare ka yaushe ka tsaya ma kai mata kallon tsab,
Amma may yasa kika damu zancen auren nan ne haka wanan yarinyar ma fa bata kai wani shekarun aure ba.
Nifa Amma kin sani auren biyayya ne zan maku don haka duk lokacin da kaga ya dacd sai a fada min.
Kallon kai a suwa Amma tayi mai taja tsuki tare da fadin banga laifin ka ba tunda idon ka ya bude yanzu da masu dan bujen nan.
Ban san da su a falon ba dawowa na ke nan daga unguwa nida su Aisha ina saye da les dinkin buje da riga yau anyi sa,a na saka mayafi a jikina .
Sai kitson da ke kaina daya dan fito don daurin dan kwalin danayi sai kamshin da jikina ke fitarwa don daga wurin bukin kawar Aisha muke don tare suka kare karatun su dasu salma akai mata aure.
Yana hangoni yaji gaban shi yayi mumunan faduwa saboda saboda shigata ra yau ya fitar min da surana na asali a fili.
A hankali ya lumshe ido daga inda yake zaune merry ko tana ganin mu ta shiga washe baki gare mu tana fara,a tace dama tana tunanen ta tambaye mu kada ta tafi bamu gana ba.
Kallon inda yake sukayi suna fadin yaya ina wuni kunzo lafiya ?
Ya amsa ba tare daya dago kai ba da lafiya nikan wurin Amma na nufa ina fadin Amma yau duk na gaji wallahi a cikin muryan da ban san inayi ba wanda mai saurare zan dauka shagwane.
Merry ta tace in zo kusa da ita tana son muyi sallama gobe zata koma kasar england maiyuyuwa ba zata dawo kasan nan maza ba idan ta haihu.
Jin haka na yasa Aisha ta ce ba zaki tsaya ki haihu a nan ba mu dauki baby tayi murmushi tace gaskiya ba zata iya zama nan kasa ta haihu ba .
Ban san ya akayi bakina ya furta amma uban babyn naki ai a nan aka haife shi kuma kema ai yar kasan nan ce.
Ba tasan may nake fadi ba sai kallona ina magana tayi tana fadin nayi fushi da kika zo gun grany kika nufa bayan kin gani a falon.
Dan rage murya nayi ina fadin ban kula ku bane a falon sai yanzu.
Idanuwan shi da suka sani saurin dukar dakaina ya dago ya watso min na jin nace ban farga sune a falin ba.
Nayi saurin dukar da kaina kasa tare da juya gurin Amma ina fadin Amma yunwa nake ji wallahi.
Ke yar nan yanzu kika dawo gidan buki zaki kira min yunwa a nan yanzun kuma?
Amma kin san Fatima kamar tsoron mutane take yi taki sake jiki taci komai da aka bamu a gurin .
Shine filancin ta nuna maku asalinta na kwarai ne ai macen kwarai bata zubar da mutuncin ta a duk inda take.
Amma mu zamu tafi sai kuma idan Allah ya kara sadamu da alheri don jirgin mu da safe zai bar kano zuwa lagos insha Allahu.
Yaya tafiya zakuyi ne da gaske Aisha ta tambaya bai bata amsa ba sai mikewan da yayi tsaye daga zaune.
Amma tace miskilin zai koma inda yafi wayau nan kunsan cizon shi akeyi komai tsiyan ka dai daga kauye kakani ka suke.
Ya dan murmusa yana fadin gara sai da kika tsaya akan kakanina da sai ince wani uban nawa kika gani ba kauye ?
Nikan dadi naji har cikin raina sosai jin zasu bar kasan gaba daya ina Allah yasa ma kun tafi ke nan namamajon kawai.
Jin kamshin shi kusa dani yasa na dago kaina shine kuwa ya matso kusa da Amma yana mika mata kudi tare da fadin ga wanan kiyi hakkuri sai idan na yo maki sako kuma.
Ya dan lakuci kumatun ta yana fadin Amma ki kula muna da kanki kin san muna ji dake sosai daga haka ya juya ya fara tafiya merry ma ta mike tana fadin zasu tafi tana kallon Amma din.
Hannu amma ta daga mata tana mata na bebaye alaman a sauka lafiya.
Wanan tafiyan nasu ni ji nayi kamar an min albushir da aljanna don ina ganin ya samu ya kurce masu ke nan ba zai dawo ba kuma nan maza.
Don ko hjy maryam sai daga baya take jin wai sun tafi basuyi sallama dasu ba dan gara ma mamu don shigan merry ta san zasu koma amma batai tsanmanin zai tafi bai sallame su ba ai.
Bata dauki wanan komai ba a gurin ta don ba bakon abu bane haka a wurin ta sai bayan sun tafi ne sai ga Aliyu da sako a boye ya kawo masu yana mai basu hakkurin rashin yin sallama dasu da bai sami daman yi ba.
Hjy maryam.tace ita kan ko ba sallaman baki ai ya gama mata komai ko Allah dai ya kaisu lafiya dashi da arniyar shi.
Sai dai mamu bata ji dadin hakan ba don taso suyi magana dashi a kan merry sai gashi kawai tafiyan shi taji daga sama babu sallama .