SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Bayan su kawu sun dawo gida da washe gari da safe yayi waya da yaran sa maza a kan komai sukeyi su bari su hadu gida ranan talata mai zuwa.
Allah ya taimaka daga cikin su ba wanda ya fadawa hjy su don su a zaton su tasan ko may yasa yake nema su din .
Dan dama Aliyu da suna waya yake tambayan ta baba lafiya yake kuwa tace may ka gani yana nan lafiyan shi kalau,
Daga haka ya basar sai bai dauki abinda muhinmanci ba ranan sai ga Aliyu da habibbi sun iso da rana yan part din su sukai ta murnan zuwan su.
Sun shiga gurin Amma sun gaisa sai dai har yanzu babu halin shiga sauran part din gidan don basu saba ba ma dasu din.
Sai cikin dare umar ya sauka garin don haka gida shi ya nufa sai da safe ya shigo gidan nasu a natse.
Yana saye cikin bakar suith ya kara haske sosai ya goge don yanzu kusan shekara da rabi rabon shi da kasan.
Aisha ce ta fara ganin shi ta fito daga gurin mamu sai ganin mutum tayi tace yaya umar sannu da zuwa ya amsa mata a dakile kamar wanda bai gane ta ba.
Har lokacin yana jin ba dadi a ranshi don zuwan dole dole yayi ya shigo ne da niyar kwana biyu kawai ya koma don akwai aiki mai tarin yawa a gaban shi sosai.
Aisha da kamar dole har ya wuce ya nufi sashen mahaifiyar shi tace ya su anty merry da ummi karama ya amsa ba tare daya juyo ba da suna lafiya.
Suna zaune falon Amma sai gata da murna tana fadin mutanen nan abinsu kamar hadin baki jiya su yaya habbib dunzo yau kuma ga yaya umar yashigo shima.
Cikin fara, a Amma tace ikon Allah duk gaba dayan su sunzo a lokaci daya.
Allah yasa lafiya dai don uwarsu bata rasa abin tsegumi a gaban ta ko yaushe wata kila kuma wani abin suka zoyi sai dai ni bakin cikina da sadauki zuwa ds wanan kafiran haka tsirara a gidan nan.
Dariya suka kwashe dashi suna fadin kai ji amma fa irin ku ne yan sa ido kan mutane.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:11 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM, , , ,
A can garin misau kuma bayan mun dawo wurin manjo na tayar da ita tare da gabatar mata da abinda aka sawo mata yar tsohuwar ta mike jikinta har rawa yake da ganin kayan dake zube a gaban ta.
Gabana ta sai da naga taci sosai sai ta dago kai tana fadin nifa nace banjin yunwa sosai don naci abinci gidan su Atika.
Tace ba zai yuyuba A ruwa yau naji kunya a gidan nan yadda iyayyen ki suka zo ko ruwan gidan nan basu sha ba haka suka juya suka tafi.
Sai ta fashe da kuka tana fadin kai duniya abin tsoro ne A ruwa lokacin da kakanku yana raye muna zaune ne garin ikko dashi.
Sai idan munzo ganin gida muke zuwa nan nahiyar a lokacin mulkin shagari kakan mai kudine sosai yana kasuwanci bayan aikin gwaunati da yakeyi.
Idan zamu zo zaki ce wani sarki ne zai sauka a garin don yawan jamma,a motoci ko tun a wacan lokacin sai mun shigo da guda uku garin nan daya yana dauke damu iyalin shi dayan kuma na makaraban shi sai ta kaya da yake rabawa itace babban mota.
Yan uwa na nisa dana kusa haka zasu dinga tururuwa a gidan mu ana zuwa gaida mu nidashi muna raba alheri gare su.
Saidai kaya mutuwa bata barin wani don wani yaji dadi tun lokacin da kasa ya rufe idon kakan ku sanadiyan hatsarin mota kamar yadda mahaifin ki shima ta wanan sanadin ya tafi haka ma kakan ku don sai gawan su kawai aka kawo muna a gida.
Kuka ne yaci karfin ta ta kasa magana juice din dake gaban ta na dauka na tsiyaya mata a kofi na mika mata sai dai ta kasa amsa tasha.
Da kyat na iya budan bakina da yai min nauyi nima nace manjo ki sha kin san baki da lafiya kada ciwon ki ya tashi don Allah.
Bata karbi cup din danake mika mata ba sai dai ta tsagaita kukan nata tana dan share hawaye ta dan ja jikin ta zuwa dan langa langan dake a matsayin bango a dakin ta jingina jikin ta dashi.
Nima zuciyana babu dadi yadda ta ban dan labarin na dan lokaci kafin taci gaba da fadin watau a ruwa duniya babu gaskiya tunda can haka take don mutum abin tsoro ne.
Kinga bayan mutuwan kakan ku tun lokacin na fara fuskantar rayuwa mai tsanani gashi a lokacin mahaifan ku ba wani girma sukayi ba sosai.
Kafin kice haka abokan kasueanci dama yan uwan shi duk sun wawashe dukiyan daya bar muna haka muka tataro muka dawo sai motar daya mallaka min da gidan daya gina a nan azare muka dawo ciki.
Ashe tsugune bai kare muna ba don nan ma yan uwa sai cewa sukayi suma gidan da muke ciki ya zama na gado duk dasu don gonan su na gado ne mahaifin ku ya noma ya samu aiki a karshe ma ya sayar ya tafi ikko yayi dukiya don haka yanzu rabawa za a yi abinda muka samu shine rabon mu.
Haka ina ji ina gani aka sa gidan nan kasuwa aka saida shi dan kudin da suka bamu dashi na sai wani fili dashi da niyar mu gina idan na samu sarari.
Cikin ikon Allah sai ga amin mahaifin su na nan misau AD Rufa,i ya aiko min da wasu kudi dake tsakanin su da maigidan nawa ban bari kowa ya sani ba na dauki kudin nan na sai muna gidan dashi shine wanan gidan da muke zaune a azare dakika sani.
Da sukaga haka sai kuma suka fara zargina kan na boye wani dukiya dama na hanasu ne don kada a raba tare dasu abu har kotu sai can ne nayiwa alkali bayanin komai.
A ruwa nasha wahalan rayuwa wanda har yau a cikin sa nake tun rasuwan kakan ku zance na dan ji dadi lokacin da mahaifin ki ya taso ya fara aiki a wanan lokacin gaskiya wahala ya kawu.
Saidai ashe shima rayuwan ba mai tsawo bane kwatsam sai ga labatin rasuwan shi a hanyar shi ta komawa wurin aiki munyi sallama dadi dadi dashi sai kuma labarin rasuwam shi ya girshe mu.
Badon nakai zuciya nesa ba da sai nayi shari,a da kanin mahaifin su don a ranan sun samu matsala dashi don Abubakar yazo mai da maganan filin su na mahaifin su daya rage mutumin nan ya murje ido yai mai rashin mutunci har gida a gabana ya furta mai sai ya gani gobe bai kara tuntuban zancen filin su.
A ranan mahaifinki bai kwana duniya ba Aruwa innalillahi nace a fili tare da fadin manjo dama su baffa suna da yan uwane a Azare ?
Murmushin takaici tayi tare da fadin ras kuwa Aruwa ba ko adadi amma duk sun share mu sun fita batun mu nima hakan yasa na share kowa daga mazan har matan su kuwa.
Babban takaicina shine baffan ki Amadu yanzu tun lokacin da yazo min da zancen auren lami ban so abin nan ba don ba gidan kwarai lami ta fito ba.
Abinda nake gudu ga auren lami shine ya faru don sanin halin baffan ki ba mai yawan son magana bane.
Wanan tabarbarewan yaran Amadu yana ci mun rai sosai a ruwa ace yara babu daya na gari da zai zama mutum yau a dube shi har shima ya duba nasa iyayyen .
Yau naji dadi a yadda na ganki kin koma din nan ina godiya ga Allah da bai kashe ni ba har naga ingantar rayuwan ki A ruwa ta sanadiyar mahaifiyar ki mutumiyar kirki mai sanin ya kamata wace bata manta alheri.
Kasake nayi ina sauraren ta na kasa furta komai a gare ta sai kallon tausayi nakewa kakan nawa lokacin don ba abu mai sauki bane ace yau ka wayi gari ka tsunci kanka cikin wanan halin da manjo ke cikin sa.
Jin shirun danayi ta dauka ko barci nakeyi tace ko zaki je gidan su Atika ki kwana can ne kinga ninan sai a hankali wurin nawa.
Da sauri na girgiza mata kai tare da fadin manjo kema kika iya zama nan ni mai zaisa ba zan iyaba ba wurin su Atika nazo ba gunki nazo don haka ko wani hali kike a nan zan zauna.
Tace to ki hau wanan kayan ki kwanta ni sai i kwanta nan inda nake sallah ko nace tare dai zamu kwanta dake manjo ki gama cin abincin ki sai in gyara wurin idan kin tashi.
Tace nagama ke nan don naman ya fita min rai ko ai naci rabona ubangiji ya saka maku da alheri dama rabona da nama tun a gidan kawin ki da mukaje kano din nan banci nama haka ba sai yau din nan ta sanadiyar ki.
Nace naki nefa manjo dan ke na sayo shi haka kici sai kin koshi in kai masu sauran waje.
Da sauri manjo tace ba zaki basu ba wa yan nan marasa tausayin da rashin imani a ruwa mutanen nan barsu nan inda kika gansu har yanzu halin nasu yana nan basu canza ba kamar yadda kika san su.
Dazu ma ai bayan fitan ki saida naciwa lami mutunci a kanki gidan nan wai kilama sun dawo dake ne kin ishe su a can.
Nace ta taba ganin inda uwa taki dan dan ta to ba dawowa dake akayi ba kinzo ne ki gane mu ki koma.
Mutane ba abinda suka aje a ransu sai bakin sheri da gulman tsiya du kuma tsuliyan su tab da kashi.
Wan yar gurin lami har ciki tayo na banza ban san ya sukayi suka barar dashi ba a gidan nan bayan ciki ya girma kowa ya gama gani ta dashi a gari.
Tasha wahala kamar zata mutu Allah dai yayi da sauran shan ruwan ta bayan taji sauki sai gashi kuma ta koma harkan banzan yanzu ai baki ga tun shigowan ki garin nan bata gidan nan ba.
Wani irin ba dadi naji har cikin raina dan dan uwanka dai dan uwankane ko yaya wani abu mara kyau ya samay shi dole kaji daci.
Mikewa nayi ina daukan ledan naman zan fita manjo tace ina kuma zaki dashi nace su umma saude zankaiwa kada ya lalace tace ban abina nan gobe ke dumama min inci ko ki muna miyan shi.
Manjo ki bari a basu don Allah goben sai a sayo maki maikyau in maki miya da akwai kudi sosai a wurina ai.
Ba dan taso ba haka ta kyale ni na fita tana mita kansu naje kofan dakin najiyo muryan saratu din ta dawo tana fadin a ruwa fa mama saude.
Tace ita kuwa saratu girman dan mutum baida wuya wallahi kinga yadda yarinya ta goge ta zama wata yar birni da ita haka ?
Tayi kyau kamar a waje take zaune ba a cikin kasan nan ba ni canzawa yarinyar ya ban mamaki sosai.
Umma lami tace kai saude tun dazun fa kike dada yarinyar nan wa yasan tsiyan da take shukawa a can.
Sallama na yasa su dakatawa da maganan na shigo falon sai wani warin da gahi ya doki hanci na nace ina mikawa mama saude leda ga wanan manjo na sayowa ta kasa ci kada ya lalace.
Da sauri ta karba tana fafin a, a kuma dai babba yanzu sai a hankali muryan saratu ne ke fadin wai a ruwa kece nan da gaske ?
Murmushi nayi nace nice anty saratu mun samay ku lafiya ai tun dazun nake tambayan ki akace bakya nan.
Ina kokarin juyawa tace don Allah tsaya in kara ganin ki wai kece a ruwa haka ?
Murmushi nayi tare da fadin anty saratu bari da safe ma hade zan gyarawa manjo wurun kwanci ne.
Ina fita naji mama na fadin may ye a cikin wanan leda din ta bude tace may nama ne mai tarin yawa fa.
Ai gaba daya sukayo ruuu wa nan nan aka fara gardaman yadda zasu raba ba tare da saura diyan sun gani ba daga ciki anty kubuta tace ina jinku wallahi a rabashi kowa ya samu ehee.
Tare muka kwanta da manjo saman katifan nata na ragga sai dai nayi dabaran gyara wuri ta bakin katifan idan tayi barci in sulale in koma sama hakan akayi.
Don ina jin tayi barci na dawo kasa ina ta tunanen labatin da manjo ta bani yau wanda ban taba sanin shi ba.
Washe gari kiran sallah masalacin unguwar ne ya tayar damu tunda nayi sallah na zauna ina karatun kur,ani na wajen do yanzu na sauka sai dai tulawan da nakeyi din.
Sai da rana ya dan haska na mike na fito gidan babu motsin kowa don ba zance sun tashi suyi sallah ba ma lokacin daga dakin manjo na fara na share ko ina.
Sai na fito tsakar gidan shima na gyara ko ina jin motsina yasa mama saude fitowa tana fadin fatu har kin tashi a raina nace ni yasu nikan naci suna kala kala a duniya.
Amma a fili dan dariyan yake na sakar mata tare da rusunnawa ina gaida ita da kwana ta amsa a washe tana fadin baki gaji da gajiyan hanya ba kika hau aiki da wanan safiyan haka ?
Mama wurin ne yai min ba dadin gani shine nake gyarawa na bata amsa tace kin san gidan namu ne ai sai a hankali.
Bayan na gama na shiga hura wuta ruwa wanka na fara kaiwa manjo kafin in dawo na dora na shayi don nayi niyar yau a gidan sai kowa yasan nazo garin.
Bayan na dora na fita na sayo bread mai yawa leda biyu yadda zai ishi kowa da kayan tea ban samu a shagon isah ba kamar yadda nayi tunane sai dana dan taka zuwa gaba na samo abinda nake son saya.
Na dawo na samu manjo ta fito ina shiga take tambayana ina naje nace na sayo abin karyawa ne waje.
Tace da kin bar naman jiya da bamu karya dashi din ba dariya nayi mata nace manjo kefa kikace ya isheki naba masu ci yanzun kuma zancen naman bai fita ranki ba har yanzu ?.
Ba kunya ranan har fada suke wurin rabon bread din dana kai masu da ruwan shayin dana hada mai yawa kowa yasha.
Na dawo na zauna na mulke jikin manjo da mai tun tana fadan hakan har ta kyale ni nace ko may yasa ku tsufin nan baku son mai haka nake fama da Amma idan tafito wanka sai na mulke ta da mai itama .
Sai lokacin na tuna da zancen tsaraban da Amma ta ban in kawowa manjo mikewa nayi na dauko da kyat ina mamakjn may ye a cikin kayan haka mai nauyi ajewa nayi gabanta ina fadin wanan sako ne daga Amma tace a kawo maki.
Kallon kayan tayi kafin tace ikon Allah wanan duk may ye a cikin sa haka ?
Ban sani ba na bata amsa tare da fadin ga dai abin da nauyi sosai tace bude muga abin arziki nikan wa yan nan mutane suna kashe ni da farin ciki a duniya.
Bayan na bude na fara zaro kayan a hankali abune a cikin leda baka an nade sai wani buhu wanda na bude semo ne ciki irin na leda leda din nan su tumatur da galon din mai sai shimkafa irin wanda diyanta ke kawo mata ko wani lokaci bata ci sai mama hadiye da yaran ta ke amfani dashi.
Shine ta bayar a kawo wa manjo din yanzu ikon Allah wanan matar ta kashe ni da kunya na zauna ina bude ledan turmin zani ne a ciki guda biyu suma dai irin da ake bata din nan ne kyauta ta hadowa manjo dasu.
Naja kayan gefe na dauko nawa tsaraban na fara fitarwa ina nuna mata harda abinda ban sani ba mamu ta hado min irin sabulu dasu omo clean man shafi masu yawa don rabo.
Manjo tace yar nan wanan uban tsaraban haka mai yawa mutanen nan basu gajiya haka da dawainiya.
Duniya ke nan baka san inda zakaci arzikin wani ba rabonki yasa muna ci daga tsagon wanan mutumin yanzu a ruwa.
Allah baibar maki mahaifin ki duniya ba gashi ya baki uban goyon da ko mahaifin ki na raye sai hakan gare ki.
Manjo ke nan nace ina zama don bude jakkar da na shako da kaya wanda duk rabi na kyautane a cikin su ga wani ghana most go dana shake daban don ni ko yaushe cikin yi min kaya mamu take shiyasa na iya kwaliya kamar may yanzu.
Duk wanan kayan da kike fitarwa na maynene manjo ta tambaye ni nace bayarwa zanyi amma sai Atika tazo ta zaba ikon Allah yau A ruwa kece mai ba da kaya hakan ga wasu.
Ta kara jijiga kai tana fadin abin Allah wuya gare shi yau ina lami mai maki gori da sallah ta fito taga ikon Allah tunda farar safiyan nan haka ?
Nace kai haba manjo ki barsu kawai Allah yafi su akaina ko yanzu ai hakan dadin kine manjo koba haka ba na fadi ina kallonta don kawai in hanata wani katobara don nasan abu nacin ran tsohuwar sosai.
Atika ta shigo na baje mata kayan ta zabi wanda ranta yake so a ciki don ba zan manta halarcin su a gare ni ba ni da kaina na tayata zabe na kwashi kayan nakai wasu kubura sauran.
Ban samay su wurin ba sai na bawa mama saude dake aiki kamar jaka a tsakar gidan ita kadai na basu nasu tsaraban danazo masu dashi.
Fita mukayi da Atika zuwa gidan su acan na aika akayo mun chafane na dawo na hadawa manjo abinci mairai da lafiya har da ganye na hada mata.
Naba kowa na gidan rana har da godiya akai min hakan da umma lami taga inayi sai hassada ya shiga cikin zuciyar ta da yamma sai gata ta yafa wai zata unguwa.
Ta dan jima da fita na sharo dakinn na fito ina share waje mama saude ta dan fita ta leka waje sai gata ta dawo naji tace nikan fatu ina son yin wata magana dake idan zaki rufani.
Da sauri nace mama may ke faruwa ne kuma tace tau zan dai fada maki gaskiya kiyi hankali da yaya a gidan nan don ta fito fili ta fadi tana bakin ciki dake fatu.
Yanzu ma wanan fitan nasan wani sheri za,a tafi kulla maki don ki aka fita tace sai ta danbalaki kin koma kowa na kyamarki duniya.
Innalillahi nace tare da fadin may nayi mata mama saude na fada cikin tsshin hankali tayi saurin fadin rufa min asiti fatu kada babba taji zancen nan don Allah.
Kin san idan baba taji yau akwai tashin hankali a gidan nan sai a dauke ni munafaka kuma.
Nayi maki alkawarin fada maki duk wani mugun nufin da yaya ke yi a kanki ko ba yau ba don har nima bata barni ba.
Yanzu dai don ki yarda dani har in indan ta amsa wani sheri zakiga ta baki abin dadi tace wake kawai ta dafawa shi kada ki yarda kici wanan abin idan ma son samu ne kawai ki kiyayyeta ki saka mata ido na kwana biyu ki fahinci komai a kanta.
Nace mama na gode tace don Allah kada ki bari babba taji wanan zancen din ba zata iya rikeshi a ranta ba.
Naji mama na gode nace na juya na tafi zuciyata cike da fargaba zancen sai tunanen abinda naiwa umma lami nake a raina sai dai na rasa kamo amsa.
16/11/2021, 23:11 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM