SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Haba yar uwa mayye ribanki cikin daukan alhaki ki saida imanin ki don kawai ki gyawa wasu rai bada abinda zan hada ki dashi sai daran Allah dana Annabin rahama sai darajan iyayyen ki.
Uhumm wai duk baki dubaba saboda son zuciya da da hassada kin gwammace mu abiki hakki gobe kiyama baki san ko kwayan zarra sai an futarwa mutum hakkinsa ba kina ganin kamar a nan duniya zamu tabbata ne.
To ki sani yanzu Allah baiba mutum bashi tun duniya zaka girbi abinka wallahi na biki hakki dake da kika fitar da wanda kika turawa ya yada Allah ya bi mu hakkina.
Ranan dai idan nace nayi barcin kirki a gidan nan karya nayi maku don tunane ya cika min zuciya na da firgice saboda na rasa gane mai nayiwa umma lami har take son ta illantani duniya.
Washe gari kamar kullu ina tashi bayan na idar da sallah karatun kur,ani nayi sai da gari ya haska na mike dan gyara wuri da wuri nayi ma manjo abinci nace unguwa zamu da Atika don haka nai mata abincin da zai isheta har wani lokaci.
Bayan na gama ne na dibar masu nasu kashi biyu na mikawa kowa nasa hikimar yin hankan gare ni umma lami ne da yaranta zasu cinye su kadai.
Ruwa na debo a bakin famfo na surka na shiga wanka na dade a zaune ina shiri duk da ba kwaliya nake yi ba amma ranan na bata lokaci ina kwalliya.
Wani yello less na saka a jikina mai dan flawer da zare bulle a jikin shi sai duwatsun dake shana shi idan ka gitta.
Takalama da jakka blue na dauka sai dan oud dana shafe jikina ya dauki kamshi don mamu ta saba min da shafa turare mai mai na arab a jikina ko tufafina banda hammata da chest dina kawai ban shafawa don gujewa cancer.
Manjo na tambaya ko tana son wani abu sai cewa tayi bana son komai yar nan dan dama wanan lemon kwalban mai sanyi.
Murmushi nayi ina fadin wann bakin dai naki manjo na gane kwadai yake so a cikin sa fita nayi zuwa waje inda shago yake na sayo mata multina da fanta guda hudu na kawo mata .
Yayin da idanuwan su kubara dake kwaliya a kofan shiga wurin su yayo caaa a kaina har saida na tsargu da kalln da suke min din.
Ban dade da manjo nayi mata sallama bayan na aje mata komai a kusa da zata bukata a wuni hatta ruwan sha na sayo mata mai sanyi nayi mata dibara sakawa a wani tsohon kulan dake dakin tana fadin kin ga maganin ajiyan tsofi gwaggon duk zuwa sai ta min korafin in yarda shi naki.
Ina fitowa duk suna waje nasan gulmana wa yanda ke waje suka kai harda umma sai da nagani a wurin na taka kamar tarwada zuwa wurin su tun kan inyi magana mama saude tace yau kan yar gidan babba ina za a haka da wannan kwaliyar ?
Muushi nayi ina fadin zamu nan gidan samirace yar ajin mu da tai aure na juya ina fadin umma zamu ziyar ne yau zan tafi.
Ba zaki dade ba ke nan ko ta tambaye ni cikin kallon fuskana kada plan din ta ya baci nasan nace zuwa sha daya insha Allahu zamu dawo.
Tace to a dawo lafiya ina bada baya taja tsuki tana fadin sai na kasaraki ai yanda ko kare bai sunsun naki don bakin jini mu za,a kawowa barkado a gida ?
Ke a dole uwarki ta fifitaki akan yayan mu wallahi karya ne baku isa ba daga ke har uwartaki da kike kuri da ita.
Haba umma ni ban son irin haka wallahi fatima fa yar uwan mu ne umma idan kin kasarata ai mun kara yawa ke nan muku a gida ?
Kubura wallahi ki fita min a idona tun ban saba maki ba wawiya daba tasan inda ke mata ciwo ba kinfi bukatan ta dinga kwaso tsumakara tana kawo maku kwance kuna jin dadi sakawa ba ku hakan zaima ku dadi ko hakazaifi maku dadi ?
Nidai don Allah da kin barta har sau nawa fati kr zuwa garin nan da zamu ganta harara ta watsa wa yar nata sai ta kasa karasa maganan don kallon da uwar tai mata.
Hjy jummai tayi mamakin ganin yayan nata data gani kamar daga sama washe gari ne suna zaune Umar ya shigo falon kamar an jefo masu shi sai mamakin ta ya karu sosai.
Abinci aka gabatar mai bayan yan gaishe gaishe tana fadin ku lafiya wanan tafiyan haka babu sanarwa zuwa ai maku tanadi.
Daddy bai fada maki komai bane mama Aliyu ke tambayanta hakan cikin tsure ta da idanuwan shi.
Alh kuma ni bai ce min komai ba ta fada slowly a cikin muryan mamaki da tunane a ranta.
Ko ma dai mainene ai zai fada muna tunda ya kiramu kuma gamu munzo inji habbib ya fada a miskile shiko umar baiko ta kansu don ko abin karyawan da aka aje mai bai taba ba.
Kodai wani abinne ya taso yake neman mu hakan cikin zolaya Aliyu yace zancen auren ku ba kila wani kallo habbib ya watsa mai tare da fadin kainan daban ne idan ma auren ne ?
Wani aure kuma hjy tace tana mere bakin ta tace aure kai ai yabi ruwa kowa yaje gaba ya neme nasa badai diyana da wanan gamin gambizan ba.
Mama ni fa har yau ban ko san yarinyar da daddy ya lika min ba don koda yace inje mu gana wani zuwa danayi banje ba har na wuce.
Ai gara ma yar wurin bros wancan zuwa naga ta girma sosai tayi clean gaba daya lokaci guda kodan ban ganta da katon hijjab din nan bane oho ?
Umar ya dago kai daga abinda yake a cikjn waya ya watsa mai wani kallo ya kama dariyan mumuke .
Yace Allah bros da abin mai yuyuwa ne akwai iri mai kyau fa gurin don ko ina zaka shiga da ita nan gaba.
Kai karabani da zancen haushi a gabana habbib ke wanan irin magana ko da itace autar mata ba zata taba shigowa ahali na ba mudfin ina raye.
Kyau dan maciji ko kunama may ake da irin da ko asalin su basu gama sani ba maimuna fa har yau bata san uwar ta ba a duniya.
Kai wai mama da gaske ne wanan zancen ni tun tasowana nake jin ana wanan maganan fa ashe gaskiya ne ?
Yo ina tasan ta dama irin yan cin ranin nan ne ai ubanta ya gani ya aura da iyayyen ta zasu koma kasar suna sudan suka matsa saida ya sakae masu ya suka tafi da abinsu har yau basu kara waiwayan ta ba.
Shegiya dama ta tafi da wanan annoban amma hajiya ta hana a wanan lokacin dole ta tafi tabar yar a nan ashe annoba zata zomowa mutane nan gaba.
Umar ya dago kai ya kalleta don jin zagin da ta aikawa mamu din tace na zagi kanwar uwar ka ko miskilin banza.
Maimunan nan kamar tayi ma wani asiri a kanta tun kuna yara nake rabaka da ita kuna leke da juna.
Dan murmyshi yayi yace kai mama zagin dai ne ba dadi maimuna kuma tare muka taso a gidan nan muna yara shine shakuwana da ita ba wani abu ba.
Koma dai may na hana wana hurdan a tsakanin kai baka ko kishina da alama mai kina kake shigewa jiki.
Shidai bai daga kai ya kalleta ba sai dakilan wayan hannun sa yakeyi can dai ya mike ta kalle shi tana fadin ina kuma zaka yanzu.
Zan leka Amma ne a wurin ta nasan yanzu tasan nazo don akwai yarinyar data ganni gidan nan nasan zata fada mata nazo.
Ko dai yar tsanarkace ta ganta hjy ta kalle shi tana tsuki tace wanan yar banzan yarinyar bana wai ta tafi garin su ganin gida nima jiya maryam ke fada min tafiyan su.
Shidai yasa kai ya fita ya barsu a gurin yana ficewa tace wata kila wani abin ne ya bata mashi rai da zuwan shi haka ?
Yana tunane iyalin shi daya barone ba shiri kila don kiran gagawan da akai mai ba shiri yazo.
Arniyar matar nan zan waiwayeta don har yanzu bata kwanta min a raiba na tsani ganin ta a rayuwana.
Babu wanda ke son ta a gidan nan idan ka dibe shi daya kwasota gidan nan kaf in maka na mahaukaci kyamarta suke.
Ba wani abin kyama halin merry dai na rashin son yayi hurda da yan uwanshi shine matsala ranan fa munje gidan ta hana muna ruwa common ruwan sha fa mama.
Ta gyara zama tana fadin ita din da kanta lale arniyar nan ta samu guri da yawa zafin ran babawo na banza ne.
Shiyasa nake kara kyamatan wanan bakin hadin da Alh ke son yi maku don maimuna na iya kwace min da da kilibibin nan nata.
Shiru sukayi suna sauraren ta ba tare da sun furata komai ba ga kalaman ta da takeyi akan maimuna din.
Sallama yayi kofan falon tace lale marhabin da mutanen turai sadauki kaine yau ka leko mu kasan nan ai ka kyauta duk da dai kadade baka zo din ba ko yar nan da aka haifama bamu santa ba.
Zaku santa Amma idan sunzo don zuwan merry kasan nan ba yanzu ba don yarta sai kila idan ta girma zamu shigo dasu wani lokacin yana zama yake wana magana wa Amma din da take tambayan shi.
Sadauki irin dadewan nan haka ba a leko gida ba baida dadi wallahi an san aiki yana yawa amma mutum ya share gida har wani lokaci.
Ai hakkuri Amma nima hakan bada son raina nake dadewa ba don aikina ne da yaimin yawa ko wani lokaci.
Ina mai dakin naka take da yarta ina suna lafiya ya kuma jama,an wurin naku suke ?
Dan bata rai yayi yana fadin suna lafiya Amma baki san dalilin kiran mu da daddy yayi ba haka a cikin gagawa ?
Shiya kiraku kasa nan ashe tayi mai tambayan malam bahaushe mai ban haushi.
Mayar da kanshi yayi saman kujeran da yake zaune a kai ba tare daya iya bata amsa ba ga nata tambayan.
Itace tace wata kila dai akan wani maganan siri ne ya aika kuzo haka sai dai ni bai sanar dani komai ba gaskiya.
Shidai baiyi magana ba sai faman tunane yakeyi a ranshi ko dai maganan mama gaskiya ne idan haka ne mai zaisa daddy ya lakantani da zancen dukiyan shi bayan yasan ina da nikin baninkin din su a hannu na koma dai may nene zamu ji ai yace.